Showing 3001 words to 6000 words out of 29040 words

Chapter 2 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt

dawo ba shine nabita, tun dazu nake nemanta banganta ba, shine nazauna acan da dare yayi.


Salati suka sa jin abinda yarinyar tace. Mutumin yace kinsan unguwarku? Lawisa tace ai mu idan za'aje garinmu se an hau mota 2 Kuma akwai nisa. Girgiza kai mutumin yayi yace Asabe kinsan abinda na fahimta da labarin yarinyar nan?


Duk yanda akayi ba cikin garin nan suke ba, kila de a kauyen garin nan suke, domin tace se an hau mota 2, kuma kinga idan aka shigo cikin garin nan unguwarmuce farko dole ita zata fara sauka, kinga zefi mata sauki ta ajeta tayi saurin juyawa.


Asabe tace ni kuma ina ganin yarinyar kamar bada aure aka sameta ba. Jinjina kai yayi yace toyanzu ya kikeso ayi? Kallon yarinyar tayi yanda ta kwanta lamo ajikinta tace malan inde ka amince kawai mu riketa, idan mutane sunganta muce masu diyar dan uwanace muka daukota daga kauye.


Kallonta yayi yana murmushi yace gaskiya naji dadin wannan shawara taki, Allah yayi maki albarka, kuma yabamu ikon riketa da amana. Hannu yarinyar yakamo yana fadin Lawisa tunda mamarki bata sonki daga yau ga mamarki nan.


Kin taba ganin babanki? Girgiza kai tayi yace yauwa to nine Babanki, dama wajena zata kawoki shiyasa tabarki anan, saboda haka zaki rika kwana anan gidan, kuma zan saki makaranta ai kinaso ko?


Dariya tayi tana daga kai. Yauwa to inaso idan safiya tayi duk wanda ya tambayeki kice daga kauye muka daukoki kinji? Daga kai tayi, yace yauwa tashi kiyo fitsari ki kwanta. Tashi Asabe tayi tana fadin mukam Allah yakawo mana diya daga sama, dama gidan yana mun shiru tunda Jamila tayi aure.


Malan yace ai ga diya kinsamu daga sama dama Jamila ita kadai Allah yabamu. Tashi sukayi suka shiga ciki suna me cike da murna. Tun daga ranar rikon Lawisa yadawo wajensu, kuma yanda sukace haka suka fadama jama'ar unguwarsu daga kauye suka daukota.


Haka suka sata makarantar boko da islamiya. Sosai suke kulawa da ita, sede Allah yasa Lawisa batajin magana, akwaita da tonon fada duk ta addabi yan unguwar.


Da haka ne suka hadu da Maimuna. Wadda ita kadaice a wajen iyayenta, suna sonta sosai, kuma suma sunada rufin asiri dede gwargwado. Tunda suka hadu da Lawisa jininsu yahadu, duk da Lawisa ta bata yan watanni amma baka ganewa domin Maimuna tana da jikin girma.


Haka suka taso da kawacensu, har suka gama primary suka shiga secondary. Dayake makarantar dasuke hade take da maza hakan yasa Lawisa tafara shige masu, kujerarsu daya da Maimuna kuma kusa da wasu maza suke.


Wannan daliline yasa take jansu da fira, ko break aka fita seta cema Maimuna taje tasiyo masu abinci su zauna cikin aji suci tare da mazan, daya sunanshi Babawo, abokinshi kuma Sani.


Haka zasu zauna a aji suci abinci sunayi suna yan tabe tabe. Tun maimuna bata kulasu har itama tafara biyema Sani sunayi, ko tashi akayi basa tafiya gida da wuri, kuma basa bin hanyar da sauran dalibai suke bi.


Haka suka taso tun abun yana faruwa kadan kadan har ya girma. Lokacin dasuka shiga aji 3, sosai suke soyayya dasu Sani, Maimuna da Lawisa sun saba da abubuwan da yan mazan suke masu.


Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya iyayensu basu fahimci abinda suke aikatawa ba. Alokacin da suka shiga aji biyar kuwa sun zama manyan yan mata, har wani waje suke zuwa inda kango ne na Baban Sani.


Zuwa wannan lokacin babu abinda basu aikatawa na lalata, sede haryanzu basu yarda sun wuce gona da iri ba. Wata rana da safe Lawisa ta biyama Maimuna zasu tafi makaranta, lokacin iyayenta sun fito zasuje unguwa.


Bayan sunyi sallama da ita suka fada mata kafin su taso daga makaranta ma zasu dawo ba dadewa zasuyi ba. Kudi mahaifin Maimuna ya dauko yabasu yace sutafi kada su makara. Bayan suntafi suma suka nufi tasha dan su hau mota.


Lokacin da su Maimuna suka dawo gida haka tasamu kofar gidansu cike da mutane. Saurin karasawa tayi wajen kanin mahaifinta wanda yake ta kuka.


Kamata yayi suka shiga ciki, suna zuwa tasamu mata dayawa aciki. A nan yafada mata iyayenta sunyi hadari kuma duk sun rasu. Bakaramin tashin hankali Maimuna ta shiga ba. Tasha kuka ita da Lawisa.


Haka aka cigaba da zaman makoki. Bayan kwana bakwai, suka zauna domin asan wanda ze dauki Maimuna tunda ita kadaice awajen iyayenta, gashi mamanta yar Minna ce.


Kanin mahaifinta shine yace ze dauketa tunda takusa gama karatunta data gama se ayi mata uare kawai. Da wannan shawarar Maimuna ta koma gidanshi da zama.


Bayan wata guda aka hada komai da iyayenta suka bari aka saida domin araba gado. Kasancewar kanin mahaifinta su biyu ne kuma basuda iyaye yasa shida Maimuna ne suka samu gadon mahaifinta.


Ita kuma aka hada mata dana mamanta. Duk da yan uwar mahaifiyarta sun so idan tagama karatu abasu ita amma sam kanin mahaifinta yace beyarda ba, idan tagama zata kawo masu ziyara kafin tayi aure, idan yaso seta cigaba da zumuncinta a gidan mijinta.


Lokacin da suka shiga aji shida idonsu ya gama budewa ita da Lawisa, domin matar kanin mahaifin Maimuna irin matan nan ne marasa kula, sam ba ruwanta da damuwa da yanayin da Maimuna take. Wannan dalilin ne yasa suke abinda suke so, domin shima mijinta neman kudinshi kawai yasa gaba.


Wata rana sun tashi daga makaranta Babawo yace Lawisa ina alkawarin da kikayi mani? Murmushi tayi tace to wai kai idan ma na amince maka ina kakeso muje muyi abinda mukeso inda baza'a ganmu ba? Sani yace kawai kuzo muje dakina tunda a zaure yake kuma mamana bata nan yau dan abinci ma tunda safe tamun tabani na aje acikin dakina.


Biki taje kuma seda dare zata dawo. Babawo yace yauwa gama guri munsamu muje muna kara batama kanmu lokaci. Lawisa tace Maimuna muje. A sanyaye Maimuna ta kalleta tace nide tsoro nakeji. Kina ganin muna SS 2, aka taba kama wata tayi ciki aka koreta kuma kowa seda yaganta.


Babawo yace haba Maimuna sekace baki waye ba, hannu yasa a aljihu yaciro wata takarda yace kinga wannan maganin hana daukar ciki ne, nima awajen Ummata nasanshi domin ta dade tana aike na chemist ina siyo mata.


Ada bansan amfaninshi ba, amma wata rana naji tana fadama kwarta shine take sha dasun kwanta da Babanmu yana tafiya bandaki take daukarshi tasha, kuma gashinan haryanzu bata kara haihuwa ba nine autanta.


Murmushi Lawisa tayi tace wato kai harma ka shirya ko? Yace emana, kinsan me chemist din ya sanni shiyasa jiya da Umma ta aikeni dama inada kudi nace yabani guda 4, na bata 2, nataho da 2, kuma duk daya na kwana 10 ne, kafin yakare zan kara sama mana wani.


Da wannan dadin bakin sukaja Maimuna suka nufi dakin Sani. Tare da temakon shedan suka samu damar kawar masu da budurcinsu. Sun sha wahala sosai, hakan yasa Lawisa tace ma Maimuna tana tsoron kada taje gida mamansu ta ganeta, sutafi gidansu Maimuna tunda ita ba'a samata ido.


Cikin sa'a basu sameta agidan ba, haka suka shiga suka dafa ruwan zafi suka gasa jikinsu sukayi wanka, seda Lawisa ta huta sannan takoma gida, tana zuwa tasa kuka, mamanta tace meyafaru ko yauma dukanku akayi?


Lawisa tace wani mugun malami aka kawo mana, wai dan bamuyi shara ba shine yace idan antashi duka ajin kada mutafi seya hukunta mu. Mama haka yasamu tsallan kwado bakiji duk cinyoyina ciwo suke ba, bantaba yin tsallan kwado ba ashe haka yake da zafi.


Dariya Maman tayi tace ai dama idan kana aji shidda ba ruwanka da kowa sede malamai, haka zakuyita hakuri kowama haka yayi, damma ba makarantar kwana kikeyi ba ai da sekinfi haka shan wahala. Ai kun kusa gamawa se hakuri.


Tashi kije kicire kayan ga ruwan zafi can kiyi wanka inbaki robb kishafa zakiji sauki. Da wannan karyar Lawisa ta kauda kan mamanta dan kada tagane tafiyarta ta canza. Tun daga lokacin suka zama yan hannu, sosai suka kara dinkewa dasu Babawo, duk sanda suka aikata lalatarsu Babawo ne yake basu magani suna sha.


Da haka suka gama makaranta. Kuma a wannan lokacin ne marikin Lawisa yarasu, sun sha kuka, haka suka cigaba da zama ita da Asabe. A yanzu basa haduwa dasu Babawo sosai, shiyasa sukace zasu koma islamiya ita da Maimuna, wannan damar ce tasa suka cigaba da aikata abinda suke so da sunan zuwa islamiya.


Tafiyarsu Babawo makarantar gaba da secondary ce tasa suka rabu dasu Maimuna. Kuma a wannan lokacin ne kanin mahaifinta yace ta fiddo miji yayi mata aure. Lokacin data fadama Lawisa ita ce ta zigeta akan kada ta yarda, idan ma ze matsa mata to yabata gadonta su shiga gari sukama sana'a.


Sam Maimuna bata yarda da shawarar Lawisa ba, haka suka rabu bata amince ba. Tundaga ranar kullum Lawisa seta yimata maganar gadonta. Ita ko Maimuna har lokacin bata amince ba. Ba komai bane yasa Lawisa takeso subar garinsu ba se dan tunda malan yarasu rayuwa tafara yimasu wuya shiyasa take son barin gidan.


Shikuwa kanin mahaifin Maimuna ganin shiru bata fiddo miji ba yasa yace ma wani abokinshi yazo suhada yaransu aure, bayaso ya mutu beyima diyar Yayanshi aure ba, dan besan wane irin hali zata shiga ba, sam bayason takoma wajen dangin Mamanta.


Domin shi beyarda da rikon su ba. Jin haka yasa abokinshi yace ya amince, yana yima danshi magana shima yace ya amince. Lokacin daya fadama Maimuna kuka tasa tace ita wallahi bataso tayi aure yanzu.


Haka yayi ta faman lallashinta amma sam bata amince ba. Lokacin data fadama Lawisa tabata shawara akan tace ta amince amma da sharadin za'a fara bata gadonta kafin a daura auren. Maimuna tace to idan kuma yabani kuma akayi auren shikenan kin kwareni?


Lawisa tace kede kije kifadi haka, yana damka maki kudinki zamubar masu garin. Maimuna tace gaskiya bazan iya barin mahaifata ba. Lawisa tace to naji, ammade kinsan Bauchi babban gari ne ko? Bakiso mushiga birni muga rayuwa?


Dan haka semu shiga can cikin gari muyi rayuwarmu me dadi. Shiru Maimuna tayi batace komai ba. Dafata Lawisa tayi tace kiyarda dani, idan muna nan babu abinda zamu sani na rayuwa. Yanzu tunda kike kintaba zuwa cikin garin bauchi kika ga duniya? Girgiza mata kai tayi.


Lawisa tace to idan muka shiga garin acan zamuga manyan yan gayu, kuma muyi abinda mukeso. Amma munzauna nan komai se abinda akace mana zamuyi, yakamata muma mu zauna da 'yancinmu.


Haka Lawisa tarika yima Maimuna kalamai har seda ta amince. Haka taje tasamu Kawunta, bayan ta gaishe shi tace Kawu dama wata magana nazo da ita. Kallonta yayi yace to Maimuna ina jinki meke tafe da ke?


Dukar da kai kasa tayi tana wasa da hannunta tace dama inaso kafin adaura mani aure afara bani kudin gadona a hannuna. Kura mata ido yayi alamar tuhuma. Kara kasa tayi da kanta.


Murmushi yayi yace Maimuna kin tabbata wannan shawarar daga zuciyarki tafito? Kai tadaga mashi. Jinjina kai yayi yace shikenan, bazan hanaki gadonki ba. Domin kin kai minzalin hankali zaki iya zama da kanki, asalima aure zakiyi.


Amma meze hana kibari idan yan uwan mamanki sukazo wajen biki inbaki kudin agabansu dan suzama sheda? Saurin dago kai tayi tace nide Kawu yanzu nake bukatarsu. Kuma ai zamu iya yin rubutu shima ai sheda ne.


Murmushi Kawu yayi yace Maimuna niba zanyi wani rubutu ba, idan kuma kinaso muyi to zan kira mutane 3 muyi agabansu, domin komai yana bukatar sheda. Maimuna tace to ka kirasu se ayi.


Haka Kawu yakira abokinshi, da makwafcinshi tare da wani a bokin kasuwancinshi. Agabansu yadauko takardar da akayi rabon gado da ita, bayan yagama karanta masu abinda kowa yasamu yabasu suka kara dubawa.


Wata jaka yadauko yace wadannan sune duk kanin kudaden Maimuna na gado data samu, domin komai na gadon kudi aka maidashi sannan aka raba. Allah yasani tunda aka bani kudinta nazo na boyesu.


Kome dakina bata taba sanin inda na ajesu ba, kuma bantaba daukar ko naira nace zan juyata ba. Gashi nan malan ku kirga idan sun cika amika mata hakkinta. Bayan sungama kirgawa kudi haka suke.


A bayan takardar da aka raba gadon Kawu ya rubuta sunanshi, da kwanan wata, kuma ya rubuta yamika ma Maimuna hakkinta na gado.


Bayan yagama itama ta rubuta cewar ta amsa, haka yan sheda suma suka rubuta cewar sun tabbatar. Bayan kowa yasa hannu Kawu yace ze aje wannan takarda idan dangin Mamanta sunzo yabasu.


Haka aka fara hidimar biki, Maimuna kuwa tunda ta amshi kudin ta kaima Lawisa domin ta aje masu. Ana saura sati daya biki cikin dare Lawisa ta biyoma Maimuna aranar suka gudu daga gida.


Washe gari haka matar Kawu ta duba ko ina bataga Maimuna ba, Kawu tafada mawa, nan suka fara nemanta. Gidansu Lawisa sukaje, sede suna zuwa Asabe tace itama yanzu take niyar zuwa ta tambaya ko Lawisa taje can.


Dakin Lawisa aka duba babu kayanta. Murmushi Kawu yayi yace tabbas dama zuciyata tafara zargin akwai wani abu dayake shirin faruwa. Babu ko tambaya yaran nan guduwa sukayi bayan sunyi sa'ar amsar kudin gadon Maimuna.


Dafe lirji Asabe tayi tana salati. Kuka tasaka tana fadin dama ai tsintacciyar mage bata mage, kuma barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba. Hakika Lawisa kinyi mana butulci. Amma bakomai, Allah yagani mun rikeki tsakinmu dashi.


Kawu ya kalleta yace Asabe dama Lawisa ba diyar dan uwanki bace? Girkiza kai tayi tana share hawayenta......... Labarin abinda yafaru tabasu. Sosai sukayi mamaki. Kawu yace lallai kunyi kokari, kuma Allah shine ze baku ladar temakon da kukayi.


Wannan hali na butulci da yayi yawa a wannan zamini shine yake jama sauran masu gaskiya, domin a yanzu kowa yana tsoron temako saboda ba kowa ne na Allah ba. Lallai Maimuna tayi rashin wayau data biyema shawarar Lawisa.


Bakomai, ki kwantar da hankalinki, duniyar da suka shiga suna tunanin tafiye masu zama agabanmu zasuje su iske dede dasu. Kuma insha Allah seta koya masu hankali. Asabe tace, nima bazan cigaba da zama garin nan ba, gara inkoma wajen yan uwana zefi mani.


Dama nikadai ce nake anan, shima aure ne yakawo ni, tunda wanda nazo danshi yatafi ai gara inkoma kauyenmu. Kawu yace bazan hanaki ba, domin kazauna kusa da yan uwanka yafi, kome ze sameka kana gabansu, kuma sunfi kowa sanin muhimmancinka.


Haka sukayi mata sallama suka koma gida. Da yamma dangin maman Maimuna suka iso. A nan suka iske tashin hankali, sunyi kuka sosai kuma sun godema Kawu abisa irin rikon da yayima Maimuna.


Kwanansu daya suka juya, suma abinda sukace bazasu nemeta ba, idan duniya ta koya mata hankali zata nemesu da kanta. Haka Kawu yasamu abokinshi wanda danshi ze auri Maimuna yabashi hakuri.


Tunda su Lawisa sukatafi haka suka shiga cikin garin Bauchi, suna zuwa suka sami wani mutum sukace dan Allah suna son kama gidan haya ne. Mutumin yace to gaskiya ni bansan wanda yake bada haya ba, amma akwai wanda nasani shine yake nema ma masu neman hayar gida.


Haka ya kaisu wajen wani mutumi, suna zuwa sukaci sa'a akwai wani karamin gida me daki biyu da bandaki se kitchen da wata mata ta tashi. Kallonsu yayi yace dubu 50 zaku bada. Lawisa tace to mungode, amma dan Allah munaso muje kasuwa musiyo kayan amfani.


Yace ai bakomai, akwai wani yaro zan hadaku dashi ya kaiku kusiyo abinda kuke so. Haka suka bashi kudin yabasu mukullin gida. Bayan sun shiga sun aje kayansu yaron yazo suka tafi kasuwa.


Duk wasu kayan amfani seda suka siyo, haka suka gyara gidansu. Bayan kwana 3 da zuwansu Lawisa tace Maimuna zama hakanan fa baze mana ba, dole mukama sana'ar dazatasa muyi saurin yin suna awajen maza.


Maimuna tace wace irin sana'a kike ganin zamuyi to? Lawisa tace meze hana muje kasuwa mudauki hayar shago murika dafa abinci muna akaiwa can? Maimuna tace kumafa kin kawo shawara me kyau.


Koba komai zamurika fita kullum muna ganin gari. Lawisa tace kinsan yanda masu saida abinci suke, yawancinsu kazamai ne, inaso namu salon yazamo daban, mushiga kasuwa musiyo kaya masu kyau, da kayan kwalliya.


Kinsan ance da kudi ake neman kudi. Maimuna kina da kyau duk wanda ya kalleki dole yasoki, kinga ai zamuyi saurin samun shiga. Dariya sukasa, Maimuna tace ammafa girki da wahala, bare kuma a icce.


Lawisa tace ai zamu fara ne, idan komai yayi dede kinga semu dauki masu aiki, su dafa mana su kai mana shago, aikin mu muje murika zubawa, me wanke wanke tanayi. Maimuna tace haka ma yayi, tashi mutafi.


Cikin sa'a suka samu shago a kasuwa, haka suka fara abinci, kulolin da suke zuba abincin kansu masu kyau ne, hatta da plate din zuba abinci bana roba ba ne, se robobin ruwa da suke zuba zobo ko kunun aya.


Duk abinda zasu zuba basa barinshi abude, komai nasu cikin tsari yake. Haka suka fara zuwa saida abinci akasuwa, idan kagansu bazaka taba cewa masu saida abinci bane. Domin bakaramin ado sukeyi ba.


Dama Maimuna akwai kyau, gata fara, duk wanda yagansu se sun burgeshi. Aranar dasuka fara zuwa kasuwa aranar suka fara samun customers. Gashi sun iya abinci, kuma suna canza kalar abincin dasuke saidawa, harsu dambun shinkafa sunayi.


Kafin kace me, duk wani namiji dayake sayen abinci awani waje ya koma kansu, komai nasu atsari sukeyinshi. Cikin lokaci kankani arziki yafara zauna masu. Kuma da haka,ne, suka cigaba da sana'arsu ta neman maza. Dan wani lokacin mazan har kwana sukeyi. Dama unguwar dasuke bawata me taro bace, kuma gidansu abaya yake, babu taron mutane awajen.


Tun daga lokacin su Lawisa suka dage da saida abinci, har suka samu masu aikin da suke tayasu kuma su kaimasu kasuwa. Wannan shine takaitaccen labarin su.




Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻

Nah
Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)


www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey


Part 10 ⏩ 15


Haka su Lawisa suka isa kasuwa, babu bata lokaci kamar kullum haka mutane suka siye abincinsu har ana neman kari. Bayan me wanke wanke tagama ta hada kayan tayi masu gaba da kayan su kuma suka shiga cikin kasuwa domin siyayya.


Duk abinda zasu siya sun siya, haka me dako ya dauko masu zuwa bakin titi. Duk inda suka wuce se sun gaisa da mazan wajen domin sun sansu sosai. Dede zasu fita daga kasuwar Maimuna taji an bige mata ledar hannunta.


Kayan shafar da tasiyo duk suka zube, saurin juyowa tayi caraf idanuwanta suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login