Showing 12001 words to 15000 words out of 25431 words

Chapter 5 - Mahaukaci ko boyayyen masoyi complete by Maryam Yarmawa .txt

15 Dec 2024

2437

suka kutsa kai ciki


Aka budewa annur mota,aka shimfidamai cafet,kuyangi suna watsa fulawa,annur rike yake da minal da har yanzu bata farfadoba






A katon falo akayi masauki wanda fadin haduwar falon nan karyane,yan uwa da dangi suka zauna anata gaisawa da annur,anamai murnar samun mata ta kirki


Saudat ce tashigo daga ita sai dogan riga mai hannun singlet,tayi buzu buzu da gashinta;sai taunar cingum take,


Mamakine ya cikata da taga wata matasshiyar budurwa a cinyar annur,tana bacci,wani uwar ashar ta dibo tace kai annur aina kasamo karuwa ,daga bisani ta kalli mai martaba tace dad kana kallonsa da wata daba tasaba amma kayi shiru shiyasa nace an tsaneni wallahi antsaneni




Tsawa momy ta daka mata tace ke saudat ki shiga hankalinki,kamar yanda kike matar prince annur haka itama take awurinsa don haka kimana shiru kizauna,ko akwai sa,anki anan dakike mana shouting




Ihu saudat ta zunduma ta dora hannu akai tace nashiga uku anci amanata an hadamin munafurci wayyo dadyna




Cikin lallashi mai martaba yace saudat yahakuri ki zauna a warware matsalar nan




Harara saudat ta dakawa mai martaba tace anki azauna din wallahi dolema ya saketa donni ba,ayi ni don in zauna da wata yar talaka ba.




Annur ransa ya bace,amma yasan yana magana mai martaba zai taresa,yayi shiru yana shafa fuskar minal,


Dakyar aka roki saudat ta zauna tana kumbure kumbure da daukar alwashi iri iri




Mai martaba yace son inaso ka bani labarin yarinyar nan yar wacece,aina ka sameta kuma tayaya akayi ka aureta?kasan a tsarin gidannan ba auran yar talakawa ko wata bare ko?




Annur yaja doguwar zuciya yace,lokacin naje kano,don koyawa kano pillars wasan buga kwallo ina cikin motata,na hangeta tana tafiya,binta nayi har kofar gidansu na gani,na nemi labaribta naji,nasamu,tausayinsune yakamani,sai na fito mata a siffar mahaukaci,abin mamaki yarinyar nan bata kyamaceni ba,tanada hangen nasa haka ta aureni,namata abun bacin rai kala kala bata damuba,komai tasamu nawane,haka annur yabasu tarihin minal da yanda mahaifiyarsu ta bata,da yadda rayuwarsu tazama,da zaluncin da abba ya musu




Kuka aka dingayi,har mai martaba,banda saudat data tabe baki sai harare harare take tana magana kasa kasa wayasani ko karyama yake




Mai martaba yace allahu akbar gaskiya yarinyar nan yar kirkice don haka annur ka lura da ita sosai,ita kuma yayarta intana da burin cigabada karatu,saita zabi kasar da takeso ta tafi karatu duk abinda takeson karanta




Nan falon ya dauki tafi da sowa yayinda aziza ta fashe da kukan farinciki,dama akwai ranar da burinta zai cika?na karasa karatunta


Momyce ta rungumota tace yata karki damu wannan kadan daga cikin karamcin king estate house.








Mai martaba yace annur dauketa ku tafi gidanku,inyasa saudat tabiyoku daga baya ,Allah yamuku albarka.


Annur ya dauki minal cak,wani tsalle saudat ta daka tace wallahi ba,a isaba tab,lallema ,wallahi baza,a hadani dayar talakawa ba tab haka kurrum ta shafamin talauci ina.


Bawanda ya kulata,annur ya fita daga falon,bin bayansa aziza zatayi,momy tace a a kidawo daughter bazaiyu ki barni ni kadaiba daga yau kin zama yata tajini




Murmushi aziza tayi ta dawo tazauna akusa da momy tana tunanin ya yar uwarta zata tsinci kanta,i tunda tanason annur yana sonta aishikenan ba damuwa




Ahaka falo ya watse aka bar saudat sai zage zage take,momy tana danasanin auren annur da saudat diyar sarkin gombe








By
Maryam yarmama
[15/03 6:15 pm] Maryam Yarmama: Y *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*46☆50
By
Maryam yarmama


*Dedicated to*
My salmaty








Tukasu ake,motoci bibbiyu gaba da baya,hmmmm jinin sarauta,mai martaba,ne yakira annur yace prince ka shirya gobe akwai hadadden party dana hada muku,donhaka ku shirya
Murmushi annur yayi,yace Allah yaja zamani dad,godiya nake.
A hankali minal ta fara bude kyawawan idonta tana karyata,lamarin anya ba mafarki takeba,yakamata dai ace ta farka,kara bude ido tayi,sanyin a.c din motar ne,yasa jikinta ya fara kyarkyarwa,annur ya ciro suit dinsa yasa lulluba mata


Tashi tayi cikin kunya tace annur meyasa ka yaudareni?meyasa ka zabi kasamu farin cikinka fiye da nawa why annur,?kamin karya ka dora wa kanka ciwon karya




Annur yace minal nasan ku yayan talakawa ba kasafaffai kukeson auren masu kudiba,shiyasa na taho miki awannan sirfar kuma gaskiya nayi dace nasameki yanda nake bukata,kina da tawwakali,hakuri juriya,kin nunamin soyayya dan Allah,badan kudinaba?kuma saidai kiyi hakuri inada mata masifaffiya yar sarkin gombe ce sunanta saudat,saidai kiyi hakuri da halinta domin gida daya zaku zauna,


Murmushi minal yayi tace Allah ya bamu zaman lfy mai dorewa ,to dan Allah waye *boyayyen masoyin da ya taimaki rayuwarmu dana yar uwata*wlh inason ganinsa inmai godiya,




Murmushi annur yayi yace hmmmmm zagi ganshi watarana, nima kaina bansansa ba amma ina mishi godiya bisa kullarmin da wiffy dina.


Minal tace wallahi inason ganinsa,Ubangiji yasamakai da alkhairi,nima in Allah ya yarda saina yimai fiye da yadda yamin






Dariya annur yayi yace ameen my wife


Rufe ido minal tayida taffukayen hannunta tana murmushi


Wani tafkeken gida gari guda naga an nufa,gate ya bude da kansa,sojojine suke gadin gidan,sai sarawa annur ake,shiko yana daga musu hannu yana murmushi,harabar gidan abin kallone


Wajen ajiye motoci suka yi parking,bude musu akayi,minal ta kalli annur dayake taku daidai tace annur pls ka daina sawa ana budema mota,da kuruciyarka. Za,a dingama hidima yakamata ace komai kanayi da kanka,ba wanda yasan gobe, daukaka daga Allah ne,mulki daga Allah ne, yakan bawa wanda yaso,




Murmushin farinciki annur yayi,har hawaye ya ziraro a idanunsa yace ya Allah nagodema da ka bani minal,minal nagode da tunatar dani da kikayi,




Riko hannunta yayi yasa pasport a kofar dazai sadasu ga general falo,sunan minal ne a falon tafkeke ,a katon glass din hoton da akayi elergiment da sunan minal,minal tacika da mamaki




Haduwa iya haduwa falon yahadu,sai sambarka


Bangarenta annur ya kaita komai lemon green and orange colour ne part din ya mata kyau sosai,wanka ta fada ,tsullum taga annur a bathroom,kara tasaki ta tsuguna ta annur dan Allah ka fita,




Annur ya shagwabe fuska yace uhummm nima nazo anty tamin wanka,anty nifa badan iska bane




Minal dai tana rakube acikin bath tub,amma dariya take kasa kasa,bata ankaraba ya fado bathtub din,wani kara tasaki,




Amma ahaka ya mata wanka tana mammake jiki,ya goyota yana ai my wife yanzu babu kunya atsakinmu mun zama jini daya, kin manta lokacin dakike ban abinci a baki?




Minal ta tuno littafin data karanta na ma,aurata,kissa da kissina dashagwaba




Murmushi tayi tana bayansa daure da tawul,dan cizo ta gantsaramai a kunne,kara yasaki,tazame tafada kan gado tana dariya kanta a sunkuye,


Annur yace taho in shafamiki mai


Hararar wasa tamai tace tab sai kace wata baby anki wayon


Karbar man tayi tanashafawa,ta je wardrobe kaya tagani sunfi Kala dari ajere,wani doguwar riga ta hango pink mai adon fari da dankwalinsa sawa tayi,wow yayi masifar kyau ,fadin annur


Gaban katon madubi ta nufa,ta fara tsantsara kwalya,tana kallon annur daya kafa mata ido yana murmushi,martani ta maidamai,tadan sunkuyar da kanta alamun kunyatace dan Allah kaje kasa kayamana annur


Annur ya matawani kallo yace a chanzamin suna in bahakaba zamu shekara anan
Minal a hankali tace to *my husband*






Annur ya noke kai yace a a ba wannanba,


Minaltace to heart beatfa


Annur yace good ficewa yayi daga dakin yaje yasako riga t_shirt shima pink colour da farin wando




Shigowa yayi,minal tace kai yamukayi anko nidakai
Murmushi annur yayi yace aiduk kayan da kike dashi anan gidan inadashi,zo mudanyi hoto mana dear,kamota yayi,suka dinga daukar selfie,sannan ya mata ita kadai,kunyane ya cikata dama haka annur yake da iya soyayya?in Allah ya yarda ba wanda ya isa ya rabani da mijina


Karar fashewar abu sukaji a general parlour




Minal ta tsorata ainun,annur ko ajikinsa yace zamuje dear nasan bazai wuci mahaukaciyar nan ne tazoba don kadan daga aikinta


Annur ya rungumi minal suka wuce general falo,aikwa saudat ce dauke da katon wuka a hannunta,gashi tayi raga raga da hotan minal da akayi elergiment da sunanta




Annur yace ke dabbar inace kishi haukane,ko mamanki ita kadaice a gidanku,ai itama alfarmar wata taci




Saudat tace ni kake ciwa mutunci annur ta ubanka mai martaba kake zagi,tsohon najadu,mugu azzalumi




Annur yace zanso saudat ki fadi abinnan agaban mai martaba,yaji dama albarkacinsa kike ci,kuma tunda kika zagarmin mahaifi saina babbalaki a gidannan




Cikin karaji da takama tace bismillah inda jini aka haifeka kazo ka tabani wallahi dagakai har yar iskarnan da kuka gama wattsakewarku a titi sainayi ajalinku


Zuciya tadauki annur da nufin zuwa yawa saudat mugun duka,minal ta rije hannunsa tana kuka tana jijjiga kanka tace dan Allah karkaje,bakaga wuka bane a hannunta kar ruddun shedan yadauke ta yima illah




Annur yace kinga minal sakeni innunawa yar iskarnan kura kurenta




Saudat ta nufo wajen da kudu ta fara jibgar minal,tana yakushinta da dogayen faratanta na kanti,annur ya hankade saudat shima ya dinga jingarta




Kokuwa kakeji ,saudat tana ihu,da kukan saita illata minal,wuka salma ta dauka tana bin minal dashi,sai zagaye falon suke minal taga tashin hankali sai kuka da ihun kiran azizatake




Annur ne ya sha gaban minal ya boyeta abayansa,yana inkin isa ki kasheni tunda ke mahaukaciyace




Cikin huci saudat tace ka matsamin ko in hadaku tare in kasheku




Da gudu saudat ta nufi wajen ta cakawa annur wuka












By[19/03 11:14 pm] salmah pinky💅🏼💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*51-55
By
Maryam yarmama
Dedicated to
My salmaty










Cikin zafin nama,annur ya rungumi minal suka tsuguna,wukar tabi iska


Ran saudat yabace kamar tayi hauka tace wallahi kayi karya annur kaci amanata kazaba niko ita.




Annur ya wanketa da mari kyawawa guda uku yace nazabeta akan mahaukaciya irinki,aini ko zanyi butulci bai kamata inwa minal rabin rayuwata butulciba tasoni ina mahaukaci banda komai.
Amma kefa na tabbata da kece na rike miki hijab kamar yanda na rikewa minal da tuni zakisa a shekeni bakida asara


Ran saudat yabace cikin bambamin fada tace wallahi inkasan wani bakasan wataba,saina kashe minal din inyaso nima akasheni saime?




Minal dake faman rusa kuka tana bayan annur,annur ya juyo gareta yace masoyiyata kiyi hakuri nan gaba zan raba muku gida kizabi,state din dakikeso in rabamuku gida








Saudat tace a a ba gida zaka raba mana ba ranka zaka rabama asararre rago kawai,aini nazata zakamin tsinannen duka ashe zuciyarka a muce yake irin ta ubankane.




Ritse ido annur yayi dabadan alkawarin daya daukarwa mahaifinsa na rashin dukan yarinyar nanba dasai yaci ubanta da duka kuma ya duki banza abanza.,hannun minal yaja sukabar saudat awajen tana ta zage zage.










Tare suka shiga kitchen ,minal tayi shiru sai hawayene ke tsiyaya a kwaryar idanuwanta ta kalli,annur da fuskarsa alamun damuwa tace annur shikenan mun rabu da aziza kenan?




Annur yace kiyi hakuri karatu zata tafi kasar waje amma ai zata dinga zuwa hutu karki,damu da wannan zancen annur ya kwantarwa da minal hankali tadinga walwala








Ahaka suka dirji amarcinsu cikin jin dadi da kwanciyar hankali,minak tayi fresh tayi kyau,duk hantarar da saudat take mata bata damuba,ko wucewa minal tazoyi sai saudat ta bangajeta tayi wucewarta tana zaginta da nuna kyama a gareta








Minal ce zaune akan dinning,annur ya tafi kasar waje buga ball,tana danne danne wayarta *iphone*tanacin abinci fried rice a hankali,ji tayi an dauki abincin an watsa mata ajiki


Saudat ce tsaye tace ke yar talakawa jikar talakawa da akwai abinda yafi talauci dana kiraki dashi,anzo an zauna anacin abinda ba,a saba ba ,to ga wankina chan kije kimin








Minal tace zanyi karki damu da wannan but kisani talaka da maikudi duk ubangijin talikaine yayisu,kuma yayimu talakane bawai don baya kaunarmuba,bawanda yafi wani awurin Alllah,sai wanda yafi imani da tsoransa,don haka ki daina nuna bambamci dukanmu yayan adam ne da mamanmu hau,wa,u






Rike baki saudat tayi tace Allah?i see idon mage ta waye donhaka inzakiyi wa,szinki kije chan kofar massallaci ki dauki loudspeaker kiyi zakifi samun lada banza a banza kawai






Haka kullum daban rashun mutuncin da saudat take shukawa har annur ya dawo bata fasa halintaba






By
Maryam yarmama
[19/03 11:14 pm] salmah pinky💅🏼💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*56→60
By
Maryam yarmama


*DEDICATED TO*
SALMA ALI WADAH








®online hausa writters






Minal ce zaune a main parlor tana kallon zee aflam an sako wani film mai dadi yatafi da hankalinta,ji tayi an zagayota bayanta an, rufe mata idanuwa.




Tasan waye murmushi tayi tace nawan harka dawo kenan.




Aziza tace to yar soyayya bashi bane nice nan.




Tsalle minal ta daka tajuyo,cikin murna tace oyoyo yar uwa ashe da rabon zamu hadu kafin ki tafi london?


Murmushi aziza tasaki tace kinsan gobene tafiyarfa shekara uku zanyi,kinga lokacin saidai inzo in tadda yarki ko dangi dan shekar biyu






Minal jikinta yayi sanyi tace aziza shikenan nida ganinki sainan da shekaru uku ai sai mai rai.




Aziza tayi murmushi tace meye zaki damu bayan ga farincikinki a kusa,abinki kwadeshem




Dariya minal ta kyalkyale dashi,saudat ce tafito daga shashinta tana tafiyar kasaita,ta kalli minal tace ke yaki kizo ki wankemin inner weaes dina.




Har minal tatashi azixa ta daka mata tsawa ta koma ta tashi taje gaban saudat ta nunata dadan yatsa tace ke ba baiwarki bace ,kuma bakida iko akanta mijinkune yake da iko a kanta bawai ke ba,kuma kisani kinyi nafarko kinyi na karshe karki karasata aiki




Saudat tace keeeeeh kinsan wacece nikuwa au minal din bata baki labarinaba?




Dariya gami da tafi aziza tayi tace tabbas nasanki ke mara kunyace,mai zagin iyaye ,yar rainin,hankali,raina miji,saike,kuma saidai ki nuna mana dukiya that all




Ran saudat yabace tunda take ba wanda yataba jefarta da munanan kalamai sai aziza daga hannu tayi da niyyar dauke aziza da mari,aziza ta yarfar da hannun tace keeee?karki kuskura ki taba lafiyar fuskata inbahaka saikinyi nadama.




Minal cikin kuka tace aziza zoki fice ki tafi banson tashin hankali


Cikeda mamaki aziza ta kalli minal tace minal ina matsayin ysr uwarki kike korata kin zabi ki zauna kita bauta,?








Cikin kuka minal tace eh tunda mijina yanasona aishikenan bazan damuba na rokeki aziza ki tafi banson rigima.




Saudat ta kalli aziza tasheke da dariya tace aike ko mayyace yaci ace kintafi tunda yar uwarki da kuke uwa daya uba daya ta koreki,minal taji zafin kalmar nan amma ba yanda zatayi


Haka tanaji tana gani aziza tadauki jakarta ta nufi hanyar kofa,sai alokacin minal tace aziza,daga mata hanni aziza tayi ta fice daga gidan


Kuka minal take saudat ta kalleta tace malama tashi ba kuka zakiyiba ki tashi kije ki wankemin kayana.






Jiki a salube minal tatashi ,saudat tace tsaya malama anan in dakko miki karki shafamin farar kafa,shiga ciki tayi ta dakko,su kayan abokiti tace ,to gasunan sora amin halin sata don ranar dakikamin wanki breziyana daga aka kawomin daga dubai banganiba kawai nayi shirune,kuma karki wankemin a machine.






Bude baki minal tayi tace nida sabon sharri,haka ta dauki wankin ta nufi bangaren washing machine,tafara zanzage kayan kwayoyin maganin zubar da ciki tagani kala kala,abin yabata mamaki badai saudat zubar da cikin annur tadingayiba,tausayin annur ne yakamata yanda yake matuwar son yara.




Amai taji yataso mata kwararawa tadingayi,nan ta fuskanci tanada ciki,murnane yakamata tana bazata gayawa annur ba harsaiya gane da kansa,kuskure bakinta tayi taci gabada aikinta tana murmushi ya annur zaiyi inyaji wannan batun,




By
Maryam yarmama








Minal ce sai jibgar
[19/03 11:14 pm] salmah pinky💅🏼💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*61→65
By
Maryam yarmama
Dedicated to
My besty salmaty








*this page is given to my sweet friends, _seemaluv,sunhera,ummy agos,dijah waziri,cwtjiddah,mixx xoxo,asykhaleel,zahrah bukar,autar hajiya and others_*










Minal ce kwance a cinyar annur yana mata tsifa,annur tace my wife wai meye naga saiwani fresh kike kinyi bul bul dake abinki kodai na girba abinda na shukane?




Fari minal tayi da ido tace idon matambayi?




Annur yace haba wife ki gayamin mana har yanzu bakiji wani alert ba.




Minal tace niko naji alert tunda yau watana biyu nayi batan wata


Wani uwar ihu annur ya daka yace dagaske?alhamdudillah dole su mom suji labarinnan,wow mezan siya miki,




Minal ta tabe baki tace zuciyarka nakeso,ina bukatar kulawarka dear,nidai kabari incikinnan yayi kwari saika gayawa duniya ka godewa Allah ma baibani wani wahalaba.




Annur yace tab lalle dole mutafi asibiti yanzu duk likitan daya faramin albishir shi zan bawa kyautar gida bari in kira abokina likita safwan da jiya ya dawo daga london




Jin an ambaci safwan gaban minal ya fadi sai yanzu ta tunada safwan tsohon masoyinta wanda yafara,taimaka musu arayuwa dariyar yake tayi tace Tom Allah ya kawoshi lfy




Annur yace gaskiya dole inmiki wani abu daga yau bake ba aiki acikin gidannan


Minal tace kaidai da naiman rigima kake sokake in nazo haihuwa insha wahala ,ai ana son mace tadinga exercise






Annur yace banson mussu kiyi abinda nakeso banson ki wahalarmin da babyna.


Karar takalmin saudat sukaji tashigo tanacin cingum kas kas tace annur inada wani magana dakai in bazaka damuba




Annur yace maizai hana ki gayamin anan kinga yanzu ina busy.


Saudat tace auhakane?ta kwalla kira yar labai kashigo.




Wani matashin saurayine yashigo yasha kayan alfarma ya kalli minal yace wa annur dama wannan matarkace?


Annur yace bangane me kake nufiba mallam matatace ta sunna mana.






Mutumin ya kalli minal yace minal kinci amanata dama baki da aure kike zuwa hotel din danake,muna aikata sabon Allah mukayi alkawarin aure?


Cikin rudu da mamaki minal tace ni?gaskiya to bani bace




Mutumin yace haba minal abin yaudarace ke da har waya mukayi dake inzo gidanku kina dauke da cikina?


Annur ya tashi tsaye yace what?karyane wannan zancen wallahi karyane na yarda da matata.


Saudat tayi murmushi tace kaito bawan Allah ka nuna mana shaida mugani mana,
Mutumin yace hakane kinyi gaskiya,hotuna ya dakko sama da goma ya mikawa annur.








Hannun annur yana karkarwa ya anshi hotunan,minal ce kwance ajikin wannan mutumin,minalce a club daga ita saidan kanfai da bra,hannunta dauke da barasa,sauran hotunan kuma minal ce da wannan mutumin suna aikata masha,a ,wullar da hoton annur yayi ya zube a kujera yana numfashi sama sama innalillahi wa,innahiraihi raji,un kalmar da minal take nanatawa daukar hoton tayi taje ta durkusa agaban annur tace mijina wallahi sharrine hadani akeso ayi dakai,wallahi bazan taba cin amanarkaba cikinnan da yake jikina nakane shi kuma wannan bawan Allah bansan shiba karya yakemin




Saudat tace wai borin kunya sharare sharare gashi munga abu baro baro ai saiki rufawa kanki asiri ki auri mutumin nan tunda yana sonki








Annur rike yake da kirjinsa yana numfashi sama sama,ihu munafurci saudat tasa ta nufi wajen da annur yake kwance tana annur karka mutu ka barni wayyo minal zata kashemin mijina,ritse ido annur yayi shi yasan zafin da yakeji dama ashe saudat ce mutuniyar kirki ashe minal mutum a fuskace?






Tsugune minal take tana rizgar kuka,saudat sai gwalo take mata gami da harara,mutumin yace nidai natafi minal inkin haihu ki bawa mijinki na yafe dan ko yar








Saudat ta rushe da kuka tace ina mijina bazai rike shegeba ina wallahi




Mutumin yace oho dai nidai kunga tafiyata,fita yayi daga falon minal yayi tafiyarsa








Kukan minal ya tsananta annur yaki magana ya ritse ido ya rasa wani hukunci zai dauka,a hankali ya bude ido




Ya kalli minal yace minal kinyi daidai duk hallarcin danamiki ki rasa abinda zaki sakamin dashi sai cin amana dabin mazan waje,banyi mamakiba dama ai ance ku yayan talakawa bakuda tabbas ,zan kyaleki har sai ranar da kika haihu sai agwada ko jininane wallahi indai ba jininabane sai na daureki har karshen rayuwarki,kuma bani bake komai nagidannan ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login