Showing 18001 words to 21000 words out of 29040 words
Chapter 7 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt
sosai.
Kara matsawa kusa da ita yayi yace dan Allah kibar wannan kukan kada kitara mana mutane, kinsan fa haka jami'a ta gada, idan har mutum yazo yana bako dole ya fuskanci kalubale, musamman idan shikadai ne, kuma besan kowa ba.
Duk wadan da kikaga sun saba to suma da haka suka fara, kuma idan kika koma gida shikenan kinjama iyayenki asarar kudin registration din dasuka maki, domin de makaranta bazata maida masu kudinsu ba. Shin ya sunanki ma?
Sumayya, Allah sarki kinga sunan kanwata kenan, ni kuma sunana Naseer, muga wane course suka baki? Mika mashi takardar hannunta tayi tana fadin micro biology suka bani, murmushi yayi yana fadin ai course din mu daya ma.
Wannan course form ne, zamuje kifara kaiwa ayi maki singning seki kwafi time table. Amma wannan badamuwa bane, yanzu muna da class, muje idan muka fito zan rakaki ki kammala komai, se in baki time table domin kisan time din da muke da class.
Murmushi tayi tana fadin nagode yaya, shima murmushi yayi yace bakomai ai duk wanda yatemaki wani shima Allah ze temakeshi. Haka suka jera suka nufi class. Suna shiga aka bisu da kallo, wasu daga cikin maza suka fara fadin kaga class capting yau da wata mace.
Dariya suka sa wani yace ina jide kanwarshi ce,wani yace bawani kanwarshi kila de shima yasamu kawa dama ai duk munafunci ne ustazancin nashi, dariya suka sa, duk abinda suke fada yana jinsu, banza yayi dasu yasamu waje yazauna tare da nunama Sumayya wajen zama.
Haka tazauna ko kanta takasa dagowa domin gaba daya a tsarge take, haka malaminsu yashigo gaba daya class din akayi shiru. Tambayar abinda sukayi jiya yayi, Naseer ne yatashi yabashi amsa.
Haka yacigaba da gabatar da darasi, yana cikinyi ya jefo tambaya, shiru ajin yayi babu wanda ya bada amsa, can malamin yaji an bada amsa a hankali, gaba daya ajin suka fara waigen wadda tayi maganar.
Malamin yace wacece tayi magana? Naseer yace Sumayya ce malam, wacece Sumayya tashi tsaye, ai cikin Sumayya lokaci guda yafara kara, gaba daya jikinta yafara rawa, Naseer yace tashi mana babu abinda ze maki.
Tana tashi kowa yabita da kallo, amma takasa daga idonta ta kalli malamin. Murmushi yayi yace mekikace? A hankali takara maimata abinda tace, malamin yace da kyau, kin bada amsa dede atafa mata. Gaba daya ajin ya dau tafi.
Malamin yace amma ke bakuwa ce ko? Kai tadaga mashi, yace meye sunanki? Sumayya Labaran, yace da kyau, zauna. Nan fa ajin yafara surutai kasa kasa kowa da abinda yake fada. Ana cikin haka su Nabeel suka shigo.
Zubaida da Khairat sun dauki wanka sunyi masifar kyau, suma mazan sun sha wanka, kowa yabisu da kallo, Sumayya kuwa sakin baki tayi tana kallonsu Zuby, sosai suka burgeta, jitake inama ace itace. Bayan sun zauna malam yaci gaba da darasinshi domin yariga yasaba da halin su shiyasa baya ce masu komai idan suka shigo yana ciki. Bayan yagama kowa yafita.
Naseer shiya raka Sumayya har tagama abinda zatayi bayan sun dawo yabata time table ta kwafa, wani guri suka samu suka zauna, kallonta yayi yace lallai kanwata kina da maida hankali, duk da bada ke aka fara wannan course din ba amma gashi har kin fahimceshi, kinga nima zan karu dake kenan.
Murmushi Sumayya tayi tace haba Yaya ai kaine zaka rika nuna mani abinda ba'ayi dani ba,dan naga semister har tayi nisa. Yace haka ne domin next week zamu fara test, Allah yaso kinzo da wuri. Haka suka cigaba da tattaunawa har lokacin shiga wata lecture yayi.
Bayan sunfito sukayi sallar azahar, Naseer yace ma Sumayya suje suci abinci tunda karfe 4 zasu gama lecture, haka suka nufi wajen wata me saida abinci, dadi taji dabe kaita wajen yan gayu ba. Plate biyu yasa aka yimasu yabiya.
Bayan sungama ta fara bude jaka tana tambayarshi nawa ne, murmushi yayi yace kibarshi kawai na biya mana, Sumayya tace anyi haka kuwa? Yace harma anyi, dariya suka sa yace muje mukara duba abinda aka mana kafin lokaci yayi.
Haka suka gama lecture wannan rana Naseer ya rakota har bakin titi seda ta samu abin hawa sukayi musayar number sannan shima yatafi gida, domin shima dan bauchi ne. Sosai Sumayya taji dadin abinda Naseer yayi mata, duk da taso ace tafara haduwa da yan gayu.
Tun daga wanannan ranar Sumayya tafara sakewa da makarantar, kullum suna tare da Naseer sede idan sukayi sallah take tafiya taci abinci dede kudinta domin ta lura idan suna zuwa tare shine zerika biya mata kuma tana jin kunya. Tun yana mata fada akan tadena tafiya ita kadai har ya kyaleta.
Sede idan tagama su hadu wajen dasuke haduwa. Duk shige da ficen su Nabeel akan idanun Sumayya suke yinshi, sosai suke burgeta, wani lokaci setaji kamar tayi masu magana amma seta fasa domin bata ma samun lokacin ganinsu, wani lokacin suna cikin lecture suke fita.
Kuma kafin sutashi sun bar makarantar, haka ta hakura tacire ran zata shiga cikinsu, a haka tafara samun kawaye acikin course dinsu, domin Sumayya akwai kokari duk abinda aka masu dan da nan take daukeshi, kuma ko assignment aka basu lokaci guda takeyinshi, idan bata gane ba Naseer ya nuna mata, shima idan be gane wani abun ba ita take temakonshi.
Sosai shakuwa takara shiga tsakanin Sumayya da Naseer, suna mutunci sosai har gidansu yana zuwa, wasu da yawa suna tunanin soyayya sukeyi. A haka har suka yi mid semister test, kuma duk wadda sukayi Naseer da Sumayya suna cinyewa, sosai iyayenta sukejin dadin yanda take maida hankali.
Lamarin su Nabeel kuwa abun ba'a magana, domin neman matan Nabeel yayi yawa, kuma yawanci duk abinda yakeyi Ummanshi itace take goya mashi baya, kuma take kareshi a wajen Abbanshi. Itama harkarta kawai takeyi ta neman mata, domin yanzu ta kware sosai, hartafi Lawisa domin ita ba kananan kudi take sakar ma mutanan ta ba.
Abba ne a falo yana ta zagayen falonshi fuskarshi cike da damuwa, Ummace tayi sallama tana zuwa tace Alh, lafiya na ganka cikin yanayin da bantaba ganinka ciki ba? Juyowa yayi yasamu waje ya zauna yana fadin, dole ki ganni cikin wannan yanayin.
Na dade inajin jita jita akan halin da Nabeel yake ciki, amma bantaba yarda ba, ayau naje kuma naganema idona, Nabeel da abokanshi sun fito daga gidanshi na Nasarawa tare da wasu yan mata, bakiga yanayin shigarsu ba.
Daure fuska Umma tayi tace dakata Alh, dama tun ba yanzu ba nafara gane kana zargin danka,dama tun kafin kabashi mukullin gidan kafara korafi akanshi, dama ai bakin iyaye yana kama dansu, kuma kaine kafara yimashi bakin hakan.
Kuma ni wallahi bazan taba yarda Nabeel yana neman mata ba. Kuma da kake maganar kaganshi sun fito da mata daga gidanshi wani abu kaga suna aikatawa? Kada kamanta ko kotu kaje dole seka gansu turmi da tabarya kuma dole seda shedu 3.
Dama ai dole kaga Nabeel da mata domin ba makarantar maza zalla ka kaishi ba, kuma kada kamanta Nabeel cewa yayi zasu rika zuwa karatu agidanshi idan sun gaji, shikenan kuma sekace wai yana kai mata gidanshi, ai dole yayi abota da mata ko kaima zakace dakayi makaranta bakayi abota da mata ba?
Dago kai Abba yayi yana kallon yanda Umma ta rufe ido tana ta masifa abinda bata taba yimashi ba. Hannu tasa kamar tana goge kwalla tace shikenan nagode Alh, tunda har zaka iya daukar maganar mutane, ashe dama baka san akwai masu jin haushin yanda kakeson Nabeel ba? Idan baka sani ba kasani akwai mutane dayawa dasuke jin haushinka kaida Nabeel.
Kukan karya tasa,tana fadin yau ka nuna mani kafara gajiya damu, saurin rufe mata baki yayi yajawota ya rungumeta yana fadin kidena fadar haka, abinda nagani ne kawai na fada. Nabeel danmu ne, bantaba zuwa maki da maganar da mutane suka fada mani ba seda yau na tabbatar da kaina.
Duk yanda mukeson Nabeel dole semun kula da tarbiyarshi, domin masu iya magana suna cewa kasa yaro kuka tun kafin yasaka kuka, kuma icce tun yana karami ake lankwasashi, idan ya bushe sede ya karye. Wannan dalilin ne yasa naki kai Nabeel waje yayi karatu.
Domin ina tsoron turawa su bata mani yaro, to meyasa yanzu dayake gabanmu bazamuyi kokarin gyarashi ba? Gara ace bama sonshi yazama na kirki da ace son da muke nuna mashi ya kaishi ga halaka, yau kome Nabeel ze zama daga gare mune, idan yazama na kirki mune, idan yazama na banza mune.
Idan har Nabeel zerika zama tare da mata suna karatu acikin gida, tabbas wata rana shedan zeyi tasiri azuciyarsu harsu kai ga aikata abinda ba'aso. Dan haka inaso kibani goyon baya muyi kokarin tsaida wannan barnar datake niyar shigo mana cikin gida, bawai dan bama son Nabeel ba.
Tashi zaune Umma tayi takama hannun Abban Nabeel tace dan Allah Alh, kabar yaron nan yayi rayuwa me dadi, Nabeel fa ba mace bane, mezesa murikeshi agida mu hanashi more rayuwarshi, wallahi a wani wajen kamar Nabeel iyayenshi sun sallama ma duniya shi, domin shi namiji ko ina ze iya shiga aduniya, kuma kome yayi ado ne agareshi.
Amma idan muka fara takura mashi tabbas zamu jawoma kanmu babbar matsalar da semunyi kuka da idonmu, kuma yanda yasaba jindadi rayuwarshi ze iya bijirema umarninmu matukar yaga munaso mutakureshi waje guda. Amma kabarni dashi zan san yanda nayi na hanashi kai mata gidanshi, idan zasuyi karatun zance surikayi a makaranta. Haka Umma tayita kwantar ma Abba hankali har ya hakura yabarta tayima Nabeel magana.
Tun daga lokacin da Umma tafadama Nabeel Abbanshi yakusa karbe mukullin gidanshi Nabeel ya canza taku, sam babu wanda ze iya gane lokacin da suke shiga da kuma fita, alokacin ma yakara maida hankali wajen neman mata.
Sumayya ce tashigo cikin makaranta tana ta sauri domin yau ta makara, sam bata kula dasu Nabeel ba da suke zaune saman motarsu suna fira, su Zuby suna daga cikin motar suna shan lemu. Garin sauri tayi tuntube litattafan dasuke hannunta suka zube.
Kafin ta duka ta dauka iska ya figi wata takardarta, saurin kwashe sauran tayi ta ruga domin ta dauko takaradar, jikin wani icce takardar ta tsaya, dede kusa da inda Nabeel ya dora kafarshi yana zaune saman mota.
Hannu ya kai ze dauki takardar yaga kota mecece, yana kai hannunshi Sumayya tayi saurin dauke takardarta. Tana dago kai idanuwansu suka sarke da juna, cak suka tsaya suna kallon kallo.
Sumayya ce tayi saurin dauke manyan idanuwanta daga kallonshi ta juya domin ta tafi class, lumshe ido Nabeel yayi domin bakaramin tafiya dashi tayi ba. Dariya Saif yasa tare da dukan kafadarshi yana fadin to mayen mata kallon ya isa haka.
Murmushi Nabeel yayi yace tahadu Saif, kaga yanda idanuwanta suke kuwa? Kara lumshe ido yayi yana murmushi. Najib yace to wannan de ustaziya ce garama kamaida zalamarka. Saurin saukowa Nabeel yayi yana fadin wallahi inasonta.
Kama hanunun Saif yayi yana fadin da gaske inasonta, ni idan ma Abba ze aura mun ita wallahi zan aureta. Dariya suka samashi ganin yanda ya rikece masu, kamashi Saif yayi yana fadin haba abokina kazama namiji mana,kama dena maganar aure haryanzu fa baka kai shekara 25 ba.
Zuby ce tafito tana fadin haba Nabeel duk yan gayun dasuke makarantar nan basu isheka ba seka jawo mana wannan kazamar? Yanzu daka tabata zata fara cewa Allah yace annabi yace, kai bakaga irin shigarta ba? Wani irin kallo Nabeel yayi mata hakan yasa tayi saurin hadiye sauran maganarta.
Khairat ce tafito tana fadin haba Nabeel ai abun be kai haka ba, karka damu wannan yarinyar course dinmu daya da ita, kai baka taba ganinta ba? Girgiza kai Nabeel yayi, Khairat tace to kada kadamu insha Allah nizan shawo maka kanta. Murmushi Nabeel yayi yace nagode khairat, idan kikamun haka tabbas kin biyani, domin ina ganin nasamu matar aure dan yakamata nima nabar wannan shiritar nashiga sahun manya in kyaleku kucigaba da harkar ku.
Saurin kallon juna su Saif sukayi, murmushi Saif yayi ya dagama Najib gira, lokaci guda suka saki wani mugun murmushi.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Part 40 ⏩ 45
Shiga mota Nabeel yayi yana fadin zanje gida inga Umma se kun taho, Khairat dan Allah kimun wannan kokarin. Murmushi khairat tayi tace angama, Saif yace wai duk ganin ustaziyar ne yasa ka wannan saurin? Nabeel yace no, kawai inason ganin Umma ne. Najib yace shikenan semun hadu.
Yana tafiya Najib ya kalli Saif yace lallai jindadin mu yakusa zuwa karshe, yanda Nabeel yake mana facaka da kudi kuna ganin idan yayi aure zecigaba da abinda yake mana? Kunaji de yace idan yayi aure ma kyalemu zeyi.
Murmushi Saif yayi yace kai har wannan maganar tafara damun ka? To wai duka nawa Nabeel yake ma da har ze fadi magana kayarda, idan baka sani ba, Nabeel mota ne, ni kuma nine sitiyarin nashi, dan haka kabarni dashi, bazan taba barinshi yayi aure yanzu ba.
Zuby tace haba dear kai kuma ina ruwanka da aurenshi? Hannun Zuby Saif yakama yana fadin nasan Nabeel da gaske yake yana son waccan yarinyar, matukar ya aureta nasan zata iya rabamu dashi, kuma kinga ku dukanku tare kuka gammu dashi.
Murmushin gefen baki yayi yace bama zeyuwu ba, aure? Muna a 100 lvl yace zeyi aure, tabbas nasan iyayenshi zasu iya mashi auren gata domin suna matukar kaunarshi, amma nikam bazan bari yayi aure ba, idan har yana sonta ni nasan yanda zamu jawo ra'ayinta tadawo cikinmu, amma Khairat inaso kibi abun a hankali.
Dariya Najib yasa yana fadin shegen kaya, wallahi kai mugu ne, nasan ma zataso Nabeel domin ya hadu, kuma kasan shawo kan mace ba abu bane me wahala. Haka suka rika tsara duk yanda zasu hana Nabeel aure.
Saurin dago kai Umma tayi alokacin dataji abinda Nabeel yafada, Abba kuwa murmushi yayi yana shafa kanshi yace lallai yarona ya girma, kada kadamu nafada maka babu abinda zaka nema awajena banyi maka shiba matukar be saba ma Allah ba.
Saurin kallonshi Umma tayi fuskarta adaure tace haba Alh, wace irin magana ce haka? Duka nawa Nabeel yake daze fara maganar aure yanzu? Idan kamanta bara na tuna maka shekarar Nabeel 22 yaushe kake tunani zamuyi mashi aure.
Gaskiya nide banyarda da wannan maganar ba. Murmushi Abba yayi yace haba Umman Nabeel, tsoro kike kada ace kamarki kinfara aje jika? To meye dan munyima Nabeel aure yanzu? Kada kimanta babban abinda yake hana mutane aure shine rashin kudi.
Meye Nabeel bedashi? Ko yanzu yace bayason makaranta yanada hanyar daze iya rike mace sama da 2, dan haka kibar wannan maganar, tunda kikaga yazo yace yana son aure toshikadai yasan abinda yakeji, kuma musulunci be hana muyi mashi aure dan yana da shekara 22 ba.
Kamo hannun Ummanshi Nabeel yayi kamar zeyi kuka yace Umma dan Allah kibarni na aureta, wallahi yau kawai nafara ganinta amma bakiji yanda nakejinta araina ba, kinga idan nace sena gama karatu ita mace ce iyayenta zasu iya yimata aure a koda yaushe dan Allah Umma.
Hannu tasa tana shafa kanshi tace shikenan Nabeel naji, banaso kabari hawaye su zubo maka saboda mace, kada kataba bari kazama rago akan soyayyar mace har ka bari tagane, domin zata wahalar da kai, kuma idan har kanaso naso duk macen dazaka aura to kada kabari son da kake mata yafito fili.
Bazan taba bari wata mace ta maida mani yaro bawa ba. Kallon Alh, tayi tace naji ze aureta amma nima inada sharadi. Alh, yace fadi koma wane sharadi ne tunda kin amince da bukatarmu. Nabeel bazeyi aure yanzu ba harseya gama 100 level tunda yanzu sun kusa fara jarabawa.
Murmushi Abba yayi yace dan wannan babu matsala kafin lokacin ma sun kara fahimtar juna, dafa kan Nabeel yayi yace yarona kada kadamu kamar gobe ne zakaga lokacin yayi, kaga kaima sekaje ku kara fahimtar juna da ita.
Murmushi Nabeel yayi ya rungumeshi yana fadin nagode Abbana, nagode Ummana. Dariya suka samashi, Umma tace to mu baka fada mana sunanta bama. Sosa kai Nabeel yayi yace Umma nimafa yau nafara ganinta ammade tana da kyau sosai. Abba yace to idan kaje ka tambayo sunanta seka fada mana.
Tun daga wannan rana Nabeel yadena fashin makaranta, kuma da wuri yake zuwa, haka yasa su Saif suma suka rika zuwa kullum sede idan sun tashi sutafi yawonsu. Sam yarage kula yan mata sede idan abunshi ya motsa.
Kullum idanuwanshi akan Sumayya, sosai sonta yakara yawa a zuciyarshi, duk lokacin da yayima Khairat magana akan taje wajanta setace e taje amma taki kulata. Ganin Nabeel zeje wajenta da kanshi yasa Saif yace kai wasa fa take maka.
Murmushi Nabeel yayi yace metace to? Saif yace tace kabari adawo next semister saboda yanzu karatun exam ne agabanta. Wani murmushi Nabeel yasaki yana fadin zanjira dan bana son in takura mata.
Kuma ma su Abba sunce damun gama 100 lvl zamuyi aure. Dariya suka sa mashi Najib yana fadin lallai muna da babban biki. Saif yace yanzude tunda ta amince zata kula ka idan angama exams se kacigaba da harkar ka.
Haka suka shiga mota tare da fita suna cike da nishadi. Sumayya kuwa kullum tunanin Nabeel take, tun ranar data ganshi taji tana sonshi, bare kuma da kusan kullum take kamashi yana kallonta, atunaninta ko sonta yakeyi amma ganin yanzu yama dena yawan zuwa makaranta tagane ba sonta yake ba.
Haka suka dage wajen karatun exam ita da Naseer da wata kawarta Mansura, kullum da sun fito daga class suke tafiya library karatu, duk lokacin da Nabeel yaso ganinta haka zeshigo class ya zauna yasa bakin glass yayita kallonta batare da kowa ya gane ba.
Da haka suka fara exams dinsu ta first semister cikin sa'a suka gama lafiya, sede ba kowace exam su ke zuwa ba, haka suka gama suka tafi hutun sati biyu. Aranar har gida Naseer yaraka Sumayya, sun dade suna fira kafin yatafi.
Tunda suka rabu Naseer ya tabbatar ma kanshi son Sumayya yake da gaske, domin bayan rabuwarsu yaji kewarta sosai, kuma kullum seya kirata sun gaisa, yaso yafada mata yana sonta seyayi tunanin kada tace bata sonshi kuma alakarsu ta baci. A ranshi ya bari duk ranar data rage masu saura shekara daya su gama ze fada mata yana sonta.
Nabeel ne zaune shida su Saif gaba daya ranshi abace