Showing 6001 words to 9000 words out of 25151 words

Chapter 3 - The Sexxy Boss Part 4 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt

01 Jan 2025

4217

shi take da kallon dake nuna tsantsan tsana da ƙiyayyya . Ina Son ki ,kuma kema dole ki Soni.! Yayi maganan yana takowa zuwa inda take . Wannan shine maganan da kayi mun tun da fari . Amma kuma kai yaci ace ka ƙaryata kan ka ,tun da ba na Son Ka har yanzu . Kallon ta yayi yana sa hannayen sa biyu tare da tallabo kuncin ta ,idon ta ya ƙura ma ido yana kallon ta .kamin yace " Ƙarya kike ga So na nan ina gani a idon ki .! Umaima kina Sona, Bama So kaɗai ba...Fuzgar kan ta tayi daga garesa tana cewa " A haka zan So ka? Ka kasance mazinaci, Mashayi , wanda har duniya an yi maka shaidar Shaye² .na haɗa zuri'a da kai me ƴaƴan da zamu haifa idan suka tashi zamu ce masu ?. Nan da nan fa.....maganan nata ne ya sarƙe tana sakin kuka tare da sa taffan ta tana rufe bakin ta . Sorry Yah Umair , baxan Zauna da kai ba . Ban san mene zan faɗawa yara na ,baxaka sauya ba . Ba zaka daina abubuwan da kake yi ba . Nan a gidan muna zaune da Momy muke gani a news ake watsa labaran ka , na tayatar da ka amsa a ƙwalɓe , da kuma lalata sunan Ƴan uwan ka likitoci ... Ni dai a'a ya Umair ka sauya tukuna .




Jah baya yayi yana kallon yanda take xubda hawaye , a hankali yake motsa hannun sa , Jikin sa gaba ɗaya yayi sanyi , a Rayuwar sa abu ɗaya ya tsana shine ya bude ido yaga Umaima a cikin wannan hali ... Umaima wannan wani irin magana kike ? Hajiya Turai tayi maganan cike da rashin jin dadin maganganun ta , a ganin ta kar Umair ya fusata abubuwa su dagule .




Kamin Umaima tayi magana ne , ta ji Muryar Umair yana cewa " Momy zanyi magana da matata. Saurin ware idanun ta Umaima tayi ,Kana tace " Me kake nufi to??. Kamin yyi magana ne Hajiya Turai tayi saurin cewa ' A'a bari na baku wuri . Momy babu inda zaki je , Kasan wacece wannan kuwa?. Na sani , yayi maganan yana kallon idanun ta . Haɗa ido sukayi nan ya daga mata gira yana cewa " Yass nasani Yayar Umman ki ce ,wacce take uwa gare ki. To ka sani kake wannan maganganun ? To babu inda zata je . A'a bari dai na fita. Cikin Muryar Kuka Umaima ne ta kuma kwatse shi da cewa " A'a Momy babu inda zaki . Kamin ta rufe baki ita dai taji ya rungume ta ne yana haɗe bakin sa da nata , wani irin hot kissing yakeyi mata , wanda jikin Umaima ne ya hau rawa so take ta ƙwace kan ta daga gare shi ,amma ya rungume ta ƙammm a tare da shi . Juyawa Hajiya Turai tayi da sauri tana fichewa daga ɗakin. Tafe take tana sambatun da bata sani ba tana cewa ' Oh Ni Turai Ni naga Zamani?? Shi yasa yace na basu wuri , wannan tacewa da mai yayi kama???. Naam Hajiya magana kike yi?? Muryar ƴar Aikin ta taji ,wannan yasata farga ashe a sarari take maganan . A'a zubaida ba dake nake ba. Wuce yar aikin tayi cikin sauri tana nufa falon ta. Itako Zubaida da ido ta rakata a zuciyar ta tana cewa " Yau Hajiya Lafiya kuwa ?.






Kusan mintuna biyu da sakanni suka ɗebe yana tsotsan bakin ta ,kana ya shagala ƙwarai ya saki jikin sa a natse yana Kissing ɗin labɓan ta tayi saurin janye kan ta tana yin baya , tare da cewa " A'a Umair... Shiiiii yayi saurin sa yatsar sa a laɓban ta ,hannun sa ɗaya ya riƙo nata , bin sa da kallo take tare da cigaba da xubda hawaye . A hankali taga ya sa gwiwowin sa a ƙasa yana kallon ta cikin Muryar karaya da ladabtawa tamkar yana gaban na gaba dashi .Umaima faɗa mun abubuwan da kike so na daina daga yau nayi miki alƙawarin dai nasu. Na bar shan barasa ,na bar shan sigari ,haka na daina Sex da kowacce mace sai ke kadai mata na... faɗa mun abubuwan da kike kuma son na daina yin su zan daina badon komai ba saboda ke...!




Aƙwai supliment masu ƙyau da inganci babu illa ,muna sayar da na breast da kuma na hip up. Aƙwai na ƙiba , da kuma na hasken fata mai ƙyau ba na bliching ba. Ga masu buƙatar ƙarin bayani You can chart me up .


*MMN TEDDY*
*08081202932*
*Littafin the sexxy boss na kuɗi ,duk wanda ya karanta bai biyani ba ALLAH ya isa.! Regular group₦300... VIP group₦500...SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki turo da MTN card ta wannan Numbobi 08081202932*








***






_Kuyi manage da posting yau , wallahi mun koma school ,next week kuma zamu yi resuming work, kunga yanzu sai kuna haƙuri da posting babu yawa,Amma a hakan zan rinƙa ƙoƙarin yi mana sau biyu , ko zuwa can dare zana rinƙa maku night update in Sha ALLAH.!_




"Kallon sa Umaima ta tsaya yi kaman maitantaman wani abu na daban kamin cikin sanyin murya tace " Ni ai ba tawa rayuwar ka gyara ba naka ne?. Idan ka daina duk abubuwan da ka faɗi zaka daina alhmdllh shine Abun da zana ce. A matsayin ki nawa kenan a guri na? Yayi maganan yana zuba mata lulun idanun sa . Shiru tayi tana murza ƴan yatsun ta kana daga bisani tace" Ai ni kasan daiii...Pls Umaima ki yafe mun , wallahi tun bayan rabuwa na dake na daina mu'amala da kowacce ƴa mace. Kawai dai abun da nasan ina cigaba da aika tawa shine shan barasa na . Kuma daga yau na daina . Bana komai yanzu ki sa na bar wannan duk abun da kika san ina yi. Pls Umaima ki zauna dani Muyi rayuwa mu haife yaran mu masu kama dake. Kunya ne ya kamata saurin ƙasa tayi da idanun ta da kallon sa tana murmushi , hannun ta ya kama yana miƙewa daga tgurfanan da yayi gaban ta . Murmushi shima yake wanda rabon da yayi irin wannan sanyayyar murmushi ya manta . Kallon sa tayi cikin sauri tana zame hannun ta , tare da cewa " Kar Momy ta shigo ta gan mu ...Aaa ke ba mata na bace ba? Ai wuri ta bamu. Saurin fiddo da idanun ta tayi waje na mmkin tare da jin nauyin furucin nasa ,kana ta juya da sauri tana ficewa daga Bedroom din . Murmushi Umair yayi yana sa hannayen sa sama tare da godiya ga ALLAH da ya nuna masa mafarkin sa a zahiri , hamdala yayi yana biyo bayan ta . A dirning Area ya tadda Hajiya Turai da Umaima da ta amshe ta aikin tana taya ta hidimar haɗin karin kumallo .




A'a Umair Har ka fito?. Hajiya Turai tayi maganan cike da fara'a . Saurin kallon Ta Umaima tayi kana ta juya suna haɗa ido da Umair . Ɗaga mata gira yayi yana murmushi ,bai damu da Hajiya Turai dake gaban sa ba. Saurin kauda kan ta Umaima tayi tana cigaba da gyara zaman wani babban bowl dake akan Dirning table ɗin . Hajiya Turai ne ta cigaba da cewa " Ai baka tafi ba , don yanzu nake haɗa maka break nasan bakayi ba a gida ka fito . Murmushi yayi yana cewa ' Momy sauri nake yi yanzu haka zan wuce Lagos ne wani aikin ujula ya kamani ,shi yasa nazo nayi sallama da Matana . Eyyaaa kuma bata faɗa mun wai tafiya zaka yi ba. Cewan Hajiya Turai tana juyawa tare da kallon Umaima da itama batasan wai tafiya zaiyi zuwa wani wurin ba .




Murmushi yayi har hushiryar sa na bayyana kana yace "itama ai taki tsayawa ta saurari abun da ya kawo Ni ,guduwa ma tayi ta bar Ni kaɗai . Murmushin yaƙe Hajiya Turai tayi kana tace " To ai shikenan Allah ya kaiku lafiya . Ammm Momy don ALLAH kimun wani ƙoƙari mana kamin dawo. Kallon Sa Hjy Turai tayi cike da mmkin yanda ya tausasa lafazin sa kana tace " Ƙoƙarin mene ne Umair??.




Don ALLAH Momy kisan yanda za'a yi kamin na dawo a maida Umaima gida na , Ni nayi magana da Ammie ko a gida na nan Abuja zan zauna na hakura da zaman Lagos ɗin . Ki shawo kan Daddy ya amince . Murmushi Hajiya Turai tayi tana ƙara faɗaɗa Fara'a kana tace " In Sha Allah Umair zaka dawo ,ko Umaima bata tare ba ,tana gab. Thknyou . Yayi maganan tare da Kallon gyefen da Umaima take ita dai tayi shiru tana faɗawa tunanin rayuwar su idan ya kasance daga ita sai Umair ɗin ..wani irin gwagwatuwa zatayi a hannun sa .




Zo ki mun rakiya.! Taji Muryar sa ya katse ta , amm...Tsayawa tayi tana kame kame don tana tsoron bin sa , bata san me kuma zai mata a farfajiyar gidan ba a gaban ma'aikata , don bai ji kunyar Hajiya Turai ba , inaga kuma sauran ma'aikata da baya ganin su a bakin bakin komai . Hajiya Turai ne ta katse su da cewa " Aaaa Umaima raka sa mana ? Mijin ki kuma zai wuce kin kasa masa Rakiya . Ɗago da idanun ta tayi kawai sai ƙwallah ya ciko idanun ta suna dab da zubowa . Saurin cewa Umair yayi " A'a mom ta bar shi kawai sai na dawo.! Yana maganan ya fice daga falon . Bin ta da Kallo Hajiya Turai tayi ,kamin tace " Meke damunki ne Umaima??. Shiru Umaima tayi tana sada kan ta ƙasa ,tare da cewa " Ba komai . Ohk kina ji ,nasan ba Son Umair kike ba , ki sa a Ranki zaman da zaki yi dashi na ɗan lokaci ne ba mai ɗorewa ba Kinji Baby na.! Murmushi Umaima tayi tana jan kujera tare da cewa " Mom Bara na fara breakfast . Alright . Abun da Hajiya Turai tace kenan tana juyawa tare da nufar Kitchen. cookies Ta fara kaiwa bakin ta , amma sam bata jin daɗin abincin nata ,wannan yasa Umaima turewa gyefe tana ɗaukar tea cup tare da sa spoon tana juyawa , shiru tayi tana tunanin abubuwa da yawa dangane da Hajiya Turai akan Umair . Me yasa Momy bata Son Ya Umair da alheri? Me yayi mata ne?? Dole ina Son sani. Sauke ajiyar zuciya tayi tare da kai cup din bakin ta tana shan tea ɗin kaɗan tare da saukewa . Tun da na sauya Ya Umair itama in Sha ALLAH zan sauya Momy ta koma tamkar sauran iyaye mata masu fatan alheri da kowa , bazan iya cutar da Umair ba , Saboda Ni kaina nasan ina Son sa a zuciya ta ,tun ban san So ba nake Son ya Umair , har daga ƙarshe na yarda da cewa Zuciyata ta kamu da Son Umair . ALHMDLLH da sauyin da Allah yayi mun ina sake godiya. Wayar ta ce tayi ƙara dubawa tayi kirar Fa'iza ne kusan sau goma sha Ciki har dana Fahad.




Mikewa Tayi daga dirning Area tana nufar Bedroom din ta . A hankali ta fara shafa wayar nata tare da fara kirar Numbern Fa'iza . ringing ɗaya biyu ta ɗauka . Umaima kina ina ne??? Me ya faru?? Umaima ta katse ta da wannan tambayar . Tun jiya Fahad yake neman ki da mutanen sa har gidan mu sun zo . Yanzu dai haka in taƙaice maki Yana hanyar zuwa Abuja ,wai zai kira ki idan ya iso.! Ƙirjin Umaima ne ya buga dam... shi Fahad ɗin ? Eh mana.!






*ANTY MMN TEDDY*
Tun da Umaima tayi shiru bata kuma cewa komai ba sai Fa'iza ce dake ta faɗin " Hello kina jina Umaima...Shurun da taji ne yasa ta katse kirar yayin da ita Kuma Umaima ta Juya tana jefar da Wayar Ɓarayi guda . Dafe kan ta tayi gami da kuncin ta tana maganganun sa dana Sauran Abokanan sa na dawo mata " Wannan da kuke gani Budurwar Fahad ce a wannan makarantan kar wanda yayi kuskuren... Umaima..! Muryar Hajiya Turai ne ya katse ta , wanda bata san ma ta shigo ba , gigif tayi tana buɗe idanun ta tare da amsa ta da" Na'am . Kallon ta tayi tana ƙare mata kallo baki ɗaya kana tace " Kina lafiya kuwa?. Murmushin yaƙe Umaima tayi mata don ta nuna mata babu komai nan tace " Momy komai lafiya , Waya muka gama yi yanzu da Fa'iza ,tayi mun maganan school shine hankali na ya karkata gare ta . Shiru Hajiya Turai tayi kamin ta dafa Umaima tana cewa " Kin san dai me Umair yace dake ko??. Maganan makarantar nan a barta , saboda Umair juyayye ne . Kallon Hajiya Turai Umaima tayi cikin ɗan damuwa Umaima tace " To Momy kuɗin da Kuka kashe mun fa ? Duka a barshi ?? . Eh ki barshi ... To shikenan Momy . Amma ina Son Na je gida na gaida su Umma na. Ai wannan me sauƙi ne . Ki kirya ina so Anjima kaɗan ki raka Ni ,zanje mall Nayi siyayya na dawo . To Umaima tace da ita kamin Hajiya Turai ta fice ita kuma tana komawa tare da bin lafiyar gadon tana ƙwantawa a hankali tare da tunanin abubuwa , ita dai har ga ALLAH bata jin Zata iya rabuwa da karatun ta akan zancen Umair. Wannan ma fa ɗan rainin hankali ne , ban da rainin wayo da tunani har ya manta abubuwan da yayi mun a baya tun yanzu ya fara sharaɗɗa mun wasu zancen wofi ?. Taɓ to yanzu ina ga yaganni a cikin gidan sa abin ai sai inda ya kai kuma.
***


Kaman yanda Umaima tace zata taho gida , hakan ya faru , a tunanin Hajiya Turai gidan ne kawai a zuciyar ta , bata san zuciyar ta tunanin makaranta bane. Don tana komawa A washe gari ta shirya tsaf tayi na makaranta . Rayuwarta kawai take yi , don ita sam ta fara mantawa da Umair a ƙwana biyu ,sai dai wani abu ɗaya da yake sakata tunawa dashi shine ,duk idan Fahad yazo gareta ko ya jata zuwa wani wuri babu wanda take tunawa face Umair , a haka ta cigaba da rayuwar ta . Wanda duk shige da ficen ta har dawowan ta Umair ya sani . Bai tada hankalin sa ba ,sai da yaji labarin Fahad. Wannan yasa shi kirar Ammie Hankali tashe yana tambayar ta da izinin waye Umaima ta koma Makaranta??. Ammie da taji abun nashi yayi ƙamari ne yasa ta cewa " Au Har Makarantar ka kashe mata ne Tun yanzu yanzu ??. Sai a sannnan ya tuna da basu yi maganan da ita ba , wannan yasa shi datse kirar cikin sauri yana kirar Hajiya Turai .




Salallami Hajiya Turai ta ɗauyi tana faɗin Umaima ce ta koma makarantar?? Bari zan kirata yanzu . Gida fa tace zata koma ,tana Son ganin Umman ta. No Mom Kar ki kirata Bari zan dawo.! Zaaakk kamin Hajiya Turai tayi maganan ne taji ya katse kirar . Cikin sauri ta fara lalaubar lambar Umaima amma baya shiga . Kaiwa da komowa take tana faɗin " Umaima wai me take nema da zafi ne akan wannan karatun nata?? (Kuji mun Rainin hankali ma🙄) .Haka Ta cigaba da kirayen wayann ta amma amsan daya ne Wato Is not reachable at the moment .


***


Fa'iza ce ta taɓo Umaima tana ce mata a hankali " Fahad ya shigo . Saurin ɗagowa daga rubutun da take yi tayi , tana kallon Fahad da yake kurɗaawa ya iso har zuwa inda take , ba tare da yayi duba ga lecturer ɗin tasu ba.




A gaban su ya tsaya yana kallon Umaima wacce itama shi take kallo . Yau me ake maku? . Kallon Fa'iza tayi kamin tayi masa magana yana juya yana kallon Whiteboard din da lecturer Ke gyefe . Ohk taso mu tafi sai na koya maki . Miƙewa Umaima tayi tana kallon ɗaliban da lecturer a ido ido ,amma da mamakin ta sai ji tayi lecturer tace " Dr Fahad Hala dai wannan itace Surikar shiyasa kake cika zaƙewa da yawa?. Dariya Ɗaliban suka yi har da shima Fahad ɗin kana ya rike da jakar Umaima suka fuche daga hall ɗin . Mayafin Abayar ta ta gyara tana kallon gyefen ta , wani irin yanayi ne taji ya kamata , tsoro ne ko meye taji yana kai kawo a zuciyar ta . Bin filin wurin tayi da kallo , ganin motoci ne wanda dama suka zama ana aje su a wurin don gaban hall ɗin tasu fili ne sosai da ake aje kowani irin abun hawa .ji tayi gaban ta na faɗi. Wanda ya sata ja ta tsaya . Saurin kallon ta Fahad yayi tare da cewa " Menene?? Meke faruwa??. Cikin rawar murya ta kalle shi tana cewa" Ina ji a jiki na kamar Ya Umair yana wurin nan??. Kallon ta yayi kamin yace " Waye shi??...Kamin ta bashi amsa ne taji Ƙamshin sa ya durar ma ko ina na wurin . Can ɗan nesa ta kalla , ganin sa tayi ya fito daga cikin moton sa , wani guard ɗin sa ne ya biyo bayan sa , ammma sai kuma taga ya ja ya tsaya , shi Kadai Umair ɗin na takowa zuwa inda suke . Jikin ta ne ya hau rawa karrr³ , hannun ta tasa tana ƙoƙarin Amsan jakarta , amma sai Fahad ya riƙe jakar yana mata wani irin kallo na rashin fahimta .


Ƙari kowa zuwa inda suke Umair yayi ba tare da ya sauke bakar gilashin sa ba , fuskar sa a murtike take haka girar sa da yake a haɗe , sam baya tsammanin zai iya duba da inda Fahad yake tsaye , wanda ko ba'a ce masa ba ,yasan shine wanda Umaima take kokarin hada soyayyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login