Showing 1 words to 3000 words out of 25431 words

Chapter 1 - Mahaukaci ko boyayyen masoyi complete by Maryam Yarmawa .txt

15 Dec 2024

2243






























*💥MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI💥
(A LOVE STORY)
01
BY
MARYAM YARMAMA










*APOLOGY*
AM SO SORRY MY followers I CANT CONTINUE ,THE STORY *CAPTAIN SHAYEEDA BUT I WISH ONE DAY I WILL CONTINUED,I NEED UR PRAYER


*starring*
Adorable minal
Stubborn gal aziza
Hansome guy annur
Play boy safwan
Ummi
Saudat
Hasiya
AND OTHERS..........




*VOTE OF THANKS*
zahrah bukar
Asykhaleel
Salma ali wada
Halal dady gal
Hauwa mamee
Maman hafsy(hajara)
Lubna(lalata writter)
Miss xoxo
Raz
Aisha gana
Pretty minnah
And others friends






*KANO CITY*
Kuka minal ta saki sakamakon mafarkin datayi na mahaukacin masoyi,kuka tafara tana wai yaushe zanga mahaukacin masoyina iye,mahaukacin masoyi ka nunamin kanka,meyasa kake firgitani a mafarki,wlh ina matukar kaunarka.idan bakai bazan iya rayuwa ba pls ka cikamin burina my blue eyes


Aziza dake faman sharar bacci tashi tayi taja tsaki tace" nifa minal kina damuna,da wannan banzan mafarkinki,haba dan Allah akanki akafara soyayya mutumin ma dabaki taba ganiba amafarki kika ganshi,dan Allah kiyi mana shiru ko kuma inje inkira umma






Rufe baki minal tayi tana kuka mai tsuma zuciya tace yar uwata bazaki gane son danakewa mahaukacin masoyinnan bane,wallahi inna hadu dashi agaske wallahi kinji na rantse da Allah ko ya yake saina auresa






Razane ido aziza tayi tace yar uwa kina da hankali kuwa lalle kuwa zaki dakko ruwan dafa kanki ba kadan ba iye lalle ma,kinga kwanciyata saida safe


Minal ta doshi hanyar waje ta dauki ruwa a buta tadauki buta tayi alwala tazo tafara nafilfila tana rokan Allah ya bayyana mata mahaukacin masoyinta,






;::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Washe gari,gidansu minal ko sanwar abinci babu, kanwarsu auta da yake bata jure yunwa yarinyar shekara hudu,sai kuka take tana,wayyo cikina,zan mutu yunwa nakeji, umma ki taimakeni


Minal uwar tausayi ta fashe da kuka,ta kalli umma datayi tagumi tace umma yazamuyi ne,nifa nafi tausayin auta,kuma kinga tanada sickler karya tashi wlh ina tsoro






Umma cikin taurin zuciya tace to minal yakikeson inyi mukune,saidai inzakije gidansu hasiya wajen baffa ki tambayo mana kudin gadonmu wanda yace zai yi mana jari dashi ,in sunki subada sai mu barsu da Allah, dama mun dade muna hakuri




Hawaye yafara kwaranya a idonuwan aziza tace a a umma abarsu kawai,Meye gado,mutum ma yana mutuwa yana barin duniyar balle gado,ai kayan duniya na shedanne?a tsirara mukazo a tsirara zamu koma meye zai damemu,Allah zai sakamana kawai abar maganar gadonnan




Idon autane ya fara kakkafewa da sandarewa.


Minal ta rungumo auta tana ihun auta auta karkiyimin haka,umma mutafi asibiti,






Saka hijjabi minal tayi ta fita dagudu kan titi tana rungume da Auta da numfashinta yake sama sama,


Su umma ne suka rufa mata baya


Adaidaitasau suka tara suka shiga,nasarawa hospital suka nufa,sunashiga aka karbi auta aka shiga dakin emergency da ita.






Likitane ya kira minal yana lashe baki,umma zata bishi yace a a umma ita kadai nace zatayi signing a office dina




Aziza tace anya umma anya likitannan akwai Allah a lamarinsa ,daga ganinsa dan iskane jibifa wai minal ce kadai zata bishi office






Umma tace kul kidaina fadin zarcenan,ai Allah yana tare damu, Allah ba azzalumin bawansa bane








Minal tsayawa tayi acikin office din,






Kanne ido likitan yayi yace baiwar Allah kizauna mana




A tsorace minal ta zauna,tana kallon kyakyawan likitan,matashi tace ina
...kwana






Murmushi yamata lfy matsowa kusa da ita yayi har suna iya gogon juna,minal a tsorace tace pls yallabai kaban takardan dazanyi signing mana,






Lashe lebe ya tashi kamar zaije ya dakko takardan ,bayan minal yabi ya dafata,yana fadin gaskiya kin burgeni






Kuka tafara rusawa tana dan Allah likita banson irin wannan kuda aka sanku da taimakon al,umma, kaji tsoran Allah




Kokarin sa bakinsa yake abakin minal,yana zura hannu a hijjabinta,kuka minal tasa;tayi iya karfinta ta hankadasa gefe,tafita da gudu








Karo sukaci da aziza,da take faman sharbar kuka tace kema minal yanaga kina kuka likitan ya gaya miki auta ta rigamu gidan gaskiyane?






Cikin mamaki,minal ta kalli aziza tace da gaske,auta ta ta tafi,


Aziza tace tabbas ta mutu saidai hakuri,yanzuma gawarta zamu dauka mu koma dashi






Kukan zuci minal take tana mudai haka rayuwarmu zai kasance ina umma






Jawo hannunta aziza tayi tace tana dakin da gawar auta take,bata wani tashi hankalintaba,Allah ne ya daukewa auta karshen wahalarta naciwon sickler dinnan








Minal kukanta yafito fili dataga wannan likitan kamar mutumin kirki yanata bawa umma baki,
Mamaki ya cika minal to tawani kofa yashigo,har ya iso dakinnan








Yana ganin su minal ya kallesu da alaman tausayi a fuskarsa yace sannu yanmata sai hakuri,zaro dubu goma yayi yabasu yace gashi wannan asiya abin sadaka.


Aziza uwar son kudi ta kawo hannu da niyar ansa,minal ta amshe ta watsawa likitan kudin a fuskarsa tace munafukin Allah bama bukatar kudinka,meyasa tun wuri baku taimaki rayuwar yan uwataba sai yanzu zaka taimakemu, kaji tsoran Allah kuma ka tuna zaka mutu




Ji tayi an bata mari tas,batason lokacin da ajijiya ya kamataba tafada jikin likitan da tafi tsana aduniya




Taku kulllum
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*02
By
Maryam yarmama
Dedicated to
All my fans






_wannan shafin nakine *aunty yar mitsila* saboda kaunar da kikewa littafina,kina karamin karfin gwiwa,you are in tha part of my heart,i wish you more happiness and beautiful life and age_










Umma ce cikin kunar rai tace ke tsabar ke shedan ce ammana kyauta kinki ansa,to kisani gidanmu bada halinnan muka tashiba,har Mahaifinki ya koma ga mahallacinsa kullum mutane kyakyawar sheda akemai,






Tashi minal tayi ta durkusa agaban umma tace umma ki share hawayenki indai akaina ne bazaki sake kukaba,zakiyi alfahari dani,zanyu biyayya agareki har karshen rayuwata,ta kalli likita tace kayi hakuri mungode da kyautar da kamana




Likita safwan nan yaji yarinyar kaunarta ya kara dilmuwa azuciyarshi yaji gaskiya bazai iya rabuwa da itaba,yace bakomai muje insa a saukeku agida




Umma tace haba dannan kai da wahala haka ashe kanada kirki haka,
Minal azuciyarta tace,tab umma dakinsan me yake shirin yiminba, Amma dai koma menene








Haka suka fito daga asibitin suna kuka,safwan ya bude musu bayan haddaden motarsa,umma da aziza suka shiga,har minal zata shiga umma tace a a minal kishiga gaba,mana,nan yayi kadan kuma ga gawar auta


Minal tanajin an ambaci gawar auta ta rushe da kuka tana ashe dagaske auta ta mutu




Safwan ya kalleta da idonsa mai narkar da yanmata yace yanmata kishiga mana sai hakuri wanda ya mutu ya riga yamutu,sai hakuri




Takasan ido,minal ta gallamai harara tace ina ruwanka da kukana,kallon kafanta tayi sai yanzu ta lura kafarta ba takalmi,buzu buzu yake,kunyane yakamata tashiga motar shima safwan yashiga yana tukawa a sannu a hankali,yana satar,kallon kyakyawar fuskar minal daya rine da hawaye


Jin kukanta yake har ransa,amma ba yanda zaiyi yahanata, yarinya mai tsoran Allah haka




Minal kallon titi take,gano wani kyakyawan mahaukacin masoyin datake mafarki tagani,gashinsa yayi luf luf kamar ns indi,a ga idonsa dara dara,yana dauke da faffadar kirji,dogo;fari kal dashi,ga hanci har baka,amma kash daga ganinsa bashi da hankali,kai duk inda ake neman namiji,in aka cire safwan to mahaukacin masoyi yakai,domin safwan ba baya bane awajen kyauba.




Kara minal tasa tace likita ka tsaya ka tsaya dan Allah,naga wani abun dana dade ina muradi da nema




Cin burki safwan yayi,da gudu minal ta bude murfin mota,ta duba hagu da dama sama da kasa bataga abin sontaba,hawayene ya fara shatata a idonta,ta dawo cikin mota jiki asanyaye


Umma dake bayan mota takalli aziza tace wai meye minal ta tsayar da motane?


Aziza tace oho ita zataki tambaya,don inaga minal takusa zaucewa
Umma tace Allah ya kyauta




;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;,;;;;,,,;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;






A kofar gidansu minal likita safwan ya tsayar da motarsa,yana kallon rubabben gidansu cikin tausayawa da jimami,duk gidan ne yafi kowa muni a layin gabaki daya,




Bude musu motar yayi,ummi suka gani a tsaye a kofar kyakyawan gidansu,tana ganinsu ta fara murmushin jin dadin ganinsu minal ta taho,ta dafa minal tace besty nashiga gidanku naga shiru lfy






Fashewa da kuka minal tayi,ta fara nunawa ummi gawar auta tana ihu da kukan auta ta mutu auta tabarmu aduniyar nan mai cike da wahala da kuncin rayuwa


Salati da ihu ummi ta zunduma ta nufi wajen umma dake rike da gawan auta,jijjiga auta take tana auta auta abokiyar kowa,auta akwai ki dashiga rai meyasa kika barmu innalillahi wa,innahilaihi raji,un


Makotane sukafara fitowa wasu nakukan rashin auta,wanda duk cikin yayan umma tafi shiga rai,da son wasa,kowa natane




Haka akafara zaman makoki


Umma da takejan chasbahana tacewa aziza taje gidansu abba ta gayamai rasuwarnan tunda yanzu shine uba,


Safwan sai hidima yake,komai shi yayi agidan mutuwarnan




Can anjima saiga aziza tashigo gidan da kuka tafada jikin umma tace umma wallahi ba Allah a zuciyar abbansu hasiya,haka yace bashi ya kashetaba balle yaxo,indai don abin sadakane wai saidai mu mutu bamuyi sadakarba,wai ahaka zamu kare ba rayuwar kwanciyar hankali




Yan gidan mutuwa suka fara jimami suna ta Allah ba tasaba saidaishi ya mutu badai kuba






Haka aka share zaman makoki ,komai safwan ne yakeyi,ya canja kamannin gidansu umma,an mai gini mai kyau,ya zuba kujeru da fridge,da t.v da jennareto,yacika store da abinci da komai.


Umma sai shimai albarka take,minal ko ajikinta ta tsani safwan,itadai burinta ta karacin karo da mahaukacin masoyinta




Abbane kanin babansu ya tako gidan ranar yazo da rashin mutuncinsa,yaga gida yayi kyau,nan ranshi ya sosu yace lallema matar nan,tafara tura yayanta duniyar karuwanci kenan






Shiga gidan yayi ba sallama, ga gidan an chanja shi harda tyles,wani uwar ashar ya dura yace ke karya ina kike kifito, ki gayamin inda kika samu kudi har kuka can a fasalin gida


Aziza dake goge tyles da mopping stick tace karka kara cewa uwata karya saidai na tsayanne bakin kare, Alade irinka




Nufota yayi yace wallahi zanga uban daya tsaya miki agidannan kike cemin kare,mara kunya kawaj


Aziza ta dankaramai harara tace to tsohan najadu inajiranka, ai wallahi ka gama zubar da mutuncinka a idona, kai da kare a wajena, wallahi kare yafika mutunci da imani... Zaiyi magana amma ya cize yatsa yana daukar Alwashi




Minal dake girki a kitchen tafito ta durkusa har kasa tace abba ina wuni




Abba yace ban wuniba munafuka yar iska,karere, shegiya sumi-sumi mutum a fuska




Dafe kirji minal tayi tace abba nagode,ta kalli aziza tace haba yar uwa yakikeson karya umarnin mahaifiyarmu kinsan tashiga,gidan hajiya tace duk wanda yazo ya takelemu da fada karmu biye masa,pls ki daure kibi umarninta






Aziza tace to shikenan taci gaba da aikinta,minal takoma kitchen tanata girki






Abba sai zage zage yake,dayaga bawanda ya kulasa,yayi tafiyarsa
By
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: _PERFECT WRITTER FORUM_(P.W.F)
*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*
BY
MARYAM YARMAMA
*DEDICATED TO*
MY FANS






*WANNAN SHAFIN NAKINE MAMAN HAFSAT,INA FATAN ZUMUNCINMU ZAI DORE HAR ABADA,KINA RAINA*










bayan kwana biyu umma ta aiki minal zuwa gidansu,abba ta karbo mata ankon bikin hasiya


Hijjabi ya wuce gwiwa minal tasa,tana cike da farin ciki yau,tayi mafarki tayi zata hadu da mahaukacin masoyinta mai kaunarta






Ta tsantsara kwalya dama gata chocolate colour ga hanci har baka ,ga ido ,tayi masifar kyau,minal nada hakuri,gason karatu,da saukin kai,batta da surutu so silent zaka ganta,bazaka taba gane tanada tsiwa ba saika kula sosai




Tafiya take a sannu a hankali,kamar tana tausayin taka kasa,ji tayi an rike mata hijjabi ta baya,faduwar gabanta ya tsananta...




Wani murya mai uban dadi taji abayanta yana anty ki gaya musu su daina tsokanata sunacemin mahaukaci


A hankali ta juyo karo taci da wanda take muradi wanda koda yaushe yakE manne a birnin zuciyarta,ya kara kyau dahaske,rufe ido tayi tanajin sansayar iska yana kadawa sonsa nakara narkuwa azuciyarta




Firgigit ta farka daga dogan tunanin da take sakamakon jin ya kara ambatar anty ki gayamusu su daina tsokanata




Kallon gefensa tayi,yarane sunfi ishirin sun tsaya suna kallonsa,dayan yaronne yace kash gaka kyakyawa amma ba hankali




Tabule fuska yayi yace anty ki gayamusu ni wlh






Minal ta kyalesa cikin sanyin murya tace,to ka sakeni zan gaya musu ,kallon yaran tayi tace haba kukuwa idan yayankune kodan uwanku ya ke da wannan laluran yazakuji iye?




Jikinsu yayi sanyi a hankali suka fara watsewa suna barin wajen




Kallonta yayi yace aunty nagode zaki aureni,ki dinga korar min yaran, basu da mutunci fa a shagwabance yayi maganar




Dariya minal tayi tace hmmmm mai kyau ya sunanka?


Cikin alamun jin kunya yace sunana annur sunana aunty kiyi alkawari zaki aureni muryarki da dadi




Minal tace,a-a ni kadaina cemin aunty minal sunana ba auntyba ai zan aureka in Allah ya yarda






Ihu gami da tsallen murna yayi yace wooo aunty nagode dafatan zaki dingamin wanka kisamin pampers








Kunyane ya rufe minal tace kaga sai anjima ma hadu kasan gidanmu nan bayan layi kazo ka dinga karban abinci




Murna annur ya fara yafece aguje.






Jikin shaukin kauna minal takallesa tana in Allah ya yarda sai na auri annur na maidasa mutum kamar kowa




Tafiya taci gaba dayi abba ta tadda a kofar haraban gidansu maikyau yana ganinta tundaga nesa ya fara yar maula ki koma ai yau ba jumma,a ba, ko ummarku bata gaya mukuba








*pls my fans am so sorry ,this is a short page ,am so sorry,am studying*




By
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: _PERFECT WRITTER FORUM_


*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-4
By
Maryam yarmama
Dedicated to
All my fans








Kunya ta kama minal,domin akwai dandozon mutane awajen,




A sannu a hankali ta iso wajen abba ta durkusa tace abba ina wuni,abba yace ban wuniba yar mace meya kawoki gidanmu?
Minal tace dama munji haseeyace zata yi aure,abba ya amshe zancen shine kikazo ki rusa ko to ta Allah batakuba,minal tace aa anko nazo amsar mana naga bikin saura sati biyu,washe baki abba yayi yace ai bama kusaniba mai kudi sosai zata aura,anya zaku iya siyan ankon don ankon kala biyar ne?kuma sai yaran manyane zasu iya siya


Minal tace in Allah yayarda ko kala dayane zamuyi,bari inshiga ciki


Tashi tayi abba nata yada mata bakakken maganganu.




Shiga ciki tayi tana kallon gidansu nada wanda aka kwace musu karfi da yaji lokacin da abbansu ya mutu,hawayene ya subuto mata amma tayi saurin gogewa




Su haseeya da luba suna zaune da kawayensu a harabar tsakar gidan suna cin kaza a plate sunata hira




Suna ganin minal kowacce ta hade rai daga,dariyar dasuke




Minal tace sannunku


A yacine luba tace yauwa ya akabar tsohuwar yar bariki, naji wai kun canza salon gida, tsayama ina wannan Azizar mara kunyar nan take




Minal tayi murmushin takaici tace hmmm ,ta kawar da zancen da cewa hasiya munji labarin aurenki tom Allah ya sanya alkhairi Allah ya doramu a danshinku


Rangada buda sukayi luba. Ta amshe zancen tace ai Allah bazai taba doraku a danshinmu ba ,ahaka zaku kare kuna rayuwar kunci da bin maza




Minal tace kema binta kinsan da azizace tazo nan saikunyi dambe kuma kinsan ni bamason gashin hankali anko nazo na amsa,ni Allah ya doramin hakuri dayawa kullum burina muja juna ajiki




Haseeya ta kalli dayar kawarta datasha bleeching tace kinga wannan mabaraciyar metake fada,wayake tsoran azizar,ai suk ruwan bala,in aziza bata kainiba,kidai shiga ciki kar a mana halin bera mama tana ciki






Minal jikinta tayi sanyi lukus,tashiga kofar dazai sadata ga falo,


.shiga tayi mamace a falon ta dora kafa daya kan daya,ga katon naman kaza a filet sai ja take tanaci


Hadiyar miyau minal tayi ,tace ina wuni mama,




Tsawa mama ta dakamata,firgita minal tayi ta rakube agefe,sannan tace to diyar mayu maiya kawoki gidanann
Cikin sauri gami da tsoro Minal tace dama mama ce tace nazo ansar ankon haseeya ne




Mama tadan saki murmushi,don duk maison bikin hasiya bakaramin dadI takejiba ,tace ok Allah yasa zaku iya anko din, bari in dakko miki,kima daina tunanin zantafi in bar kazata,don dashi zan shiga ciki,bazanma nuna muku lefenba,karkuje ku nuna halin bera, Amma kaya yayi kaya yan bakinciki saidai su mutu






Shiru minal tayi,mama tashiga ciki
Idon minal ya sauka akan wani jaka mai kyau rataye a falon,ahankali tatashi ta dauki jakar,tana budewa abinda taci karo dashi yasata razana,sarkan gwal din da agogon gwal din da lokacin da babansu yake darai ya siyawa ummansu a dubai ta gani




Daukewa tayi ta aje jakar a inda yake ta sa sarkar da agogon a cikin rigarta ,faduwar gabanta ya tsananta,sai ta tuna lokacin da babansu ya mutu yana rashin lfy umma ta nemi sarkar da agogon ta rasa,abinda aka siya kimamin,miliyan biyu,shine su mama suka sace




Mamace tafito da kyallen ankon ahannunta,saida ta karewa falon kallo taga komai daidai yake,sannan ta wurgawa minal ankon tace kussan bikin saura sati biyu don haka ana saura sati daya zakuzo saboda akwai ayuka diyawa ,sora kuki zuwa wlh saina muku rashin mutunci




Minal tace in Allah yayarda zamuzo Allah ya kaimu lokaci sai anjima
Ko bata amsa mama batayiba taci gaba dacin namana


Tashin da minal zata tashi sarkan ya fado,mama bata luraba ,minal ta wullar da yadin tayi kamar kyallen ne yafadi ta dauka ,tayi hanyar waje


.su hasiya suna ganota suka kwashe da dariya suna ihun inna ta gaida assha






Minal fita tayi tana tafiya taga motar safwan ya tsaya,zuge glass yayi ya fito yace gimbiya sarautar mata


Minal ta hade rai




Safwan yace nidai saidai duk abinda namiki ki yafemin,don gobe zan tafi kasar england karo karatun shekara uku,gashi iyayena ba,anan suke ba balle kisansu, gashi Allah ya doramin kaunarki kina wahalar da zuciyata




Minal taji ba dadi ,duk tsanar da takewa safwan taji yabata tausayi ,shirrin kuka tafara tace yanzu bazakuje kuyi bankwana da ummaba




Safwan yace a a saura hour biyu ,girgin mu yadaga,but tunda na ganki ga sako ku bawa su umma,miko mata leda yayi mai nauyi,da wani envelope




Safwan yace wallahi minal i will miss you,wayarsa ta dakko yana tamata hoto


Kuka minal tafara tana tunanin wannan shine haduwarsu ta karshe, sunyi rashin mai taimaka musu kenan??




Safwan shima yaji hawaye ya tahomai,yace karki soma ki daina kuka nidai ki jirani,zakiga wasika daya naki daya na umma




Shiga mota yayi yana daga mata hannu


Minal ta kara fashewa da kuka,safwan ma dake mota shima yakara kukansa kamar yafasa tafiyarnan,tunda ya fuskanci minal ta fara kaunarsa






Minal barin wajen tayi,tayi hanyar gida tana shiga ta fara zubar da hawaye safwan ya musu hallaci sosai,sai yanzu take missing din muryarsa da kalamansa da kamshin turarensa da kyawun fuskarsa,




Aziza ce tafito daga daki,daga ita sai best da ta dora zani da alamu daga bacci ta tashi,ta kalli minal datayi tagumi tana kuka ga katon leda ahannnta,tace yar uwa badai wayannnan yan iskan bane suka tabamin ke






Kara rushewa da kuka minal tayi ta labartawa azixa labarin safwan


Zama turus aziza tayi jikinta yayi sanyi lukus;shikenan wahalarsu ya dawo,tunda gatansu ya tafi


Minal ta kalli aziza tace a a Allah zai kawo mana chanjin rayuwa tunda naga sarkan gold din umma da ta dade tana nema.
*labari yanzu aka soma karku damu da gajertar page,labarin tanada tsaho*
Da yanma zancigaba


By
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: _PERFECT WRITTER FORUM_
*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-5
By
Maryam yarmama
Dedicated to my fans








Ihun murna aziza tasaki,umma data fito daga bayi,itama butar dake hannunta ya subuce ya fadi tace dagaske kinga tsarkan dana dade ina nema iye




Minal ta kwashe labari tabawa umma,murna umma tafara tana godiya ga Allah,haka rami sukayi auka binne sarkar saboda sunsan idan su abba sukaga ba sarkar gwal dinnan, zasuzo nema




Bude ledar safwan sukayi,makudan kudine aciki zasukai dubu dari biyar,ga katon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login