Showing 3001 words to 6000 words out of 25151 words
Chapter 2 - The Sexxy Boss Part 4 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
wanda ku kayi alƙawarin Auree? Cewan Ammie tana dafa ta. Gyaɗa kai Umaima tayi a sanyaye tace " Eh Ammie. Sai kuma ta sunkuyar da kan ta ƙasa ,don tana jin nauyin Ammien.
Kam bala'i...! Wannan wace irin shashashan yarinya ce?? Tana shirin lalata mun duk abun da na tsara . Hajiya Turai ke maganan cike da tashin hankali a zuciyar ta . Saurin miƙewa daga Tsaye Umair yayi kallon ta yayi yana cewa Waye shi ? Me ya taka waye uban shi???. Ganin yanda yake haki kaman damisa yasa ta saurin yin baya tana barin wurin da sauri . Bin bayan ta zaiyi nan Daddy Yayi saurin dakatar dashi tare da cewa " kar ka fara.! Cike da tashin hankali ya kalli Daddy Yana cewa " Daddy zan mata magana , Daddy ka fahimta Umaima bata Son kowa sama dani , kawai ta faɗa ne. Nima dai Haka na gani .! Hajiya Turai ta katse su cikin sauri . A'a tun da ta faɗa aƙwai ne.!
Saurin juyowa yayi yana kallon Ammie da tayi wannan furucin kana yace " Ammie zan rasa rayuwa ta ,zuciya ta buga mun take. Kamin su Yi aune sun ga ya wuce sune ce cikin sauri yana kirar sunan Umaima. Falon da ta shiga ya bita . Yayin da Ammie suka yi saurin biyo bayan sa.. hango ta yayi a ƙayataccen bed din ta ,Tayi rufff da ciki idanun ta na fidda zafafan hawaye. Key yayi ma ƙofan yana kirar sunan ta ' Umaima..!
A hankali ta ware idanun ta da suka tasa na kumbura . Aƙwai wanda zaki so sama dani a rayuwa???. Dama Ni ban taɓa son ka ba. Yanzu ne dai na fara soyayya a cikin zuciya ta. Na samu wanda ya iya tattalin So ba irin ka da komai kake yin shi in arrogancy . Ya San ya ya ake rarrashi ana sin kai da komai a tsawa kake yin shi . Yah Umair Bana son ka ba xan taɓa son ka ba. Fahad shine ....keeeee!!! Ya Kira ta da wannan sunan tare da kai hannun shi yana dunƙulawa ya buga a jikin bangon gyefen sa da sai da bangon yayi giirrr³ kaman zai faɗo ƙasa . Saurin miƙewa tayi ganin yanda kamanin sa ya sauya . I can tolerate nonsense ,Ni kike faɗa mawa kin Son wani ,ina Son ki Umaima kuma dole ki soni. Su Ammie dake bugun ƙofar har hannun su yayi zafi hankulan su a tashe yake sun tsaya cirko cirko a bakin ƙofan ,Surayya ce ke faɗin Pls Ya Umair kayi haƙuri kar mata wani Abu . Takowa Umair yayi dab da ita . Hannun sa yakai yana Kama kuncin ta da sai da ta rintse ido . Zan iya jurar ki furta baki sona , Amma ki sani baxan iya jurar jin kince kina Son wani bayan Ni ba. Any thing will be happen if I hear that again . Zan iya kisa . Zaro ido Umaima tayi tana kallon sa . Gyada mata kai yayi kamin yace " Yasss... Ki goge shi ki goge lissafin shi a rayuwar ki ,zan kashe shi na kashe banza indai akan ki ne. A'a ina kuka haɗu..??? Ya ƙara maganan a tsawa ce. Cikin Muryar kuka da firgici tace " Wallahi Yah Umair ba zan faɗa maka ba. Sai dai ka kashe Ni . Huuuuu Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai kamin yace " ba zan miki komai ba ,but na gargaɗeki ki cire shi a dausayin da kika saka shi . Ni Umair dani kaɗai zakiyi rayuwa . Kuma kar kiji Daddy Yayi maganan za'a baki yaƙi akan ki zabi wanda kike so.! Ni ke da igiyoyin Auren ki ,sai na ga daman sakin ki . Sakin kuncin ta yayi tana yin baya kaman zata faɗi .
Juyawa yayi a fusace yana nufar ƙofar yasa key ya buɗe ,Ammie ne tayi saurin wuce shi tare da shiga don taga halin da Umaima ke ciki. Kallon Hajiya Turai yayi fuska murtike kana yace " ina Umaima ke zuwa. Cikin sanyin jiki don ita kan ta ta tsorata da ganin yanayin sa tace " Makarantar ta . Ta samu admission ne? Eh nursing . Daga yau na soke fitan ta ko ina.! Kamin ya ji daga bakin ta ne ya wuce fuuuuii tare da nufar farfajiyar gidan.....!
RAMSY HERBAL💃💃Tabbas da kaji wane ba Banza ba , wani kaya sai amali , rugun babban motsi , margamargan dutse kafi gaban Aljihu ,wannan nima kaina da baki na na faɗi haka yake🤞. Ina kuke ƴan Uwana manyan mata ,shin kuna ina?💃 Matso kusa ga babban dama ta samu daga hannun wannan shahararriyar ƴar mutan Sokoto RAMCY HERBAL ta shirya tsaf don kawo mana magunguna da dama meye matsalar ki Amaryar Oga??
Uwar gidan Alhaji kefa? Maza saurara kiji wannan magunguna daban ne da saura daga taskar ƴar mutan Sokoto .
-Maganin ƙanƙancewar gaban ɗa namiji
-Maganin sanyi na mata da na maza
-Gumbar riɗi , gumbar aya ,gumbar ƙwaƙwa , gumbar dabino.
-Zumar ni'ima
-Zumar ƙiba
-Zumar goran tula
-Dambun ni'ima
-Zumar ƙwakwa da ta dabino
-powder hip up Dana breast elargement .
-tsumin ƴar gata
-Tsumin tabaje
-Maganin ciwon sugar
-Maganin hawan jini
RAMCY HERBAL ba anan ta tsaya ba , ta kuma taho mana da kayan gyarar jikin mu...💃💃
-Dilka Soap
-Whitening Cleanser
-malato soap
-Half cast soap
-shu'umin Humra tare da turaruka masu ƙamshi ,da zai rikita Oga in a few sec.
Ga masu buƙatar ƙarin bayani maza hanzarta ku tuntuɓi wannan number 07032209881 / 08109511467 .
Address: Sabon titin sokoto rima , kafin wajen sha'aban mai kankana mun gode.!
*MMN TEDDY*
*Littafin the sexxy boss na kuɗi ,duk wanda ya karanta bai biyani ba ALLAH ya isa.! Regular group₦300... VIP group₦500...SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki turo da MTN card ta wannan Numbobi 08081202932*
Da ido Hajiya Turai ta raka shi , yayin da a zuciyar ta take faɗin " Wannan wacce irin musiba ce ,wannan baƙin Zuciya haka? Tun da nake a tarihin Rayuwa ban taɓa ganin fitinanne mai shegen zuciya irin Umair ba, tun yana yaro idan yaso Abu to a bashi kawai ,idan kuma ba'a bashi ba shi zai san duk yanda zaiyi ya samu . Ɗan tsuwa ta ja a hankali ,kana a sarari ta furta " Umaima zata lalata mun komai na shiri na , banda iskanci ga yanda muka yi dake , sai Kice kina da wanda kike So.! Hauka tayi ne???. Jin Muryar Ammie na rarrashin Umaiman daga ciki yasa Hajiya Turai kutsa kai tana shigewa daga ciki ita ma. Ammie kam sai rarrashin Umaima take , don Umaima ta gama tsorata da lamarin Umair , wato shi ba zai taɓa sauyawa ba? Bai san yaya ake rarrashi da ban haƙuri ba ,koda kuwa shi ne da laifi akan komai . Surayya ne ta buɗe baki tana cewa " Umaima kiyi haƙuri , Don ALLAH ki zauna da Yah Umair , Kin san a yanzu kece koman sa kaman yanda yace ,kece zaki controling nasa , kin san gargagarar halin da ya shiga sanadiyar rashin ki a tare dashi . Pls Umaima kiyi Haƙuri ki zauna tare da Yah Umair ... To ya na iya?? Hakan nan zan zauna dashi tun da ya riga ya zama miji na..! Ƙare maganan tayi tana sakin marayar kuka mai ban tausayi , a hankali take tunanin a zuciyar ta , don da fari cewa take Umair ya koma tamkar sauran maza babu wannan maganan a gadaran ce . Ashe ina har yanzu ba sauyawa yayi ba . Haka ake So? Tambayar da take mawa kan ta kenan ,kana tace " Wannan bashi ne So ba , sai da Haukan So . Dafata Da Ammie tayi ne yasata firgigi tana dawowa hayyacin ta ,Muryar Ammie ne taji tana ce mata" Umaima kiyi haƙuri Kinji , kin san halin Umair ba bu mai lanƙwasa sa shi.... Maslaha ɗaya Ammie gare ta shine ta daina Kula kowani namiji , ai Ya Umair shine mijin ta bai dace tana kula wasu ba ,don nasan duk wanda zaki kula basu kai ƙyau da nagartar Yah Umair ba. Hamdala ya kamata kiyi ki gode mawa ALLAH da har namiji Ajin farko kaman yaya Umair ya ce yana Son ki. Fareesat ce mai wannan maganan a gadarance. Sunkuyar da Kai Umaima tayi don dama tuni ta fahimta wacece Fareesa ,Sam bata da kirki , ita a Son Ranta ma Umair ba zai zauna da Umaima ba . A cewan ta yayi baya ,kaman shi ya rasa wanda zai aura sai dangin ƙasƙantattu talakawa... Wani irin Kallo Ammie ta watsa mawa Fareesat wanda yasa ta tasha jinin jikin ta . Juyawa tayi tana sa ƙafa tare da ficewa daga Bedroom ɗin . A hankali Surayya ta sauka tana bin bayan ta ...
****
Ɓangaren Umair kuwa yana fita a falo ya tadda Daddy Kaman yanda ya barshi . Zubewa yayi gwiwowin sa ƙasa gaban Daddy Hankalin da tashe yake roƙon sa akan cewar kar a raba shi da matar shi ...Amma Daddy sai yayi ruwa yayi tsaki wurin cewa " Abun da Umaima take so ,shi zaiyi mata ,itama tamkar ƴace a gareshi ba zai mata dole akan Abun da bata So ba . Yana gama faɗa masa haka ya tashi yana kakkaɓe babbar rigar sa ya bar Umair anan . Dafe kan sa yayi da yake sara masa . Kusan mintuna biyar yana a haka ,kana ya miƙe cikin ganin jiri yana barin falon tare da nufar farfajiyar gidan moton sa ya shiga yana mata key tare da ɗaukar hanya yana barin gidan .
***
Surayya ne ta biyo bayan Fareesat , a falo suka tsaya Surayya tana bin Fareesat da wani irin kallo na ba ta ji daɗin Abun da tayi ba. Ke Fareesat wannan meye kika yi kenan? Ya wa'annan kalamin zai dingi fitowa daga bakin ki? Ke ma fa macace?? Kuma sanin kan ki ne Abun da Ya Umair yayi bai kyauta ba. Ya cutar da Rayuwar ....Don ALLAH ya isa.! Cewan Fareesa tana ƙwatse Surayya cikin sauri. Dama ke ai na daɗe da fahimtar baki da kishin naki. Kina gani ba fa ,a gaban idon kowa ta nuna tana da wanda take So ba Ya Umair ba , Wato shi zuciyar shi tayi bindiga ta fashe kenan ?. To wallahi ta ALLAH ba nata ba . Zata ga Ya Umair ya rayu ,kuma Inshaallh sai ya cireta ya goge ta a tarihin Rayuwar sa ,sai ta Auri wanda take so. Ina banda So makaho ne ,har ita ajin Auren Ya Umair ne ,ai ya fita tamkar sama da ƙasa don ko a ƴar Aikin gidan sa ba zai ɗauke ta ba . To kuma dai a hakan ya ganta ya kuma ji yana Son ta sai akayi yaya??? Ban sani ba. Fareesa tace ga Surayya cike da tsiwa. Surayya ne ta kalleta tana cewa " Kin san dai Hali na , wlllh yanzu kika mun na daka ki ,na dake banza . Dariya Fareesat tayi kana tace To bismillah , wai duk akan waccen Banzan ne kike shirin duka na? To ai gani . Girgiza kai Surayya tayi tana juyawa tare da barin Fareesa tsaye tana cigaba da rashin kunyar ta .
***
Kusan Mintuna talatin Ammie ta ɗauka tana rarrashin Umaima kana daga bisani tayi masu sallama tana fitowa tare da zummar Tafiya . Hajiya Turai ne tayi masu rakiya har zuwa farfajiyar gida ,don a wannan karon har da Fareesat aka shirya Za'a tafi , a cewan ta zata je ta rarrashi Yayan nata ya cire soyayyar Umaima a zuciyar shi. Ya nemi dai dai shi ba ita dangin talakawa ba .! Tun da Ammie ta fita Umaima ke zaune tana tunanin kalaman Ammie n , A hankali a zuciyar ta ta furta" Ina ma Umair ya biyo halin Ammie? Amma shi komai a gadara da miskilanci yake yin shi . Ɗan tsaki ta ja tana faɗin mugu kawai. Wallahi ba zan zauna da kai ba , a wancen j
Karon kwana biyu ne ana uku nayi da kai ,Kabi ka gama wargaza mun Rayuwa , kullum baka da aiki sai na saduwa , kayi mun Rauni ba kaɗan in just 3 days , Ina ga kuma yanzu ace maka Ni na zama taka har abada .? Gaskiya bazan iya ba ,Ni tsoro ma nakeji , sunan kayi na dama ne ,amma Ni ban haƙura akan Abun da kamun ba.! Murɗo Handle door ɗin Hajiya Turai tayi tare da takowa tana isowa zuwa inda Umaima take zaune . Umaima wannan wani irin shashanci ne??? Ya zaki ce kina da Wanda kike so? Ahir kar na ƙara ji ,kisa A ran ki Umair ne mijin ki bayan shi babu wani ,wannan ai sakarci ne ma. Kina sane da abun da zamu yi. Dole kece wacce zaki cika mun burina a kan Umair , tun da tun tasowar shi bai ɗauke Ni a uwa ba,sai Dai Hajiya Maryam . Don haka kisani Ko da Daddy ya tambaye ki , Kice kin yafe masa zaki zauna dashi a matsayin miji . Komai nasa sai naga bayan sa sannan idan na rabuwar Auren ne kuyi.
Kallon ta Umaima tayi tana mmkin meye Umair yayi mata hakan? Sai kuma ta yi shiru tana nazarin wannan wani irin hali ne Hajiya Turai ke dashi ?. Muryar Hajiya Turai taji tana cewa " Idan kuma ba zaki iya ba , zan nemo wanda zasu yi mun aikin na biya su . A'a Momy zan yi , Ni mene damuwa na a ciki ,kawai dai na tsane sa . Murmushin jin daɗi Hajiya Turai tayi kana tace " Haka nake son ji. Kema sai ki ɗau fansar abun da yayi maki. A satin Nan zan shirya komai na tarewan ki a gidan Umair . Shiru Umaima tayi kamun daga bisani tace to .
***
Da misalin ƙarfe 7:00am ne , Umaima dake ƙwance a gadon ta ,tun da ta tashi da Asalatu ta gama sallolin ta ta kasa rintsawa ,maganganun Hajiya Turai suke mata yawo a ƙwaƙwalwa . Ji tayi ana buga mata ƙofa ,sai kuma Muryar Hajiya Turai da taji tana magana ƙasa ƙasa amma bata san da waye take yi ba...A hankali ta sauko da ƙafafuwan ta ƙasa tana nufar ƙofar tare da zare key ɗin tana buɗe wa ... Saurin baya tayi ganin Umair tsaye wanda bata yi tsammanin ganin sa da wannan safiyar ba....Ya Umair me kuma ka zo yi?? Ba bata amsa ba sai kutso kan sa da yayi cikin Bedroom . Tsayawa tayi tana kallon Hajiya Turai da itama ita take kallo ,kana tayi saurin bin bayan sa tare da maimaita tambayar ta , Yah Umair me ya kawo ka da wannan sanyin Safiyar? Laifi ne don miji ya zo ya duba matar sa..?
*MMN TEDDY*
*Littafin the sexxy boss na kuɗi ,duk wanda ya karanta bai biyani ba ALLAH ya isa.! Regular group₦300... VIP group₦500...SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki turo da MTN card ta wannan Numbobi 08081202932*
Tsayawa Umaima tayi sororo tana kallon ikon ALLAH , to wannan me ma zata kira abun da yake mata rainin hankali ko mulkin mallaka?. Shiru tayi ba tare da ta tanka shi ba , Muryar sa ne ya kuma katse ta tana kallon Hajiya Turai itama da ta tsaya tana kallon Yanda Umair ke masu mulkin mallaka ,tun da take dashi bai tabo wuto ko ina na falon ta ya shigo har ƙurya haka ba. Maganan tasa ce ta kuma katse su yana cewa " Momy wai Haka kika ba ƴar taki Tarbiyya? Yayi maganan yana kallon Hajiya Turai da ta rasa bakin magana ,duk iya karya lafazi nata ,yau dai ta kasa ko tanƙwara kalma ɗaya ,don tayi amfani dashi wurin masa magana gaba ɗaya ya cika mata ido ƙwarjini yake mata tun ba yau ba . Taho ki gaishe da mijin ki .! Yayi maganan yana yafito Umaima da hannun sa. ganin ta tsaya bata motsa ba sai raba ido take ta kalle shi ta kalli Hajiya Turai ne ya saki murmushi mai ɗan sauti kana yace " Ni mijin ki ai na yi maki Tarbiyya... Kallon sa Umaima tayi tana cuno bakin ta tare da cewa " A'a nifa ba kai ka bani tarbiyya ba , ka ganni da haƙora na talatin kace kai ka bani tarbiyya ?. Iyaye na suka suka yi mun komai a rayuwa , su suka bani tarbiyya tare da nuna mun abubuwa da yawa wanda yin su da aikata su yake babban zunubi , tun a duniya mai aika ta su ,yake ganin Sakamako . Na ɗaya shine Zina, na biyu shan giya da duk wani Abu da zai gusar mawa bawa daga tunanin sa . Ni iyaye na sun....Keeee da wa kike wannan maganan?. Yayi maganan cikin daka mata tsawa ,wanda sai da Hajiya Turai tayi saurin kama hannun Umaima . Idon ta ta zuba akan nasa , duk da taji tsoron sa ,amma sai ta dake tana kallon sa tare da cigaba da cewa " Ai kai ka bukaci nayi wannan maganan ,kuma naga duka tunatarwa ne , bance da kai nake yi ba. Umaima ..! Ya kira sunan ta irin na mamaki , da kuma yaushe har ta iya yayi magana ta basa amsa kan ta tsaye babu tsoro haka . Tun da yake a rayuwar sa bai taɓa haɗuwa da wata mace ta fuskance shi ido cikin ido tana watsa masa maganganu irin haka ba .
Ni kike faɗa mawa Wannan maganganun? Kallon sa tayi kana tace " To Sir Umair yi hakuri naga wannan ai duk tunatarwa ne?. Sir Umair??. Ni kike kira da wannan sunan? Meye matsayin ki a wuri na? Ni mijin ki ne ,ki Kirani da sunan da zai sa inji daɗi a zuciya ta .
Wani irin kallo ta watsa mashi ,idon ta na ciko da ƙwallah , sai hawaye sharrrrrr³ , ganin yanda Take xubda hawayen taana sauke ajiyar zuciya , wannan ya nunar she shi ,ko a juya tayi kuka har ta gode Allah. Ya Umair Me yasa ba zaka sauya ba? Abun da take faɗi kenan a zuciyar ta a sarari kuma jifan