Showing 12001 words to 15000 words out of 29040 words

Chapter 5 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt

namiji da zejiki ajikinshi ya kyaleki koda shine ya yankema ustazanci cibi.


Dariya Maimuna tasa tana fadin wallahi bakida dama Lawisa, Lawisa tace ba dole ba, keyanzu idan kika samu ciki kika haihu ai kinsan Yaya seya rasa irin kyautar daze maki, dan haka kawai kimanta dawani abu domin yanzu duniya seda kudi ake soyayya.


Maimuna tace tonaji, amma yaushe zaki dauko kayanki? Lawisa tace rufamun asiri, yanda zaku bude sabon amarci agidan nan yaushe zanzo intakura maku. Kede kawai kuyi zamanku nima naje nayi harkata domin nasamu wani danyen yaro da ya iya harka sosai.


Maimuna tace wallahi nide kinmun wayau, shikenan se inta tsayawa a waje guda. Lawisa tace aikuwa dole kicire wannan tunanin aranki, domin kece fitilarmu idan kika da kushe muma zamu da kushe, dan haka kicire komai aranki.


Haka Lawisa tagama shirya mata komai, se dare tayi mata sallama haka Maimuna tacikata da kayan arziki da kudi masu yawan gaske sannan ta tafi.


Bayan ta tafi wajen karfe 10 Maimuna tagama shiryawa, tafeshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi, haka tafita da hijab a jikinta.


Tana lekawa tafara kwalama Babaye kira cike da tsoro, a kidime yataho dagashi se singileti da gajeran wando, yana zuwa yace hajiya lafiya meyefaru? Kamar zatayi kuka tace shigo Babaye kaga wani abu, wallahi motsi nakeji acikin daki.


Yana shiga ta kulle kofar falon, haka yashiga gaba tana binshi abaya tana fadin kashiga kagani bazan iya shiga ba, yana shiga itama tashiga tare da kulle kofar dakin, kafin yajuyo tacire hijab dinta, lokacin daya juyo se yayi arba da Maimuna cikin wasu matsiyatan kaya.


Saurin runtse ido yayi yabude baki zeyi magana kawai ta fada mashi, basu sauka a ko inaba, se saman gado, kafin kace me Maimuna ta fara ruda Babaye, haka shedan yayi tasiri azukatansu suka cigaba da aikata alfasha, dama shima dan hannu ne.




Washe gari Babaye kasa tashi yayi, itako Maimuna tunda wuri ta tashi tayi wanka taje kitchen ta dafa mashi abinci ta zuba maganin da boka yabata, kafin ta koma Babaye yayi saurin shiga yayi wanka yayi sallah.


Tana zuwa ta aje mashi abinci tafita falo domin taci nata. Yana gama cin abincin sam ya manta da abinda yafaru, duk wani tsoro yafita daga ranshi, haka ya koma saman gado ya kwanta, Maimuna tana shigowa tayi murmushi, domin tasan magani yafara aiki. Haka tacire kayanta tahau saman gadon tana zuwa ya rungumeta suka cigaba da aikinsu.




Tun daga wannan rana Maimuna da Babaye suka koma tamkar miji da mata, hatta da kayanshi daukosu yayi yadawo dakin Saraki da zama, kullum gate dinsu a kulle, dama Maimuna bata da wata kawa datake zuwar mata gida. Lawisa ce kawai take zuwa se kuma Gaje, itama kafin tazo seta sanar mata.


Kullum suna waya da Saraki sede yakasa fadamata dalilin dayasa baze dawo ba, itama taki tambayarshi lokacin daze dawo. Haka suka jigaba da shan amarcinsu ita da Babaye, lokaci guda yakara haske da kiba.




A ranar da suka cika sati 4 suna aikata masha'arsu aranar Saraki yakirata yace gobe ze dawo. Kuma tun daga ranar tacema Babaye daga ranar kada yakara zuwa inda take, daga ranar alakarsu tayanke. Babu bata lokaci ya amince, haka ya hada kayanshi ya koma dakinshi.


Washe gari Saraki yadawo, sosai yayi murnar ganin Maimuna yanda takara kiba tayi haske, se tsokanarta yake yana fadin anya babu ajiyata ajikinki? Murmushi tayi batace komai ba. Bayan yayi wanka yaci abinci suka kwanta domin agajiye yake.




Washe gari haka ya fiddo mata tsarabarta data Lawisa, Babaye ma ya ware mashi tashi. Bayan sati guda da dawo warshi Maimuna ta tashi da zazzabi da amai, cike da tashin hankali suka tafi asibiti, awon farko aka gano tana da ciki wata 1.


Ai tun a asibitin Saraki ya rungumeta yana dariya, hatta da likitan daya fada mashi seda yasamu kyauta me tsoka. Haka ya rubuta masu magunguna suka tafi gida, Saraki yarasa inda zesa Maimuna saboda farin ciki.


Haka yace sede Lawisa tadawo gidan dazama tarika tayata aiki, amma Lawisa tace ita kunyarshi takeji sede zata rika zuwa da safe tana tafiya da yamma, amma ya samo mata masu aiki, babu yanda ya iya haka ya amince, dayake akwai wasu dakuna agidan daga baya seyace masu aikin zasu zauna can.


Haka yadauki son duniya yadorashi akan cikin Maimuna, duk wata kulawarshi ta koma kanta. Masu aiki 2 aka samo wasu dattijai domin surika kula da gidan, Lawisa idan tazo da safe da yamma take tafiya.


A haka cikinta yakai wata tara, Saraki yaso ya kaita waje ta haihu amma sam takiyarda. Haka ya hakura domin bayason bacin ranta. Ranar asabar da safe Maimuna ta tashi da nakuda, haka suka nufi asibiti tare da Lawisa Saraki duk ya rude.


Suna zuwa bata wuce minti talatin ba ta haifi namiji me kyau dashi. Saraki yama rasa wane irin farin ciki zeyi, besan lokacin da hawayen farin ciki suka zubo mashi ba, hakika Maimuna tagama mashi komai, besan da abinda ze biyata ba, amma aranshi ya aje wani babban abu da zeyi mata wanda ze sata farin ciki har karshen rayuwarta.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻

Nah
Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)


www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey


Part 25 ⏩ 30


Fadar irin kayan da Saraki ya sayama Maimuna da danta baze yuwu ba, domin bakananan kudi yakashe masu ba, walima sosai yashirya wadda koda bikinshi beyita ba. Masu abinci na musamman aka dauko domin suyi abinda za'aci wajen walimar suna.


Ranar suna takama asabar yaro yaci sunanshi Nabeel Lamido Saraki, da misalin karfe daya da rabi abokan Saraki suka halarci gidanshi domin suci abincin da aka tanadeshi saboda su. A harabar gidan aka kafa rumfuna.


Mutanan da sukazo wajen basu kirguwa, haka kowa yarika taya Saraki murnar samun karuwa, anan kowa yazauna masu raba abinci suka fara aikinsu, se abinda kakeso zakaci. Lemuna gasunan kala kala.


Acikin gida kuwa mutanan da sukazo basu da yawa, yawancinsu duk jama'ar Gaje ne, domin su Maimuna basuda wasu mutane, ko makwaftansu bata mu'amala dasu sosai, hakan yasa ba kowa ne yazo ba, sede wasu daga cikin abokanshi sunzo da matansu hakan yasa taron yakara armashi.


An raba abubuwa mejego tayi kyau harta gaji ita da danta, Lawisa ma tayi kyau, haka kowa yaci yasha, masu diba suka diba suka tafi dashi, bayan taro ya tashi masu aiki suka fara gyaran gida, kasancewar sunada yawa cikin lokaci kadan suka gama,gida yadawo kamar ba'ayi taro ba.


Haka suka cigaba da renon Nabeel cike da kauna, Saraki komai nashi ya maida sunan Nabeel ajiki, haka ya saimashi share a banki da kamfanoni, account guda ya bude mashi yana saka mashi kudi aciki duk wata. Babbar super market dinshi ma Nabeel ya barma ita. Duk wata riba da aka samu a account dinshi ake sakata.


Haka yaro yataso cikin gata gaba da baya, kyanshi se kara fitowa yakeyi, yana kama da Maimuna, kuma yana dan kama da Lawisa, har mamaki Lawisa take tana fadin kinga yaron nan yana dan kama dani, Maimuna tace kinsan ai ni dake muna dan yanayi shiyasa zakiga haka, Lawisa tace haka ne, sede kunfi kama dashi sosai, kamar ma seya fiki kyau.


Maimuna tace kinsan wani abu? Wallahi har tausayin Abban Nabeel nakeyi yanda yake nunama Nabeel so, yanzu fa komai nashi yamaidashi da sunan Nabeel, danayi mashi magana yacemun yayi haka ne saboda mutuwa.


Yasan yana da kudi sosai, idan har ya mutu yan uwanshi zasu iya cutar da Nabeel, amma idan sukaga komai na kadararshi sunan Nabeel ne dole zasu hakura. Wata takarda ta mikama Lawisa tana fadin kinga nima kyautar da yayi mani saboda na haifa mashi da.


Dariya Lawisa tayi tana fadin kina nufin yabaki gidan manshi daya? Kai Maimuna ta daga tana murmushi. Jinjina kai Lawisa tayi tana fadin dama nafada maki, zaki ji dadin rayuwarki, yanzu bagashi ba cikin lokaci kadan kinzama babbar hajiya. Ni daga yanzuma hajiya zan rika kiranki duk da bakije makka ba.


Maimuna tace itama zamuje kuma hadake, yace sena yaye Nabeel zamu tafi gaba daya. Guda Lawisa tayi tare da shewa tana fadin, lallai bariki tayi mana rana, dole mu so Nabeel, domin ta sanadiyarshi gashi arziki yana fito mana ta ko ina.


Dafa Maimuna tayi tace inaso ki bude kunnanki kiji abinda zan fada maki. Naji kina maganar wai Yaya yafara baki tausayi saboda Nabeel ba danshi bane. To wallahi idan ma zaki cire wannan tunanin aranki kicire.


Domin babu abinda ze haifar maki se damuwa, arzikin da kikeso kisamu ya gagareki ci, duk duniya babu wanda yasan da wannan maganar se mu biyu, ko uban yaron besani ba, dan haka zamu bata matukar kika kara mani maganar nan. Maimuna tace insha Allah daga yau nadena. Dariya suka sa.


Tun daga ranar Maimuna bata kara tada maganar ba, haka suka cigaba da more rayuwarsu, kudi masu yawa Maimuna tabama Lawisa tafara kasuwanci, sosai arziki ya wuce na da, ganin harkarsu tafara kwari yasa Saraki yakara mata jari tafara fita waje tana saro kaya.


Gaje take bama wasu tana dora ribarta itama tana saidawa, kafin kace me, Gaje takara zama babbar hajiya, shiyasa take son su Maimuna, mutane da yawa sun san Lawisa saboda tana kawo masu kaya kala kala, kuma bata sama kayanta kudi dayawa, domin Lawisa tace tafison suna akan kudi.


Lokacin da aka yaye Nabeel haka Saraki ya biya masu kujerar makka su biyar, suka tafi, gidan ma kulleshi akayi domin hada Babaye aka tafi. Bayan sun dawo suka cigaba da renon Nabeel cike da so.


Lokacin da Nabeel ya isa shiga primary haka aka sashi private school me tsadar gaske, sede sam Nabeel baya maida hankali akan abinda ake koya mashi, sanin irin son da Babanshi yake mashi yasa babu me tabashi acikin malamansu.


Haka Nabeel yataso cikin gata islamiyya ma malami Saraki yadauko mashi yana koya mashi agida, sede duk abinda zeyi malamin be isa ya dokeshi ba, domin Nabeel ko fada be sani ba bare duka.


Babaye kuwa harkarshi ta bin mata se abinda yaci gaba, domin yanzu har kwana suke zuwa suyi agidanshi, kuma har yanzu Saraki besan yanayi ba, domin yasan lokacin fitarshi da dawo warshi. Umman Nabeel ce kadai tasan yana kawo mata.


Lawisa kuwa yanzu abun nata yazarce tunanin me karatu, domin bata dauki aikata zina abakin komai ba, fitar da takeyi waje yasa ta koyo harkar mata, shiyasa yanzu tadena neman maza sede mata. Kasancewar sunada Gaje yasa take samun kayan gyara sosai.


BAYAN WASU SHEKARU


Abban Nabeel ne da Ummanshi sukaje graduation din Nabeel na gama secondary school dinshi, da gudu ya rugo ya rungume Abbanshi jikinshi sanye da rigar graduation, yayi matukar kyau, gashi fari kuma dogo. Bayan an kammala haka suka dawo gida cike da farin cikin kammalawar karatuni na gaba da primary.


Wata sabuwar mota me tsadar gaske Abbanshi yabashi amtsayin kyautarshi. Sosai Ummanshi tayi farinciki, Nabeel kuwa rungumeshi yayi yana murna. Umma ce ta kalli Abbanshi tace amma de a waje zaka samar mashi gurbin karatu ko?


Murmushi yayi yana shafa kanshi yace gaskiya yanda nakejin Nabeel bazan iya barinshi yayi tafiyar kwana daya batare dani ba. Kinga kuwa bazan iya kaishi waje yayi karatu na tsawon shekaru 4 batare da yana kusa dani ba.


Duk da nasan akwai karatu a waje, amma gara yazauna kusa dani yayi karatunshi, ya kwana gida yaje makaranta nasan idan yagama gida zedawo komin dare ya kwana. Wannan dalilin ne yasa ban kaishi makarantar kwana ba.


Murmushi Nabeel yayi yace nima Abba banason zuwa ko ina, nafiso kullum ina ganinka, kuma ni banason zama cikin turawa nafison hausawa yan uwana. Hannunshi yakama yana murmushi yace yauwa yarona, babu inda zakaje.


Murmushi Umma tayi tana fadin nima ai nafiso yazauna kusa dani. Nabeel yace ammade Abba kaga abokanai na agidansu sunada part dinsu amma gashi nagama secondary zanshiga wata amma haryanzu ina cikin gida.


Dariya Abba yayi yace kada kadamu, yanzu kam ai kazama babba dole arika yima komai na manyan maza, zansa a gyara maka wancen part din na gefen dakina amma kuma Nabeel kofarshi ta wajen gida take, kode insa a hadesu amaido kofar ta cikin falo?


Shagwabe fuska Nabeel yayi yana fadin nide Abba abarshi haka, yanzu fa nazama big boy shikenan idan friends dina sukazo dole se sun shigo ta cikin gida, kuma idan kuna zaune falo haka zamuyita wuceku muna shiga da fita. Kagafa Saif agidansu part dinshi daban yake.


Dariya suka sa mashi, Abba yace e da gaskiyarka, nima inason privacy, shikenan yanda kakeso haka za'ayi maka, amma abinda nakeso ka dage kayi karatu sosai, kuma malaminka me koya maka karatu zecigaba da zuwa kafin exams dinku ta fito,


Idan kafara zuwa makaranta seyarika zuwa week end, nafiso kataso da iliminka duka biyun. Kallonshi Umma tayi tace haba Alhaji, yanzufa Nabeel ya
girma ina yake da lokacin karatu biyu, abinda yasamu yana karami ai ya isa, so kake abokanshi surika mashi dariya ana zuwa koya mashi karatu?


Nabeel yace e wallahi Abba, nide ya isheni haka, nasan abubuwa da yawa ina yaro, zamurika karatu dasu Saif idan mundawo daga makaranta. Kallonshi yayi Nabeel yace plsss Allah zamuyi karatun.Jinjina kai Abba yayi badan yaso ba, sedan bayason bacin ranshi ya amince.


A washe garin ranar Abba yasa masu aiki suka gyara mashi part dinshi, duk wani abu na bukata seda aka samashi yanda kasan gidan me mata. Yayi kyau sosai, Umma da kanta tasa Gaje ta samo mata wata budurwa wadda zata rika gyara mashi part dinshi tana kula da komai nashi.


Babu bata lokaci Gaje ta samo mata wata yarinya a kalla zata kai shekaru 16, wani daki dayake kusa dana masu aikin gidan aka bata, hatta da kayan sawa seda Umma ta siya mata da kayan kwalliya domin Nabeel yace bayason kazama.


Sabuwar waya tabata tasa mata number Nabeel shima tabashi tata saboda idan yana nemanta, duk wasu sharudda seda Umma tafada mata, tun daga gyaran dakinshi, wankin bandaki, da gyara mashi kayanshi duk itace zata rikayi.


Yarinyar me suna Sa'adatu ana kiranta da Ada,sosai tayi mamakin irin aikin da aka sata, a tunaninta namiji yakamata ace ansa wannan aikin amma aka sata. Sede kuma data tuna kudin da Gaje tace za'arika bata yasa tayi murmushin jin dadi, domin dubu 30 Umma tace zata rika bata duk wata.


Kuma tace matukar tana kula da Nabeel sosai zata iya kara mata. Murmushi Ada tayi tana fadin wannan kudi sekace me aikin gwamnati? Ga sababbin kaya, ga kayan kwalliya, ga kwanciya aguri me kyau, ga abinci me dadi. Lallai nima nakusa shigowa gari. Me ake da zaman kauye.


Tun daga ranar Ada tafara yima Nabeel aiki, duk abinda yake bukata idan bayason shiga cikin gida to ko karfe nawa ne haka zekira Ada takawo mashi koda tafara bacci, haka kuma hatta da ruwan wanka itace zata hada mashi, yanda kasan wani Yarima.


A hankali Ada tafara burge Nabeel, cikin lokaci guda sha'awarta tafara darsuwa a zuciyarshi, sede alokacin yadauka ba wani abu bane shiyasa ya share domin duka alokacin shekararsa 22 domin yashiga makaranta da wuri.


Ana cikin haka ne yasamu admission a ATBU bauchi ze karanci Micro biology. Lokacin daya fadama Saif shima yace abinda ze karanta kenan, sosai sukaji dadin samun course daya. Haka Abbanshi yabashi makudan kudi domin yaje yayi siyayyar abubuwan dayake so, dan yasa ayi mashi komai sede kawai yafara zuwa makarantar.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻

Nah
Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)


www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey


Part. 30 ⏩ 35


A ranar monday Nabeel yafara shiga makaranta, lokacin daya isa bakin depertment dinsu gaba daya mutanan dasuke wajen seda kallonsu yakoma kanshi, tundaga tsayuwar motar kowa ya kosa yaga wanda zefito daga motar, domin motar kanta abun kallo ce.


Ya dade befito ba, dayar kofar aka bude sega Saif yafito cikin kananan kaya masu masifar kyau da tsada,fuskarshi dauke da bakin glass shima daga ganinsa zeyi tsada. Nabeel ne ya bude kofarshi yafito, ai gaba daya sakin baki sukayi suna kallonshi. Shigarshi da Saif iri daya, yanda sukayi se sukayi kama da yan biyu.


Murmushi yasaki suka rufe kofar, tare da takawa zuwa inda sukaga mutane suna shiga domin ganin malaminsu yashiga. Haka suka samu waje suka zauna, duk yan matan dasuke wajen rabin hankalinsu yana kansu Nabeel. Haka malaminsu yafara da introducing kanshi sannan yasa kowa yatashi yayi introducing kanshi.


Bayan kowa yagama haka yacigaba ta gabar masu darasinsu. Bayan yagama kowa yafito, alokacin wata mota ta tsaya, murmushi Saif yayi yana fadin shegen kaya seyanzu ya iso. Nabeel yace wanene? Saif yace wannan friend din nawa danake fada maka munyi primary dashi Najib.


Murmushi Nabeel yayi yace ok naganeshi. Najib yana fitowa yazo suka rungume juna shida Saif, hannu ya mikama Nabeel suka gaisa, jerawa sukayi suka nufi wasu kujeru suka zauna. Gabatar da Nabeel Saif yayi wajen Najib kara gaisawa sukayi, nan suka cigaba da firarsu.


Saif ne yace Nabeel tsaya kaga wannan film da nake fada maka na kalla jiya, Najib yace Saif kaifa dan iska ne kada ka koyamashi kallon irin films dinka. Dariya Nabeel yayi yace kyaleshi ya nunamun yanzu ai seda kallo.


Saif yace kai bafa irin film din daka sani bane, wannan bakowa zaka bari ya kalla ba, kuma yafi dadin kallo idan kayi shirin bacci kashige bargo. Nabeel yace wane irin film ne haka? Saif yace kaide tsaya ka gani.


Mika mashi yayi yana dariya, saurin mika mashi wayar Nabeel yayi yana fadin wallahi nayarda kai dan iska ne, aini bantaba kallon irin wannan iskancin ba tunda nake. Saif yace wallahi abokina zakaji dadin kallonsu. Nabeel yace nikam bazan kalla ba.


Ai ko Ada tafi wannan matar kyau wallahi. Najib yace wacece Ada kuma? Kada kace mani sunan babynka ce? Kallonshi Nabeel yayi yace Baby kuma? Adar? Lallai ma yarinyar da take mani aiki ce fa. Dagajin yanayin maganarshi zakasan akwai yarinta aciki da tsabar shagwaba sosai, domin su Saif sun girmeshi.


Dariya Saif yasa yana fadin wallahi na lura su Umma sun shagwaba ka, wato har me aiki suka aje maka? Yatsuna fuska Nabeel yayi yace komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login