Showing 12001 words to 15000 words out of 25151 words

Chapter 5 - The Sexxy Boss Part 4 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt

01 Jan 2025

4209

stairs a hade uku suka haye sai dai ganin ta tayi a wani makeken ƙayataccen bedroom Wanda a ganin ta tsaruwan shi yafi na ko ina . Saurin kallon sa tayi , kamin ta juya tana zame hannun ta daga garesa . Cike da mmkin take bin dukiyar da yayi kuka a wurin da kallo , kamin ta motsa bakin ta tana shirin masa magana ne ,ya katse ta da cewa " Wane ya baka wannan arziki? A ina kake samun wannan kudade??. Nasan shine tambayar dake a Ranki da zuciyar ki ,shine tambayar da zaki mun ko Umaima?. Ji tayi ƙirjin ta ya buga ,don tabbas shine tambayar dake bakin ta . Wannan wani irin masifaffen brain yake dashi ? Abun da take fadi kenan a Zuciyar ta... Gani tayi ya matso dab da ita idanun sa ya zuba a fuskar ta , wanda ta kasa kirar hakan , sunkuyar da kan ta ƙasa tayi kana ya cigaba da cewa " Umaima Ni haka Allah yayi Ni , ina da brain Ni kaina na san da hakan , a lokaci guda na fahimci dalilin zuwan ki , amma kin san menene? Tun a lokacin na kamu da ƙaunar ki a zuciya ta . Kuma ban kokarin Azabtar da ita ba ,na yarda da na kamu da Soyayyar ki Umaima , ina Son ki har Abada bazan iya daina Son ki ba , Pls ki Soni Domun Soyayyar da nake maki , kiyi min Alƙawarin ba zaki bar Ni ba ,ba kuma zaki guje mun ba Har Abada .




A hankali Umaima taji hawaye na sauka daga idanun ta . Saurin kai hannun ta tayi tana ɗaurawa a Fuskar Umair tare da tallabo kuncin sa . Ganin ƙwallah tayi a cikin idanun sa . Kai To meye na wannan hakan ne?? Tayi maganan a ɗan shagwaɓe , sai kuma tace" Hawaye ne fa naga Ni a idanun ka miji na.! Ware idanun sa yayi yana kallon ƙwallahn da ya taru ma ƙwarmin idanun sa na gangarowa . Juyawa tayi tana ware ware cike da tsokana irin nata ta fara cewa " Ina kuke masu tsaro ,kuzo kuga Hawaye A idon Boss ɗin naku Ƙyauta . Duk hakan na meye wannan ? Yayi maganan yana ƙare haɗe ta da jikin shi . Ku taho ku gani kunji , babban Soja kuma Arrogant boss Wai yana kuka ku taho ku gani a kyaut...maganan nata ne ya maƙale sakamakon jin bakin sa da tayi ya haɗe da nata yana shan mata tamkar ya samu alawan yara . A wannan karon bata yi yunkurin hanasa ba ,sai da ya tsotsa Son ran sa kana ya zare bakin sa yana kallon ƙwayar idon ta tare da faɗin " I love You".




Juyawa tayi tana kallon sa tare da cewa " Wai kai baka gajiya da faɗin " I luv you ne?? Sai kace Bature ko jinin sss....jan bakin ta tayi cikin sauri tana kama harshen ta , tuno da katoɓaran da take shirin yi , don Hajiya Turai ta sanar mata da komai na Umair , da dangin Mahaifiyar sa da mahaifiyar tasa da suka kasance turawa . Kauda kan sa yayi yana kallon Gyefen ta , tare da cewa " Me kike kallo ?. Yi hakuri.! Tace dashi tare da kallon sa . To ba karya kika yi ba ai , Ina Son ki sai na ɓoye na bar ma zuciyata ?. Girgiza kan ta tayi tana murmushi tare sada kan ta ƙasa. Kema kina Sona ai Bakya faɗa mun ne kin ɗauki ɗabilar Kunya ta Hausa Fulani . Murmushi tayi tana cewa " Oho ka rama kenan ?. A'a ba ramawa nayi ba. Yah Umair Ina Son Ka, A da baya ban san ina Son Ka ba , duk idan na tuno ka sai nayi kuka kawai , ƙawata Fatima ce ta faɗa mun hakan wai zuciyata ta kamu da Soyayyar ka . To amma yanzu ya zanyi da Momy na??. Kallon ta yayi kaman zaiyi magana sai kuma ya sa kan sa tare da manna mata kiss a saman goshin ta . Juyawa yayi nan tayi saurin riƙe hannun sa . Pls Yah Umair Ka Mai dani gidan Momy ,nayi maka alƙawari a satin nan zan dawo gidan miji na da zama , zama kuma ta har abada. Wani irin sanyi ne yaji mai daɗi yana ratsa zuciyar sa . I lab you my dear wf. Ohhh Koda kince bana Gajiya. Dariya tayi tana riƙe hannun shi muje ka koma dani to.....












*AUNTY MMN TEDDY*
*Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne Regular group ₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ku tura katin MTN ta wannan number 08081202932*




_Kuyi voting Sabon littafin da zai fito nan ba da daɗewa ba , yawan ƙuri'un da muka samu a cikin wa'anan guda biyun #MR ROMANTIC ko kuma #THE VIRGIN MAID , wannan sune littafan da zan fitar mana in ALLAH ya yarda , kowa na da daman zaɓan wanda yayi masa a ciki , wanda ƙuri'iur sa yafi yawa sai mu ɗauke shi mu fara in Sha ALLAH . labarai ne ko wanne mai ɗauke da sabon salo ,daban dana saura , tamkar yanda nawa alƙalamin yake daban dana ki Hajiya ta ,haka wannan labaran suke daban a cikin jarangiya , masu voting afara kaftowa lahiya💃_






Murmushi yayi yana cewa " Ohk ina zuwa . Juyawa yayi cike da takon sa na tsayayyen namiji ya nufi can wani coridor , juyawa Umaima tayi tana kallon gyefen da gyefe tana bin ko ina da kallo , Kaman baƙauyiya .
*Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne Regular group ₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ku tura katin MTN ta wannan number 08081202932*




_Kuyi voting Sabon littafin da zai fito nan ba da daɗewa ba , yawan ƙuri'un da muka samu a cikin wa'anan guda biyun #MR ROMANTIC ko kuma #THE VIRGIN MAID , wannan sune littafan da zan fitar mana in ALLAH ya yarda , kowa na da daman zaɓan wanda yayi masa a ciki , wanda ƙuri'iur sa yafi yawa sai mu ɗauke shi mu fara in Sha ALLAH . labarai ne ko wanne mai ɗauke da sabon salo ,daban dana saura , tamkar yanda nawa alƙalamin yake daban dana ki Hajiya ta ,haka wannan labaran suke daban a cikin jarangiya , masu voting afara kaftowa lahiya💃_






Murmushi yayi yana cewa " Ohk ina zuwa . Juyawa yayi cike da takon sa na tsayayyen namiji ya nufi can wani coridor , juyawa Umaima tayi tana kallon gyefen da gyefe tana bin ko ina da kallo , Kaman baƙauyiya .
Tana anan a tsaye ne taji takowar sa a gaban ta ya tsaya yana fuskantar ta tare da miƙa mata lemu a glass cup , ki Sha kana mu wuce. Mika hannun ta tayi cikin zumma tana amsa , tare da kai lemun mai sanyi bakin ta . Tun da ta fara Sha bata waiwayo shi ba sai da ta shanye sannan ta miƙa masa tana cewa ' to mu tafi. Jin shirun nasa da take expecting Jin maganan sa amma sai shiru ya biyo baya yasata saurin kallon sa tana zuba idanun ta a saman nasa , Gani tayi yayi mata ƙurrr yana kallon ta ,haɗa ido sukayi yana sakin mata murmushi mai dadewa a zuciya , Murmushin tayi masa tare da motsa bakin ta tana cewa " Ya Umair . Hannun sa yasa yana haɗawa da nasa tare da cewa " Mu tafi ".


***


Hajiya Turai dake ta aikin kaiwa da komawa ta hana kan ta zaune tsaye , Bakin ta sai motsi yake kaman mai cewa wani Abu , sai kuma ta kai ta kawo jikin ta na rawar kyarma .




Tako taji na takalmi Mai tudu amma sam bata juyowa ba daga kai ƙawon da take yi . Momy lafiya me yake faruwa ne??. Umaima tayi mata maganan tana ƙarikowa zuwa inda take . Cikin sauri Hajiya Turai ta juyo tare da sakin ajiyar zuciya kaman wanda aka mata mummunar bishara. Hannun ta takai tana riƙe Umaima tare da cewa " Umaima daga ina kike?? Kin je wannan makarantar ?? Allah ya kiyaye baku haɗu da Umair ba , da sai dai ayi wanda ba'a so. Kin san shi da zafi kaman.... Momy wai shine duk hankalin ki ya tashi haka ? To ai shi ya dawo dani yanzu ya koma .




Saurin buɗe baki Hajiya Turai tayi tana kallon Umaima , Kamin tace " Shi dai Umair ɗin?? Lallai Soyayyar ta gaskiya ce ba wasa . Tayi maganan a ƙasan zuciyar ta ,bata san saurin ya fito ba . Umaima ne tace" Momy kika ce mene?? . A'a shiga ciki mayi maganan daga baya . Ohk Umaima tace tare da juyawa tana barin Hajiya Turai anan falon da ta koma ta tsaya ƙyammm kaman soja .




Juyawa tayi tana ɗaga wayar ta tare da karata a kunnen ta ,Ohk Daddyn Fareesa Amma ya kamata mu duba al'amarin yaran nan , kar mu shiga masu hakkarin juna , Umaima tun ba yau ba ,ta nuna mun tana Son mijin ta ,abar su kawai su....Shiru tayi tana sauraren sa tare da katse nata maganan. Ohk to babu damuwa sai ka taho ɗin , Allah ya kawoka lafiya ".


***




Yau kwanan Umaima uku da dawo gidan Hajiya Turai , kullum sai Umair yazo bashi safe bashi rana bashi yamma ,kullum a aikin zuruntu yake , Wannan ya Dada faranta ran Hajiya Turai . Don tuni ta samu Ammie da maganan A shirya tarewan Umaima a satin nan , Wanda Ammie Maryam ta tsaida maganan a ranan Juma'a za'a taru ƴan uwa ,a ranan za'a tare da Amarya .


Jin haka yasa Hajiya Turai sanar mawa Su Baba da Hajiya Balki , acewan Hajiya Turai dangi da yan uwa su taho gidan ta anan Abuja a zauna ayi taron bikin anan gidan ta sai akai amarya , ɗakin mijin ta daga nan kowa ya watse .




Hajiya Balki ne tasa Bala'in kan cewa " ita sam a'a Gida za'a dawo da Umaima , ayi taron bikin daga nan sai su ɗauko hanyar Abuja . Nan baba Shima yace hakan za'a yi . Ana saura kwana uku tarewa Umaima da Hajiya Turai suka ɗauko hanyar dawowa gidan Hajiya Balki don dole ba don Turai taso hakan ba .


A ranan da suka sauka ,a ranan aka fara saka Amarya a lalle da sauran Abubuwan mu ta al'ada . Tun da Umaima a ka lukume ta a uwar ɗakar Hajiya Balki ,babu fitowa acewan Hajiya Balki shirya amarya ake yi . Mai gyarar Amarya kuwa tun daga Ƙasar mu ,wato Mali , aka ɗauko bhuzuwa da ta iya haɗa amarya ciki da waje .




Zaune ake a falon Hajiya Balki har da Su yaya Hannatu , Fatima ce ta leƙo tana cewa " Hajiya Ina Umaiman take ne??. Ai shigowa zakiyi daga ciki kuyi gulman taku .... Alama Fatima tayi mata da hannu , wanda Hajiya Turai ne ta leƙo tana cewa " Hajiya Angon ne dea yazo ya kasa haƙuri , saura kwana biyu amma sai zaƙwaɗi yake yi . Jin ance Angon yar jikalle yasa Hajiya Balki wangale baki tana Faɗin " Wayyo ALLAH sarki , Don Allah jika na ka kula mun da Umaimatu yarinyar kirki ce... Dakin ne kowa yasa Dariya , Umair da Julyb dake waje suma dariyar suke . Umaima Fito maza sako hijabi gudun rana...Kamin Hajiya Kaka Ta ƙare maganan ne Suka ga Umaima da hijabi tana cewa " Ku bani hanya ,don dama ita a takure take an rufe ta a daki zafi duk ya isheta.




Da ido Hajiya Balki ta bita a sarari tana cewa " Amaryar zamani kenan . Dariya Su yaya Hannatu sukayi kana suce " ai ke Hajiya kin rufe ta a ɗaki ba dole ta gaji ba. To ai gata nake mata ,mazan yanzu sai sunji mace ko ina zam³ sannan sai kaji zaman lafiya shiru ya ɗore .




Kamin Umaima ne ta fito Hajiya Turai ta nufi dasu Julyb ɗakin Halima Matar Ƙanin Baba , Wato Ɗan juma. Biyo bayan su tayi tana fiƙi fiƙi da ido saboda ranan dake kashe mata ido ,na ta daɗe bata fito haske ba . A hankali tasa hannun ta tana buɗe labulen tare da sallama .




Fatima ne tace Yauwa gata nan ma , Umaima ƙariko . Wow' mashaallh . Julyb yayi mawa Umair magana ƙasa ƙasa ta yanda daga shi sai shi zai ji . Ƙai Boss kaji Wani irin ƙamshi ,anya ta shiga hannu zaka barta tasha ruwa ma kuwa?? Kar fa ka kashe masu yar mutane ,don kasan kayi mata girma... Bige sa Umair yayi yana bin UMAIMA da ta ƙara masa wata ƴar lukuta , fatan ta sai sheƙi yake ta wani irin masifar ƙyau . Gyefen Hajiya Turai ta zauna , wanda kamin ta ƙare zama Umair ne yace " No taso muje mota muyi maganan acan Ni dake . Kallon sa Hajiya Turai tayi , Kamin Tayi magana ne Julyb yace " Kaji malam da rainin wayo ,me zaka yi mata a motan?? . Wurga masa Harara Umair yayi don ya gane ya ramfo sa ,sai cewa yayi kai fa ɗan iskan mutum ne . Na dai ji ku zauna anan cewan Julyb yana sa mawa Umair dariyar shakiyanci .




Hajiya Turai ne tace " Umair zauna , zamu baku wuri kuyi maganan taku anan ,Amma Hajiya Dako Rana bata barin ta fita ,sam ba zata yarda da fita har waje ba . Miƙa Julyb yayi yana kallon Fatima kamin yace " Ƙawar Amaryar mu taho muje naji me kuke buƙata . Murmushi Fatima tayi tana bin bayan sa tare da cewa " Ai su Fa'iza ma na hanya , kila da wani abun da Ni ban fadi ba . Hajiya Turai ne itama ta mike tana mawa Umaima wani kallo , wanda Umaima cewa Tayi " Momy na sani ai .






Kallon ta Umair yayi ,yana fahimtar duk wani shu'umancin na Hajiya Turai , don kallon ki kula dai tayi ma Umaima . Fichewa Hajiya Turai tayi a zuciyar ta tana furta " Shashasha . Bin bayan Hajiya Turai Umaima tayi da kallo , wanda kamin tayi Aune bata farga ba taji Umair ne yasa Mata fuskar shi tare da shigar da hancin sa yana shaƙar ƙamshin ji kin ta ,yasa kan sa baki ɗaya tsakankanin ƙirjin ta da suka ƙara cika na tsaban shan garirika , saurin matswa tayi tana yin baya tare da cewa " Yah Umair meye wannan kuma??. Amaryan kin yi kyau sosai , anya ma idan an kawo mun ke a washe gari zan iya matswa daga jikin ki??.






Banza ta masa tana cuno bakin ta a shagwaɓe tace " Nidai bana So.! Lumshe idanun sa yayi na jin wani yarmmmm komai nata tada masa da feelings take . Ohk Na bari Kinji .




Kallon sa tayi ganin yanda idanun sa har sun sauya , kauda maganan nata tayi tare da cewa " Yah Umair baka ga Yanda nayi ba , Wallahi Hajiya Kaka babu abun da take mun sai gasa Ni da zafin Uwar ɗakar ta , da ƙyar nake numfashi don Wahala . Kecewa yayi da dariya yana faɗin " duk ana gatan ta mu ne . Kaman ya kenan ? Tayi maganan tana kallon sa...!




VOTER'S
#THE VIRGIN MAID
#MR ROMANTIC
ZAƁI NAKY NE💃🕊️


*AUNTY MMN TEDDY*
*Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne Regular group₦300 VIP group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko MTN card zaku tura ta wannan Numbobi 08081202932*






A maimakon taji ya bata amsan maganan nata ji tayi yasa Hannun sa yana shafa gyefen Haɓar hannun ta . Saurin kallon sa tayi tana watso da idanun ta waje tare da kallon sa ,gani tayi ya fito mata da harshen sa yana mata wani Abu tamkar zai lashe zumar jikin ta . Tsoron sa ne ya kamata da sauri ta fin cike hannun ta daga gare shi , Tana Ficewa da gudu daga Ɗakin . Baiyi yinƙurin kirar ta sunan ta ,ko dakatar da ita ba , don ta san ba zata dakatu masa ba , ƙaɗan daga Cikin zalaman da yake akan ta ya nuna mata , wanda ya gagare hakan , Hannun sa yasa yana shafa kewayayen Sajen fuskar shi , Sauke Ajiyar zuciya yayi yana ɗaukar Wayar sa , text message ya tura mata kamin ya miƙe yana ficewa daga Ɗakin Halima .




Ke Umaima Mijin naki sun tafi kenan?. Umaima da ta laƙume a can cikin ƙuryar Ɗakin Hajiya Balki ne tace " Eh mana Hajiya kin fa fiye saka ido . Na saka ɗin , Bari ayi Auren a Tare kayana kaf zan ɗauko na dawo gidan naku sai naga ƙaryar ta tsiya.! Buɗe baki Umaima tayi cike da tsiwa zata yi magana kawai sai taji sako ya shigo ta wayar ta , jan bakin ta tayi shiru da sauri ganin Mai sunan me turo da saƙon. Shiru Umaima tayi tana dubawa , This is the begging of all ,I luv you forever my Wife. Begging Shine Umaima ta furta Ni ban fahimta ba , anya Ya Umair bai fara zaucewa akan Mace ba kuwa??? , Umaima magana kike yi ne??.




Taji Muryar Hajiya Balki , jan baki tayi shiru bata tanka ta ba ,a Zuciyar ta tana faɗin Hajiya Balki kenan Shegen Son Gulma .


***


A ranan Friday gidan Hajiya Balki ya cika yayi Al'umma ƙwarai ,Umaima mai jama'a mutanen ta tun na ƙuruciya duk sun shigo mata shagalun biiki yayin da kowa ke fatan Alheri tare da fatan itace matar har abada. Kowa ya shigo ya fita gidan Hajiya Balki da mamaki da jin daɗin irin dangin Ahalin da kuma Mijin da Umaima ta aura suke yi . Kayan Solveniance kuwa ,haka zaki ga Mutane na tahowa dashi hannu ciccike a wasu irin jakunkuna wanda da dama basu taɓa ganin irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login