Showing 9001 words to 12000 words out of 19651 words
tare da xara sai
yadinga jin haushinta zahra ta kasa gane kansa dan kullum ynx sai sunyi fada yaita mt fada.
Takanas umma taje gidansu jafar ta fadawa umman jafar aikuwa tahau ta xauna fada kamar
mai taima umma godiya.
Abu kamar wasa sai gashi yaxama gaske dan mahaifiyar jafar tace ita bata yadda adaura
auran ba ta inda tashiga batanan tashiga ba mahaifin jafar bai dauki abin da mahimmanci ba
ganin ya dau abin dawasa dan hk taje tasanar da innarsa taxo tai ta bala'inta indai yasake aka
daura bashi ba ita yai ta bata hakuri dakansa yaje ya samu yayanta yace ya vashi lokaci danyai
buncike.
Kawun nasa yakirashi kamar yadda nace mk xanyi bincike nayi abunda suka fada hakane
yarinyar batada asali yayarsa taxo da ita daga kaduna kawu yafa tabvatar mana shine ya
haifeta ehto koshi ya haifeta to bada aureba.
Inko haka ne gaskiya malan sule bai kyautaba ta yaudaremu aida sai ya sanar damu komai
inmumga xamu iya muyi gaskiya koda inada niyyar dana ya auri yarsa tunda ya rufeni baxan
yardaba.
Koda yakoma gida yakira jafar ya fada masa yadda suka yanke bai wani damuba dan daman
kwanannan hanya kawai yake nema da xasu rabu balle kuma ga wannan mgnr .
Tun abin vai damun zahra har yaxo yana daminta rabonta dashi yau sati biyu kenan takirashi
yafi a kirga akashe wataran kuma ta kari ringing dinta yaki dauka tunaninta ko baida lpy dan
haka yau tasa aranta after lecture xasu je gidansu itada su xafira dan dubo ko lpy.
Basuyi maganar ba jira take sai anfito ta musu mganar lecture dinma gaba daya batasan mai
akeba duk bayan minti kadan sai ta duba wayarta ada indai xasu shiga ajaka take ajiye wayar
anman yau tana hannunta ji take karta ajiye jafar ya kirata kamar ance duba ta duba alamar
sako ta gani ya shigo tana ganin daga jafar ne ta saki wani murmushi da batasan ma ta sakiba
bata wani jiraba ta bude shi.
*Assalamu Alaik*
*Bana bukatar tambayar yaya kike ko lafiyarki dan banjin kin cancanci haka*
*Zahra ban tabajin ko ganin axxaluma munafuka macuciya kamarki bantava tsanmanin kedin
haka kike ba zahra kin cuceni mai yasa tun farko kika kasa fadan ke wace ko da yake kinso
munafinta ta keda macucin marikinki da kike fafa dashi inasan kisani ki kuma daka aranki babu
ni babu ke ki mance dani pls kamar yadda na dade da cireki araina kitaima kawa kanki ko
sunana kikaji karki tuna dani balle kiyi tunanin kin taba soyayya da me sunan*
*Jafar*
Hawaye ne kawai ke bun fuskarta da gudu ta mike tabar ajin tama mance a lecture room take
gaba daya suka bita da kallo malamin ya tabe baki gami da watsa hannu alamar i don't care ya
cigaba da abinda yake.
Da'ace lokacin da zahra ta tari adai daita sahu tasan idan taxo gida abin da zata tadda kenan
dana san wani gun xata ce ya kaita ba nanba.
****************
Malan mahaifinta ta gani tsaye yana hawaye wasu mt na xaxxaga bala'i sina ganinta suka hada
da ita sukai mta tatas taja malan sukai ciki dan ita saima taji gaba daya kukan ya dauke.
Ada zahra vata taba yadda malan bashine mahaifinta ba bata taba yadda batada iyaye ba sai
yau tabbas buri yayi kama da mutun dan ko bahaushe yn cewa ba rami mai yakawo rami.
Ganin malan baijin dadi tun bayan abunda ya faru yasa zahra takasa tunkararsa da batun da ke
ranta duk tabi ta rame tai fiyat baka ganin komai sai dogon hancin nan idanunta sun fada
alamar cuta.
Tun bayan cin kashin da'aka ma malan jiki yaki dadi kullun cikin cuta da wannan an samu ya
lafa sai wancan tun yn iya fita har abu yaki dadi makarantarma xahra ba koyaushe take xuwaba
tana kula da malan koda muhd yaxo hutu dakyar ya roki malan suje asibiti ai kuwa suna xuwa
aka basu gado jininsa ya hau sosai ga xuciyarsa data kamu . Hankalinsu ya tashi sosai abu kamar wasa ciwo yaki dadi daga karshema nasarawan suka
maidasu Aminu kano.
Yau kam jikin dadan sauki zahra na xaune akan kujerar da ke gefen gado malan na bacci
muhd kan tabarma yana bacci duda itama din ba cikakken bacci take ba tana dan
gyangyadawa sama sama kamar daga sama taji muryar malan zahra bakiyi bacci ba tai saurin
bude ido eh baba ya miko mata hannu tai saurin kamo hannayen gani baba kece zahra eh nice
baba sai gani tai yana hawaye sannu baba ciwonne bari na kira doctor yi xamanki ba ciwo bane
inaso muyi mgn kaf labarinta ya bata har yadda yaxo gurinsa kiyafemun xara'una naso kaina da
tun farko ban bari kinsan iyayenki ba ban bari kin taso da sansu ba sai nasa miki sona da
kaunar yan uwana na bari kullum addu'arki akaina take karewa bacin iyayanki suka fi bukatar
addu'arki tasa hannu tana goge masa hawayen yayin da nata yaki tsayawa haba baba ka daina
neman afuwata ko kadan ni baka mun komai ba nasan kamun haka ne dan kana sona duniya
banda wani uba bayan kai umnata kuma Allah ya jikanta kije dakina xakiga wata akwatu to ciki
akwai dan wasu abu buwan na ummanki to baba Allah yakara sauki jitake kamar tai tsuntsuwa
taje gida dan yau xatace ta rike wani abu na ummanta . Washe gari sukai sallama da malan tai gida dan kawoma muhd abinci.
Tana xuwa gida dakin malan ya shiga tahau dube dube taiko sa'ar ganin akwatun a kuryar
daki jikinta na tawa ta bufe ba komai sai hotuna guda biyu sai yan takardu na makaranta ta
bude hoton matasa ne guda biyu mace da namiji sanye da uniform din hygiene sai dayan
macen ce kawai . Kallon hoton take cikin ranta tana jin dadi duk su biyun sun kwanta mt arai wani sansu ke
shiga ranta ta rungume hoton a kirjinta sai takejin dama ummanta ce ta rungume da yau tafi
kowa jin dadi bata wani dade ba tai asibiti dan tanasan xuwa ta tambayi malan ko dayanne
mahaifinta duda kuwa taga kamarsu daya amman tafisan tabbatarwa. Su aunty xulfa tagani duk sunyi tsaye a bakin dakin muhd nakai kawo tai saurin xuwa gun anty
xulfa aunty lpy ya jikin baban yana ciki tun daxu likitoci ke kansa ana hira kawai sai haki kinga
har yanxu basu fitoba sai hawaye wayyo babana Allah ya baka lpy kaine gatana kai kadai
karagemin banida kamarka xulfa ta ruketa kiyi shuru zahra xai warke Doctor ya fito yana share
gumi gaba daya sukai guns ya kallesu ya dubi muhd biyo ni office ku kuma ku jirashi sukai office
din.
Naga kai kadaine na miji yan uwan naka duk mata ne nasan xaka fisu dauriya duniya ba
matabbata vace komai yai farko xai karshe sai kunyi hakuri likita ban fuskance kaba ya jikin
malan din jiki kam yayi sauki cuta ta tafi na har'abada malan yaje inda ba'a dawowa muhd yasa
salati sai hawaye likita bai hanashi ba sai dayai mai isarsa sannan yace Allah yajikanka baba
ynx likita xamu iya daukan gawar yana fita gabaki daya su shidan da yayansu da sukaxo sikayo
gunsa yana ganin yan uwan nasu sai kuka tausayinsu ya kara kamashi musanman zahra suna
ganin haka suma suka fara kuka aka rasa mai rarrashin wani muhd yai ta maxa ya je yasamo
mota suka dauki gawar sai gida.
Zahra bata kara yadda ta rasa malan ba saida taganshi kwance cikin likkafani kan makara jitake
kamar karya ne babanta xai tashi masu daukan gawa suka daukeshi sukai waje wani sabon
kukan yaxo mata ta mike xata bisu juwa ta debeta ta xube yub jama'a suka kanta.
A hankula take bude idanta da xatonta aranta tana fadin Allah yasa mafarki nake anman mai
mai makon ta dora idanta kan malan kamar yadda in ta suma shi take gani kanta sai ta dora
kan wasu kuka ya kwace mata shikenan na rasa babana mai sona tasani duniya bata da
kamarsa wayyo ni na shiga uku shikenan babu wanda xata bugu kirji tace shidin mai santa ne
tasani komai da yafaru akan ta ne wayyo kai cona .
Bayan arba'in malan salihu abokin malan ne yaxo da wasiyar malan kan yace yanasan a hada
auran zahra da muhd sannan ya bata dakin mamarta kyauta daman gadon yayar tasa ne ta
kuma bata da sahannun doctor sai shaidu biyu umma ta hau ta dire ina wallahi bata yadda
shiko muhd yace ina sai ya cikawa babansa burinsa. Tun tasowar zahra muhd yake santa saidai sirrin da mahaifinsa ya boye yasa ya kasa
bayyanawa dan gudun wani abu ya tabbatar dashi ya bayyana baban ya rasu baxai taba
yafewa kansa va.
Aure kam ansa rana komai anma zahra muhd sai rawar kafa yake waishi ango abunda umma
bata saniba yadda batasan auran xahrama haka bata so tanai ma muhd din karane kawai dan
wani sa'inma intaga ya xage yana mata kalaman soyayya ko yana kokarin faranta mata har
mamaki take wato shi namiji baida kunya ko kadan yama manta ita kanwarsa ce ita inyana wani
abun kunyama yake ba. Yau sauran sati guda auransu da muhd har mamaki take wai ita xata auri yayanta koya xasu
xauna da umma ko xataso xurriyarta aikema kinsan baxata taba soba muhd ya tafi xariya dan
karbo wasu takardunsa zahra na kwance umma ta shigo da sauri ta tashi xaune adan tsorace
dan ita bata taba ganin xuwan umman ya xame mt alkairiba.. So nake in rokeki alfarma ki taimake ni ki bar gidannan dan Allah ki daure ki bar mn gidanmu ki
tai mk ki bar mn xurriyarmu ta huta dan Allah kibarni ha karasa rayuwata cikin jin dadi ina
tabbatar miki inkika ci gaba da xama damu tabbas nima ciwon xuciya xai kasheni kamar yadda
ya kashen miji ta durkusa tana gawaye wallahi zahra na tsaneki ki daure kisa aranki kin taba
rayuwa damu zahra ta mike basai kin rokeni ba xan tafi insha Allah xanyi abinda kika ce harta
kai waje ta dawo au dankinga ina rokonki shine xaki dawo takarduna xan dauka ta diba dana
ummanta tabar gidan gaba daya kwakwalwarta ta tushe ta manta da kowa da komai kidaure ki
mance kin taba rayuwa damu abinda take tunawa kenan to yaxatai ta manta dasu kibar kanon
kawai tabi shawarar xuciyarta sai tasha tana sauka a adai dai ta samu taji mai lodi na fadi kanya
babura magarya batun yauba taji ana cewa magarya nijar ce xuciyarta ta ce to mai xai hana
kibar Nigeria dinm tinda kowa yaki acikinta ta aminta da xuciyarya dan haka kawai ta shiga.
Hatsarin ya farune dai dao lokacin da suka wuce kanya wata mota ta tunkaro su mai motarsu
yai kokarin kauce mata saidai mai ya kasa yai dadi inda ya daki wata bishiya baiko shura ba
yayin da da dama suka suma wandama basu sumanba basusan inda kansu yake ba inkadaike
wani yaro dake kuka kan ummansa yana ta tashi rayika kam anrasa.......
*Zahra Yar'amana*
*95-100*
*Na F.A.Ya'u*
*wannan paging naki ne zulaihat Abdullahi isa (my zuly)*
Cikin wadanda basu san inda kansu yake ba harda zahra dan tayi mummunar buguwa ga
karaya kafa da hannu banda daddaujewa.
Kai tsaye asibitin garin aka kaisu abin yafi karfinsu taimakon gaggawa kawai suka iya basu
aka wuce dasu asibitin koyar wa dake xariya har sukakai su asibitin zahra batasan inda kanta
yake ba.
Sai da zahra tai kwana bakwai da barin gida sannan muhd ya dawo dauke da tsaraba kala
kala wadda inka dauke tsirari duk na zahra ne a kokarinsa na kyautata mata daya ke da
yadawo masallaci ya wuce koda ya dawo daga masallacin yaga umma taxubo ms abinci iya
saninsa dik runtsi zahra ke zuba wa kowa abinci bai ce komai ba zatonsa ko umma ta sauya
tsarin ya cinye ya baima umma tsarabarta bega tsaraba nan xuciyatsa ta dan zargu duda yasan
xahra ta sauya anman hakan baisa ta dena bashi girma ba ya mike gami da ture kwanon
abincin yai dakinta wayam yaga dakin sai kura da tarkace da yada da haushi yakara kuleshi
iyakar saninsa da zahra bata kaxanta tun tn yarinya to dan mene se ynx data girma adan
fusace ya fito yana tambayar umma wai ina yarinyar nan ta shigene taji tambayar kamar daga
sama gabanta ya yanke ya fadi ta hade rai wacce yarinya fa umma zahra fa nake nufi au kace
karuwa haba umma inda kara kodanni aikya rangwantawa xahra yanxufa surukarki ce ta xaro
ido rufan asiri dannan Allah ya kiyashe ni da surukuta da wannan tambadaddiyar maras asali
naji umma ynx dai tana ina tatafi yawan ta zubar dinta kasan ta tsotsa a mama yadan kada kai
umma mai kike nufi abinda nake nufi shi nake nufi yau rabonta da gidannan har na manta
rabonda nasata a idona kwana bakwai mun kwanta da ita bamu tashi da itaba kasan
tsintacciyar mage malan kesanta anman ita batasan malan da xurriyar malan tunda gashi dan
kawai yace ka aureta ta gudu bai karasa jin batun ummanba yai waje idansa ya kada yai jawur
iyakar kololuwar tashin hankali hankalinsa ya tashi fatansa Allah yasa tn gidan su zaem koda
yaje suma hankalinsu yai mummunan tashi dan bataje ba tun rasuwar malan sukai sukai ta
dawo tace tunda da ran malan bai bada itaba bayan ransa baxata vada kanta ba gidansu xafira
yaje da xakiyya suma hankalinsu atashe yasa mesu dan sunxo nemanta fanin bata xuwa sch
umma ta koresu.
Duk inda muhd yake tunanin zara na xuwa yaje ba labarinta nan ya kom asibitocin dake garin
kano da police stations babu koda mai kama da ita.
Muhd ya kasa dangana akullum ranata fito akullum sai ya fita sati uku kacal da batan zahra
yabi yai baki ya rame muhd da yake fari doga mai yar giba dedai shi shine yai baki ya rame kai
kace yai jinya ne.
Tun jafar naganin abun kamar wasa har'abu yaxama babba kullum baya iya bacci sai tunanin
zahra tabbas koda jikinsa sun abince sun br xahra xuciyarsa baxata taba iyawaba sai ayanxu
yakejin haushin kansa toma wai ada mai yasameshi bashi da buri ayanxu inbanda yaga zahra
yasani da wahala ta iya yafe ms anman xaiso gwada sa'arsa koda sau dayane shi ya amince
koda daga sama ta fado yanxu xai aureta.
Yau yai niyar zuwa har hall dinsu dan bata hakuri ko mai xata mai yaji xai jure yau sati uku
kenan yana jele tsakanin faculty dinsu danasu zafira baya ganinta inda suka fara haduwa kuwa
kullun sai yaje babu kosu xakiyar yasani tanasan gurin tasha fada masa watakil yanxu ta tsani
wajen duk lefinka ne inji xuciyarsa . Yau kam lecture dinsu gabaki daya ba wadda bai shiga ba saidai ba xahra dan haka yana
fitowa yai faculty dinsu zafira koxaiga daya daga cikinsu zafira ya hango suna mgn da wani ta
hangoshi ta hade rai baima kula da yanayin fuskarta ba dataga da gaske ita ya doso dasauri
tace muklis mu hadu anjina ok yace tai saurin yin gaba ganin haka yasa yadan dada sauri pls
zafira badanniba dan sanki da annabi dan girman Allah ki tsaya kariga ka cuce ni ka hadani da
wanda ba'a hadani dashi nakiyi minti uku xan iya baka taja ta tsaya inajinka daman xahra nake
san gani tadan xaro ido ne kace yasan taji bai kasa aguwwa ba ya mai maita wai wace xahran
kake nufi xahra nawa kikasan inada ta tabe baki lallaima kai harkana da karfin guwar kiran
sunan xahra ka kirata taka kai harka na da damar kiran zahra taka mai yasa ne wasu mutanen
gabaki daya basa aiki da kwakwalwarsu to inasan fada maka burinka ya cika zahra ta bata inma
neman ta kake ka karadata to sai kaje ka xuba ruwa a kasa kasha tai tsaki tabarshi nan tsaye
kamar dutse.
Tunda ya koma gida ba'abunda yake iya tunawa sai batun zafira burinka ya cika zahara ta
bata gabaki daya haushin kansa yakeji yakasa ko sau daya yaji xafin xafira na maganganun
datai masa da gaske xahransa ta bata kuma a dalina gaskiya baxan tava yafema kaina ba.
A hankula take bude idanta dishi dishi take gani daga bisani ta dora idanunta kan fankar dake
wulgawa a ta maida kallonta gefe inda tai arba da robar jinin dake shiga jikinta gefenta kuma
wata ce kwance daure da robar ruwa hakan ya tabbatar mata tana asibiti ne ta yunkura xata
mike da sauri doctor din dake rubutu kusa da ita ya komar da ita hihakuri kina da ciwo ne ta
daga ido ta kalleshi sannu ko ya kike jin jikin bata ce komai ba kingaji da kwanciya ko tai shiru
nurse da ke baima wata magani ya kira sister tagaji da kwanciy xaunar da ita to doctor ya wuce
daya gadon sai da yagama round dinsa ya dawo gadonta badai abin dake damunki ko bata ce
komai ba illah ta bishi da ido.......
*Zahra yar'amna*
*100-105*
*Na F.A.Ya'u*
Baxan gaji da gode miki ba
Zulaihat Abbdullahi Isa amaryar gobe.
Asannu ahankali jikin xara ya a kyau yau satinta na biyar kenan a asibiti yanayin kulawar da
likitan ke bata yasanya tadan bafara sakin ranta dashi yadamu sosai akan rashin lafiyarta duda
ta kula halinsa ne haka bawai ita daya yake ma haka ba