Showing 15001 words to 18000 words out of 25151 words
Chapter 6 - The Sexxy Boss Part 4 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
sa ba .don Ordering nasu akayi daga Dubai . Wasu zaka ga A ciki turmomi biyu na Atampha da Turare . Wasu kuma track Suit ne da Abaya , Yan mata kenan . Wasu kuma zallar Turaruka ne na jiki dana Kaya . Abun gunin burgewa kowa da sambarka yake fita gidan .
Tun misalin Ƙarfe uku na yammaci Girgin yawo ya dire a farfajiyar layin Su Umaima ,abin da ba'a taɓa gani ba kenan , manya da yara kowa fitowa suka yi kallon jirgin da Umaima za'a yi ɗagawa ta ciki , don bazawarin iskancin da Umair ya kusa tamkawa shine " Cewa yayi Amarya kaɗai za'a ɗauko masa abun sa ,baya buƙatar kowa bayan ita ɗin ga ita kaɗai. Ihu Umaima tasa tana kirar Hajiya Turai tare da sanar da ita tana kuka , Wannan yasa Cike da Ɓacin Rai Hajiya Turai ta kira Umair take sanar masa hakan ba mai yiwuwa bane ba . Don dole tasa Aka taho da motoci don Ƙwasar Sauran dangi da ƴan uwa . A wannan lokacin kuma Umaima da Yaya Hannatu Sai Baban Kafancan suka shiga jirgin su suka kai ta gidan Sir Umair Ahmad moddibo dake Abuja ,kusa dana iyayen nashi ,wanda hakan sosai ya daɗaɗa Zukatan iyayen nashi musamman na Hajiya Turai . Tun kamin su Shiga Umaima ke Ware waren ganin Babu Fatima rabon ta da ita tun ƙarfe ɗaya . Amma kuma sam bata ganta ba . A haka dai tayi hakuri ta shiga har suka isa . A farfajiyar harabar gidan Jirgin ta sauka , Wanda tana isa ne Taga An bi hanyar wucewar su tun daga farkon da jirgin ta sauka aka shimfiɗa wani irin royals carpet red Mai masifar ƙyau da fuxgar hankali.
Tsayawa Umaima tayi har su Yaya Hannatu suka zagoyo da Baban Kafancan ta riƙeta ,kaman wanda bata taɓa shiga gidan ba haka tayi masu. Wata Personal VIRGIN MAID ce ta ƙariko garesu cikin sauri tana welcoming ɗin su tare da nuna masu hanyar da zai kaisu har zuwa falon Umaima . Buɗe Baki Umaima tayi don mmkin wannan kuma wacece ? A sarari da bata san ta furta ba tace THE VIRGIN MAID In my House?? Girgiza kai tayi na saurin cewa " Abun da ba zai yiwu ba kenan .! Ba za'ayi min sakiyar da babu ruwa ba A THE VIRGIN MAID , littafin Maman teddy , labarin da zaku na karanta tashi kiji shi a jinin jikin ki ,tamkar yanzu nan take ta faruwa . To abun ka ga Ƙwararran Alƙalami 😄 .
Juyawa Umaima tayi tana bin bayan ta Wannan ma'aikaciya kaman yanda Su Yaya Hannatu suka yi , THE VIRGIN MAID MY VIRGIN SISTER ,tuno da furucin sa akan Matar nasa... Gaban ta ne ya yanke ya faɗi ganin yanda Yarinyar take juyi ta ko ina a cike take dam , hips da mazaunan , gata jajir kaman balarabiya . Saurin shan gaban ta Umaima tayi tare da Dafa Ta tana cewa " Baiwar ALLAH nace ba.! Juyowa Tayi tana wangale mata baki alamu ya nuna budurwan mai fara'a ce kana tace " Na'am Madam . Ke ce wace a cikin gidan nan?. Ni kawai mai saukar amarya ce daga Ɓangaren Iyayen Sir Umair na Oustralia a daren yau zana koma .
Sakin mata murmushi tayi tare da cewa " Wlcm Sister. Thknyou Madam . Juyawa tayi tana jirar isowar su Yaya Hannatu da suka ce da Ita " Me kika ce mata ? Ko kin san ta ne??. Saurin girgiza masu kai tayi kamin tace " A'a tayi mun kama da wata ce ,a cikin book Ɗin THE VIRGIN MAID . Wow Gaskiya wannan labari zaiyi daɗi ba'a magana , cewan Baban Kafancan ... Murmushi Umaima tayi kamin tace " Hajiya Har daku kuma kun ce hakan, yo Ƙwarai ma kuwa , Ko daga ji kin san antaɓo ɓarayuyuka da dama , wanda haka ake Son Labari. Wacce marubuciyar ?? Ni ku bani contact nata?? Vip Zamu yi magana da ita . Dariya suka saka Sai yaya Hannatu ta buɗe Baki tana cewa " Maman teddy kenan . Marubuciya mai kirki da sanin ya kamata ,sam bata da wulaƙanci .... Kai yaya Hannatu ke kuwa ya akayi kika san da hakan?.
Cewan Umaima tana kallon Hannatu da ta ce" Munyi interview da ita Ta Special. Ehh to ƙwarai na gamsu da maganan ki . Nidai yanzu Umaima ki bamu number ta , Kar a fara babu mu sai dai muji labari ba...Zama kuji Hajiya Macace mai karamci idan kuma ta fara ,tana da dubban masoya da zasu watsa mawa masoya dama da hauni . Allah yakai mu yasa A fara lafiya Amin .
Tun daga wajen falon Hajiya Baban Kafancan ke ya ra kyawu da tsaruwan ko ina na falon . Komai an yi shi an kuma tsara shi yanda ya dace. Suna kuji ba kuji ban shiga da Umaima ƙayataccen Bedroom ɗin ta ne suka ji motsi daga bayan su . Juyawa suka yi Ganin Fatima da Julyb ashe su tuni suka ƙariko . Saurin nufowa inda take Fatima tayi tana murmushi Umaima na bin ta da kallon Ai kin ƙyauta.
Hannun ta Umaima ta riƙe tana cewa "Kun riga mu kenan dama , ina ta bulayin neman ki . Ai bar bulayi gata ita ta fara shigowa . Julyb yayi maganan yana Murmushi . Magana yayi mawa Fati da ido sai gashi ta kama hannun Umaima tana cewa " Hajiya bari mu taho. Kamin Suyi magana ne tuni ta ja hannun Umaima tana nufa da ita wani Room ,Wanda Umaima Bata San Ina bane ba. Ganin Makeup Artist tayi zaune a gaban wani mirror tana jirar isowan ta.
Cikin sauri ta tashi tana cewa " Please muyi komai cikin sauri mu suke jira .
Ita dai Umaima bata kuma cewa komai ba , nan take wannan matan ta fara kimtsa ta cikin wani Gown Golden Wanda ya amshi fatan jikin ta . Juyawa tayi tana bin Fati da kallo sai yanzu ta fahimta itama Gown ne jikin ta dark blue ,to Ina zamuje haka.? Tambayar da take mawa Kan ta kenan . Wani hill shoe tasa mai ƙyau tare da maɗauri sirara shima Golden ,sai ɗan mini poss ɗin da ta riƙe. Make up ne simple amma mai ƙyaun gaske , sosai ta yi kyau tafito amaryan ta ainun .
Surayya ne ta shigo cikin sauri tana faɗin " Komai yayi ready kuwa??. Ganin irin azabtar kyau n da Umaima tayi yasa ta faɗin Wow ANTY kin Yi kyau fa . Murmushi Umaima tayi tana cewa " Allah ko? To na gode . Kallon Fatima tayi a hankali tace " Wai ina zamuje ne ko duk budan fuska ne ake mawa wannan Adon , Tayi maganan tana ƙare rufa kan ta da siririn shara sharan mayafin da aka rufa mata fuska . Mai Makeup Artist din ne ta juya tana kama kasan Gown din ta ,Kamin Fatima tace " A wancen Baban falon mai kaman hall abokanan Sir Umair ne harda Dangin Mahaifiyar sa , mutum ne fiye da 50 a ciki muje ,zasu ga amarya kowa yayi presenting Gifts ɗin sa ga Ango da Amarya . Saurin kallon ta Umaima tayi ,a zuciyar ta tana cewa " Yanzu cikin can har da Turawa kenan ? , Hannun ta Surayya ta riƙe tana tsayawa a gyefen ta . A tsanake suka fara shigar hall ɗin .
Gani tayi ana ɗagawa wani abu tun daga shugiwan su kaman shine shine yana sauka akan su a hankali . Tafi Wurin aka ɗauka ,yayin da Fareesat dake cikin mutanen in zaka Uwar surutu tayi saurin nufar Inda Su Umaima ke takowa da sauran Mutane , don matan Wurin duka nufan su suka yi aka rufa ma Amarya baya . Saurin nufan Mr Mc Tayi tana amsan mk tare da fara ku zanta Amaryar su , Da a ƙarshe take cewa " This the best couple ever Dana taɓa gani a rayuwata ,ya sadaukar da koman sa domin ta ,haka itama ta tsaya dakon soyayyar sa na tsawon shekaru .....ihu Wurin ya ɗauka ana tafi . Nan tayi saurin nufar Amarya da suke gab da ƙarikowa wurin tsayuwar su . Hannun Umaima ta riƙe ,tana dakatar da Fatima tare da mata wani Kallo tana cewa " Kece wace??.
Tsayawa Fatima tayi sororo ,yayin da Surayya kecewa a zuciyar ta mai hali baya taɓa fasawa . Julyb ne yayi saurin ƙari kowa yana amsan kakar Fatima tare da jan ta can inda yake da Abokanan sa . Hannun Umaima Fareesa ta riƙe suna nufar Ango da yake cikin shigar Suit Bai tsaya zafafawa ba ,don shi mutum ne mara Son hayaniya a koman shi . Ɗan ɗogo ido Umaima tayi tana hangosa. Tabbas yayi masifar sihirtacciyar kyau . Yanda kasan Arab ,don dasu yafi kama . Tana hayewa Stairs ɗin da yake shida wasu abokan sa uku wurin ya ƙara rikicewa da tafi. Gani tayi Fareesa ta miƙa masa hannun Umaima tare da cewa " Yah Umair kayi alƙawarin ba zaka cika wannan Hannun nata ba kaman yanda ka riƙe namu hannayen Duk wuya duk rintsi har Abada zaka yi ta riƙon ta". Riƙe hannun Umaima yayi yana ware hannun sa Fareesa tana rungume shi .
Abun ka ga Turawa Wasu har da ƙwalla saboda tsabon ba so muhimmanci . A hankali ya raba jikin shi dana Fareesat Yana kai hannun sa tare da yaye mayafin fuskar Umaima bakin sa ɗaura a saman goshin ta , yana manna mata kiss tare da sauke fuskar ta yana sunkuyowa zuwa fuskar ta " You look ....I don't know what I will say....ya ƙare maganan tare da kashe mata ido , Ihu Hall din ya dauka da tafi .... Anan take wuri ya yamutse . Kowa na a cikin farin ciki .
Anan take Mc ya fara gabatar da Amarya da Angon ta . Kamin daga bisani kowa ya fara gabatar da kansa da yanda suke da Ango ma Amarya kana a nufi High table ana ba Amarya Da Ango wedding Gifts . A haka har aka kai kusan shida ,anci an sha , kana daga bisa masu barin ƙasar suna nufar ƙasashen su na bari . Masu nufar gariruwan su nayi . Ita dai Umaima koda ta koma apartment din ta , tuni ta tadda dangi da yan uwa sun sauka . Nan take ta nitsa cikin su . Abun da ya bata mmki shine a wannan yammacin aka tarkata kowa na cikin gidan zuwa garin su , Da Fatima zata tafi Umaima tayi kuka sosai haka Ita ma Fatiman ke share ƙwallah na Sabo . A haka suka yi sallama .
Gidan ya kasance ba kowa daga Umaima sai ma'aikata ,don Umair shima tun da yabi abokanan bai dawo ba... Har wuraren ƙarfe 9:00pm.!
_Aƙwai Ingantattun supliment na hip up ,breast elargement , sup na ƙiba da baya , aƙwai kuma na hasken fata ,wanda bana bliching ba ,kiyi amfani dashi yasa hasken ya koma kalon madara ƙarrrr , sai an gwada serious buyers ku taho . Prices ɗin mu sun fara da ga ₦3500 zuwa sama duk na yanda kuke so zaku same su ...ga masu buƙata You can chart me up ,or click this number 08081202932_
*AUNTY AISHA MMN TEDDY*
*🕊️THE SEXXY BOSS🕊️*
Bonus page
*Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne , Regular group ₦300... VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki turo da katin MTN ta wannan number 08081202932...Idan VTU transfer ne sai ku tura ta wannan number 09061466409*
***
.....Tun da Umaima ta juya taji ko ina shiru kaman bil adama basuyi marurin su a cikin gidan ba ya sata komawa can ƙurya tana hayewa wani Abu kaman Lift yana sama da ita ,ta nufi Bedroom ɗin ta kai tsaye . Bin ko ina tayi na Bedroom ɗin da kallo ,a hankali take tuna Rayuwa da abubuwa da dama da suka shuɗewa a shekaru Uku baya , Ƙwallah ne ya ciko ƙwarmin idanun ta , Wanda A hankali tasa ka dogayen yatsun ta tana ɗauke hawayen dake gangarowa zuwa kuncin ta . Naga Rayuwa .! Wannan ne kalman da ta furta tana rintse idanun ta. Kusan mintuna Uku tana a tsaye a wurin bata motsa ba . Numfasawa tayi a hankali tana furta Kalmar Alhamdulillah , Kana ta fara motsa ƙafafuwan tare da nufar Ƙayataccen Gadon nata ...a sanyaye kamar mara kuzari ta zauna a saman bed ɗin ,sam ta kasa motsa jikin ta yanda ya kamata , Niko Maman teddy nace tun yanzu ? Ba'a shiga wurin aikin daga ciki ba? Domin kuwa Ƴar mutan Katsinawa ta shirya ta gam gam ciki da waje ..kun san dai wa zance RAMSY HERBAL CENTER ,don itama gudun muwaar ta ta kawo gari ya gari , ina amarya da Uwar gida ,kai har da zawarawa masu shirin Amarcewa maza sambada mata kira ta wannan Numbobin 07032209881 don kema kisa Oga nishaɗi ,kiga ya tafi Office tun Fitar shi fuskar shi a fara'a haka zai dawo fuska sake ,yo Hajiya ai haka ake so , Kinji Haɗin RAMSY🍒 .
Ko mawa Umaima tayi tana sada kan ta da fillo tana ƙwantawa da kan ta a hankali , ji tayi gaba ɗaya jikin ta na mata sanyi , yau rana ta farko da ta tuno da Mahaifiyar ta bayan Umma , Allah yajiƙan ki Umma yasa kina kyakykywar Maƙwanci . Abun da ta furta kenan tana ƙara lumshe idanun ta kaman mai barci .
***
Kaiwa da komowa Hajiya Turai take yi cike da farin ciki , Abun da ta daɗe tana so yau Allah ya cika mata burin ta . Umair Sunan da ta ambata kenan tana sakin wani makirin dariya . Ƙara sa idanun ta tayi tana duban wayar da ta gama yanzu da Hajiya Kubra Aminiyar ta ,kuma ma'aikaciyar bin cike ta gomnati , Wanda a yanzu take sanar mawa da Hajiya Turai sun samu yardar kama Umair a saladin Suna tuhumar sa ga arziƙin sa a karo na biyu . Wani irin bushewa da Dariya Hajiya Turai tayi ,kamin ta tsagaita tana cewa " Abun yayi dai dai , kai waye Umair? Me ka taka?? Da har akan Bikin ka da ba kowa yasani ba ,zaka yi rabon zunzurutan kuɗi kowa ya zo maula ƙaramin kuɗi shine 50k , waya ce maka ana yin haka a gida Nigeria tuni gomnati bata sa An kame ka ba?? Wannan shine Kaɗan daga hukuncin ka gare Ni yanzu wasan zata fara .! Zaka ga jami'an EFCC babu zato babu tsammani , takardar daga sama ne ,idan aka fara tuhumar ka ,zaka yi tsawon watanni koma shekaru a hannun gomnati , daga nan zan yi aikin duk yanda nake so . Ƙara sakin wani Dariya Hajiya Turai tayi kana ta juya gyefen ta ,tana ɗaukar Wayar ta tare da kirar Numbern Umaima .
***
Tana daga ƙwancen ne taji Wayar ta na e ,wanda a hankali tasa hannun ta tana duba mai kirar , kamin ta ɗau ki kirar ne taji motsin shi shigowan sa , wanda tun kan ya ƙarako inda take ƙamshin turaren sa ya gama mamaye ilahirin Wurin. A hankali ta ƙare ware idanun ta tana watsa su zuwa inda take jiyo takon sa .
Gigif ta miƙe tamkar mai tsoron sa , murmushi ya sakar mata tare da zuba mata lulun idanun sa mai ƙara rikitar da matan da ya saba yaudara , hushiryar sa na bayyana , Ɗan sakin jiki tayi tare da sauke hannayen ta. Gaban ta ya ƙariko yana takowa zuwa inda take tsaye. Shiru Umaima tayi jikin ta kawai taji ya hau rawa kar kar karrr , yau ne taga ya rikeɗe mata ya koma mata Cikakken SEXXY BOSS Kaman a da baya yanda ta san shi . Huuuuuuu taji ya hura mata iskar bakin sa . Saurin sakin ajiyar zuciya tayi tana ɗago da idanun ta tare da kallon fuskar sa da siririn saje ya kyewaye . Tunanin mene kike yi??. Ammmm..... Ammm ..Kame kame ta tsaya yi masa , wannan yasa shi fahimtar Wayar ta dake ringing taƙi ɗagawa . Matsowa Taga yayi daf da ita kaman zai shige mata duka , fuskar sa yasa yana yi kaman zai haɗa da nata , gani tayi bakin sa ya motsa kaman yana furta" Alhmdllh , Allah yau ya bani ke Umaima , amma yau zaki jure ma komai na , ba zaki mun kuka kaman a baya yanda kika saba mun ba?. Ya ƙare maganan tare da sa hannun sa yana amsan wayar hannun nata . Ganin mai kirar yasa shi miƙa mata yana cewa " Bari na watsa ruwa . Kasa basa amsa tayi har ya fice ,kana tayi saurin ɗaga kirar " Ke Wacce irin Shashasha ce?? Kina ina nake kira baki ɗaga ba?. Cike da Rawar murya Umaima tace "Yi hakuri Momy yanzu ne ya matsa kusa dani shiyasa . Huuuumm Sauke numfashi tayi mai ƙarfi kamin tace " Umaima burin ki ya kusa cika , baki na da wanda kike so ba , Fahad ko?? To kar ki bari wani Abu ya shiga tsakanin ki da Umair ,domin daga gobe kun rabu har Abada , Gomnati na bin cike akan dukiyar sa da yake gadara da izza dashi , a gobe jami'an gomnati zasu taho har gida su kama shi . Wani irin bugawa ƙirjin Umaima yayi da har sai da wayar ta kusa ƙuɓce ma hannun ta .
Hawaye ne ya fara zubo ma kuncin ta ,sam ta kasa daure mawa zuciyar ta , cikin wani irin hasalalliyar murya ta fara cewa " Mom Wai me Ya Umair yayi maki ne? Momy ina Son miji na , bazan bari wani Abu ya same shi ba,bani da wanda nake so Sama dashi ,kuma Allah ya bani kike ƙoƙarin raba mu?? , Momy yau yanzu zan faɗa masa komai don ya tsira daga tarkon ku , a yau ya bar gidan ,in da hali ma