Showing 21001 words to 24000 words out of 55607 words
kiranta mama dije wadda ke aure agarin kano tana auren wani custom,tana ya guda sunanta umaimah,wadda ita kadaice rabonta,tun rasuwar yan biyun ta na fari,sai kuma umar shine ke bima sarki Ali murai,Sai Abdul rashid ,sannan khadija,sunan mahaifiyar su sadiya suna kiranta hajiyar safkare,a takaice hajia,dukkanin su sunyi aure,..........Dr.Ammar yayi karatunsa tundaga secondry har tertiary a kasar india inda kuma kuma yasamu aiki achan shida aj,Dr ammar mutun ne mai tsantseni ga tsandar tsiya duk da yana da laziness bai yadda yasaka ma kansa kanzanta ba,baida daukar raini,dan gayu ne na asali,baida daukar raini,kuma bai da wulakanta talaka hasalima shi mai tausayinsune,mutun daya ne yake iya wa da halinsa shine dr aj kuma shine babban abokin sa,domin sun kasan ce kamar yan biyu kamar yadda iyayensu suke,dr ammar dai kyakkyawa ne na karshe,har yanzu bai da budurwa duk da harin da yan mata suke kawo masa,natayin soyayyarsu,mutun daya ce tazame masa kamar cingum itace dr malini,domin Allah yasanya mata wani sonshi duk d yana kokarin nuna mata bata cikin tsarinsa hakan baisa tayi sanya ba wannnan kenan...
SAI DR.AJ
Cikakken sunansa dr Al amin jabir muhammad soja,dane ga leutenant jabir muhammad wanda yakasance army ne na nigeria,shine shugaban sojojin arewa,sunan mahaifiyarsa husaina inda suke kiranta ummi,Aj yanada kanne uku inda namijin dake bimasa yarasu tun yana karami mai sunan mahaifinsu jabir ,sai mai bima margayi jabir sunanta sumayya,sai Auta Asma'u suna husnat,wadda taci sunan kakarta su ta wurin uba,Aj sa,a ne da dr. ammar kwana arba'in ne tsakaninsu,Sai sumee wadda take da shekaru sha tara sai auta husna nada shekara goma sha uku,aj da sun taso komai sunayinsa atare,Aj shima baida wata tsayayyar budurwa har yanzu Wannnan kenan...
*MUDAWO LABARI*
------------------------------------------------------------------
*~~NIGERIA ZAMFARA~~*
*~~ BUG~~*
*~~UNGUWAR SABON GARI~~~*
...........Bayan fitowar Baba Adee daga wanka Ya shiryawar sa cikin shiga ta kamala dai dai rufin asiri cikin yadinsa mai kyau black,bayan fitowar sa wanka wanda da taimakon Bba Asabe ya shirya wanda kuma shine dalilin saukarsa da wuri dama shi ba mutun bane mai riko..
" A bangaren su Halee kuwa bayan kammala shirin su na zuwa islamiyyya suka dauki jakun kunansu,sunfito rass dasu cikin uniform ash colour hijab har kasa masu kyau sai sheki sukeyi,dukannin su sun amshe su musamman ma Halee wadda farar fatar ta tak'ara haskawa, kyakkayawar fuskar ta ta fito rass doguwar fuskar ta kara yin wani shaf mai kyau cikin dogon hijab dinta gwanin burgewa,sunata zuba kamshi mai dadi,wanda sai ka matso su zakaji shi,ba mai cutarwa ba kamar dai yadda aka annabi ya siffanta turaren mata,
'Dan Baba Adee akwai son kamshi domin mafi yawancin tsarabarsu ta turare ce,shiyasa koda yaushe zakaji su cikin kamshi....
Sallama sukayiwa Baba Adee da Baba Asabe Dake zaune a barandar gidan suna dan taba fira jefi jefi...
Miji da mata sai Allah..
ficewa Gidan sukayi bayan amsa addu,o'in da yasaba yimusu inyana gida...
Bayan wucewar su Halee islamiyya,shima Baba Adee yaficewar sa zuwa masallacin unguwartasu dan gabatar da la,asar kan lokaci.....
*~~GUSAU,ZAMAFARA~~*
Gusau ta sambo mai dimbin al umma noma shine abun alfaharinku,Gusau Babban birni ne na jahar Zamfara wanda yatara dubbanin Al umma ta kowane sashenn yarukka da yan kasuwa,musamman manoma,da ma aikatan gwamnati da manyan yan siyasa,Babban Abunda yake abun burgewa agaresu shine yadda sukayi riko da aladunsu,da addini da kuma sarautunsu,sai kuma abun da yake mai mahimmanci da suka rike shine Bin shari'ar musulunci,gari ne daza kasamu suna bin dokar musulunci wanda ko gidan karuwai zai yi wuyar samu a jihar...
*MASARAUTAR MURAI*
Babbar masarauta ce dake cikin jihar zamfara gusau wadda gaba daya nigeria suna alfahari da ita domin kafaffiyar masarauta ce tun zamanin Sarki Ali murai wanda shine sarki nafarko wanda yafara yin sarauta ajihar tun zamaninsu shehu usman dan fodiyo Na sokoto,shiyasa takasance mai mai dimbin tarihi...
'kuma shine yayi ruwa yayi tsaki gurin kafa wannan masarauta mai tarin Al ummah ,wadda tazamo abar alfahari a idon al ummar nigeria jin irin kokarin da sarki Ali murai yayi gurin kafa masarautar..
Mutane daban daban daga cikin ya yan Ali murai sun rike sarautar wannann masarauta har izuwa yanzu da ake k'ara samun cigaba...
Tattab'a kunnen Ali murai a yanzu shiyake mulkar masarautar,inda take samun kulaawa dakuma Al.ummar dake karkashin ta,Ahannun d'an d'an sarki Ahmad..
WASH TYPING AKWAI WAHALA...KUYI MANAGE DA WANNAN....BANJIN DADIN JIKI NANE.....
GOBE IN SHA ALLAH ZAKU SAMUN KARIN PAGE
Kuyi sharing,
Sannan ku danna min like akasan page din....
Ina godiya sosai masoyan amafarki
Halee tace agaishe ku...
💫FA'EEH BG💫
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️
💫P.E.W.A.💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️
Pen🖊️*is migthier than the sword🗡️*
------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE1️⃣8️⃣↔
TYPING📲📲📲
*TUSHEN MASARAUTA*
"Ali murai shine Asalin wanda yarik'a masarautar yana da mata kwaya d'aya tal,sunan ta Hajiya lubah (iyami) da "ya "ya maza biyar,d'an sa nafarko sunan sa bello,sai nabiyu sunan sa Haruna,na ukun Abdul aziz,sai na hud'unsu Isma'il,sai Autansu yahaya..
Bayan rasuwar sarki Ali murai sai aka nad'a d'ansa na farko Bello wanda shi yacigaba da kula da masarautar yana da mata d'aya da y'a y'a hud'u namiji biyu mace biyu,Bayan wasu shekaru shima Bello yakwanta dama,wanda mutuwartashi ta kowa ya jita A Masarautar saboda sak halinsa irin na mahaifinsa sarki Ali murai,Mahaifiyarsa takoka da rashinsa da y"an uwansa da ma Alummar Masarautar.
Bayan gama zaman makoki Aka nad'a d'an uwansa Haruna,Haruna yak'arb'i mulki cikin salama ,Sai bayan shekaru sittin sannan Allah yakarbi ransa..
..Abdul Aziz Yakarb'a shi kwata kwata ma bai ka shekara hamsin ba akan karagar mulkin saboda ciwon daya ci k'arfin sa na k'oda,sai aka nad'a Isma'il,Bayan Nad'in Ism'el,Sarki Abdul aziz yakwanta dama....
Isma'el ya cigaba da mulkin masarautar Bayan shekara saba'in bisa karagar mulki yakwanta dama,wanda bayan rasuwar sa,Anyi rigima sosai da Yahaya danshi kwata kwata bayason sarautar,acewar sa kayan wahala ce da takura,bai karb'a har sai da mahaifiyar su iyami ta kwanta ciwo akan hakan,ciwon zuciyaar ta yatashi wanda yasameta tun bayan rasuwar mijinta sarki Ali murai,sanadin bak'in cikin
Yahaya da yakafe bazai k'arb'i masarautar ba,masarautar da mijinta sarki Ali murai yasga gwagwarmaya wurin ginata,daga k'arshe dai yakarb'a ganin yadda ran mahaifiyar sa ya b'aci gashi harda kwantawa ciwo....
'Anyi bikin nad'in sarauta da ba'a tab'a yin irinsa ba alokacin kowa kaga fuskar sa da annashuwa da farinciki kamar sauran lokutta domin sun san cewa ba su shiga mugun hannu ba dan duk cikin ya"yan sarki Ali murai babu wanda yamusu mugun riko,Yahaya yakarbi mulki cikin aminci tare da alkawalin kula da Alummar masarautar,yana da shekara talatin akaragar mulki matar shi tahaifi namiji wanda shikad'ai ne rabonta har tabar duniya,yaron yaci sunan margayi tsohon sarki Bello,bayan wasu yan shekaru,Kwatsam ranar aka wayi gari da mutuwar sarki Yahaya murai,wanda mutuwar sa ta girgiza kowa musamman yaronsa sa Bello,Bayan rasuwar sa da kwanakki itama tsohuwa Iyami mai ran k'arfe ta kwanta dama,tana da shekaru D'ari da hud'u a Duniya.
Wanda kowa yaji mutuwar wayen nan bayin Allah Acikin Masarautar da ma wajen Masarautar..
Bayan rasuwar yahya Anyi rigima sosai A fada akan wayenda za,a dora akwai d'an wajen margayi bello da yace yanaso sai kuma d'an wajen magaji wanda yaya ne ga Sarki Ali murai,daga k'arshe dai Muhammadu bello D'an wajen sarki Yahaya shi aka bawa bisa ga chanchantarsa duk da akwai k'aranta atare dashi dan duk sun girme masa.
Anyi nad'in sarauta tareda Daurin Auren Sarki Bello Alokacin yana da shekara ishirin da hud'u A duniya,Bayan hawansa akaragar mulkin yana d'a yan uwansa manyan muk'a man masarauta,domin cigaban Alumma .
Ya Auri yar wajen sarkin zazzau na hud'u alokacin mai suna Gimbiya Ruk'ayya bayan shekara gimbiya Rukayya ta haihu ta samu yan Biyu maza,Alokacin ne kuma matar tsohon sarki margayi yahaya uwar muhammadu bello tabar duniya,Anyi taron suna cikin alhinin wannan rashi,tacigaba rainon yan biyu dinta,Bayan wasu shekaru tasamu wani cikin inda tahaifi Namiji yaci suna Aliyu,sunan tsohon sarki...
'A Daren sunan Aliyu ne wani Babban tashin hankali yafaru inda wuta ta kama ad'akin su hassan da husaini duk suka k'one k'urmus sanadiyyar wutar lantarki suda mahaifiyar su gimbiya Ruk'ayya wadda taje dubasu daga nan ta musu Addu,ar kwanciya bacci duk da tasan cewa bazasu kwanta hakan nan domin takoyar dasu,alokacin suna shekara shidda A duniya,Mutuwar data girgiza Sarki Bello da kuma masarautar wanda sai da sarki Bello yasuma alokacin da aka sanar dashi,Bayan jimamin rashin Sarki Bello yaci gaba da rainon D'an sa Ali....
**Bayan shekara guda sarki Bello yayi Aure ya Auri wadda take baiwa ce Amasarautar, ya Aureta ne saboda ganin irin kulawar da take bawa Aliyu wanda kuma ita kad'ai yake yadda da ita,Sai ya " yenta ta kuma ya Aureta domin samun farin cikin D'an sa tilo daya.
Lafiya lau masarauta take tafiya tareda cigaba mai yawa,Bayan wasu shekaru Sarki Bello na Biyu yabar Duniya yana da shekaru hamsin akan karagar mulki,inda yabar Aliyu cikin maraici mai yawa duk da wannan yentacciyar Baiwa mai suna Nana Asma'u tana sonshi tana bashi kulawa mai kyau saboda yadda take jinsa kamar d'anta na cikinta..
BAyan gama jimamin mutuwar sarki Bello na || biyu aka nad'a d'ansa Aliyu alokacin yanaa da shekaru ishirin da hud'u a duniya.
Bayan na d'insa da shekara guda yayi Aure ya Auri yar masarautar sokoto jikar yar sarkin musulmi na ||| na uku;mai suna ummulkhairi ana kiranta gimbiya (umma),Bikin yatar dubbanin Al umma takowace masarautun nigeria da manyan yan siyasa,masu kudi..Ankawo Amarya lafiya cikin fada acikin sashen ta mai kyau,suna cin Amarcin su lafiya lau tare da zaman Amana....
Komai yana tafiya dai dai ta b'angaren mulki yadda yakamata.
Bayan shekara d'aya gimbiya umma tahaifi santalelen d'anta namiji ranar suna yaro yaci sunan sa HAMZA ALIYU MURAI,Anyi taron biki lafiya,inda tacigaba da rainon yaronta,Bayan haihuwar Hamza da wata takwas tasake samun wani cikin alokacin gimbiya ummulkhairi taso zubarda cikin ganin Hamza ko shekara bai had'a kar yasha ciki,sai dai mai martaba sarki Aliyu yahana zubar da cikin sai dai yasa aka cire Hamza daga nono...
Taraini cikinta lafiya lau batare da tasha wuya ba,watannin haihuwar cikin nayi nak'uda ta motsa amma yaro yaki fitowa ak'arshe dai CS akayi mata aka ciro santalelen d'anta mai kama da uban sa sak,yaron yaci suna Ahmad...
.....Bayan wasu "yan shekaru sarki Aliyu D'an Bello jikan Yahaya D'an Sarki Ali Murai yabar Duniya alokacin,yabar Duniya da shekaru arba'in akaragar mulki,Mutuwar sa tagirgiza y"a yansa guda biyu a duniya da matar sa ummulkhairi,inda tacigaba da kula da yayanta cikin kulawa,Bayan Rasuwarsa da yan watanni Nana Asma'u matar margayi sarki Bello na || tabar duniya...
Sarautar dole aka bawa magajin gari rik'on kwarya kafin ya'yan sarki Ali su kai lokacin iya rike sarautar,domin dukkaninsu bazasu wuce shekara goma sha biyar Alokacin ba.
Bayan wasu shekaru Ahmad yayi aure ya auri matarsa Bafullatanar Adamawa itama yar gidan sarautace sunanta Haleematu sadiya suna kiranta hajiyar safkare wanda sunan da kakarta ta lakamatane,ya Aureta yana da sheakara ishirin da shidda aduniya sunyi Auren soyayya da gimbiya halimatu,kuma aloakacin ne aka damk'a sarauta hannun Ahmad duk da sai da akayi rigima dashi dan yace bazai karb'a ba sai dai abawa y"a yanshi tunda shine Babba,Dakyar aka samu yakarba bayan ya yan nasa ya sanya da mahaifiyarsu gimbiya ummulkhairi suka tasoshi gaba....
Anyi bikin nad'in sarauta lafiya cikin annashuwa da salama,ta fannin zaman takewarsa da matar sa masha Allah za,ace gwanin burgewa.
****Bayan shekara daya gimbiya halimatu sadiya ta haifi santalelen d'anta mai kama da ubansa sak jinin fulani,farin cikin wannan masarauta bazai boyu ba musamman sarki Ahmad da D'an uwansa hamza,wanda ke ji kamar shi akayiwa haihuwar...
*Ranar suna yaro yaci sunan kakan sa sarki Aliyu Bello jikan yahaya d'an Ali murai*yaro yasamu gata ta kowanne fanni,Alokacin shima Hamza yayi Aure ya Auri Gimbiya Hauwa'u yar masarautar Fulanin Bungud'u ana mata lak'ani da fulani,fulani macece mai fadin rai da rashin son talaka,da mugun son kanta,ba kamar gimbiya halimatu ba mutuniyar kirki mai mutunci,BAyan Aurensu da Hamza sai tafara nuna mishi ai sarautar dashi ta dace domin shine Babba yace abashi sarautar,ai shine dana farko ga sarki Ali Bello,sai ya rik'a nuna mata baida buk'ata,kullum haka suke rigima da ita,har zuwa lokacin da tasamu cikin Mustapha A lokacin kuwa matar sarki Ahmad Halimatu tasamu ciki na biyu ta haifi umar,sunan mahaifinta kenan,tana kiransa da emir,Bayan kamar wata takwas sai ga wani cikin na ukku inda ta tahaife sa lafiya,tasamu Abdul rashid,tacigaba da rainon ya yanta cikin kwanciyar hankali.
Daga cikin abin bak'in cikin da yafaru Akwai rasuwar gimbiya ummulkhairi matar tsohon sarki Ali,Mahaifiyar sarki Ahmad da Hamza,sunyi rashin mahaifiyarsu abar kaunar...sai dai muce Allah yajikanta da al ummar musulmi baki daya.........
*Yaa Allah Duk wata mahaifiya 💔💔dake kwance akarkashin k'asa,Allah kajik'anta da rahaama,da musulmi baki daya,Yaaa Allah wayenda suke raye kuma ka k'ara musu lafiya mai amfani tare da tsawon rai mai albarka*🙏
Rashin uwa rashine 😭Babba Arayuwa
Allah yabar mu dasu 🙏
--------------------------------------------------------------
Matar Hamza Fulani tak'ara samun wani cikin nabiyu ta haifi d'anta namiji mai suna Muhammad ana masa lak'ani da Malan,tana da ya"ya biyu kenan.
Itama sarauniya halimatu taka'ara samun wani cikin bayan shekara uku inda ta haifi yarta mace mai suna khadija inda daga gareta haihuwar ta tsaya mata chak......
Sarauniya Halimatu yaranta sun taso cikin soyayyar junansu Da yan uwansu yan gurin magaji hamza,domin shi d'an uwansa ya nada magaji bayan rasuwar wanchan magajin.....
Duk da tsangwamar da Fulani take nuna musu amma hakan bai hanasu jan yan uwansu ajiki bah.
Ta b'angaren magaji Hamza kuwa yana shan matsin lamba gurin Hauwa'u (fulani )kan karbar mulki alokacin takara samun ciki tahaifi ya mace mai suna ummulkhairi suna kiranta (khairiyya) dan taci sunan kakar ta ne wanda daga gareta haihuwar ta tsaya ma fulani chak..
A lokacin Duk fulani tana masa matsin lamba wanda har tafara cin galaba akan sa,dan bata tsaya haka nan ba,sai da talek'a gurin malammaan tsibbo (bokaye) Wal iyazubillah....
bokaye mana domin tahakan ne wasu suke amfani dashi sai suce ai malami ne shi bokan,ana amfani da sunan malamman ana shirka ana cutar Al umma..ALLAH YAYI MUNA TSARI DASU...Masu zuwa gurin bokaye Allah yashiye su🙏
MU HADU GOBE IN ALLAH YAKAIMU
YAU KAM KUNSAMU LONG PAGE,DAN KONI NAJI AJIKI NA,KUNGA NA GOGE LAIFINA NA JIYA,DUK DA BANI DA LAFIYA NE
NAGODE SOSAI ALLAH YABAR KAUNA🙏
KUFARA SHIRI ANKUSA GAMA FREE PAGES,DAN BATUN SAMBAD'O KUD'INKU......
Kucigaba da bibiyar Alkalamina
Yau duk sai A hankali typing din domn page d in yatado mini da rashin da mukayi...Allah yajik'anku da rahama Baba Bello,kakana Baba Yahaya,Alhajin Auki,Mariya,gwaggo yar sarki, Allah yasa Aljannna takasance makomarku da dukkan musulmi baki daya..AMEEEN...
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,Na episode two*!!!✌✌💥💥
*TALLAH!!! TALLAH!!! TALLAH*
*Ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,ga dama tasamu domin Muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harda ma k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntubarmu ta lambobin waya kamar haka*......
+ 2348069059746
+ 2349078741775
-----------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION 📚🖊️
💫P.E.W.A.💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️
Pen🖊️*is migthier than the sword🗡️*
------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE1️⃣9️⃣
TYPING📲📲📲
________________________________________
" Rana ta farko daya isko sarki Ahmad da maganar yana son sarautar ta dawo hannunsa,Sarki Ahmad bai nuna komai ba akan fuskar sa,sai dai murmushi da ya wanzar akanta tare da furta masa zaiyi magana da manyan masarauta,duk da yasan lallai su amince ba,saboda tun farko da yardarsa aka d'orasa,kuma ba,a chanza sarki kai tsaye ba da kwakkwaran dalili ba a wanchan lokacin..
Koda sarki Ahmad yagana da manyan masarauta sun nuna k'in Amincewarsu kaitsaye.
'kiran d'an uwan nasa yasanar dashi domin badashi anakayi zaman ba,kamar ganawar sirri ce,daga su sai maimartaba sarki sarki Ahmad sukayi ta,yana yin yadda yaga D'an uwansa yana kuka kasharb'an hankalinsa yatashi sosai,dole yasanya taron gaggawa yace yayi murabus kan kujerar tare da katse duk wasu tambayoyin da aka so tsiyesa dasu inji manyan masarautar..
'Farin cikin da yagani kwance akan fuskar d'an uwan nasa Hamza shine Abunda yatsaya masa arai,Bayan komawar sa gida bai b'oyewa gimbiya Halimatu sadiya komai ba,Tayu mamaki sosai duk da tasan akwai wata a k'asa sun san halin matar sa sarauniya Hauwa'u zata iya yin komai sun yarda cewa bayin kansa bane..
:::::::Rayuwa tana tafiya yadda yakamata,sarauniya Hauwa,u (fulani) mulki ya shigo hannu sai taka talakawa take yi son ranta duka bayi alokacin sun san halinta tsoronta sukeyi sosai domin wulakanta su bakomai ne awajenta ba,musamman na sashenta,Yadda take da mugun hali haka tab'ata D'anta Muhammad,shi mustapha ba haka yake ba halin babansu suka biyo shida macen da takara haifawa mai suna ummulkhairi,wadda taci sunan kakarsu Ta wajen uba,suna kiranta khairiyyah..
A lokacin da akayi juyin mulkin duka ya yan sarki Ahmad maza basa nigeria suna wajen karatu,Aliyu yana china yana karantar Business Administration,sai umar yana Kasar Uk yana karatu fannin bincike da tsaro,sai Autan maza Abdul rashid yana kasar sudan yana karantar MBBS karatun likitanci kenan,Duk da alokacin sunji mulkin yabar hannun mahaifinsu ba wanda yadamu dan dama basu wani dauki mulkin wata tsiya bah.
Bayan kamar shekara bakwai lokacin umar yagama nasa karatun har masters ya had'o,yadawo gida alokacin ne kuma mahaifinsu sarki Ahmad yakwanta dama,😭mutuwar data girgiza kowa dole dukkaninsu suka dawo nigeria dan ganin gawar mahaifinsu,wanda kafin suzo ma an binne ta,ganin basu iso da wuri ba,khadija kadai tasamu damar isowa da wuri ita dake Adamawa gurin kakaninta tana karatun a wata private school ta Nursing wanda tashiga a wannan year din,koda suka iso rashin ganin gawar ta mahaifin nasu sai takara rikita su,in kagansu alaokacin sai ka sun baka tausayi,wannan mutuwa basu