Showing 21001 words to 24000 words out of 29040 words

Chapter 8 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt

yake, Saif ne yace abokina yaude ka kwantar da hankalinka na gano maka gidansu Sumayya, saurin kallonshi Nabeel yayi tare da sakin murmushi yana fadin dagaske kake? Saif yace wallahi da gaske nakeyi.


A cikin abokanmu akwai wanda nasa ya dubo mani gidansu, Nabeel yace tashi mutafi yanzu dan Allah, Saif yace haba de, kabari seda dare ai zefi amma yanzu kawai semuje fira ido naganin ido. Nabeel yace shikenan nagode.


Tsaye suke a jikin motar Nabeel sun sha manyan kaya sosai sukayi kyau bakamar Nabeel, domin baya sasu daga juma'a se juma'a, su biyu kadai sukaje shida Saif. Yaron da suka aika ne yafito yana fadin ance gata nan zuwa, kudi Nabeel yaciro yabashi.


Tadan dade kafin ta fito, akofar gidansu ta tsaya tana jiransu su karaso domin Babanta ya hanata barin kofar dakalin gidansu idan zatayi fira, ganin bata karaso ba yasa Saif yace abokina muje kasan mata da sarauta, takawa sukayi suka matsa inda take.


Da sallama suka isa, Sumayya kanta na kasa ta amsa tare da gaishesu. Nabeel se murmushi yake, Saif ne yace Malama Sumayya kiyi hakuri bakisan da zuwan mu ba gashi mun fiddoki. Murmushi tayi tace ai bakomai.


Saif yace nasan kila baki gane mu ba kodan duhu ne yasa hakan. Ni sunana Saifullahi, wannan abokina ne sunanshi Nabeel, kuma muna karatu a makarantar da kike asalima course dinmu daya.


Saurin dago kai Sumayya tayi domin tasan sunan Nabeel a wajen yan course dinsu, kasancewar akwai hasken wuta yasa ta iya ganin fuskarshi dauke da murmushi. Tsayawa tayi tana kallonshi, fuskarta dauke da mamaki, jitake kamar mafarki takeyi.


Tafi Saif yayi ganin yanda suke kallon junansu, saurin kawar da kanta tayi cike da kunya, Saif yace nasan yanzu kin gane mu ko? Daga kai tayi tana murmushi. Saif yace to Sumayya gamu munzo gareki, duk da bamusan ya zaki karbe mu ba.


Abokina tun ranar daya fara ganinki sonki yashiga zuciyarshi, munso muyi maki magana se mukayi tunanin kada mu hanaki karatu, shiyasa yanzu da aka gama mukace bara muzo, ina fatan bamuyi shishshigi ba?


Dukar da kanta tayi tana murmushi, jitake kamar a mafarki wai Nabeel ne yake sonta? Lallai tayarda mahakurci mawa daci, wasa ta cigaba dayi da hannunta batace komai ba.


Saif yace Sumayya nasan zakiyi tunanin yanayinki da namu ba daya bane,to kada wannan ya dameki, domin ni nasan abokina betaba ganin wata mace ya rude sama da ke ba, ke ko abinci sena matsa mashi yakeci, so dan Allah kada ki watsa mana kasa.


Sumayya tace to nagode da zuwanku, amma Saifullahi kana ganin yanayin Nabeel da ni yadace kuwa? Kalli fa yanda gidanmu yake, kana tunanin banyi zari ba idan nace zan amince da soyayyarshi?


Gyara tsayuwa Nabeel yayi tare da shagwabe fuska yace haba Sumayya, meye wani abun fadar haka? Kinsan ma wani abu? Abbana yace ze nema mani aurenki matukar muka gama 100 lvl, kuma Ummana ma tana sonki to meyasa zaki fadi haka.


Dariya suka sa mashi ganin yanda yayi da fuska yana koro bayani. Dafashi Saif yayi yace ina ruwan dan Abba da Umma, kai kuma waya fada maka anama budurwa shagwaba? Ai itace yakamata ace tana maka shagwaba.


Duka Nabeel ya kaimashi yana murmushi, yace ai gaskiya nafada ko Sumy ta? Murmushi tayi tana kallonshi. Saif yace da alama de munsamu karbuwa, wannan fara'a haka. Nabeel yace yauwa Saif kamanta baka fada mata ba.


Kallonshi sukayi, yace Sumy Allah yasa baki kula kowa? Kinsan fa ina da kishi, kuma ni banaso arika hadani da wani. Dariya suka kara samashi, Saif yace to tajika, kaga dare yanayi kada ayi mata fada agida yakamata mutafi.


Juyawa Nabeel yayi yaje yadauko wata leda acikin mota, kayan zaki ne kawai aciki, yana zuwa yace Sumyta ga sweet nasiyo maki, karba tayi tana murmushi tace nagode. Hannu yamika yana fadin muga wayarki in samaki number ta.


Mika mashi tayi, bayan yasa mata yace gashinan nasamaki My King, zaro ido tayi tana kallonshi, gira yadaga mata yana fadin ko beyi ba? Idan beyi ba ki canza to. Ni kuma nasa maki Sweet Sumy.


Karar wayarta ne ya katse mashi maganar da yakeyi, saurin kallonta yayi yana jira yaji waye, kin daukar wayar tayi, Nabeel yace waye ne? Murmushi tayi tace yaya Naseer ne. To meyasa baki dauka ba? Kawai nasan idan yafara mani fira seya dade shiyasa nabari idan nakoma gida se muyi waya.


Saif yace babanku daya dashi ne? Girgiza kai tayi tana fadin class capting din mu nefa. Saif yace ok wannan ustazin zakice mani, na ganeshi. Nabeel yace saurayinki ne ko? Tace a'a kawai muna mutunci dashi shine guardian dina.


Nabeel yace ai kuwa wallahi daga yau kun rabu, daga yanzu nine komai naki, yanda yayi maganar fuskarshi adaure yabasu mamaki, zatayi magana kenan Nabeel yace Sumy kishiga gida kada Baba yayi maki fada.


Murmushi tayi tana fadin nagode, haka suka tafi Nabeel yana me cike da farin ciki. Sumayya kuwa tana shiga ciki Babanta yafara tambayarta waye, nan tayi mashi bayaninshi da abinda yace.


Wani murmushi Mamanta tasaki tana fadin toshidin dan gidan waye? Sumayya tace naji de ana fadin dan gidan Lamido Saraki ne, washe baki Mamarta tayi jin abinda tafada. Amma ganin Babanta ya daure fuska yasa tayi saurin boye murnarta.


Kallon Sumayya yayi yace kinajina? Inaso daga yau kicire tunanin kara tsayawa da wannan yaron, domin kwata kwata ba sa'anki bane, kilama kin girmeshi, sannan kuma ni bazan taba daukar diya ta in bama wannan yaron ba.


Tabbas nasan mahaifinshi mutumin kirkine, amma mutane suna jita jitan ba'asan asalin Uwarshi ba, kanwarta da sukazo garin nan tare bata da aiki se bin maza, yanzu ma naji ance har mata take bi, kuma asalinsu yan tasha ne, domin akasuwa suke saida abinci.


Mamanta tace malan kai waya fada maka haka? Murmushi yayi yace kada kimanta nidin meshiga cikin mutane ne, kuma sanin labarin masu kudi ba abu bane me wahala, domin basuda wani sirri komai nasu abude yake dasu da yan siyasa.


Waye besan yaronshi mane min mata bane? Saboda haka komin kyan halin mahaifinshi ni bazan iya amincewa da tarayyarku ba, barema har kizo kifada mani wai mahaifinshi zezo nema mashi aurenki.


To bara kiji Sumayya, yanda na saida gonar gadota na hakura da ita dan kiyi karatu, haka babu wanda ya isa yasa nayi maki aure batare da kingama karatunki ba. Dan haka kicire tunanin yin aure azuciyarki harsekin gama makaranta.


Mamanta tace haba malan ya zakace haka, yanzu fa ba zamanin da bane, yanzu rayuwar tacanza, kana ganin kananan yarama aure ake masu, amma yazakace seta gama shekara 4 kafin kayi mata aure, idan kuma takasa daukar wannan hukuncin naka fa?


Hannu yadaga mata yana fadin ya isa Zainab, banaso kiyima diyata mugun baki, ni nasan irin tarbiyar dana bama diyata, kuma nasan bazata taba aikata wani mugun abu ba, dan haka kisani wannan yaron da kuke karatu Naseer shi kadai nayarda kucigaba da alaka dashi, daga yau na hanaki fita fira da kowa, idan Naseer ne yazo ku gaisa yashigo zaure.


Domin nasan dan gidan mutunci ne, kuma nasan yana temakonki akan karatunki, daga bashi ba banaso inkara ganin kowa a kofar gidan nan. Tashi kitafi. Haka tashiga daki cike da bakin cikin abinda Babanta yake mata.


Tadade tana jin haushin irin takurar da yake mata, duk da yanda yasata saka hijabi amakaranta hakan be hanata samun saurayi dan gayu ba, gashi kuma yanzu yana so ya rabata dashi, saman katifar ta tafada.


Wayar tace tafara kara tana dubawa taga my king, murmushi tasaki tare da gyara kwanciya tadauka, sun dade suna firar soyayya ita da Nabeel, cikin lokaci kankani yakara saye zuciyarta da muryarshi medadi da kalamanshi masu cike da shagwaba.


Seda suka dauki kusan awa 1 da rabi suna fira kafin sukayi sallama, rungume pillow din ta tayi tana jin son Nabeel yana kara shigarta, hakika tasamu irin saurayin datake so, koba komai itama zata fara fasowa a cikin makarantarsu, domin duk wanda zeganta da Nabeel dole yakara ganin girmanta.


A hankali tace Baba sede kayi hakuri, domin son Nabeel yadade azuciyata tun kafin ya furta mani. Tabbas zan san yanda zamurika kasancewa atare batare da Baba yasani ba. Juyi tayi tare da kara rungume pillow dinta.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻

Nah
Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)


www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey


Part 45 ⏩ 50


JINJINA GA DUKKANIN MASOYANA, INA MIKA SAKON GAISUWA ZUWA GAREKU, NAGODE DA ADDU'ARKU AGARENI ALLAH YABAR ZUMUNCI😘😘😘😘


Tun daga wannan rana Nabeel da Sumy suka kulle, soyayyar gaskiya sukema junansu, acikin kwana biyu kadai amma jisuke kamar sunyi shekara da fara soyayya,duk yanda Nabeel yaso yazo gidansu Sumy ta hanashi.


Daya gaji ya tambayeta dalili, setace Babanta ne ya hanata fita fira yace se tagama karatu, Nabeel yace amma baki fada mashi labarina ba? Tace se jiya nafada mashi shine yace to inbari sena gama second semister sannan mufara fira.


Shiru Nabeel yayi can yace amma Sweet kinsan bazan iya hakurin rashin ganinki har mu koma makaranta ba ko? Jinjina kai tayi kamar yana ganinta tace wallahi nima my king bazan iya hakurin rashin ganinka ba.


Nabeel yace kinga dole ki samo mana mafita, Sumy tace shikenan ai Ummana nasan zata kareni, anjima zance mata zani gidan kawata da yamma, zanje bakin gate din makarantarmu seka sameni acan. Kiss yayi mata ta waya yana fadin nagode sosai, lallai yau zamusha fira.


Babaye ne suka fito shida wata yarinya me tallar gyada, a kalla bazata wuce shekara 17 ba, se washe baki yake haka suka fito daga bangarenshi, suka nufo hanyar gate. Ada ce tafito zataje kiran da Umman Nabeel take mata,domin tunda Nabeel yagama yayinta yadena kulata, sede idan yazo bacci yana bukatar ta sannan yake kiranta su kwana tare, shiyasa yanzu yake mata wahalar gani, sede taje tayi mashi aiki kawai.


Tsayawa tayi tana kallon yanda Babaye yake kamo hannun metallar suna ta dariya, tsaki taja tana fadin wannan tsoho dashi amma besan ya girma ba, yarika neman diyar cikinshi. Allah yasa wata rana Alhaji yaganka.


Wucesu tayi tashiga part din Umma, dede sun kai bakin gate yaji karar horn din Abba, a kidime ya ruga sam yamanta da yarinyar, bayan ya bude mashi yashigo yarinyar ta nufi gate tana ta sauri, bayan yafito yanufi Babaye da gaba daya hankalinshi atashe yake.


Bayan sun gaisa Abba yace Babaye wannan yarinyar fa daga ina? Hannu yadora a kai yana sosawa yace wallahi me tallar gyadar datake kawo mani ce, to yau tazo bakin gate bata ganni ba shine tashigo, to nima nafito daga daki naganta tsaye abakin dakin gate shine nazo nasiya.


Kallon tuhuma Abba yayi mashi yace, ammade kafada mata kada takara shigowa wajen dakin ka, kasan sharrin zuciya, kuma mutanan gidan zasu iya zargin wani abu. Babaye yace haka ne, ai bata taba shigowa bama, kawaide dan taga nasaba siye shiyasa da bata ganni ba tashigo. Abba yace Allah ya kyauta ya shige ciki.


Yana shiga ciki yaji beji motsin Umman Nabeel ba, hakan yasa ya nufi bangarenta, ita kuma alokacin suna can wata yarinyar ta tazo suna shirin fara aikata masha'arsu, se yarinyar tace tana jin kishi, Umma tayi murmsuhi tace to bara na kawo maki ruwa, kiyi hakuri na manta ban kawo maki komai ba, wallahi duk kingama rudani ne da wannan kwalliyar taki.


Haka tafito jikinta daga ita se towel, tana fitowa dakinta taci karo da Abba, saurin ja baya tayi cike da firgici, har seda towel dinta yakusa faduwa, saurin kamoshi tayi, shima Abba yayi saurin zuwa kusa da ita ya rikota.


Idanuwanta a waje take kallonshi, janta yayi ganin a firgice take suka nufi dakinta. Saurin ja dabaya tayi tana kokarin seta kanta tace wallahi kabani tsoro, wanka fa zanshiga naji inason insha ruwa shine nafito kawai sena ganka. Murmushi yayi yace ai naga alama, muje dakin se inkawo maki ruwan kinga nima se ayi wankan dani.


Saurin kamo hannunshi tayi tana fadin muje kawai insha da kaina, kallonta yayi yace towai meyasa bakiso inshiga dakin? Murmushi tayi tace bakomai nasanka idan kashiga hanani wankan zakayi kuma sauri nakeyi domin wata kawata zatazo karabar wasu kaya da Lawisa ta aiko mani.


Murmushi yayi yace to muje kisha ruwan nima mantuwa nayi nazo in dauka, ajiyar zuciya tasaki tana fadin nide nasan ai ba lokacin dawowarka bane yanzu. Bayan ta sallameshi yatafi, seda taga Babaye ya kulle gate sannan tayi saurin komawa tana fadin Allah nagode maka daka rufa mani asiri, daban fito ba yau daya kamani dumu dumu, haka takoma suka cigaba da aikinsu.


Kamar yanda Sumy tashirya haka ta fadama Mamanta, Maman tace to Sumayya kada kidade kinsan halin babanki, Sumayya tace kai Mama, yanzu shikenan ni arayuwata bazan rika fita ba, duk wani jin dadi kina gani Baba ya tauyemunshi kamar wanda beyarda dani ba. Tsaki Mamar taja tana fadin nima narasa wannan bakin hali irin na malan.


Kina ganin yanda 'yar gidan Laure take tara manyan samari a kofar gidansu,rannan naje gidan bakiga yanda wani saurayinta yakawo mata kaya ba, itama kanta uwar dubu 5 yabata, amma shikenan ni se ya hanaki sauraren kowa.


Idan kyau ne ai kinfita kyau, na tabbata dakina fita samarin dazaki samu se sunfi nata yawa, dan haka ni bazan hanaki fita ba, domin kowace Uwa tanaso taga itama ana kula 'yar ta, ai ba bokon zamu kai maki daki ba, idan kina kula samarin da haka zamu fara tara kudin kayan dakinki. Kitafi idan yazo nasan yanda zan ce mashi. Godiya tayima ta tafita cike da farin cikin samun goyon bayan Mamanta.


Nabeel ne tare da Saif se faman duba agogo yake yana jan tsaki, dariya Saif yayi yace ka kwantar da hankalinka, tunda de tace zatazo zata zone, Nabeel yace kallifa har 4 da rabi da kusa, yaushe tazo har mukayi fira, kuma nasan da taga magriba tayi zatace zata tafi.


Saif yace amma idan tazo kawai kutafi gidanka, domin idan kuka tsaya cikin mota wani ze iya ganinta kaga kada yafadama Babanta. Nabeel yace wannan ustaziyar ce zata yarda, Saif yace tana fa sonka, duk abinda kace mata nasan zata yarda matukar baka nuna mata son da kake mata yafi nata yawa ba.




Kuma kasan halin mata, idan har kanaso soyayyarku tayi karfi to dole se kuna samun exchanging na feelings shine abunda ze kara sa Sumy ta mace a kanka kuma ka tsaya mata a zuciya takasa mantaka. Nabeel yace ina tsoron kada na tabata tacemun dan iska.


Saif yace kanaji ko? Cikin dabara zaka fara taba hijabinta, kanayi kana kallon fuskarta, idan kaga bata canza fuska ba, to kayi kokarin kama hannunta, shima idan bata hanaka ba, to tabbas bazata hanaka komai ba, inaso ayau kasamu kadanyi romancing dinta ina me tabbatar maka bazata iya kwana daya bata ganka ba, daga haka kuma se ka cigaba da buga game kawai, dariya sukasa.


Nabeel yace shikenan, karar wayarshi ce ta katseshi, saurin dauka yayi yana fadin haba sweet haryanzu? Dariya tayi tana fadin ina bakin gate din makaranta, murmushi yayi yace muma gamu nan cikin makarnatar ai, bara mufito.


Suna zuwa Saif ya bude mata baya yana fadin kishiga kada yan sa ido suganki, dariya tayi tashiga, bayan sun bar wajen ta gaishesu, Saif yace haba Sumy yazaki sacema abokina zuciya kuma kirika hanashi ganinki? Dariya tayi tana fadin ai ba laifina bane shima yasani.


Saif yace aikuwa tunda kuna son junanku dole kusamu mafita, kinga yanzu duk inda zakuje dole asamu wasu wadanda suka sanki, shiyasa nace kawai kuje gidanshi kusha firarku acan, kinga babu wanda zesan kuna tare.


Shiru tayi gabanta yana faduwa, Saif yace ya naji kinyi shiru ko bakiyarda da abokina bane? Murmushi tayi tace haba de, shikenan hakan ma zefi, Saif yace yauwa kinga nima budurwata tana can tana jirana agidan semu hadaku zumunci ma, akwai budurwar Najib ma kinga akwai yan uwanki mata acan ma.


Ajiyar zuciya tasaki jin ance akwai mata agidan, Saif yace waini abokina tun dazu ka kosa Sumy tazo amma tazo naga kayi shiru se murmushi kake, Nabeel yace ai kasan idan farin ciki yayima mutum yawa yana kasa magana, dariya sukasa mashi.


Bayan sun isa gidan Saif yafita ya bude masu gate suka shige, haka Sumy tafito kamar tanajin tsoro, a bude suka samu kofar, suna shiga suka iske su Zuby sunata kallo suna dariya, Khairat da Najib suna zaune a kujera daya tana kwance a jikinshi.


Zuby kuwa wasu kana nan kaya ne ajikinta ta bazo gashin doki, tana ganin Saif tayi saurin tashi ta rungumeahi, Sumy kuwa da kallon mamaki tabisu, gabanta se faduwa yake. Daure fuska Nabeel yayi ganin haka yasa kowa yakoma mazauninshi.


Bayan sun zauna Saif yace Zuby, Khairat gafa Sumy yau tazo mana ziyara, murmushi sukayi Zuby ta tashi tadawo kusa da ita tare da kama hannunta tana fadin sannu da zuwa Sumy, hakika labarinki yarigaki sani a wajenmu.


Kin sace zuciyar Nabeel, inafata bazaki kara bari yasha wata wahala ba? Murmsuhi Sumy tayi tace insha Allah, khairat tace sannunki da zuwa, inafatan zaki saki jikinki damu, domin daga yau munzama yan uwa, dadi Sumy taji zata zama kawar yan gayu, tace nagode da karramawarku.


Najib yace sannu da zuwa Sumy, tace yauwa, Najib ko? Dariya suka sa yana fadin nasan Nabeel ze fada maki ai, tashi Zuby tayi tana fadin bara nakawo maki lemu, Saif yace abokina kuje daga ciki kusha firarku kada mu hanaku sakewa ga lokaci yana tafiya gara mu maidata dawuri domin gobe.


Nabeel ya kalli Sumy seya sadda kai, tsoro yake kada yace suje daki tayi mashi wani zargin, murmushi Saif yayi yace Sumy tashi muje in rakaki naga alamar kunyarki yakeji, murmushi tayi ta tashi tabi bayanshi, suna tafiya Najib yace shegen kaya, wai yau kaine ake tayawa kula da mace.


Murmushi Nabeel yayi yana fadin ba dole inji tsoro ba, kasanfa ustaziyace kada tayi saurin ganoni ta rabu dani, dariya sukasa yatashi yashiga daki, Zuby kuma ta kai mata lemu. Saif yace to asha fira lafiya nima zanje inyi tawa firar.


Yana fita Nabeel ya matso kusa da Sumy ya zauna, kallonta kawai yake yana murmushi, hura mashi idonshi tayi tana fadin wannan kallonfa? Murmushi yayi yace nakine mana. Hannu yasa yadauko lemun da aka kawo mata yazuba akofi.


Kallonta yayi yace to bude bakin in baki, dariya tayi tana fadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login