Showing 24001 words to 25431 words out of 25431 words

Chapter 9 - Mahaukaci ko boyayyen masoyi complete by Maryam Yarmawa .txt

15 Dec 2024

2246

Da su Abba sukaji lamarin, nan Abba ya fara matsar hawaye yana "ai da baku wahalar da kankuba, da kun barni na mutu... Nan dai suka dinga kwantar mai da hankali.... Inda nan take safwaan ya Kira masu aikin Gina, inda za'a rushe gidan ayi ginin zamani... Kukan kunya mama ta dingayi tana godiya, inda su aziza dasu lubaba ana gefe ana hirar bayan rabuwa, har luba take basu labarin abinda yafaru...... annur dake tsaye sai ido yakewa minal da su taso su koma masaukinsu ya gaji.... Kamar umma tana zuciyanshi ta kalli minal da Aziza tace "yakamata Kuje ku huta, saboda gajiyar hanya, Aziza kamar jira take dama umma tayi magana, inda tayi wuf ta tashi tana eh umma nima barci nakeji, minal kuma tace"Aini umma yau a wajenki zan kwana"...... Dakuwa umma tayi mata tace "tunda ni kike aureba... Kibi mijinki... A hankali ta tashi, su luba aka rakosu kofar gida har wani yanga ake, dama tuni sun kashe sugar awarar sukayi sadaka... Nan dai minal suka shige mota... Luba ta mika mata Malika dake barci tace "sister minal bazaki barmin daughter dina ta kwana anan"..... Annur ne ya chafe cikin sarauta yace"ina, diyata bazata iya kwana mosquito ya cizeta ba ... Just gobe zamu dawo ai karku damu, nan ya dakko kudi masu yawa yabasu, suyi cefenan yau.... Sallama sukayi, suka wuce masaukinsu, dama guest house ne ... Inda minal tana zuwa ta kwantar da malika, ta hada musu ruwan wanka, suka shiga wanka tare..... Suna fitowa ta shafa mishi mai, ta taje mishi kai, sannan ta fito mishi da kana nun kaya, itama dressing tayi cikin wani gown mara nauyi... Annur tsaye yake jikin madubi yana murmushi... Inda minal ta rungumoshi ta baya tana "thanks you sweetheart for everything, samunka a rayuwa alkhairi ne, nagode da abubuwan da kayimin a rayuwa... Ashe kaine mahaukaci kuma BOYAYYEN MASOYI, wonderful... Ubangiji Allah ya biyaka da gidan Aljanna lalle, nayi dacen miji, mr blue eyes, now nazama MRS ANNUR, KUMA MAMAN MALIKA,.... murmushi annur yayi ya juya ya rungumeta yana fadin "ni nayi dacen mata kamila, mai tausayi, mai tafiya, komai Allah yabaki.... Ubangiji Allah ya barmu tare, inason mu rayu tare mu mutu tare baby...... Hawaye minal tafara, itama ta rungumeshi tsam.... Nan labari yasha bam bam.... 🏃‍♀️🏃‍♀️basu farka ba sai da sukaji kukan Malika. Kowa so yake ya dauketa.. Annur ne ya goya malika... Yana lallashi, inda minal ta zauna tana mishi dariya🤣🤣🤣.....




****†"




Abubuwa sun faru, an Gina wa Abba tamfatsesen gida a cikin kwana, sannan harda rasuwar Abba ana gobe za' a tafi dashi india... Kuma a ranar luba ta gigice ta haifi danta namiji.... Nan hankali ya tashi, yan uwansu Abba sunzo dai koke-koke suke, inda sukaga su minal, nan kunya ya dinga kamasu... Gida yacika da su minal anata karbar gaisuwa, harsu Maman marayu dasu iyayen safwan duk sunzo.... Aziza kuwa saida ta wanke yan uwan babanta da soso da sabulu, wasu harda kuka, dakyar umma ta basu hakuri... Sannan tasa aziza a daki, tayi mata fada.... Minal ce ke kula da luba,saida akayi sadakar bakwai sannan kowa ya watse,wanda wasu yan kauye sun ga gida sukace ai sufa sunzo bazasu komaba, mama ce ta koresu, inda minal tace zasu dau umma su tafi da ita, umma tace subarta anan... Zasu zauna da mama dasu lubaba... Annur ne yasamo yan aiki guda biyu da tsohuwa da budurwa, sannan da maigadi, aka siya mota, aka nemi driver zai dinga zansu mama duk inda zasuje... Nan sabon kuka yadawo.... Godiya kam ba wacce ba'ayiba.......


Minal saida suka nemo inda MUTANEN da suka taimaki umma suke, sukayi musu Alkhairi mai tarin yawa.. Sannan ta nemo gidansu kawarta ummi, shima annur ya Gina wa Maman ummi dankareren gida, sannan yabawa ummi jari, tana gidan mijinta da tsohon cikinta......


Minal da aziza anzama manyan mata, inda sukasa taimakon marayu da marasa karfi agaba... Inda suka dau umma, sukaje umrah daganan suka wuce wajen danginta sunyi murna sosai da GANINSU... Nanma minal yayi musu abin alkhairi
*TARIHIN ANNUR*
(Kiyi hakuri, ina sane bansa da wuriba)


Annur da daya tilo a wajen sarkin zaria..... Wato mai martaba sultan abdullah.Wanda shima gada yayi a wajen mahaifinshi Dayake duk yan uwanshi matane, kuma shine dan fari.. Annur yayi karatunsa a UK.... Baisan komai kan sarauta ba, yafi maida hankalinsa akan kwallon kafa inda yayi suna... Kuma ya karbi lambar yabo.... Annur mutumin kirkine, kuma mai tausayi ya gado kyawun mamanshi wacce ta kasance yar gidan sarautar Agadaz... Yar dangi kyakyawa sunanta Hauwa... Ga kyawun hali.... Duk shima mai martaba yanada nashi kyawun
Mai martaba ya hada auren annur da saudat yar sarkin gombe.wanda saudat tanada shekara 26 a lokacin, tanada Jikin girma, kyakyawace ba laifi . Dayake tun suna yara sukayi alkawarin aurar dasu, annur shi bayaso, saboda tun yana yaro, yasan saudat bata da junta amma haka yabi umarnin iyaye, ita kuma saudat tana mutuwar sonsa. . amma batada Halin kirki ko kadan ga nuna tsanar talaka da bakin kishi.... Kuma batason yara.... Haka ta tashan kwayoyi tana zubar da cikin, tun annur yana kokarin cusata a ranshi, harts fice mishi a rai, Domingo fitsararta, shiyasa yadau alwashin auren yan talaka, .... Rayuwar annur ya canza lokacin da yaje kano ya tsalla ido yaga minal, nan yace zai iyayin komai don sonta, don kuma ya zauna da ita.... Haka yasa kanshi a hauka, ko bikin luba shine prince din da akata Kira yazo baizo ba... Saboda lokacin bayason asirinsa ya tonu... Duk lokacin dayaga minal sai ya canza kayansa zuwa mahaukaci, tana tafiya zai dawo normal... Hatta kudi ya bawa yara suyi masa wakar hauka..... Kuma shine boyayyen masoyin nan.......




*Bayan shekara uku*


Minal tanada yara uku Malika da twins Sultan da imran inda sukaci sunansu mahaifin annur amma suna cewa sultan, yerima while imran kumma Abba.. Kyawawan yara dasu... Lokacin haifuwarsu, har hawaye annur yayi da yake rike hannunta tana nakuda, sai cewa yake thank you baby, Allah yayi miki Albarka...... Yanzu dai dukansu suna gudunsu ko 'ina...... Inda yaran sunfi jin turanci ma... Aziza ma tanada yaranta biyu mata duka... Fatima da Hindu.... Rayuwarsu suke cike da sha'awa... Dangin safwan suna son Aziza duk da tanada fada har yanzu.... Don ita bata barin ta kwana.... Suna kula dasu ummah da gidansu amaru.... Inda suka dawo da umma da mamah abuja, suke zaune a dankararren gida harda masu aikinsu... Da wasu yan uwan mamah.... Rayuwa tayi dadi....


Minal tazama babbar mace, inda taso komowa makaranta amma fafur annur ya hanata.... Wai sunada kudi Tunda tanada ilimin karatu da rubutu ai shikenan... Business kawai takeyi wanda suka hada hannun jari da Aziza suka bude kamfanin takalmi da kaka, wanda yayi fice daga Nigeria har kasar waje.....


Su luba ma duk sunyi aure, suna zaune a kano... Suma annur da safwan sun bash jari....




Annur da minal suka aje yaransu a Gidan mommy, suka tafi honeymoon kasar germany.... Inda suke ta dizzar soyayyarsu tamkar sababbin amare... Ko rabuwa da juna baso so suyi... Kullum suna makale da juna, suyita daukar selfie da videos.... Hatta kitso annur yake zama yayiwa minal...... Sai da minal tafara laulayi sannan suka dawo gida Nigeria..... Annur ne yake kula da ita... Har takai watan haihuwarta ta haifo diyarta santalleliyar mace inda taci sunar momyn annur hauwa... Suna ce mata "beauty"..... Suna kam anyi taron suna, inda anyi gayyata..hardasu saudat, da tayi wani auren Amma ba haihuwa, kuma cikin kishiyoyi take, sai gori suke mata. Nan minal takara suna taxama tauraruwa wanda matan gwamnoni da ministoci suke son kulla Alakar kawance da ita.....
Duka family dinsu sukaje umrah, sukayi wasu Abba adu'a, sannan sukaci gaba da taimakon Gidan marayu....




Rayuwa suke cike da so da kauna.... Inda nake musu fatan dorewa har abada......






Alhmdlh
*nan na kawo karshen littafin mahaukaci ko boyayyen masoyi, inda nayi kuskure, ubangiji Allah ka yafemin*
Allah yasa sakon da yake ciki ya isa inda Akeso...


*MASOYA INA GODIYA, DA BAZARKU NA TAKA RAWA.... KUMA NAGODE BISA ADU'OINKU.... NAGODE BISA KAUNAR DA KUKA NUNAWA LITTAFIN NAN... WANDA YADAU LOKACI, KUKAYI HAKURI KUKE BIBIYATA... HARDA MASU KIRANA A WAYA DA WAYANDA NA GA KYATUTUKAN JIN DADI DA BAJINTA, WALLAHI BANSAN Hka littafin nan yayi suna ba har yafita kashashen waje, har kirana mutane daga chad! Cameroon, ghana, 🇳🇪 niger, da dai sauransu.... Nagode Allah ya bar zumunci, sai kun kara kina a sabon littafina mai suna "LOKACINE"
(Rikicin cikin gida) Labari wanda yasha babban da sauran litattafaina... Is coming very soon......


Ga MASU fatan Alkhairi ga num 07030772637
Pls a dinga sharing, saboda WAYANDA suke neman complete samu nagode

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login