Showing 21001 words to 21630 words out of 21630 words
maganganu kasan bana jin fulatanci to ban gane
abin da take faɗa ba.
da sauri mukhtar ya cire wayar sa , daga kan kunnen sa , sai kuma ya mayar yace '' asim shaɗi
fa kace ?.''
Asim yace '' mukhtar zan faɗa maka karya ne?.''
Mukhtar yace '' a'a amma asim kai ne ya saka ka amince da kayi mata wani wayon mana ni
gwara a daura auren daga baya iyayen ta , sai su sani amma kamar kai da fuskarka ba
boyayyiya bace za kayi shadi.''
yar dariyar rainin hankali asim yayi yace '' ta dauke nima rago kenan ta raina ni mukhtar ina da
fa kudi kuma kasan kudi ba yaren da basa ji, zan bawa saurayin ta ta hakura yabar min ita.''
Uhmm uhmm asim kasan me ake nufi da bararo (bararoji ) ? Wallahi Allah ba jinsin da yakai su
taurin kai da kafiya da tsayawa akan ra'ayi ɗaya karka taro abin da zai fi karfin ka ba ko wanne
yare, kudi yake ji ba wallahi ko anan akwai wa'yanda kudin ka ba abin da za su yi musu kai duk
talaucin su asim baka gogu da jama'a ba , rayuwar da kayi rayuwar jin dad'i ce baka san
wannan hali al'umma suke ciki ba ka tashi girman turai ka dawo nan ka buɗe asibiti ka fara aiki
a jami'a dan haka , duk a bin da na faɗa maka kayi shiru kawai.
ASIM yace '' kaga kan ka ake ji yanzu gida zan tafi gwara ayi ta da zafi zafi zan fadawa mommy
kaga sati na gaba tafiyar ta america ta fadawa su kahu sunusi suje sune mo min auren ta kai
shadin ma zan iya tun da afiyaaaah ta faɗa min amfanin auren ta.''
Mukhtar yace '' ashe itama ta gano amfanin auren ta?.''
Yayi hakane domin ya lura asim baya cikin hayyacin sa kai wannan AFIYAH Ubangiji Allah ya
kawo silar rabuwar su , ya raya wannan a cikin zuciyar'sa
ASIM yace '' eh wallahi.''
Sallama suka yi ya kashe wayar.
shiga toilet yayi, ya wanke hannun sa ya fito haɗa kayan sa yayi, ya fita daga office ɗin kai tsaye
inda ya ajiye motar sa ya nufa, buɗe wa yayi ya shiga.
cikin kwanciyar hankali yake tuki ba wani abin da yake damun da har ya isa gidan su horn yayi
me gadi ya buɗe mai.
tura hancin motar sa yayi ciki har ya isa parking space.
parking yayi, ya fito ganin motar aunty jidda yasan boom ta zo baya jin tsoran kowa amma ita
da kahu sunusi za su iya cewa basu yarda ba fitowa yayi ya dauki brief case ɗin'sa ya rufe kofar
motar 'tasa.
cikin izza da katsai ta haka yake tafiyar sa, komai nasa abin sha'awa ne kofar da zata sada shi
da parlour mommy ya nufa.
shiga yayi bakin sa , dauke da sallama aunty jidda ta ture dauri gaban goshi da sauri tace ''
yauwa zo idan ita uwar taka , ta zuba maka ido to mu ba zamu zuba maka ido ba wallahi nan ba
DUBAI bace da zata barka sangameme dakai babu aure.''
ASIM ransa ne ya ɓaci tun yana yaro ya ƙi su aunty jidda saboda a gaban kowa cin mutuncin
mahaifiyar sa, suke ya rasa wannan ɗabi'ar tasu da mahaifinsa ya faɗi ya mutu tamkar an
tunzura su, suka ƙara ƙarfin ci mata mutunci musamman ma kahu sani da yace zai auri mommy
ta ƙi yarda shikkenan ta ƙara bakin jini a gurin su.
Littafi fa ya kusan karewa free page me kuke jura ku hanzarta biyan kudi kar ayi babu ku.
Amina alhasan Muhammad opay 1k
8141785374
Ku turo da shedar biya ta wannan number
08141785374.