Showing 6001 words to 9000 words out of 29040 words
Chapter 3 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt
sauka akan wani babban mutum kyakkayawa dashi, gashi dogo fari, sede ga duk kan alamu yadan manyanta.
Saurin dukawa yayi yana fadin dan Allah kiyi hakuri ina amsa waya ban kula dake ba, Maimuna kuwa batama san yanayi ba, ta shagala wajen kallonshi,dariya Lawisa tayi ta tabo Maimuna tana mata nuni alamar ta tayashi kwasar kayan.
Saurin dukawa tayi tana fadin haba dan Allah kabarshi zan kwashe ai bakomai. Bayan sun gama kwashewa yakara bata hakuri tace bakomai, Lawisa takama hannunta tana fadin mungode, muje kada yaron yayita jiranmu.
Haka suka wuceshi, shikuma yabi Maimuna da kallo. Suna tsaye bakin titi Maimuna tana fadin haba Lawisa, kinsan yanda yatafi da imanina kuwa, shine zaki wani jawoni ko gama gaisawa bamuyi ba, kika sani ma koyace inbashi number ta.
Lawisa zatayi magana sukaji ance haryanzu baku samu abin hawa bane? Saurin juyowa sukayi, Lawisa tana fadin wallahi kuwa. Murmushi yayi yace to muje in aje ku mana.
Haka suka saka kayansu Lawisa tashiga baya Maimuna tashiga gaba, haka suka rika nuna mashi hanya har suka isa. Murmushi yayi yace nan ne gidanku kenan? Lawisa tace wallahi kuwa kaga dan gidanmu nan, shima haya mukeyi.
Jinjina kai yayi yace amma naga gidan akulle ku kadai ne aciki? Lawisa tace mukadai ne aciki yanzu ma daga shagon mu da yake kasuwa muke kasan muna saida abinci ne. Kallonsu yayi cike da tausayi yace Allah sarki.
Gashi yanzu ina sauri, amma idan kun bani dama zanso indawo domin inji kadan daga cikin labarinku. Lawisa tace lah! Ai bakomai, amma idan zakazo sede kazo da dare koda yamma sosai, domin da rana bama nan.
Yace toshikenan, nagode, ni sunana Alh, Lamido Saraki, ku kuma meye sunanku? Ni sunana Lawisa, ita kuma Maimuna, murmushi yayi yace Maimuna sarkin yin shiru ba, da alama batada hayaniya.
Murmushi tayi tayi kasa da kanta batace komai ba, bude kofar Lawisa tayi tana fadin to sekazo mungode. Maimuna ta bude kofar tana fadin mungode fa. Murmushi yayi yace bakomai, amma samun number dinki kada inzo inrasa yanda zanyi.
Bayan tasa mashi sukayi mashi sallama suka shige gida. Suna shiga suka saka dariya tare da rungume juna. Lawisa tace se kawata, ai dama nafada maki wata rana semun shana, ke kinga yanda wannan Alhajin yamace a kallonki?
Maimuna tace wallahi ya hadu, ai da naji haushi da kika jawoni. Lawisa tace ai nasan seya biyomu shiyasa na jawoki. Zama Maimuna tayi tabuga tagumi tana fadin Allah de yasa beda mata. Dariya Lawisa tayi tana fadin haba kawata.
Meye naki na saurin karaya? Ai koyana da ita wallahi se tabar gidanshi, mune fa? Haba idan har na barki kika zauna da kishiya ashe iskancina be kai ba. Haba munga jiya, munga yau, gobe ma insha Allah semun ganta. Kede kibari yashigo hannu.
Maimuna tace amma de ba aure zamuyi ba ko? Zama Lawisa tayi tana fadin bangane ba? Kema kinsan daga ganin wannan mutumin beyi kama da yan duniya ba, da ace dan hannu ne, yana kawomu seya shigo.
Dan haka inaso ki aureshi kawai. Maimuna tace ni bazan iya aure in kyaleki ba. Lawisa tace aiko dole kiyi aure, idan kikayi aure nima zan ji dadi, ni kobanyi aure ba zan iya zama haka, domin kullum sabuwar kyankyasa akeyi ta yara maza.
Kinga idan har kikayi aure dole a sama mani babban gida inzauna aciki, domin bazan iya biyoki muzauna tare ba, domin bazan iya kawo maza gidan matar aure ba. Ni kuma nafi karfin inbi namiji inda yake, sede shi yazo gidana yagama yatafi yabarni.
Allah de yasa yace yana sona. Lawisa tace dole ma ze fada, kede kibashi daga nan zuwa kwana 3. Ina me tabbatar maki baze wuce gobe bezo nan ba. Dariya suka sa Maimuna tana fadin Allah yasa.
Alh, Lamido Saraki. Haifaffen garin bauchi ne, shi kadai iyayenshi suka haifa, bayan yagama karatunshi a jami'ar garin bauchi iyayenshi suka rasu, kasancewar beda wasu yan uwa yasa yacinye gadon iyayenshi.
Haka yafada harkar kasuwanci, cikin lokaci kankani yazama me arziki, ya gina katon gidanshi a unguwar Tambari sede ba cikin estate din yake ba, babban fili yasamu yayi gininshi me kyau yana da gidajen mai guda 3, sannan yana da mayan super market guda 2, haka kuma yana siyen manyan motoci yana badasu ana mashi haya dasu.
Manyan DAF dinshi 2, suna legos ana aiki dasu, harkar kasuwanci babu wadda bayayi, yana da manyan store kayan abinci ne kawai aciki. Alh, Lamido ya dade beyi aure ba. Babu abinda yake tsoro se halin matan zamani.
Domin yaso ace yayi aure tun kafin yayi arziki haka, amma ayanzu yasan duk wadda zata aureshi to saboda dukiyarshi ne. Shi mutum ne meson temako, duk juma'a seya kai ziyara gidan marayu da asibitoci.
Mutane da yawa abokan kasuwancinshi suna mashi tallar 'ya'yansu, sede sam yaki amincewa da tayinsu, domin yasan suma saboda kudinshi ne suke so su hada zuri'a dashi.
Mace ta farko daya aura diyar wani me kudi ce, ganin mahaifinta yana da kudi yasa yayi tunanin kudinshi bazasu tsone mata ido ba har taso cutar dashi. Aurensu ko shekara beyi ba yago tana mashi sata.
Kuma ba kana nan kudi take dauka ba, lokacin daya kamata rana ta karshe, aranar ne ya saketa, dama bata da ciki. Ya dauki tsawon shekara 3 bayan rabuwarsu bekara kula kowa ba. Wata rana yadawo daga unguwa yaga wata yarinya budurwa tana bara.
Bayan ya tsaya yabata sadaka seyaji yarinyar ta kwanta mashi, gatade budurwa amma kuma tana bara, haka yanemi gidansu, seya gano talakawa ne sosai, nan yasa aka gyara masu gidansu ginin bulo, kuma yabama mahifinta jari, shida mamanta.
Bayan wata guda aka daura aurensu, babban dalilin da yasa ya aureta saboda talaucinsu, domin ya auri yar gidan masu kudi beji da dadi ba, shiyasa yace bara ya auri talaka yasan tasan wahalar rayuwa bazata taba bari tayi wasa da damar data samu yanzu ba.
Kamar gaske suke zaune da ita lafiya, bayan shekara 1 da aurensu ta fara canza hali, babu abinda bata satar mashi, tun daga kayan abinci, kudi har suturarshi dauka takeyi, idan yau ya cika store din gidanshi da abinci bayan kwana 2 idan yaduba seyaga an kwashe rabi.
Haka yarika binta har ranar da yakamata kuru kuru, yafita kasuwa se yayi mantuwa yadawo, yana zuwa ya iske ana loda kayan abinci za'a tafi dasu. A nan hankalinta yatashi tafara kuka tana rokonshi.
Babu bata lokaci ya sallameta ita da megadinshi domin hadashi ake hada baki. Godiyar da yayima Allah ma bata da ciki. Haka yashiga daki kamar karamin yaro yarika kuka, babban abinda yake damunshi shekaraunshi sekara tafiya suke amma haryanzu beda da. A ranar yasha kuka.
Kuma tun daga ranar aure yafitar mashi arai, haka ya maida hankalinshi kan kasuwancinshi, ahaka ya shekara 2 babu mata. Gidanshi dagashi sewani mutum dayake zaune a BQ din gidanshi, kuma shine yake kula mashi da gida.
Sunanshi Babaye, sun kai shakara 2 dashi, shima beda iyali dan asalin wani kauye ne dayake Darazo.Wata rana Alh, Lamido yadawo daga unguwa da dare dede zeshigo cikin garin bauchi ya hadu dashi abakin titi kwance kamar matace. Harya wuceshi yadawo, domin akwaishi da temako.
Babu bata lokaci yadaukeshi yasashi a mota suka shigo gari, wani karamin asibiti ya kaishi, bayan likita ya dubashi yace yunwace da tsananin wahala sukasa shi suma, amma zuwa da safe ze farfado.
Haka yatafi yabarshi wajen likitan bayan yasiyo mashi tea da madara da biredi yace idan yatashi abashi kafin yazo da safe. Kwananshi 3 ya warware, bayan ansallameshi suka nufi gidan Alh, dashi.
Bayan yayi wanka yabashi wasu kaya daga cikin nashi yasa. A nan ne yake fada mashi labarinshi, da kuma yanda yafito daga kauyensu yayita tafiya har Allah yate makeshi wasu masu motar kaya suka daukoshi suka kawoshi Darazo, daga can ne yarika tafiya har yakusa shigowa bauchi yafadi ya suma. Kuma yasheda mashi beda iyali tunda barayi suka kashe mashi matar be kara aure ba, hakan ne yasa da barayin suka matsa mashi yabaro kauyensu.
Sosai Alh, ya tausaya mashi,kallonshi yayi yace Babaye idan zaka iya zama dani babu damuwa, sede banida mata............Labarinshi shima yabashi, sosai ya tausaya mashi, Babaye yace bakomai nizan zauna da kai bisa gaskiya da amana.
Alh, yace shikenan akwai wasu dakuna acan bayan gida, zaka iya sauka acan, akwai komai na bukata, ka iya girki? Murmushi yayi yace sosai ma, Alh, yace to akwai kitchen zan hada maka kayan girki, ina ganin zefi maka sauki karika girki da kace zaka siya.
Dan ni a waje nakecin abinci, idan kuma kafison na siyen badamuwa zan rika baka kudin abincin. Babaye yace a'a nafiso nayi girkina. Alh, yace to ai shikenan, kayan sawa kuma suma zan kawo maka.
Kafin kasamu wata kaga semusha biki ko? Dariya yayi yace ai Alh, tunda narasa iyalina aure yafitar mani arai, nafiso na zauna haka. Alhaji yace to Allah ya rufa mana asiri,zaka rika kular mani da komai na gidan nan.
Dama ni banda megadi tunda na kamashi yahada kai da matata suna satar mani avinci shima na koreshi. Dan haka zaka rika kula da komai, ina fatan zaka rike amana? Babaye yace insha Allah bazaka sameni da cin amana ba.
Alh, yace bakomai muje inkaika masaukinka. Godiya Babaye yayi mashi suka fita. Tun daga wannan rana Alh, yasamu abokin zama acikin gidanshi, sosai yakejin dadin Babaye.
Yana kula da gidan sosai, har cikin gidan yake shiga yashare ya goge komai, dakin Alh, ne kawai baya shiga, idan kashigo gidan zaka dauka akwai mace. Idan Alh, yadawo da wuri haka zasu zauna suyita fira kafin kowa yatafi makwancinsa.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya cike da aminci, babu abinda Alh, baya siyama Babaye, kuma duk wata yana bashi albashin dubu 50, idan kasan Babaye abaya idan kaganshi yanzu bazaka iya ganeshi ba, da haka suka shekara 2 atare. Wannan shine takaitaccen labarin Alh, Lamido Saraki.
Kamar yanda yace zezo domin yaji labarinsu haka tafaru, bayan yazo yakira Maimuna tafito tayi mashi jagora zuwa ciki. Lafiyayyen girki suka shirya mashi da zobo me dadi. Bayan ya shari girki ya kallesu yace to nazo acika mani alkawarina.
Maimuna zatayi magana Lawisa tayi saurin fadin to kamar yanda kasan sunanmu, to mudin yan gida daya ne, wannan yayatace, daga ita se ni. Lokacin muna secondary iyayenmu suka rasu. Yayata Maimuna tayi aure da wani maci amana, ashe dama saboda gadonta yakeson aurenta.
Gashi bamuda wasu yan uwa sosai, ni kadai nake zaune agidanmu lokacin da tayi aure, seda yayi mata wayau ya cinye komai, sannan yayi mata dukan tsiya ya saketa saki 3, Allah yaso batada ciki.
Haka muka zauna cikin kunci, ganin rayuwar garin Darazo baya mana dadi yasa muka saida gidanmu na gado muka dawo nan dazama muka kama haya da kudin hannun mu, sauran kuma muka fara sana'ar saida abinci domin munfiso mu dogara da kanmu.
Sosai labarinsu yabama Alh, tausayi har seda yayi kwalla, kallon Maimuna yayi cike da tausayi yace kiyi hakuri kinji, Allah ze saka maki, lallai kinga rayuwa kamar yanda nima nagani...........
Labarin rayuwarshi yabasu, sosai suka tausaya mashi. Lawisa tace gaskiya Yaya kaima kaga rayuwa, bansan meyasa yanzu duniya ta baci haka ba. Kayi hakuri Allah ze saka maka.
Murmushi yayi yace yanzu kam yasaka mani, domin inaji ajikina haduwata daku alkhairi ne, inafatan zaku daukeni dan uwa? Lawisa tace zamufi kowa farin ciki kasancewar munsamu Yaya daga sama. Allah yabamu ikon rike amana.
Sun dade suna fira kafin ya aje masu kudi masu yawa yayi masu sallama yatafi. Bayan yatafi Maimuna tace lallai kanwata kin iya sharota. Wai ya akayi kika iya shirya wannan labarin haka? Dariya Lawisa tayi tace aike yarinyace shiyasa baki fahimci komai ba.
Maimuna tace kemafa da watanni kawai kika girmeni. Lawisa tace nade girmeki ko? To bara kiji, jiya banyi bacci ba seda na shirya duk abinda zan fada mashi. Kinga na farko de kinsan harkar da mukeyi, idan har mukace mashi bakitaba aure ba dole ze gane, kuma daga ranar ze tsaneki.
Amma yanzu yasan asalin halinki kinga baze zargeki da komai ba, idan kuma yasan mudin yan gida daya ne, kinga zefi daukata da daraja, dalilin da yasa nace mashi ke yayata ce kuma saboda nace kinyi aure.
Dan haka nasan abinda ze biyo baya dole yace yana sonki, domin naga hakan a idonshi. Maimuna mun riga da munsan labarinshi da irin yanda matanshi sukayi mashi. Dole zaki koyi zama dashi medadi.
Zakicire son kudinshi aranki, shida kanshi zerika maki mahau kaciyar kyauta, zaki tsare mashi komai na gidanshi, da kular mashi da harkar kasuwancinshi. Nasan a yanzu duk macen daze aura seya gwadata, koda ze rika aje kudi afili kirika adana mashi idan yazo kibashi, kada kibari kirika tambayarshi komai.
Ko kyauta yabaki kada ki amsa da wuri, iname tabbatar maki sekinga abun arzikin dazaki samu, kuma ni bazan taba yarda yace indawo gidanshi da zama ba. Nasan baze rasa gidaje ba, ze iya bani daya izauna.
Amma kafin kishiga gidanshi dole zamu cire mashi son duk wata diya mace, domin yanda yakeda kudin nan dole mata surika rubibi akanshi. Kibar mani komai a hannuna, ni nasan yanda zanyi. Sede ina fatan bazaki juya mani baya ba?
Hannunta Maimuna tariko tace haba Lawisa, tun muna yara muke tare, har abada bazan taba juya maki baya ba, bazan taba aikata komai ba seda shawararki, kinzamar mani yaya, kuma uwa. Kima dena tunanin haka zata faru. Rungume juna sukayi suna dariya. Lawisa tace, ina fatan duk lokacin da Allah ze hadani da mamata ace lokacin nayi kudi sosai.
Badan komai ba, sedan taga abinda tayarda yanda yazama. Maimuna tace wai dama Umma Asabe ba yar uwarki bace. Dariya Lawisa tayi tace kiyi hakuri duk tsawon taranmu bantaba baki labarina ba.
Nidin yar tsuntuwa ce, amma inada kananan shekaru alokacin bazan wuce shekara 9 ba, sede ina da wayau, bazan taba manta fuskar mama na ba, nasha wahala a wajenta, sede naji Umma Asabe tace tana tunanin bada aure aka sameni ba.
Sana'ar mamana saida abinci, shiyasa kikaji nakawo shawara akan murika saida abinci. Bansan waye Babana ba, kuma bana fatan insani, ayanzu wanna rayuwar tafiye mani komai dadi. Jinjina kai Maimuna tayi tace lallai kinada zurfin ciki.
Allah ya kyauta, kuma insha Allah babu wanda zeji wannan labarin. Lawisa tace shiyasa kikaga naki yarda indauki ciki, domin bazanso inyima dan dana haifa irin abinda akamun ba. Koda ace nasamu ciki kafin na haifeshi zan zubar dashi, bazan taba bari in haihu batare da aure ba. Haka suka cigaba da labarinsu har sukayi barci.
Tun daga wannan rana Alh, ya hanasu zuwa kasuwa saida abinci, duk wani abu na bukatarsu yana masu, soyayyar Maimuna tayi nisa a zuciyarshi, babban abinda yake burgeshi da ita duk yanda yayi mata kyautar kudi bata amsa, sede yakira Lawisa yabata.
Wannan dalilin ne yasa ya yanke shawarar ze aureta. Bayan yafadama Babaye shima yayi murna, dajin zeyi aure, haka yaje yasamu Lawisa da maimuna yafada masu yana son auren Maimuna, amma zasu shirya domin suje can garinsu ya gaishe da yan uwansu kuma yanemi auren ta acan.
Jin haka bakaramin data masu hankali yayi ba. Lawisa tace to ai hakan ma yana da kyau, amma kabamu nan da sati 1, semu shirya mutafi. Da haka yayi masu sallama yatafi. Cike da tashin hankali Maimuna tace yanzu meye dabara?
Murmushi Lawisa tayi tace dole mufara zuwa wajen boka, domin aurenku dashi baze yuwu ayishi anan ba,domin Alh, yanason yaga yan uwanki. Amma idan mukaje wajen boka zamu sashi ya kawar mashi da tunanin zuwa Darazo, kuma yasa mashi bin umarninki.
Da haka zamu samu ya aureki, sauran kuma sekiyi yanda nace maki. Rungumeta Maimuna tayi tana dariya tana fadin shiyasa nake kara sonki, kina son cigaba na. Yanzu ina zamu samu boka? Lawisa tace ai boka baya wahala, kede kibari zuwa gobe, akwai wata mata inda muke saida abinci kinsan muna mutunci da ita, to naga alamar yar bin malamai ce zanje gurinta seta rakamu. Da wannan shawarar suka aminta, suna fatan zuwan gobe domin suje wajen matar.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Part 15 ⏩ 20
Kamar yanda Lawisa tace haka ne yafaru, wajen matar sukaje tayi mata bayani, bayan tagama matar me suna Gaje tayi murmushi tace lallai Lawisa kin kawo kukanki inda za'a share maki hawayenki.
Kin ganni nan, ba dan narike boka nakan tudu ba dayanzu bana wannan sana'ar ta saida kayan mata, kina ganin de yanda mata suke tururuwar zuwa wajena domin su sayi kayana. Duk da bani kadai bace nake siyarwa anan amma dole duk wadda tazo gurina zata siya.
Nafi karfin shekara 5 a wajen nan, nasayi gidaje da yawa da wannan sana'ar tawa, kuma ba kowane ya tsaya mani ba se boka nakan tudu. Hakika kin burgeni yanda kika zo mani da wannan maganar.
Kuma zan temakeki, kizo gobe da safe wajen karfe 9 semutafi ina tabbatar maki da bukatarku zata biya, kuma idan har kuka rikeshi to baku ba sauran bacin rai. Sede yanada doka, inafatan duk abinda yanema awajen wadda zema aiki bazata hanashi ba? Lawisa tace haba ai duk abinda yakeso zamuyi mashi. Gaje tace toshikenan Allah ya kaimu goben.
Washe gari haka su Lawisa da Gaje suka nufi wani kauye mesuna Bununu, can cikin wani daji saman wani dutse anan bokan yake dazama. Zaune suke acikin bukkarshi. Tun kafin Gaje tayi mashi bayani yace yasan abinda yake tafe dasu.
Kallon Maimuna yayi yace kinaso a hana Lamido Saraki zuwa garinku ko? Surin daga mashi kai tayi, dariya yayi yace kuma kinaso acire mashi son kowace mace aranshi se ke kadai ko? Nan ma daga mashi kai tayi.
Wata irin dariya yayi yasaka hannunshi cikin wata kwarya sega hoton Saraki yafito, nuna masu yayi yana fadin koba shi bane wannan? Lawisa tace shine. Dago kai yayi yace tabbas aikinki me sauki ne.
Sede ayanzu zamuyi maki daya, amma na biyun baze yuwu ba harsekin aureshi, akwai abinda nakeso insaki. Wani garin magani ya dauko yana fadin ki tabbatar kinyi mashi abinci dashi kuma yaci ayau din nan, idan yawuce yau maganinki baze yi ba.
Kuma lomar farko kece zaki bashi ita, duk yanda bayaso kisan yanda zakiyi kibashi so daya, idan ba haka ba, maganin bazeyi ba. Se sharadi na biyu zaku bamu waje domin