Showing 27001 words to 29040 words out of 29040 words
Chapter 10 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt
amma ayau data canza tabbas haushinta yacika zuciyata. Allah yakicire mun sonta.
Washe gari bayan sun tashi daga makaranta haka mutane wasu daga cikin course dinsu kowa yarika daukar budurwarshi suna tafiya gidan Nabeel, da misalin karfe 2:00 mutane suka gama halartar gidanshi, bayan kowa yashigo suka kulle gate din.
Wajen yayi kyau kamar za'ayi wani party na biki, fitowar Nabeel da Sumy ce ta katsema mutane surutun da sukeyi, masha Allah, fadin irin kyan da sukayi bazeyuwu ba, domin ko iyayen dasuka haifi Sumy da kyar zasu iya ganeta ayanzu. Tasha Dinner gown red colour, anyi mata kwalliya me masifar kyau, gashinta yasha gyara an bazoshi.
Yanda kasan ba hausawa ba haka suka kasance, shima Nabeel yasha Black suit se ta cikin red, gashin kanshi yasha gyara yayi,masifar kyau, haka suka jero kamar ba musulmai ba, ba kamar Sumy ita datake mace, hatta da faratan ta sunsha fanti red.
Inda aka tana dar masu nan suka nufa su Saif suna take masu baya, suna zuwa mutane suka hau tafi, Saif ne yafara bayani, muna mika godiya ga duk kanin Mutanan da suka samu halartar wannan engagement na abokina da masoyiyarshi Sumy.
Wannan rana ta farin ciki ce agaremu domin taya abokinmu kuma dan uwanmu murnar samun abokiyar rayuwa. Kamar yanda Allah yataramu anan Allah yataramu ranar dazamu rakasu dakinsu amatsayin ma'aurata. Tafi aka dauka gaba daya.
Bayan sun yanka cake, suka ciyar da junansu, Saif yamikama Nabeel zobe yasama Sumy, haka aka dauki tafi, itama Zuby tabata tasa mashi, rungume juna sukayi, gaba daya wajen yadauki ihu da tafi. Nan aka samasu kida suka fara takawa, kowa yafara fitowa yana takawa.
Taro yayi kyau, anci nasha kuma an cashe, se karfe 6 sannan suka tashi, kafin kace me har hotunansu ya baza gari, bayan kowa yatafi Sumy tashiga tayi wanka tana fitowa Nabeel yashigo, shima wankan yayi lokacin daya fito tagama shafa mai da towel ajikinta tana kokarin sa kaya.
Karasowa yayi ya rungumeta suka saki murmushi, Nabeel yace inama ace wannan taron da akayi na daurin aurenmu ne. Sumy tace wata rana ai zata kasance ta aurenmu. Nabeel yace gaskiya yau bazan iya kwana ni kadai ba. Sumy tace inama ace a hostel nake da nice zan zamo abokiyar kwanciyarka.
Hannu yasa ya cire towel din jikinta yana rada mata wata magana a kunnanta, saurin ja baya Sumy tayi tana girgiza mashi kai, daure fuska Nabeel yayi yace dama nasan baki sona, wallahi babu abinda bazan iya mallaka maki ba, ke koda ace zaki kamu da ciwo zan iya sadaukar da wani shashe najikina asamaki matukar zaki rayu, bandamu da rayuwata ba inde ke zaki rayu.
Amma dan na tambayi wani abu kadan zaki tureni, yayi kyau, kuma nagode Allah dakika nuna mani iyakata, kishirya inmaidaki gida, dama nasan ai bazaki taba iya daukar bukatata ba, zan nemo wadda zata iya kula dani.
Juyawa yayi yana kokarin sa kayanshi, saurin matsowa tayi ta rungumeshi ta baya tana kuka tace kayi hakuri kada kayi fushi dani, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba, zan iya kula da kai wannan alkawarina ne, dan Allah kada kaje wajen wata.
Kasan komai nawa naka ne, kawai abinda nake tsoro kada inyi ciki. Murmushi yasaki tare da juyowa yana share mata fuskarta yace ya isa haka sweet banaso inga hawayenki, bazan taba bari kizubar dasu ba.
Ina sonki kema kinsani bazan taba bari kisamu abinda ze takura mana ba, zan baki maganin daze hanaki daukar ciki, kuma wannan abun dazamuyi shine zekara dankon soyayyarmu, kuma bazamu taba rabuwa da juna ba, domin munriga da mun mallakama junanmu kanmu.
Haka Nabeel yayita fadama Sumy da dadan kalamai har yayi nasarar amincewarta, shedan kuma yakara zigasu zuwaga aikata alfasha, aranar seda Nabeel yayi nasarar biyan bukatarshi awajen Sumy.
Bayan sun gama komai sukayi wanka, sosai Sumy ta wahala, magani yabata tasha yana ta yimata godiya, kallonshi tayi tace dear ina fatan Mama bazata gane abinda yafaru dani ba ko? Murmushi yayi yace kece zaki bata damar fahimtar wani abu, amma idan kika cire damuwa daga ranki bazata taba fahimtar komai ba.
Wannan maganin ciwon jiki ne, idan kinci abinci zaki kwanta kisha insha Allah da safe zaki jiki garas, wata durowa ya bude yadauko wata waya acikin kwali me kyan gaske, daga ganinta zatayi tsada, kamo hanunta yayi yace wannan kyautarki ce bisa wannan kyauta nima da kikamun.
Kuma nayi maki transfer din million 1, nagode sweet, hakika yau kin biyani, Allah yabarmu tare. Sosai Sumy taji dadin wannan kyauta, godiya tayi mashi tasa kayanta suka fita, suna fita Saif yasaki wani murmushi, kallonshi Nabeel yayi tare da mashi alama da hannu angama komai. Alamar jin jina yayi mashi, haka tayimasu Zuby da Khairat sallama suka tafi, cikin sa'a bata samu Babanta agida ba.
Nabeel ne zaune afalon Abbanshi ya jingina da jikinUmmanshi yana shan Kankana, kallonshi Abba yayi yace Nabeel wane irin taro ne kukayi yau agidanka? Ya mutsa fuska Nabeel yayi yace kai Allah kayi mana tsari da yan sa ido.
Umma tace meyafaru kuma? Abba yace dazu wani yake fada mani wai yaga motoci suna shiga gidanshi kuma yaji anata ihu ga kida yana tashi. Tabe baki Umma tayi tana fadin kai Allah ya sawake, wallahi Alh, idan kana biya ta mutane se sun rabaka da danka.
Nabeel yace Abba abokaina ne fa sukazo tayani murnar samun matar aure shine muka dan hada walima, kuma naga ai ba abu marar kyau muka aikata ba, iyakarmu harabar gidan. Jin jina kai Abba yayi yace ai na dauka kowani mugun abu ne kukayi yanda mutumin yazo yana fada mani.
Kace mun kusa zuwa nema maka auranta? Nabeel yace Abba iyayenta sunce seta gama karatu zatayi aure, nima kuma da suka fadi haka naga yadace ace nima nagama karatuna sannan inyi aure haka zefi, lokacin ma nakara shekaru kuma mun kara fahimtar juna.
Murmushi Abba yayi yace hakan ma yana da kyau, Allah yasa munada rabon gani, nide abinda zan fada maka kaji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka dage kayi karatu domin shine kadai gatan dazan maka, nafiso ko bana raye kada kayi maraicin komai, domin koda ban bar maka dukiya ba nabar maka ilimi.
Domin dukiya zata iya karewa, amma ilimi har abada baze kare ba. Umma tace wannan haka yake, kuma nasan Nabeel yarone me haka zaka baze taba bamu kunya ba, kada ma kadamu ni nasan waye yarona. Abba yace Allah yayi maka albarka.
Kallon Umman Nabeel yayi yace yakamata azo ayimashi kanwa ko kani haka nan, gaban Umma ne yafadi jin abinda yafada, saurin kallonshi tayi yana murmushi yace emana, kinsan inason inga gidana yacika da yara, idan kuma kin gaji ayo maki kanwa.
Saurin tashi Umma tayi fuskarta adaure tana fadin mene? Dariya Abba yasa yana fadin yi hakuri kada idanuwanki su fado wasa nake maki, jawota yayi suka samata dariya shida Nabeel, kallonshi kawai take cike da tsoro, yace wasa nake maki kinji.
Amma de gaskiya inason akara mani yara kamar 2 ko 3 ma sun isa ko bahaka ba Nabeel? Yace kwarai ma Abba, nima zanji dadi ace inada kannai, tashi Umma tayi tana fadin Nabeel tashi kabani waje, dariya yasa yana fadin Umma de bakiso ki tsufa dawuri shiyasa. Tashi tayi tabasu waje sunata mata dariya.
Tana zuwa daki takira Lawisa tana fadin kizo akwai matsala. Lawisa tace bana gari dazu na kaima wata kawata ziyara a abuja, amma jibi zan dawo idan nadawo zanzo, ki kwantar da hankali banaso kibari kowa yafahimci damuwarki, idan nadawo zanji koma meye.
Kashe wayar tayi, haka Umma tazauna cike da damuwa, kada de ace maganar bokace zata tabbata, domin yace mata idan har asirinta yafara karewa Alh, zefara mata maganar yara da kuma ta aure, lallai dole su koma wajenshi, dama tunda sukaje so daya basu kara waiwayarshi ba, domin bukatar ta tabiya.
Washe gari tunda wuri Sumy tashirya tace ma Babanta yau sunada lecture din safe kuma bazasu dawo da wuri ba, haka yadauko 200 yabata yayanta yakara mata 100, kamar bazata karba ba se kuma ta tuna kada Babanta ya tambayeta ina take samun kudi, karba tayi tana masu godiya tafita da kwatuwar hijabinta. Murmushi Babanta yayi yana fadin nayi sa'ar yara ni kam.
Aranar ko makaranta bata shiga ba, wuni sukayi ita da Nabeel suna aikata masha'a domin adaren jiya kasa bacci tayi, dan son Nabeel kara shiga ranta yayi, hakan yasa yau tafito dawuri dan su kasance tare. Seda ta jera kwana biyu bata shiga makaranta ba, kullum suna tare da Nabeel, sosai suka kara dinkewa, dan yanzu Nabeel becika kula kowa ba, Ada ce kawai idan yaso yake kiranta ta tayashi kwana.
Sumy dasu Zuby sun kara zama kawaye, dan yanzu Sumy itace shugabarsu, domin komai se abinda tace, kuma ta dalilinta suke samun komai daga Nabeel, babu ruwansu da tunanin makaranta, Sumy ce kawai take dan magana, shima kuma Nabeel yace mata kada tadamu ko basuyi exam ba dole abasu result, bataga first semister basuyi exam ba amma aka basu result kuma babu wanda yayi carry over, haka yayita kwantar mata da hankali har ta amince ta kuma cire damuwar makaranta aranta.
Tun acikin mota Umma take bama Lawisa labarin abinda yafaru, Lawisa tace haba kidena damuwa ai yace wasa yake maki ko, wallahi duk kin tada mani hankali, da se gobe zan dawo kawai ganin kintashi hankalinki yasa nataho, gashi daga zuwana ko hutawa banyi ba kika dauko ni.
Umma tace dole indamu Lawisa, yau idan asirina yatonu ai gaba dayanmu mun shiga 3, Lawisa tace shiyasa nace maki kisamu Yaya yakara maki kadarori, domin nasan wata rana dole asirinmu yatonu, kinga alokacin muna da madafa, amma kintsaya soyayya, ai yanzu lokacin soyayya yawuce.
Kin ganni nan nasamu wani yaro me masifar kyau, buzu ne irin yan cirani ne, kinsan nace maki na dena harkar bin maza, amma wallahi haduwata dashi yasa nakasa hakura,yanzu haka nace mashi ya hado kayanshi yadawo gidana.
Ana gobe zan tafi abuja muka hadu dashi abakin titi yana saida lemu da ayba, na tsaya zan siya naga ya burgeni shine nabashi address dina nace yazo da dare, kinsan wani abu? Aranar tare muka kwana yaron ya hadu sosai ya iya harka, shiyasa zan maidoshi gidana in ginashi yazamar mani abokin debe kewa.
Kafin infara koya mashi harkar kasuwanci kinga semu rika tafiya tare. Murmushin takaici Umma tayi tana fadin ke ana maganar matsala kina maganar wani yaro can. Dariya Lawisa tasa tana fadin ke kin cika tsoro, kibari muje wajen boka nasan komai ze warware duk da bamu kyauta ba da bamu kara waiwayarshi ba, amma yanzu semuyi mashi sallama me tsoka.
Parking sukayi daga gefen wata gona suka taka da kafafuwansu zuwa cikin dajin da bokan yake. Koda sukaje basu sami komai ba, inda bukkarshi take ada yanzu babu komai se fili, cike da tashin hankali suka fara waige waige, Umma tace kode ba wajen bane?
Lawisa tace wallahi nan ne, kamata yayi musamu wani mu tambayeshi ko Allah zesa yasan inda ya koma, gashi Gaje bata gari bare in tambayeta, kuma nan babu network bare akirata. Dafe kai Umma tayi tana fadin nashiga 3.
Wani mutum suka hango yana dibar itatuwa, da sauri suka isa wajenshi, bayan sun gaisa Lawisa tace bawan Allah ko kasan wani mutum dayake zaune a wata bukka datake wajen can? Kallonsu yayi yace kice mani wani dan iskan boka.
Lawisa tace eshi nake nufi. Dariya yayi yace Allah ya kashe tsinannan dayake lalata mana mata da yara da yan uwa musulmai, wallahi kun bani kunya gaku da cikar kamala amma kuke neman wanann la'anan nan Allah.
To idan baku sani ba, yau kusan wata biyu da bokan yayi mutuwar wulakanci, mutuwa irin ta karnuka, kai wani karenma yafishi daraja, domin kila wani karen idan yamutu yasamu a gina rami arufeshi, amma shi wannan bokan babu wanda yaje kusa da gawarshi.
Karnuka da tsuntsaye sune suka cinye namanshi, daga karshe aka sama bukkarshi wuta ta idasa cinye sauran kashinshi daya rage, dan haka yarage naku ku koma ga Allah ko kuma kunemi wani bokan.
Daukar iccenshi yayi yatafi, zubewa Umma tayi tana fadin munshiga 3, shikenan asirina ze tonu. Lawisa tace kiyi hakuri kitashi mutafi gida kada wani abun yasamemu kinga babu mutane dayawa, muje gida ai bashi kadai bane boka, kuma Gaje tana nan nasan zata nemo mana wani.
Haka suka tafi gida, bayan ta aje Umma tawuce gida domin yaronta yayi mata waya ya iso. Umma kuwa tana zuwa ta kwanta cike da damuwa, kafin wani lokaci zazzabi me zafi ya rufeta.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263