Showing 18001 words to 21000 words out of 25431 words
Chapter 7 - Mahaukaci ko boyayyen masoyi complete by Maryam Yarmawa .txt
babyn jini nace"...
Cikin kakkausar murya hawaye ya wanke fuskar minal ta kalli annur sannan ta maida kallonta ga kan saudat wanda tayi tsuru-tsuru, cikin sheshekar kuka minal tace" lalle mutum mugun icene, ban cancanci haka daga gareku ba... Ko ba komai ni marainiya ce wacce tasha wahalar rayuwaðŸ˜ðŸ˜na zauna da dan sarauta, ban duba Asali ba..nayi rayuwa da mutumin danafi so a duniya... Annur bakada da kunya? Har kanada bakin magana innalillahir wa'innailaihir rajiun.... Malikar daka sheganta? Kukayimin shedar zina, kuka koreni gami da yimin saki a ranar danasha wahalar nakuda... Annur kasan maiya faru dani a ranar? .. Kabi son zuciyarka... Zamana dakai bantaba kokarin cutar dakai ba... Amma ka cutar dani da diyata malika, ubangiji Allah ne kawai zaiyi mana hissabi.... Fashewa tayi da kuka ta runtuma a guje sannan tayi Hanyar waje.....
Safwan dake rike da Malika yabi bayanta.... Yayinda annur ya fashe da kuka mai tsuma rai yana" please minal ki dawo gareni, ina bukatar in kara rayuwa dake, nine mahaukacin masoyinki, ya Allah ka yafemin, idan na mutu mezan je nace maka" durkusawa yayi yana sharbar kuka mai tsuma rai...
Saudat dake tsaye nan take taji tsanar minal yakara shigarta cikin zuciyarta tace " nadauka na kauda wannan tsintacciyar magen, nadauka bazan sake ganinta ba, na dauka Nida ganinta sai A lahira, gashinan yanzu tazo tafara kokarin rusamin farinciki.... Ina bazaiyuba. Murmushin mugunta tasaki cikin zuciyarta ta kara fadin " wannan Karon kam lahira zatayi bako... Mutum biyu zasu ziyarci lahira.... Minal da shegiyar yarta... Ku jira ni 😰
_wannan kenan_
Minal har taje gida tana kuka mai tsuma rai a duniya idan har akwai wanda ta tsana bai wuce Annur ba..... Kallon diyarta take cike da kauna, yarinyar sai wasanta take a hannun safwan wanda yayi shiru yana nazarin abu....
Hajiya Mairo ce ta katse wa safwan tunani da cewa " ashe haka tantirin yaron nan ya muku, lalle bashida kunya tom wallahi baza'a bashi yarinyar ba, saidai inda karfinmu yakare, shi ko kunya baiji ba irin cin mutuncin da yayi wa minal, don yaga tanada hakuri wannan karon kam zan tsayawa minal, saidai ayi yakin duniya".....
.
Hajiya hanne tace "Kinga uwar marayu, yaron nanfa dan sarautane akwai karfin mulki zasu iya yin komai don suga sun karbi diyarsu don haka kawai minal a daura musu aure da safwan yau _yau subar kasar nan "
A razane minal ta dago da idanuwanta da suka rine sukayi ja tace" ba inda zani, ina tare da momy bani da kowa saiku ba inda Zanje yanzu kune dangina kune gatana "....
Shiru wajen yadauka safwan yace" minal ina bayanki ba inda zaki kunanan, kuma nayi miki alkawarin sai munga umma... Ki shirya gobe zamuje kano, muje gidan baffanku....
Gaban minal ne yafadi yabada rass! Ta furta baffa
* * *
Kwance annur yake likita yana dubashi.... Yayinda saudat take gefe tana mishi sannu
Gyada kai kawai yake iyayi... Saboda yanda zuciyarshi yake mishi zafi tamkar zai tsage tunanin minal yake da kyakyawar babynshi, da yanzu babynshi tana hannunshi yana mata wasa, minal kuma tana kusa dashi tana mishi hidima da kalaman soyayya, kara ya saki yana "ina bazai yuba dole a bani matata da diyata".....
Likitan ne yace "calm down Aboki ka kwantar da hankalinka a yanzu jininka yahau sosai ba'a bukatar ka dinga sa damuwa a ranka...
Saudat ce ta Turo baki tace" doctor safwan rabu dashi, yasa kanshi a damuwar yarinyar da taci amanarshi, diyarfa ba yarshi bace.... Karuwanci Mina...... Kafin ta karasa annur ya daka mata tsawa"karki kara zagin minal idan ba hakaba Saina dau mummunar mataki a kanki, kinga get out kawai
Cikin bacin rai saudat ta tashi ta fita tana magana kasa-kasa, sama tahau ta dau wayarta ta yi danne-dannen minti takwas sannan ta danna wani number ringing biyu aka dauka
Daya bangaren akace "hello hajiya ranki shi dade da Alama samuwa ce tunda naji kiran nan ".....
Saudat ce ta amsa da"Eh boss wallahi kwangila nakeso nabaka... Na tura maka hoto ta watsapp dinka(dama ta Turo hoton minal daga wayar annur, saboda tun a Mora tagama shirya plan dinta) , inason ka nemomin ita duk inda take, Akwai jaririya a hannunta ka hadasu ka kashesu, nasanka boss akan kudi bakada imani
Amsawa yayi yadau babbar wayarshi yabude data yana duba hoton yayi zooming "cikin kasa-kasa da murya yace ai hajiya aiki yazo gidan sauki don yarinyar ma gatanan tsaye a bakin gate din gidan marayun HUTU... Su uku da wasu yan mata, kuma dayar tana rike da jaririya.. Kuma wallahi danayi zooming itace....
Cikin jin dadi saudat tace"boss meya kaika hanyar gidan marayu kuma,
Amsa yabata yana fadin". Ai yarinyata da Mamanta ta rasu Wanda kowa Yaki amsarta ai nan nakaita, to shine yau nazo visiting, saikuma Kika kirani, hajiya kwantar da hankalinki, ai bindigata tana kwankwasona... Bari ma in Turo miki da hotonta ki tabbatar itace ko ba ita bace.... Zooming din minal yayi yadauke ta daga nesa bata saniba
Ihun murna saudat tayi tace "yes! Yes itace wallahi... Yi maza kayi shooting dinta da duka yanmatan har babyn, kanada kyautar miliyan biyar da visa na barin kasar nan.....
Katse wayar saudat tayi ta dire akan katifa tana "Alhamdulillah
Pls a dinga sharing
*🦋MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦋*
(82)
*BY MARYAM YARMAMA*
_(QUEEN MEERAH)_
*After a long break am back... Ina godiya ga tarin masoyana... Bisa kaunar da suke nunamin, duk lokacin da naga sakonku.. Ko kuma kiranku, sai inji tamkar inyi kukan farinciki*
_GARGADI_
_Ban yarda a juyamin littafina ba, ko canzamin suna... Baiwa ce ubangiji Allah yabani.... Don haka a guji juyaminv littafi a kowani siga_
Boss ya seta bindigarsa daga can nesa cike da murmushin mugunta yace yara taku ta kare.... Hannun yasa akan kunamar bindigar yana kokarin Harbawa, diyarsa abin sonsa yagani tafito daga gate din gidan marayu aguje... Cikin shaukin so ya sauke bindigar yafasa Harbin yamaida bindigar kugunsa..... Nufar wajen yayi, kafin yakarasa yar tashi ta taho tana murnar ganinsa... Nan minal da khadija suka dago da kansu daga dubar wayar da sukeyi suna murmushi, boss ne yadauki yarshi yakarasa wajen yana gaishesu da fara'a akan fuskarsa, Amma cikin zuciyarshi yana "bari ingama da yata zan dawo gareku "..... Amsawa sukayi sannan suka shiga cikin kofar gate din. Boss ne ya kalli yarshi yace " kaunata wannan kyau din da kikayi waye yake kullarmin dake"... Cikin farinciki yartashi ta kalleshi tace "Abba Aunty minal ce, tana da kirki sosai ita yakeyimin wanka tabani Abinci abaki sannan ta koyamin karatu har goyani take. cike da farinciki yace wacece minal kuma, amsa tabashi tace "wannan wacce suka tsaya anan kuka gaisa ai tanada yarinya, wannan jaririyar yarta ce".... nan take yaji tausayin kanshi Dana yarshi ya kamashi da tuni yanzu yakashe wacce take sa yarshi farinciki, nan tsoran Allah ya shigeshi, wayarshi yadauka ya turawa saudat kalamai na nasiha Sannan yasakata a black list.... Sallamar yartashi yayi yace idan tashiga tacewa minal yana godiya Allah yasaka mata da Alkhairi ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜.
Saudat dake zaune a falo tana shan lemo cike da annashuwa karar shigowar sako taji ,da hanzari ta dauki wayar sakon boss tayi arba dashi tana gama karantawa cikin bacin rai ta danno wata uwar asharr tace"lalle boss kagama sanina ,dole ka rainani tsiyar yiwa talaka halacci kenan ,aiko zakayi bayani wallahi ".............. cikin fushi ta fara kirar numbarsa saitaji wayar akashe,tsaki tayi tana nashiga uku wallahi bana burin minal tadawo gidan nan ,idan tadawo wallahi asirina zai tonu ,aikam bazai sabu ba dole minal tabar duniyar nan gaba daya,karar intercom taji alamun tayi bako .saida tagama shan kamshinta sannan tatashi ta nufi hanyar babbar falo taje ta bude kofar. momy tagani tare da aziza fuskarsu ba annuri ...................................................................dam!dam!gabanta ya yanke yafadi amma dayake ita yar duniyace ta saki murmushi tana "oyoyo mummy saukar yaushe ..aha tafe kuke da auntyn minal"...mummy tace dakata bani zakiwa makircin nan ba,zuwa nayi inyi muku godiyar abinda kukayi wa minal keda mijinki Annur ina london nasami labari amma saboda corona yasa ban dau wani mataki ba,bansami hanyar dawowa ba sai jiya nadawo... ,amma hankalina a tashe yake musamman yar uwarta Aziza saboda halin datashiga first semester akayi withdraw dinta daga makaranta,kun kyauta ina mara kunyar nan ,butulu yake wanda bai san hallaciba ,yazo ya nemomin inda minal take ko kuma in tsine mai. "...... tsaki saudat tayi cikin rashin kunya ta hada girar sama dana kasa tace"to ai mummy bani zaki balbale da fadaba ,wannan kuma ai tsakanin danki da minal ne,ni bamma san mai akayiba cikin shege ta kawo cikin gida ,shine ya koreta"....Aziza cikin bacin rai tace"wallahi karya kikeyi yar uwata bazata taba yin hakaba ,nayi imani da ubangiji na.kuma yau asirinki yana gab da tonuwa ,yau zaki shuka abinda kika girbe,.....tsaki saudat tayi tace"au tafiyarki kasar waje tare kuke yawo kenan ,Ashe ke kika koya mata halin ai bazanyi mamaki ba saboda yayan talakawa haka suke ,shidai annur yace ciki ba nashi bane tuni ya seta mata hanya,duk munafikin daya gaya muku wulakanta minal mukayi to karya yake ciki dai bana Annur bane karuwanci tayi ta samoshi,juyawar da saudat zatayi tashiga ciki ...taci karo da annur ya wanke ta da mari kyawawa guda biyu ...cikin bacin rai yace "duk ranar da kika kara aibata minal a idon duniya sai na sakeki ,Albarkacin mahaifina kikeci .....muryar dady sukaji yana"Annur idan har ka haihu a cikina,idan ni mahaifinka ne, ,inason kasaki wannan mara kunyar yarinyar wanda yau Allah ya tona mata Asiri,dagowar da annur zaiyi saiyaga hawaye a fuskar mahaifinshi ,tunda yake bai taba ganin mahaifinshi yana hawayeba sai yau .....tunkaro inda mahaifinshi yake yayi ,ya rungumeshi yafara kuka tamkar karamin yaro ......saudat ce tashige falo aguje,tayi hanyar kitchen ta dakko wuka tana yau zan kashe annur ,na kashe kaina kowama ya rasa...ba macen da ta isa ta rabi kota zauna da annur 👦fitowa tayi daga kicin din ta nufi hanyar falo ..sannan tayi wajen kofar falon inda tabar su momy nan tasamesu kowa yana kuka ,annur kuwa yana rungume da mahaifinsa ..."yana dady na rasata"......ji yayi an chaka mishi wani karfe ta baya,kara yasaki ya zube a wanwar "..................................
*MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI*
BY
MARYAM YARMAMA
83
Saudat tsaye taja wan dogon numfashi da ajiyar zuciya ta dawo daga duniyar tunanin data shiga... Furtawa tayi shedan kayi karya, da kake so inje kurkuku... Tana gama fadin haka dakai dubanta ga aziza wacce suke tsaye Suda mommy, harara aziza ta daka mata sannan suka white falon... Suka barta tana kallon annur rungume da mahaifinsa... Annur ne yakamo hannun mahaifinsa yace" dad idan har sakin saudat shine BURINKA tom zanyi abinda kace duk da bansar hujjarka ba na cewa na saki saudat".....amma daddy meye hujjarka, saudat yar gidan amininka ce, kuma ku kulla Alaka da sarkin gombe mai karfi dadi meyasa kake so ka yanke wannan karfin Amintakarku?..
Cikin hawaye daddy ya kalleshi yace son muje ciki Labari ne mai tsaho... Takun kasaita sukeyi, wuce saudat sukayi tana tsaye jiki a sanyaye..ciki ya duri ruwa. Shigewa falon sukayi sannan suka zauna, cikin sauri saudat ta rufa musu baya itama yashiga babban talon tazauna tana wani daman yatsine da hararar dady, shiru wajen yayi yayinda daddy yafara magana da cewa "Yabo ya tabbata ga ubangijin talikai,Annur dafarko kayi kuskure mafi girma a rayuwarka, ka cuci rayuwarka"ina karatunka, ina iliminka da har kayi saurin yanke hukunci akan matarka minal wacce ta soka tun batasan kai waye ba, yarinyar nan bata cancanci haka daga gareka ba.... Duk Abinda yafaru naji ta bakin wanda yazo gidanka ya nuna shine mallakin cikin minal, sannan hotunan daka gani editing akayi, shi mutumin yazo ya sami maigadin gida yace yanason magana dani mai gadin yahanashi, sai ya kama kuka shifa yanason ganin mai martaba saboda yana cikin tashin hankali... Tom cikin ikon Allah na fito ina zagayawa, ina exercises bisa umarnin likita sai naji wannan hayaniyar, sai nace maigadi yabarshi yashigo, damai gadi yabarshi yashigo... Sai na umarta akawo mishi abinci, yacemin shi bazai iyacin abinci ba saiya furta abinda yake damunshi "tom cikin kuka gafara gayamin irin kulla kullan da matarka saudat tasakashi sannan yace shi yake mata aiki" duk abinda akace minal tayi duk Sharri ne, kuma saudat ce ta kulla sharrin sannan rana daka kori minal, sai datasa yabi sawun minal domin ya kasheta da jaririyar Amma Allah bai basu dama ba
Kalmar Innalilahir wa'innahir laihi rajiun annur yaketa nanatawa, gumi ya tsofo mishi ta ko'ina a jiki,. Yayinda saudat sai zazzare ido take jiki na kyarma....
Daddy ne yace "Annur mutumin nan ya gayamin abinda yasa ya kasa samun kwanciyar hankali shine yace duk lokacin daya kwanta sai yaji kukan jarirai ta ko'ina, sannan yadinga yin mafarkin gashi yana wutar jahannama, shine da kwatance ya gano gidana domin yace yakasa zuwa wajenka bayason ku hada ido... Yana gama fadin haka, ya dakko MAGANIN kwari ya kwankwada, Kafin inyi magana ya kurma wani ihu, yayi hanyar gate yafita, fitar shi keda wuya mota ya bigeshi sai mutuwa....
Kuka Annur yasa yayi kan saudat ya shaketa yana saudat kinci Amanata, kin rabani da abar sona abar kaunata, bazan taba yafe miki ba..... Kije na sakeki saki uku... Ihn neman cero saudat take kurmawa, dakyar mommy ta amsheta a hannun Annur..... Ana amsarta ta saki kuka mai tsuma rai tayi hanyar saman benen falo da gudu, tafara hada kayanta yau shine karo na farko da tafara nadamar abinda ta aikata a rayuwarta kuka tasaka mai tsuma rai tana"minal kiyi hakuri na cutar dake na rabaki da abin sonki....
By maryam yarmama
*💥MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI💥*
84
By maryam yarmama
*KANO CITY*
nifa Abban haseeya nagaji da ciyar dakai, nagaji da jinyarka gwanda ka mutu kowama ya huta da wannan wahalar naka... Mamace take fada cikin zagin rai gami da tsananin tsana...
Kwance Abba yake cikinshi ya kumbura tamkar mai cikin wata Tara... Sai mishi yake dakyar hawaye masu zafi nabin idonuwanshi ya Kali mama yace"ladi kiji tsoran Allah a rayuwar na nayi komai ne donke da yaranki, Domin kuji dadin rayuwa, Amma dayake duniya ta juyamin baya shine kike tsanata,kike hantarata?
Cikin masifa mama tace"dakata malam karkace kayi saboda ni wallahi karyanka kawai son zuciyarka kabi, ka yi ajalin danuwanka sannan ka cutar da marayun yaransa, gashi Kaga sakayya, ita haseeyar dakayi auren jari da ita, gashi tadawo gida, ga uwar danfarar da mijinta ya mana yasa muka zuba hannun jari, kaine harda saida kadarorin marayu, hatta Gidan da muke ciki ka daga ka siyar ka kawo mu rubabben gida.sannan kadai kudade kabashi... Karshe ai mijin haseeyar guduwa yayi ya barta da ciki da ciwon kanjamau . Tana gama zubo jawabin nan ta fashe da kuka tana wallahi ka cuceni, Allah ya isa tsakani dakai
Wani irin Zafi Abba yakeji ga zagin ciwo shiru yayi yana zubar da hawaye shi yanzu burinshi kawai yaga umma da yaranta ya nemi yafiyarsu.. Kwalla mash dumi ne suka zubo mishi
*ABUJA CITY*
minal ce zaune dauke da wani karamin Hoton dasuka dauka annur yayi mata kiss suna Dariya ta kura mishi ido tana kallo..tana zubar da hawaye... Charaf taji an warce hoton juyawar da zatayi taga safwan tsaye yana mata kallon tuhuma, kunyane ya kamata tafara kokarin share hawayenta
Hade girar sama dana kasa yayi yace"bana ce kar inkara ganin kukanki ba? Haba minal save ur tears,Dama ni nasan kinason Annur, saboda da wuya ki dena sonshi.....dakatar da safwan minal tayi ta hanyar cewa"enough safwan kawai ina kukane idan na tuna Abinda Annur yayimin, baiji tausayin diyar nanba haka ya wulakantamu... Bazan taba yafe mishi....
"Shiiiiiiiiiii" safwan yayi mata Alamar tayi shiru sannan yace "minal, Annur yana sonki Duk Abinda yafaru nasan ba laifinsa bane, sharrin macene and kuma wallahi Ranar Dan Ganshi a mall dinnan nasan yayi nadamar abinda yayi, karki manta shi gwarzon namiji ne kuma yarima dan sarauta, Amma ya dunkusar da kanshi yana kuka tamkar karamin yaro, tun daga Ranar na fara giving up nasan zaku dawo, kuma nasan kunfi dacewa dajuna,
Cikin kuka minal ta Kate zancen safwan ta hanyar cewa " safwan ni dakai na dace bashiba, kai mutumin kirki ne
Amsa safwan yabata yana"minal shima mutumin kirki ne, saboda sonki ya kwaikwayi hauka, yazauna dake acikin talauci don kawai yasameki, yayi rayuwa acikin talakawa saboda ke, Maman malika kiyi hakuri ki koma Gidan mijinki, ni na sadaukar da soyayyata, namiki Alkawarin auren yar uwarki Aziza, Dama tun da basona kike....
Jikin minal ne yayi sanyi shiru tayi sannan tace "hmmm safwan inaga Mubar maganar nan sai mun dawo daga kano"....
Hajiya Mairo ce ta shigo office din bakinta dauke da sallama tana murmushi tace"minal kinyi baki fa Kafin minal tayi magana Aziza tashigo hannunta rike da baby malika.. Tsaye minal ta tashi kukan murna tafara tayi wajen yaruwarta ta rungumeta tsam,