Showing 12001 words to 15000 words out of 19651 words

Chapter 5 - Zahra Yar Amana Book Complete by F.A Yau.pdf

P.A Yau   

25 Apr 2025

1989

duk marasa lafiyar dakin na yabonsa.
Sunyi sabo sosai da doctor nasir dan har mahaifiyarsa ya kawo ta dubata abincinta da magani
duk shine.
Yau bashi da aikin safe na dare gareshi dan haka yashigo asibitinne dan duba jikin xahran
xaune yake kan kujerar dake gefenta suna fira kai kace sun shekara da juna can yace kinga
yanxu kin warke sarai sai abinda ba'a rasaba ina xatonma jibi xamu baki sallameki tai dariya ai
doctor da temakonka komai yai dedai intambeki mana inajinka wai ko ina xakuje kukai
hatsarinnan taishiru can tace magarya yai dariya ashema yar kasarmu ce kinsanfa babana da
dan niger ne a wane unguwa kuke a magarya nima bansani ba tace yakada kai badai kyasan
fadamun to yanxu bananba ko number din wani naki ne kibani nakirasu dansuxo daukanki sai
hawaye nan yahau rarrashinta saida tai mai isarta haba zahra kiyi hakuri mn innan miki wani
abu kiyi hakuri ta share hawayenta doctor baka mun komai ba wallahi tunawa danai cewar
banda kamar kaina bani da wani daxan bugu kirji inkira da masoyi na yasani kuka uwata ta rasu
marikiyyata me sona yarasu babana yarasu banda sauran wani da xankira mesona haba zahra
rashin iyaye bashi ke nufin baka da kowa ba sai kace mara dangi taisaurin cewar haka nake
doctor banda dangi iyayena basu da dangi yakada kai kodai kin bar gidane bakisan komawa ta
fuskanci me yake nufi wato zata yawon duniya nan ta baahi labarinta tun daga wayonta har
yaxuwa inda sukai hatsari ya tausaya mata sosai .
Koda ya koma gida yasanar da iyayansa komai na xara suka tausaya ya rokesu alfarmar zai
kawo zahra gidan suka amince.

Koda aka sallami zahra kai tsaye gidansu zahra aka wuce da ita dakyar nasir yasha kanta ta
amince dan cewatai tafisan tai rayuwarta ita kadai bata son takara sabawa da wasu karshe su
gujeta karba ta mutunci ta samu kannensa biyar Fadima ita ce kusan sa'ar zahran dan haka
dakin fadimar ta sauka duda tadan girme mata . Yanayin yadda suke mata yasanya ta gamsuwa iyalan gidan sun san darajar mutum ko daki
ta shige sai fadima ta kirata tun tana dari dari harta sake ana komai da ita duda har yanxu tana
dingisawa haka ta daure komai na aikin gida take yi duda kuwa sunada masu aiki.
Yau suna zaune a falo tadan kalli mumy mami pls ki rokar min dad atai maka a bincika mini
kayana gurin police tai dariya yanajinki ai yace indai bata da bakin fadi mini ni baxan jeba tai
dariya pls dad to shikenan xan dubatai godiya.
Dady da mu'allim da ita sukaje suna gurin aka bugowa dad waya yanada baki a office anan
ya barta ita da mu'allim ya wuce an futowa da zahra kayan tai sa'anata yananan da yake yan
tarkace ne takarba sukai gida da mu'allim.
Hoton ummanta kuwa kullum sai ta kalleshi na tsawon lokaci kafin tai bacci ji take kamar
ummanta ce take kallo wani abu dake bata mamaki bai fice daya saurayin dake kusa da
ummanta ba kamarsu da dadinsu Fadima take gani sai dai takasa yadda gani take kamar
idanunta ke ganin haka dan haka tabar batun aranta.

*Zahra Yar'amana*
*105-110*
*Na F.A.Ya'u*
Yau zahra sun fita da fadima dan dady yaima abokinsa dake nan college of health zariya mgn
kan yanasan form yai sa'a kuwa yace taxo ta karba dan ya gaji da xaman da take saidai tai girki
ta kwanta yai takaicin katsewar karatunta dan cewarsa damar da tasamu bakowa kesamunta ba
ta karatun likita. Gidan shiru nasir ya shigo yan aikin gidanma duk suna bangarensu mami ce kawai a xaune
tana kallo ya xauna kujerar gefenta gami da cewa wash ta dan kalleshi yadan rissina mami
sannu da gida ta amsa da yawwa yau ina yan matanki naji gidan shiru daxunnan suka fita
nasan yanxu suna hanya nasan wannan uwar gantalin ce ta jasu ko tai dariya kaidai kanasan
dorama fadima lefi to ba ita ce ta jasu ba aiken dady ne yasosa keya alamar jin kunya ya mike
yunwa nakeji wallahi yau mai aka dafa mn mutuminka ne ya yamutsa fuska kai fadima bata
kyautawa wallahi tai dariya nasiru kenan to dai yau ba fadima ce tai girkinba zahra ce mami
sanin tane bakiyi ba tsaf xatasa zahra ta dafa dan tasan banso oho dai kaji dashi Allah dan
inajin yunwa ne da baxanci ba kaga ni karka isheni inbaka ci xaka iya bar mana abunmu be
kwantai ba yaxanyi haka xan tuttura.
Duk runtsi nasir be cin abinci awaje danshi irin mutanan nan ne masu kyan kyami hakan
yasanya dasunyi tsiyar da yan matan gidan sesu fara dafa abinda beso musanman fadima da
basa rabo da hatsaniya seta jera sati tana girka abinda beso.
Yana mita ya bude kular hadadden kule le ne a ciki wanda yaji hanta kwai da attaruhu
kamshin ya bugi hancinsa baisan ya cinye duka biyar dinba sai da ya tsiyayi lemon dake
gefensa lemon amarba hade da madara mai sanyi yaji wani sanyi ya xiyarci kirjinsa yakai hannu
dan sake diban ala la yaji wayam mami ya fada ta kaga ni ka isheni inbaka ci kabar min abuba

ba adole wai kuwa kinga abinda suka ragen a'a tace wai aras mai xa'a ragen sai alala guda biyu
tai dariya ni nadauka ma daya ne kaida baka iya cinye biyu haba ashe daya ne nake xaton biyu
ne shiyasa ban koshiba tai dariya gaskiya zahra ta ciri tuta ka cinye alala biyar kace biyu ne na
sara mata ya suri jug din lemon mami se nadawo ina kuma xaka min da kofi mum kinsan aiki
inyai yawa in ina korawa dashi na rage xafi tai dariya ashe iskanci ne da yake sawa kake cewa
bakasan kule le yasosa keya mami duk cikin yunwa ne kaji dashi ta fada.
Koda su zahra suka dawo sunci dariya ai kuwa da ya dawo fadima ta takura masa da tsokana
yai dariya ai duk cikin yunwa ne kaidai kawai kace kaji dadin abinci eh naji kema kiyi xuciya ki
iya adinga jin dadin naki ki dinga yima mutane abinci kamar magani aiko fade kake fadima
badaga nan ba wajen girki yai dariya girkin turawa ba sukai dariya gabaki daya. Tunda jafar yasamu labarin batan xahra komai ya kwance masa damuwa tabi tai masa yau
asannu ahankali yake ramewa iyayansa sun kasa gane masa tunsuna fada sun koma nasiha
abu kamar wasa sai gashi shine harda kwanciya a asibiti ganin yadda ya tada hankalinsa kan
batun zahran yasa kakarsa da babarsa sukace asirine duk inda sukaji me mgani sesunje karshe
wani malami ya fada musu ba'asiri balle shafar aljanu tsabar damuwa ce ganin dagaske xasu
iya rasashi yasa mahaifiyar tasa yadda kan cewar ya auri xahra mahaifinsa da kawunsa sukace
ina su kunya sukebji baxasu iya roko malan ba tace ita xata ummansa ma tace xata kharima
wadda lokacin karbo kaya harda ita agaba gaba wajen rashin mutunci tace xata haka suka
shirya suka tafi.
Umman muhd ta amshesu hannu bibiyu muhd dake gefe bai ganesu va ya gaidasu cikin
mutunci daman mai gidan mukaxo nema muhd yadan gyara Allah sarki hala baku samu labarin
rasuwarsa ba fatan lpy suka jajanta gami da musu gaisuwa kafin su dora da batun da yakawosu
gwaggwo harda karfin halin cewa ina sirikar tamu ne ko tana makaranta muhd bai bari umma
tace wani abuba ya fara.
Sai yau kukasan shegiya nada anfani kenan ai nadauka kudin masu tsarki kamata yayi kuje
ku nemi mai tsarki irinku ku masu kudi kanku kawai kuka sani wato kunci kashinku akan baiwar
Allah yanxu kun lallabo dan ku karasa ruguxama zahra farin cikinta wato kashe mn uba da
kukai be isaba sai kun dawo to wallahi ku sani indai ina raye ni muhd to xahra ta fi karfin family
dinku saidai ya mutu cikin fushi da daga murya yake mgn pls kunga ku tashi kubar mn gida tun
kan inci mutuncinku cin mutunci na nawa kuma tunda bka duba firfira taba yai tsaki da Allah ku
tashi dannasan baku da gado cikinsa haka suka bar gidan jiki ba kwari aikuwasuna fita umna tai
kansa da fada sin sin ya fice yabar gidan dan dai uwa uwace da'ace umma ba ita ta haifeshi ba
akan xara xai iya komai sedai uwa duk rashin halinta tafi karfin raini akan dan tudun kofar gidan
ya xauna besan sadda kuka ya kwace masa ba.
Mami wai ina yaran nan ne yansu sukai sama xasu shirya wai yau birthday din isma'il yayan
salma nasan sarkin yawonnance ta shirya musu kamar kasani ana xaune daga daga waya ta
azazzalesu su tashi su tafi ai dole xa'aje shan xaki dan Allah mum wai banyi kyauba mum
takalleta inji ai ko gasar kyau kyaxo ta daya tasa dariya daman nasani ba wannan mu'allim din
bane wai ban kyau ba kyaleshi bakin ciki yake danshi baki ne inji nasir yai dariya bayan da
bleach aka wanke ki kina jari riya kinajinsa ko mum kyaleshi kai kinji ummi na zahra suka sauko
sanye da irin kayan ummi sunyi kyau sosai ina iklimar inji mami tace wai zulaihat ce xata xo ta
fasa binmu to shikenan fadima ta dau key din dake kan center table din dakin mami mun dau
aran mototarki nasir da tunda suka fito hankalinsa gaba daya ya koma kan xahra tai masa kyau

sosai mami se mun dawo harsun kai bakin kofa nasir yace kutsaya nakai ku kai yaya kai yaya
kai kullum se kadinga takura mana inbaxan kaiku ba kwa iya koma wa ba dole suka yadda
saida yagama wulakancinsa yai wanka sannan ya fito duk akan niyarsa nasu fasa dan wani
kishin zahra yake ji. Gabaki daya suka hakince a baya yako hade rai mai kuke nufi ce muku akai ni direba ne
fadima tace ummi tashi ki koma gaba ta turo baki tabdi Allah vaxan komaba pls aunty xahra
koma wato ni kika raina kunga ku nake jira inna koma gida wallahi baxakuba xahra tace fadima
ki shiga adawo wa na shiga promise tace promise ta koma gaba duda ba haka yasl ba haka
yaja suka tafi cikin nishadj da farin ciki suke tafiyar kai kace basune daxi suke kunkuniba sai
hira suke irin ta yan uwa masu san junansu.
Har jikin motar ya rakota sunjima suna mgn wadda nasir baijin mai suke cewa ya sunyi kamar
minti biyar su fadima suka fito ta bude ta shiga gaba isna'il yadan rankwafo sai naxo ko ka cika
mai maita magana af kayi lefi baka gaida yayan muba babbama kuwa kinsan inkina kusa bana
ganin komai ya xagayo babban yaya afuwan a cunkushe nasir yabashi hannu suka gaisa bai
kawo komai ba xatonsa ko haka halin nasir din yake.
Tunda suka fara tafiya ba wanda yace kala dan nasir ya kure radio koda sukaje gida bau jira
sun fitaba ya bude ya wani buga mirfin kofar yai ciki fadima tace ram maxa ya baci muje mu
bashi hakuri inji xahra tab wallahi baxaniba aikodai nima baxani ba mai mukai masa inji fadima
ya huce nidai sai naje se kindawo kya dawo da sacacciyar gwiwa. Kai kawo kawai yake adaki zahra ta shiga afusace ya juyo nakiraki ne ta kada kai nadai xo
baka hakuri ne nace kunmin lefi ne ta ce a'a nadai dauka kodan mun dade ne no ba haka bane
pls xaki fita anman yaya anman what pls out sin sin ta fice jiki a salube....

*Zahra yar'amana*
*110-115*
*Na F.A.Ya'u*

Http:/fayau26wordpress.con

*Banhakuri*

_Ina mai baima masoya wannan Labarina hakuri sakamakon tsaiko da yasamu wajen rubutu
hakan ya farune sakamakon Exam danake anma yanxu alhandulillah nagama insha'Allah nan
bada jimawa ba xan kawo karshensa_


*Cigaban labari*

Jiki bakwari zahra ta fito daga dakin su Fadima ta gani bakin falon nasa suna ganinta sukasa
dariya ansace mata gwiwa wooo wani k'ululun bakin ciki yaxo mata wuya kamar tai kuka tadai
daure ta shanye to ya ranku fes inji ummi ai daman anfada miki kikaji anfada miki shi yaya anai
masa gwaninta ne dallah ni matsa ta turesu ta shige tai bayan gida dan karsu hangota. Zaune suke suna karin safe yashigo sanye da suite ash yai kyau sosai sosai rike da rigarsa

ta aiki ya'ajeta a kujerar dake falon yai dining area morning papa morning son anfuto kenan eh
barka da safiya mami barka ka makarafa wallahi inakwana yaya yaran suka hada baki
inakwananmu kannes ke xuban abinci ba ke anan gun inji Fadima fada masa dai inji dad haba
papa kai kake sawa yarannan na raina ni wallahi saunawa xance kadena kiransu dake sorry
papa Fati zuban abinci ta turo baki xatai magana kinga bansan raini maxa zuba masa inji mami
afusace ta tura masa gabansa yafara ci yana dariya yadan saci kallon zahra, zahra'u ba
gaisuwa bata kalleshi ba tace nagaishe jine bakaiba ok kinsan nazama kurma jiya bata ce
komai ba ta mike tabar gun dan ta fuskanci magana yakeso.

Da gudu ta biyo ta kinga Fadima banasan abinda kike mun kibani ita kuma tana dariya
inkinga na baki saikin min alkawari abayan Nasir ta buya yaya boyeni tana ganinsa ta guya tana
fadin ki cinye zahra zahra yake kwala mata kira tai kamar batajishiba tai ciki ya ture fadima dake
bayansa ke barasa wace irin mutunce kin fiye tsokana sekije ki bata hakuru tunda kinsa tai fishi
ta turo baki kai yaya kullun ni kake baima lefi ta shige ciki tana sambatu yasa dariya kowa
datasa rigimar ya fuskanci zahra fishi take dashi yarasa me yasa takasa fuskantarsa yarasa
meyasa takasa gane kishinta yasashi yin haka bawa yai dan bata mata rai vane.

*Zahra Yar'amana*
*115-120*
*Na F.A.Ya'u*

Http://fayau26wordpress.com


Fadima ya gani kwance afalon ah yar hutu yau baxa'a sch din bane bata vashi amsaba sai
daga kai datai bai damu darashin amsarba yace meyasa baxaki ba ko baku da lecture zahra
dake saukowa tace bata da lpy ne ayya ya fadi gami da saurin taba jijinta subhanallahi tun
yaushe tasha magani a'a ya mike bari na kawo miki tai saurin tashi nafa warke ai bance baki
warkeba ungo sha ta yamutsa fuska ko kisha ko inmiki allura wallahi takarba tasha dakyar sai
asannan zahra tace ina kwana yaya lpy kalau ya fice tashiga dakin mami, mami na tafi kisa
fadima ta koma daki nasa taci dangakali dakyar to zahra saikin dawo Allah bada sa'a amin
mami.

Tsaye taganshi jikin motarsa tai kamar bata ganshi ba ganin sun gaisa ganin ta wuceshi yasa
yakira sunanta zahra taja ta tsaya na'am yaya kefa nake jira zan saukeki lah yaya karka makara
zan hau bus yadan kalli agogonsa yanxu bakwai tai haryanxu da time xatai magana yadora
hannu kan bakinsa shiiii alamar tai shuru karkice komai muje ko tashiga sunyi tafiya me nisa
yadan kalleta zahra tace na'am fushi ake dani ko haba yaya aika fice inyi fishi dakai ko eh mana
inda tai dedai da shigarsu makarantar ta bude ta fito tadan rankwafa nagode yaya tai ciki.
Tsaye suke daga gani gaba daya sunajin dadin hirar dasuke yadda take yawan murmusawa
kallo daya zaka musu kayi zaton sunyi shekaru suna soyayya yadda saitin hancin motarsa ya
kallosu haka idonsa akansu lokacin yai dedai da sakin dariyarsu gabaki daya wani kululun
takaici ne ya zo masa wuya jiyai kamar yaje ya shake matashin dasuke tare yafi minti goma

amotar kafin ya fito baiko kalli inda suke ba yai ciki wai meyasa zahra ta kasa fahintar abinda ke
ransa meyasa takasa fahintar shi ba santa yakeba face kaunarta kaicona ya fada gami da
dukan bangon.

*Zahra Yar'amana*
*120-125*
*Na F.A.Ya'u*

Http://fayau26wordpress.com


Zaune suna kari ummi tace papa kaface in akai albashi xaka bamu kudi muje shopping to
lashe money yaushe na fada kai papa kai papa sunan banza ne fa kuma kace no bad names in
islam yai dariya ah lallai yarinyar angirma sai aure tai saurin cewa papa when are u giving the
money waini yaishe nace zan bada tace Allah ka fada yadan daga kai alamar tunani anya kuwa
Fadima tace lokacin da malan me karatun juma'a yace maka sun iya hadda ohhh na tuna yanxu
dai ku bari ayi albashin muslim yai saurin cewa jiyafa naga kana lissafa kudi mami tace to kajifa
baxaka musu wayo ba towo kace inada sa'idinawa suka sa dariya baki daya ya mike vara naje
karna makara kibama yaran dubu bibiyu manyar shida shida suka saka ihoo that's our real papa
zahra tace mungode papa gabaki daya suka hada baki thank you papa sauran akwaxo alawowi
aikaima kasan su zasu kwaso inji mami.

Ya jima yana kallonta daga gani tana cikin nishadi kallon ball din da muslim da mua'allim sike
take ya fiskanci muslim take goyon baya dan tin tsayawarsa ya ga in muslim yaci saita saka
ihuu goal yayin da in mu'allim ne sedai ta vata rai zuciyarsa ke azazzalarsa yaje kusa da ita ya
zauna ahankula yake tafiya hakan besa taganshi ko jin takunsa ba sai kamshin turarensa daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login