Showing 18001 words to 19651 words out of 19651 words

Chapter 7 - Zahra Yar Amana Book Complete by F.A Yau.pdf

P.A Yau   

25 Apr 2025

1991

soyayyar mu kodai fasa auran xa'ai tai saurin dagowa me kace nasan kinji
sabida me kace haka sabida na fuskanci da cutar wa kullum saina rokeki kice kina sona anman
koda wasa kinkasa ko sau daya fadamin yai dariya ai kaidinne ba sanka nake ba kai kuma ka
kasa fuskantar haka jira nake kace zahra kice kina kaunata sai ince Dr. Na ina sanka ina
kaunarka zan kaunace har bayan rai Dr. Na kasa aranka zahra me kaunarka ce zahra taka ce
tace baka jiba ya dago ina kaunarka tai ciki da gudu ya rungume hannunsa ak'irginsa dadi na
ratsashi yai murmushi ahankula yace zahra nima ina kaunarki jiyake kamar ya jawo auransu
adaura yanxu zahra kenan sarkin kunya zanso ganin ranar da zakice kina sona ba hanyar
guduwa inga yaxakiyi da kunya.
Yau su nasir sukaxo dan zuwa gidan baban zahra me rasuwa yau cikin farin ciki take dan
tana dokin ganin su duda tana tunawa da maganganun umma zahra ki daure ki mance damu
sai dai batajin zata iya mantawa da iyalin babanta wanda yasota alokacin da kowa ya kita taya
zata mance da ahlinsa kosu sun k'ita sunyi sa'a duk suna gida dan ummance ba lpy duda halin
datake ciki besa ta gane zahran ba zahra naganin halin datake ciki hankalinta ya tashi sai fada
take me yasa vasu kaita asibiti nan ta kamata sai asibiti.....



*Zahra Yar'amana*
*145-150*
*Na F.A.Ya'u*

_Wannan paging nakine_ *Rasheedat Isa Mrs Idris* kinfi _kowa san Zahra yar'amana ina
alfahari dake cikin Fans dina_

Koda umma ta warke kuka ta dinga yi kan tayi hakuri ta auri muhd kan zahra tace wani abu
nasir ya rigata ai nine mijinta sati me kamawa za'a daura auranmu umma tasake fashewa da
kuka ada ta hana zahra aure dan karta je inda zata huta sai gashi tasamu fiye da wadancan
inkyaune akwaishi in kudine yanadashi in illimine yanadashi ahankula tace wannan izinace
babu wanda ya isa ya hana abinda Allah ya baka.

Tun zuwansu zahra gidansu muhd Fadima da muhd suka kulla soyayya tun tana zuzzukewa
harta ware kankace me mgn taje gun manya.

Zahra ta ziyarci kawayenta su zafira ansha hira kuwa sunyi murna sosai anan ta basu katin
dan su gayyato former mate dinsu ba buk nan Zakiyya ke fada mt itamafa sauran wata daya
bikinta ita da muktar zafira tai shiru eyye wato harmun fara surukutar haba yarinya kema kinsan
inzanji kunyar kowa vanda taki suka sa dariya ai dannaga sai kifini sanin komi tai dariya zafiran
uncle zaem kenan.
Iya kyau kam amarya da ango sunyi kyau faden kyansu ma bata lokacine da yake andaura
aure wanda dubban jama'a suka shaida hakan yavasu damar ruko hannun juna ranar families
day sunyi kyau ba karya yan bikin kansu sunyi kyau.
Saida aka kwana biyar ana shagali kafin akai amarya gidan ta na wucin gadi kafin su wuce
german.
Rayuwa me dadi suka tsarama kansu momi yadda sukeso yake tafiya akullum kara kaunar
junansu suke basasan abinda zai raba su aikima adole nasir ke futa.
Wata daya da bikinsu akaina zakiyya da muktar zafira da zaem muhd da fadma shima nasu
bikin kam ya kayatar .
Ana gama biki suka tafi german inda Nasir zai karo karatu acan zahra itama tai karatunta
fanni noma wato agronomy shekararsu biyu acan ta haifi yayanta maza duk biyun sukaci sunan
babanta me rasuwa wato baban muhd dayan kuma baban nasir alokacin data haihu take ganin
kamar nasir zai sauya saitaga shi kamar ma alokacin aka bude masa babin kaunarta . Shekararsu hudu da aure yayan zahra biyar sun saba da uban dan ita kullun tana sch be
kuma yadda da daukan nany ba dan tunda ya gama nasa yakoma dan raino ko makaranta baya
bari ta tafi dasu suna gunsa .
Zahra na gama karatunta suka dawo gida Nigeria sunyi kyau sosai da yaransu kaikace
turawane inba mgn sukai ba dan sun dage yaran sun iya hausa dan basa son yaran su taso
bada yarensu ba koda suka dawo nasir be shawara da itaba ba ya sayi fili ya gina mata
tamfatsetsen kanfani na sarrafa kayan noma sai budewa akaje yi da ita tai murna sosai ta gode
masa kan kace me kanfanin ya shahara ba iya Nigeria ba harda sauran kasashe makofta.
Yadda taga umma hankalinta ya tashi bata da lpy sosai muhd baya gari tunda yasamu
lecturing a ABU yakoma kaduna sai lokaci lokaci yakanxo matan duk suna gidajensu basu san
jikin yai tsanani haka ba hankalinta atashe takaita Aminu kano nan sukace saidai india zahra tai
komi kan futar umma waje . Zahra har niger naje ta dauko kakarta kawun babanta ya lalace ya zama abun tausayi shima

ta tawo dashi dakyar tasamu ta shiryasu da babanta ta bashi jari.
Har gida taje ta duba jafar suka yafi juna anan suka kulla xumunci har bikinsa taje ummansa
tai ta neman gafararta tace ai vakomi.
Koda umma ta dawo ta warke simul tai takuka tana kara neman afuwa ayau ta kuma yadda
da karin maganar bahaushe dana kowane kahaifa bakasan me moraba gashi ita anhar mata
zahra uwatta tarasu ita tana mora.
Zahra zaune tana bin yaranta da kallo yan biyu na game mansur na rubutun haddarsa smally
ta fado kanta tana dariya yayin da hafix ya biyo ta mamanmu kinganshi ko ta tareshi haba
yarona nasanka da hakuri kaifa babbane mai tamaka itace ina wasa da tsuntsuna ta sakeshi ya
gudu wallahi mamarmu bansaniba ya gudu to kaji bata sani ba ayi hakuri zan siyo ma wani
yasa ihuuu yawwa mamana shiyasa nake sanki waima mamanka mamanmu dai ke kuma
wayasa dake mamanmu kinga yanaimun rashin kunya ko kul yayarka ce vata hakuri sorry sis ya
wuce tace mamanmu bakice sagira ta ban hakuri ba bashi hakuri ta turo baki sorry bro yai
dariya its a bygone issue ya wuce Nasir ya shigo rige da jaka ta mike ta katbo jakar ta cire ms
takalmi da rigar sama tai ciki da lemo ta fto yakarba yana kara wash tace ansha aiki kedai vari
wanka ko ci duk wanda kika ce girmanki ne ai to shikenan wankan ai saimuje ko ta dangabe kai
baka ganin da yara ya kwaikwayi maganarta to ainima yaron ne kayi hakuri kaje pls kiyi hakuri
mu tafi tare pls tasan halinsa dan haka ta dago shi muje ko sukai dakinsa tana shiga ta fito da
gudu tana dariya ya kada kai shima yana dariyar yai bayi.

Wai in tambayeki yn cin abincin yn mgn mai kika zubama abincinnan naji yana zaki zaki aff
mantawa kai daci daci yake ohh haka nefa me kika xuba masa maganin mallaka inaso kaxama
mijin tace yai dariya yarinya kin makaro aini kan tace ne Allah ko kina mamaki ne ya kurbi
lemon lalala yanaji zafi kamanta tafasa yake suka saka dariya baki daya. Yana zaune yana kallonta tana shafa mai ya mike yana tayata shafawa sukajiyo kukan sagira
ya lakace mata man a hanci ya fice yana fita ta fada jikinsa tana kuka dakyar yasamu tai shiru
mene ba yaya ce ta dokeni ba to muje haba yaya me ya hadaku ba itace na aiketa taki xuwaba
haba sagira kidena kiwa ke kuma banda duka ya kwantar da ita kan gadonta yaja musu vargo
ya musu addu'a yawwa yan yarana sai da safe zahra ta turo eyye yaranka ma ko to sarkin kishi
yaranmu.

Dakin yan mazan suka wuce sagir na game sulaiman yai bacci hafix rubutu nasir ya kwace
rumote din game din zahra ta rufe littafin naxa akwanta dare yayi suka lullubesu suka rufo musu
kofa sikai waje.

Rayuwa kenan wataran tasaka dariya wataran tasaka kuka wai yauni zahra nake dariya
nakejin dadi nakeda miji da yarana masu sona masu burin faranta mun Allah kabarni da iyalina
ta vaya taji ya rungumota Amin maman sagir tana dariya ta daga kai ta kalleshi yadaga mata
gira batasan afili take mgn ba ahankula ta kuma cewa Alhamdulillah. Nima anan nake cewa Tammat billah daya bani ikon kammala wannan labari lpy.
*Godiya*
Gaduk wani ko wata da yabada time dinsa ya karanta wannan labari fatan duk kuskuren dake
ciki za'amin afuwa dan adan ajixine nayi labarinne dan ilmantarwa nishadan tarwa bawai dan

cin zarafin kowa ba wanda yaga wani abu da yashafeshi akasine bawai danshi naima
kirkirarrene ba labarin wata ko wani bane.
*Abin lura*

_Komi na duniya dan hakuri ne ba'a taba dawwama cikin yanayi daya_
_Dana kowane kishi kan yaya ba namu bane mata dan bake kika haifa ba bai kamata ki
dinga azabtarwa ba bakisan wane anfani zai miki agaba_
_Abin da Allah ya baka ba wanda ya isa ya kwace koda zai hado duk duniya_

*Taki Dabance*
*Salma Ali Wada*
_Loves u fans badan kuba da tuni nadena rubutu karfamin guwa dakuke kullum yasa nake
kara dagewa dan kara saku cikin farin ciki_
For comment,correction or advice u can contact me bear.
Http://fayau26wordpress.com
09028287218
F.A.Ya'u facebook page

*Nagode*

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login