Showing 24001 words to 25151 words out of 25151 words
Chapter 9 - The Sexxy Boss Part 4 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
zura hannayen sa cikin rigar ta mai kama da yar shima ,jin yanda yake mata wani salo daɗi sama da ƙasa yasa ta sakin dariya tana faɗin ' Pls Ahhh ya Umair , Jin yanda yake kutimbule da nonon ta haka bakin sa na cikin nata yasa ta sakin jikin ta don dole tana dariya ....
***
Bayan watanni bakwai.'
Ƙwance yake ya kasa ko motsawa , Ita ko Umaima sai kaiwa da komowa take tana haɗa kayan ta kaman wanda zata bar ƙasa . Sai zufa take tsohon cikin ta na a gaba shi kam kaf idanun sa na akan ta da abun dake cikin nata . Ta ƙara cika da ƙiba sai huci take na masu ciki , Sai tukuki take a dole ta gaji da masa magana. Miƙewa yayi yana maida laptop din sa yana rufewa ,kana ya kariso inda take , hannun sa yasa yana amsan jakarta tare da mayafin ta , ɗago idanun ta tayi tana kallon sa tana shirin masa maganan lokaci na ƙurewa ne taji ya zagaya ta bayan ta yana hugging ɗin ta . Hannun ɗaya yana shafa cikin ta da watanni 7 kenan . Babe How do you feel ?. Uhmmmm ta Saki gunguni tare da cewa " I'm okay dear , mu tafi don ALLAH bikin Fati ne fa ,kaima kuma bikin Aminin ka ne Julyb duka makusanta ne a gare mu , kana ta wasting time , nice first lady . Murmushi yayi yana kallon ta cike da zolaya yake bin ta da kallon kina da wannan tsireren cikin kike ce ma kan ki first lady?.
Fahimtar kallon da yake mata ne yasata kai kallabin ta tana wurga masa , saurin riƙe kallabin nata yayi yana shirin magana cikin shagwaɓa tace " Kai ka ja mun yanzu ,ban je Zaria ba har an kawo ta Abuja yanzu sai dai naje a baya kuma da yamma... To ai itama tace ki bari idan an kawo ta kwa haɗu saboda bby na na wahalar dake kwana biyu . Ya ƙare maganan idanun sa na a juna biyun jikin ta .
Numfasawa tayi tare da cewa " Bani kallabina na daura ,in ba so kake sai bayan magriba naje gidan ba.murmushi yayi yana miƙa mata kallabin duk da aso samun sa baiki ta bari sai gobe ba ,kar ta fita a yau .
***
Abun kamar a mafarki Fatima Da Umaima suke ganin al,amarin nasu . A hankali Umaima ta kalli Fatima tana cewa " Duniya kenan Fati kin ga ALLAH mai iko , wasu ƙawancen a yaranta ake rabuwa dashi , wasu kuma a ƴammatanci kowa yana Aure sai ya kama gaban sa . Amma mu namu ƙawancen gashi ta kai mu ga Har girma har Mazajen mu abokan n juna ne Aminai. Dafa ta fati tayi tana murmushi kamin tace" Umaima Ke kikayi saladin komai ya faru ya wanzu haka , ina godiya da ALLAH da ya bani ƙawa kamar ki . Kamin Umaima tayi magana ne taji Muryar wata ƙawar Fatima da batasan a ina ta rorota bA tana cewa " ya kamata amarya ki shirya an kusa zuwa sayen baki .
Juyawa Umaima tayi tana bin ƙawayen su huɗu da wani irin matsiyacin kallo ,tana tuno da gulmar ta da Umair ,sai dariyar shakiyanci yake mata a dinner ɗin Fatima . Suna cewa " Ita baƙa yar lukuta mummuna ,shi kuma mijin kyau kaman shi yayi kasan sa tamkar balarabe . Malamai kowa ta tattara ta ƙara gaba baza'a yi sayen bakin Amaryar ba . Kowa ta tafi gidan tsohon ta tun da girma da arziki . Umaima tayi maganan cike da tsiya da tsiwa .
Jin haka yasa Ƙawayen kowa tattara komutsan sa ,don sun san wacece Umaima a tsiya haka suka fita kowa da cikin ta a zuciyar shi . Suna fita suna zage ² tare da tsine mawa Umaima har suka wuce angwayen basu sani ba ,cewa suke " Kai wannan mijin ta na kokari , kuma wallahi baki gan shi ba kyakykyawa , ita ga muni ga tijara . Watace a cikin su ta amshe gobe zamu dawo ku nuna mun mijin wallahi sai nayi mata snatching . Suka wuce Su Umair suna maganan . Dariya Umair yayi haka Julyb dake sallama da Abokanan sa kana suyi sallama da kowa ne , Su biyu suka nufo ciki.
***
Gyara mata mayafin take Fatima na buɗewa ,don ganin Angon ta da suka sha farara gexna sunyi kyau ƙwarai. Ganin haka Nan Umaima ta funcike mayafin tana cewa " dama kin ƙosa ki ganshi tun da Siyan bakin ma ba zaki bari ayi ba ai shikenan bude .
Dariya suka saka duka ,kana Umaima ta zauna gyefen Umair tana murmushi , Shi kuma Julyb yana zama kusa da Fatima . Kallon su Umair yayi kamin ya fara bude wurin da Addu'a kaman yaron Sudes , niko mmn teddy cewa nayi duniya labari , lallai Umair THE SEXY BOSS ko da yake yanzu ya sauya daga shiririta zuwa hanyar miƙaƙiyya kuma madaidaiciya . Bayan sun gama Addu'oi ne suka ɗan taɓa ba'a , miƙewa Fatima tayi tana cewa " Let's down and take a picture . Ke da wannan daren cewan Umaima tana kallon Umair da yake kallon ta , murmushi ya sakin mata kana yace " A'a mai zai hana mu je daga Falo . Dariya Fatima tayi ma Umaima tare da cewa nan da 2 mount Zamu zo ganin bby ,ki tabbatar da Yah Umair yayi Kama ba dake ba... Ji fan ta Tayi da wani kallo kamin tace " Ke wallahi kika sa tsiya yanzu zan koma maki Umaimatuwa ƴar lukuta ,Mai turancin Nan kin Manta Ni ko😂 Dariya suka saka dukan su , yayin da Fatima tace " Yanzu Ni kuma na koma Maki maths teacher 🙄 Y+X meye amsan?? Wani kallo Umaima ta watsa ma Fatima cike da shakiyanci tace " amma tsokana ta kikeyi ko Malama🫣?Y da X ai duka kalmomin turanci ne😂 Dariya duka suka saka har dasu Umair da Julyb ,Fatima na kallon Umaima tana tuno da faruwar Abin kaman a yanzu.......
*To masoya anan nake cewa "ALHAMDULILLAHkuskuren da ke cikin wannan labari ALLAH ka yafe mana ,wanda mukayi shi dai dai kuma ALLAH ka bamu ikon amfani da shi Amin.*
Garaɓasa ga masoyana wanda suka karanta wannan littafi tun daga Farko har zuwa ƙarshe THE SEXY BOSS , duk wanda ya ci tambayoyi na zan Basa ƙyautar Littafi na na gaba Inshaallh💃.
1) THE SEXXY BOSS Ina so ki faɗa mun abubuwa 20 da wannan labarin ya faɗakar damu ,dakuma gyarar da muka yi na ganin an wa'azantu ....Don Allah ban da yawan tambayata , idan kin rubuta amsoshin ki kiyi mun magana ta number na 08081202932 . Daga yau zuwa Safiyar gobe zamuyi closing date". Zaku ma mu iya sharing a groups namu don sauran masoya su samu damar su suma , zamu cire na ɗaya dana biyu .
*AISHA MOHAMMED (MMN TEDDY)*
*MA'ASSALAM🕊️🕊️*