Showing 9001 words to 12000 words out of 21630 words

Chapter 4 - JAMI'A BOOK HAUSA NOVEL BY OUM YASMEEN.pdf

27 Sep 2025

3441

fa
ba iya ke kaɗai ba ko wacce mace ba zata taɓa burge shi ba ki zauna yi tunani.''

charity ta faɗa tana saurin barin gurin.
shiga toilet tayi ta kifa kan'ta a jikin bango tana sakin wata ajiyar zuciya hawaye suka shiga
sintiri akan fuskar ta.

cikin parlour kuwa sosai maganganun Charity suka ratsa ta , ta shiga auna su da sigar ma'aunin
magana , tana son tantance gaskiya ta zabe hanyar da taga zata fi mata saurin isa ga burin ta..

Wannan kenan

kallon sa mukhtar yayi lokacin da ya gama dai-dai ta parking din sa yace '' gaskiya inhar zan
baka shawara ka dauka asim be kamata kamar kai, ana ganin ka da mutunci da ƙima ba a cikin
ƙasar nan , ka ɗinga mu'amala da wannan yarinyar wata ran fa wallahi ba wanda ya isa ya
kankare ka daga zargin mutane, wannan asim ba matar aure bace kalli mardiyya yarinyar kirkir
ko ba ma ita ba akwai mata wa'yanda gidan su gidan tarbiyya ne , be kamata dan ba ran
mahaifin ku ba , ace kai da kake babba ka kasa samo mar kwarai ka aura.''
Asim yace '' daga anyi magana kace mardiyya to ka aure ta mana kai ni bana son village girl ba
abin da suka sani ba abin da suka iya gidadawa ne me zan yi da mace ba wayayyiya ba ,
wannan yarinyar da bata fi yar ciki na ba.''

Mukhtar yace '' hmmm gaskiya kayi nisa baka jin kira ni kai nake yiwa sha'awar ta , wallahi da
ba dan ina maka kwaɗayin auren ta ba , da tuni ni zan aure ta na jima ina bincike akan yarinyar
da dabi'un ta.''

ASIM buɗe kofa yayi ya fito domin idan yace zai tsaya jin maganganun mukhtar tofa ransa ne
zai ta ɓace , ai ta magana ɗaya da ba dan yasan asalin mukhtar ba sai yace maye ne wannan
magana taki ƙarewa, shifa tun da yaga yarinya ƙarfe 11:30 na dare a waje wata mota ya sauke
su ita da kawar ta yaji ya tsane ta ta tsani mazinaci gwara wanda zai fito da halin sa amma
masu saka hijabin nan mafi a kasari yan iska ne fakewa suke da hijabi.

dariya mukhtar yayi yace '' asim wallahi kana son yarinyar nan akwai abin da yake danne maka
son ta a cikin zuciyar ka.''
cikin hassala yace '' mukhtar dan Allah zo ka tafi gida na gaji magana kaɗan mardiyya idan bata
yarda da contract ɗin nan ba ka samo min wata, inshallah zan cikawa mommy burin ta.''
zama ta yarda tana da buƙatar kudi.
mukhtar ya fadi haka yana fitowa daga cikin motar.

ASIM yace '' macen da take yawon dare ai bata da wata bukatar kudi saboda tana samun abin
da take so.''

Mukhtar yace '' asim dan kaga mace a hotel an sauke ta hakan baya nuna cewa ita yar iska ce
inhar bakai ne ka gani ba da idon ka a gaban ka sukai iskancin in haka ne muma sai suce mana
munje kamawa karuwan room.''

wallahi Allah mukhtar kana da kafiya ni kaga sai da safe ina da abin yi.

Mukhtar yace '' kai da kake gauro ma kace kana da abin yi balle ni da nake da mata.''

dariya asim yayi yace '' rai dai.''

Mukhtar yace '' oni jikan rufa'i dan balaraben nan yaji hausa har da su ƙarin magana.''

banza yayi mai ya fara tafiya ganin haka mukhtar yace '' ka gaishe da mommy kace mata sai
da safe ni gida zan tafi.''

''TO.'' kawai asim yace.

juyawa zai yi sai yaci karo da tukunyar da aka saka flowers, kaucewa yayi yana dariya ya buɗe
motar sa ya shiga.

wannan kenan.

MARDIYYAH kwana tayi tana neman zaɓin Allah bayan ta gama sallah ta zauna tana karatu
idan ta tuno da jarabawar asim za su yi gaban ta faduwa yake bayan anyi sallar asuba bacci ya
kwashe ta.

karfe bakwai daidai ta tashi cikin sauri ta shiga toilet cire kayan ta , tayi shaf shaf tayi wanka ta
fito sanye da hijabi har ƙasa ramsi da take kwance kamar bata san da yau suna da jarabawa
ba.

SUHAILA da ta gama dafa musu taliya da manja da yaji daman tabar mardiyyah ne tayi baccin
da jiya bata samu tayi ba , tun da jarabawar karfe tara ce da rabi.

akwatin ta ta buɗe ta dauko manta ta shafa bayan ta gama shafa mai ta dauki bra din ta da pant
ta saka sannan ta dauki riga ta atamfa robber ta saka sannan ta cire hijabin ta.

SUHAILA tace '' tab kalli yadda kanki ya tsofa kamar ba shekaran jiya nayi miki wannan kalbar
ba.?.''

Ramsi tace '' a yanayin kan mardiyya wannan kitsom ma ai ya dade tunda gashin ta yana da
santsi.''

SUHAILA tace '' Hakane wallahi.''

MARDIYYAH janyo plate din taliya tayi gaban ta tace '' ramsi bismillah.''

zaro ido ramsi tayi tace '' Ni a'a rabani da kayan ulcer.''

hararrata suhaila tayi tace '' kema ke kikai mata tayi kim manta ita yar gayu ce kayan
gwangwani ta iya ci..?.''

mardiyya murmushi tayi bata ce komai ba da yake ita bata fiye son yin magana ba sau tari
mutane me girman kai suke kallon ta ,
gama ci suka yi, suka wanko hannun su, turare ta fesa wanda idan ba kusance suka samu da
mutum ba , ba me iya jiyo kamshin turaren nata.
fuskar ta , ta wanke ta saka hijabin ta jakarta ta dauka da yar ƙaramar wayar ta kirar nokea me
madanne sakata tayi a aljihun rigar ta exam card din ta , ta dauka da biron ta sai takardar da
take karatu.
suhaila ma tuni ta shirya cikin abaya Egypt ash colour ta yi roiling da mayafin ta , agogo ta
daura ta dauki jakar ta yar gidan dior ta rataya.
da yake mahaifin suhaila yana da rufin asiri haka ma yan uwan ta ita ce mace kaɗai dan haka
suke nuna mata gata ta ko ina tafi mardiyyah da iyayen ta ba yau babu gobe, wata ran ma sai
su kwana basu ci ba , yan shanun da suke dasu sun ƙare yanzu sauran guda biyu kuma duk
maza balle suce zasu tatsi nono su sha, gwara yanzu ma da baffa yake amsar kiwo yana fita
dasu shine har yake samun wanda zai aiko mata.
shi ya saka bata biye shigewa suhaila ba duk da ita , take janta a jiki kuma ba ta nuna mata
banbanci so tayi ta samu daidai da ita.
dafa ta suhaila tayi tace '' tunanin me kike yi..?.''

da sauri ta kalle ta , tace '' bakomai mu tafi ko?.''

Ramsi tace '' lokaci yayi ne?.''

Suhaila tace '' a'a 9:30 zamu shiga.''

okay inama da lokacin ci gaba da bacci na ba ma lallai na shiga ba ni wallahi bana kaunar jin
sunan jarabawa.

banza sukai mata suka fita.
kan'ta a ƙasa jikin ta duk yayu sanyi haka suka sauko ƙasa lokacin har ma'aikatan da suke aiki
a reception sun zo gaisawa sukai da madan Sophia.

sannan suka fita daga cikin hostel din gaba ki ɗaya theatre da zasu zauna zana jarabawa nan
suka je suka zauna a waje tun da malaman ke bawa mutum set number da zai zauna kullum
cikin canza set number suke.
ci gaba sukai da karatun su har lokaci yayi gaban tane ya fadi ganin motar asim ta zo dab dasu,

yan mata da samari da suke gurin sosai hankalin su ya karkata akan sa, iya dukiya da ilimi
Ubangiji ya ba shi uwa uba kyau da tarin ilimin addini dana boko shi ya saka yan mata da yawa
suka mutu akan son sa.
driver sa ne ya fito da sauri ya buɗe mai kofa ya jima be fito.

da alama wani abu yake me mahimmanci a cikin motar, fitowa yayi yana sanye da ɗanyar
shadda up white gezna an mai aikin monogram Black colour harta takalmin sa da hular da
agogon sa duk black ne wayar sa ce a kunnen sa da alama waya yake yana kallon a gogon
hannun sa.
cikin isa ya soma taka stair case din da zai shiga cikin theater.

mardiyya tashi tayi domin ta bashi hanya ƙirjin ta , na dukan uku uku.
ko kallon inda take beba balle ya nuna yasan da mutum a gurin.

sauran malaman department din sune suka tawo da booklet da kuma question paper a hannun
su cikin wata leda an rufe ta sai a lokacin zasu buɗe ledar iya matakan tsaro sun zuba shi a
gurin.

ajiyewa sukai yi a lokacin suka kafe set number kowa yake ya duba tasa ya dauki number sa
mardiyya ita ce number ta farko gaban tane ya ci gaba da bugu shiga cikin theater tayi checking
din ta wata mata tayi, ciro wayar ta , tayi ta bata ta ajiye mata da yake haka suke yi , Sannan ta
zauna a gurin ta suhaila yana can karshe.
fara rabon booklet suka yi asim miƙa mata tata yayi tana tunani bata san ma ya zo kanta ba
cikin ɓacin rai ya daka mata tsawa.

da sauri ta kalle sa gaban ta na faduwa fuskar'sa a haɗe kamar ko da yaushe yace '' get are
out.''

da sauri ta buɗe baki za tayi mai magana yace '' karki sake ce min komai fita baki shirya yin
jarabawa ba tun da har kina da lokacin tsayawa kiyi tunani.''
jikin ta a sanyaye ta tashi idon ta duk ya ciko da kwallah gaba ki ɗaya kowa kallon su yake ji tayi
tana neman faduwa ko ganin gaban ta bata iya yi fita tayi ta zauna a kofar theater.
kifa kan'ta tayi akan gwuiwar ta , ashe ma kuka harama ne a wannan karon kukan yaƙi zuwar
mata shikkenan yanzu tana ji tana gani jarabawa biyu ta rasa su.

Mukhtar ne ya ƙaraso yana cewa baiwar Allah me kike yi nana..?''

da sauri ta ɗago kan'ta cikin sauri yace '' mardiyya ba jarabawa kuke ba me ya fito dake..?.''

bakin ta na rawa tace '' doctor asim ne yace na fita ban shirya zana jarabawa ba wallahi ba i na
sane nayi mai banza ban san ya zo bani booklet ba wallahi ban masan an fara rabawa ba dan
Allah ka bashi hakuri.''

tausayin tane ya kama shi yace '' okay taso.''

tasowa tayi jikin na rawa ashe har an bada izinin fara rubuta jarabawa, magana yaje yayi wa

asim dakyar ya yarda ya barta ta zauna mukhtar ne ya bata booklet da question paper amsa
tayi tana dubawa asim harde hannunwansa yayi a kirji ya kafe ta da ido.

amina alhsan Muhammad opay 1k

8141785374.

ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785375

*JAMI'A*


*Episode 5*

Ƙasa tayi da Ƙan'ta zuciyar ta na faman bugu, ajiyar zuciya ta sauke ganin abin da, ta karanta
shi ya fito.
fara rubutu tayi hannun ta yana rawa saboda tana jin kaifin idon sa a jikin ta.

ASIM mamaki yake gata dai ya ganta a hotel amma babu alamar jin dad'i a tattare da ita slipper
ne ma a kafar ta.

da sauri ya yi istigifari yana kautar da ƙansa , bakin glass din sa ta mayar kallon agogon da
yake daure a tsintsiyar hannun sa yayi goma da rabi dai-dai mukhtar ya matso kusa da shi ƙasa
ƙasa yace '' malam kabar yarinya ta rubuta jarabawar ta lafiya , ka dena kallon ta , bata zama
mallakin ka ba ka bari idan ta zama sai ka kalle ta.'' ji yayi kamar ya dunƙula hannu ya naushi bakin mukhtar ya zubar mai da haƙora yace '' wallahi
mukhtar ka fita s ido na , na rufe.''

dariya yayi yana matsawa daga gurin fita yayi daga cikin theater gaba ki ɗaya wayar sace ta
fara ringing ganin sunan afiya ɗagawa yayi yana karawa a kunne cikin sanyin murya tace '' beb
barka da safiya.''

jin muryar ta ba ƙaramin sanyi yaji ba a cikin zuciyar sa yace '' Barka dai kin tashi lfy?.''

hmmmm lafiya ba lafiya ba
AFIYAH ta faɗi haka Muryar ta na rawa.

cikin nuna tsantsar damuwa asim yace '' innalillahi wa'inna ilaihir raji'un me yake damin ki..?.''
kwallar da ta taru a idon ta , ta share tace '' kai ne asim abin da kake min wallahi bana jin dad'in
sa nunawa fa kake kamar baka yarda dani ba, asim son da nake maka ne ya janyo haka, da
ace kaga ban damu da kai ba wallahi ba zakai min haka ba , ni dakai yanzu mun zama ɗaya a
nawa tunanin.''

asim buɗe motar'sa zai yi sai ya fasa ya jingina a jikin'ta yace “Please be patient, I’m about to
get into the car now. Once I park, I’ll call you.”

AFIYAH jikin ta a sanyaye tace '' to ba damuwa.''
kashe wayar tayi zuciyar ta na faman nawa wani irin ciwo ba wanda take burin da son haɗa
shinfiɗa dashi sama da asim har yanzu tana mamakin sa bashi da wata buƙata akan'ta shi ko
soyayyar zamanin nan ba ruwan sa da ita kamar ba wayayye ba.
tashi tayi zaune ta kalle Charity da take bakin kofa ta , tsaya tace '' Charity anya kuwa asim
yana so na?.''

taɓe baki tayi ta ɗaga ƙafaɗun'ta tace '' waya sani.''

dafa kan'ta tayi tace '' Charity yaushe kika fara juya min baya ne ? ada duk abin da nake so
kema kina son sa.''

shigowa za tayi sai kuma ta fasa ta tsaya a inda take tace '' saboda kina kaunar Musulmi shi ya
saka ni kuma bana kaunar ki dashi Linda ga maza nan a gari da yawa wanda sun fi shi komai a
cikin Christian babu masu kyawun da suka fi shi ne ?.''

ɗan murmushi tayi wanda iya labɓanta ya tsaya zuciyar ta cike take da wutar sha'awar ASIM ko
tunanin sa take , sai taji ta , a cikin wani irin yanayi na feeling babban burin ta be huce ta gan'ta
kusa da ita, tace
''Wallahi, there's no one like Charity ASIM is unique among men. Till today, I haven't seen
anyone better than him wallahi Charity asim ya haɗa komai sai dai ƙiyayyar sa ta saka ki kasa
gani ga iya kula da mace ga tarairaya.''

hmmm kawai tace ta juya ta fara tafiya zama tayi a kujera ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya limshe
ido tayi ranta duk a ɓace bata san taya akai ta faɗa wannan tarƙon ba ? bata da me bata amsa
cije lips ɗin'ta tayi wayar ta , ta ɗauka ta shiga cikin Instagram gaban ta har wani dukan uku uku
yake , ta shiga cikin inbox ɗin'ta duk da bata ga alamar shugowar sako ba, gaban ta ne ya faɗi
ganin ko alamar ya ga sakon babu, to wanne ne account din sa na gaskiya ko dai fake account
aka buɗe da sunan sa ?.
ganin zata wahalar da kan'ta ta , tashi ta shiga daki ajiye wayar ta , tayi ta kwanta akan gado da
sauri ta ɗago jin ƙarar buɗe kofa.

ganin Joseph ta ɗauke kan'ta, tace '' Joseph kai ne haka da sassafe?.''
ɗan murmushi yayi ya shugo yana rufe kofa yace '' wallahi kuwa kun tashi lafiya?.''
charity miƙa tayi tana turo kirjin tace '' lafiya sai godiyar Ubangiji.''

hawa kan gadon yayi yace '' me ya faru?.''
kwantar da kan'ta tayi a cinyar sa tace '' AFIYAH bata gane wa soyayyar wannan mutumin
maƙiyin mu ta rufe mata ido, bana son abin da zai saka Murphy's wallahi Allah zai iya kashe ta
duk da tana taƙama yana ungiyar Spreaders of the dark spell kasan Murphy's besan me tazo yi

nan ba ta rufe masa gaskiya tace ta , tazo yin wani bincike da yasan asim ta biyo ta ɓaro
*EASTERN CAPE (South Africa)* wallahi da sai ya hallaka su domin har ita ba zai bari ba.''

Joseph yace '' bata san irin tsaurin ƙabilar ta ba ? da zata dauko kwangilar da tasan zata iya
tarwatsa rayuwar ta Xhosa kabila ce da take da ƙima da daraja da take mutunta ɗan cikin ta ,
amma bata duba wannan martabar da kabilar mu ta bata ba shi ne take ƙoƙarin rusa mu tabbas
duk lokacin da Murphy's yasan har ta canza addini saboda wani ta canza suna ranar sai dai tayi
kwanan rami.''

wai waye adon tafiya.
KABILAR XHOSA

Tarihin Xhosa:
Xhosa ƙabilar Bantu ce dake kudu maso gabashin Afirka ta Kudu. Sun samo asali ne daga
tsofaffin mutane masu amfani da harsunan Bantu waɗanda suka fara zama a wannan yanki tun
shekaru aru-aru da suka wuce. Xhosa suna da tsari na kabilanci mai zurfi, da shugabanci na
sarakuna da manyan mutane. A tarihinsu, suna da al’adu da yawa na gargajiya, ciki har da imani da ruhun kakanni da
abubuwan al’ajabi. Suna da kyakkyawan tsarin zamantakewa da nishadi kamar rawa, waƙa, da
labarai.
Addinin Xhosa:
Yawanci Xhosa sun rungumi addinin Kiristanci tun lokacin mulkin mallaka na Turawa,
musamman Anglican da Methodist. Sai dai kuma, har yanzu akwai wasu da ke ci gaba da bin
addinin gargajiya na kabilarsu wanda ke da alaka da imani da ruhun kakanni da kuma wasu
abubuwan sihiri na gargajiya. Saboda haka, addinin Xhosa ya haɗu ne da Kiristanci da addinin gargajiya na kabilarsu.


Al’adun Xhosa Game da Bautar Kakanni

*Amadlozi / Amatongo*
A tsarin Xhosa, kakanni wadanda suka mutu (ana kiransu *Amadlozi* ko *Amatongo*) suna
da matsayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login