Showing 18001 words to 21000 words out of 55607 words

Chapter 7 - A MAFARKI NASANTA BY FA'EEH BG FIRSTLADY .txt

28 Dec 2024

3834

kansa..


Duk sai sukayi na,am da maganarsa,yacigaba da magana nasan abunda kuke tsoro kar gwamnati taji abunda yafaru na suspension din da yabaku,namuku alkawaro bawanda zaiji,nasan cewa incident din da yafaru d'azu da safe ne yasanya sa baku wnnnan hukuncin duk da banga alamar fushi afuskarsa ba,dan shi mutun mutune wanda baicika bayyyanar da fushinsa ba...


Godiya duk suka masu nuna jin dad'i har ya juya sai sabirkhan ya tsaidashi ta hanyar fad'in sir,juyowa yayi dan ga tsoho sabirkhan yace da aj yallab'ai ban tari numafashinka ba,amma inaga da kabar hukuncin yadda yake saboda ina da tabbacin duk wannnan abun akan ka yayasa saboda fahimtaar da yayi ranka ya sosu alokacin da aya aika akaima maka mota,kuma ba,aje da wuri ba,shiyasa,dan nima na fahimci bada son ransa ya furta musu maganar suspension ba ,shiyasa tunda yafara maganar sa ban nuna alamun b'acin rai afuskata ba sai dai murmushi da ya wanzu akanta,inda ka lura ko d'ago kansa baison yi gudun had'a ido dani,kabarshi kawai dan inyaga katsaidamu zaiga kamar ka kwatse sane.....................


Murmushi kawai aj keyi har zuwa lokacin da tsohon nan yagama maganar sa,yak'ara da cewa kuma inada tabbacin ransa ya b'aci matuk'a dan naga alamar hakan alokacin da zai fita suka biyosa ya furta bai bukatar kowa ya bisa acikinsu....Kuma kasan halinsa baison ya sanya doka atake,nasan wani laifin ne kuma binsa da sukayi,mukuma yallabai kasan munyi rantsuwa akan zamu kare ku ta ko wanne yanayi kuma nasan kasan mahimmancin rantsuwa.


Uhmm aj ya furta yana mai girgiza kansa tare da sakin murmushi a fuskarsa,toh shikenan father dan haka suke kiran tsoho sabirkhan,kuje amma nan da kwana uku ku dawo nasan zuwa lokacin ya sauka ya furta musu,touh suka amsa masa dashi.Suka fara watseqa suna shisshiga motocinsu domin zuwa quaters nasu dake chan gaba da gidan su aj,bayan sun mimmika car keys ga aj dakuma gate controller...
Dr.Ammmar dake chan tsaye kan windown din dakinsa ne ya furzar da iska mai zafi abakinsa yana mai jin ba dad'i aransa duk da yasan yayi ne dan ya farantaran dan uwansa,A hankali yabar bakin window din yana komawa kan hadadden gadonsa ya kwanta flat yana kallon ceilling daga shi sai towel dama fitowar sa daga wanka kenan....


Aj nashiga shima ya wuce nasa dakin wanda izuwa lokacin har ankara gyara falon sai tashin kamshi yakeyi ankwshe food flask din dasuka ci abinci angyara lungu da sako sai sanyin ac daya kara ma falon natsuwa ko ina masha Allah.


💫💫Fa'eeh BG💫💫


Aj ne bayan shigarsa nasa dakin ya aje car keys din da gate controller din ya jawo wayar sa yana dialing numban sabirkhan gate man....
Bayan yad'aga kiran sun gaisa cikin mutunci,tambayar sa yayi daya turo mai dai daga cikin yaransu wanda zai kula da gate din kafin su dawo aiki to kawai yace sannan sukayi sallama...


A b'angaren dr.Ammar nan bacci yakwasheshi bai farka ba sai dayaji ana kiraye kirayen sallar la,asar,A hankali kiran sallar ke shiga kunnuwansa mikewa yayi a hankali yana addu,ar tashi daga bacci tare da ambaton kalmatu shahada.....fuskarsa yake yamutsa wa bayan duba hadadden agogon dake kan bedsite drowernsa hud'u dai dai ya gani ta buga shi yasanya sa tashi da hanzari dan yaga lokacin yayi kusa,ankusa tada sallah,shaf shaf yashiga wanka bayan yayi brush yayi wankansa tare da dauro alwallah,bayan yafito tsane jikinsa dayayi turare kadai ya fesa sannnan ya bude sip din sa yazaro dai daga cikin jallabiyoyinsa da short,da vest baka dasauri yazura jallabiyar bayan sanya underwears din yasauka kasa yana ta sakin kamshi,koda yasauko kasa yatarar da aj tsaye yana jiransa,shima cikin shirin jallabiya irinta dr ammar sai dai banbancin colour shi aj tashi fara shikuma ammar dark maroon wadda ta karbi fatarsa,ba wanda yaceda dan uwansa kala har suka fita falon suka shigamota aj yajasu zuwa masallaci....Dama mai gadin ya iso yakarb'i gate controller din suna zuwa ya wanagale musu gate din ta hanyar danna remote din,yau da mota suka fita ganin sun makara ,duk da masallacin basu da nisa dashi cikin unguwar tasu ta manyan masu naira maisuna gujarat 105 estate.......


Next page monday in sha Allah
Like pls...Nd comment






* Allah yasa mudace*🙏🙏
Pls like share and comment






💫 A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
pha,eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫




Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️


💫 P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️
Pen*🖊️is mightier than the sword🗡️*


EPISODE1️⃣
FREE PAGE1️⃣6️⃣


TYPING 📲📲📲


--------------------------------------------------------------*DRUG ABUSE
🚭❌❌❌
SHAYE SHAYE ILLANE GA RAYUWARMU,INA SAMARI, INA YAN MATA KU GUJI TA AMMALI DA MIYAGUN K'WAYOYI DOMIN SUNE ABU MAFI SAURIN HALLAKAR DA RAYUWAR MU....MUNA📢📢📢 KIRA DA BABBAR MURYA,DAKUMA BADA SHAWARA A GUJEWA DUK WANI KAYAN MAYE DAN SAMUN INGANTACCIYAR RAYUWA MAI AMFANI*
-------------------------------------
HANYOYIN DA ZAKA KARE KANKA💁 DAGA AIKATA WANNAN DABI'A SUNE
*KAUCEWA ABOKAN BANZA
*ZAMA DA MUTANE NA GARI
*SANYA TSORON ALLAH AZUCIYAH
*BADA SHAWARA TA KWARAI GAMASU AIKATAWA
*CIRE KWOKWANTO GA AL AMURRANKA
*KAUCEWA MASU AIKATAWA
*YADDA DA KADDARA KO WACE IRI CE ILLA MAI KYAU CE KO MARA KYAU CE.


🙋🙋MU KIYAYE DOMIN RAYUWAR MU ABA CE MAI AMFANI ATATTATARE DAMU,DOMIN AMANA CE UBANGIJI YA BAMU....ALLAH KAYIMUNA MUWAFAK'A🙏🙏
----------------------------------------------------------------
**********
*****
***
**
*Bayan sun dawo daga masallaci suka cigaba da kallonsu afalo a tashar da ake hasko wasan ball, har magriba ta gabato suka dunguma akafa sukaje a wannnan karon domin sauke farali...

"kowannen su dakin sa yawuce direct bayan bayan dawowar daga sallar dan fresh up,AA ne fara fitowa Dan bakar yunwar dayake ji shiyasa bai tsaya shiriritar sa ta shiryawa ba,dama yunwa ce kadai kesanta sa yayi gaggawar yin abu sa dasauri sai kuma in yasan suna da tarin patient da zasu gani ko kuma akwai emergency case a hospital din....


A hankali ya doshi kan dinning din nasu yana baza kamshi cikin shigar short trouser fari da kuma vest blue wadda takara haska fatar sa ...


''zaman shi keda wuya sai ga sajidkhan dan dama yaga fitowar ogannasa daga tagar kitchen ta chan mai kallon dining,


"barka da dare yamasa sannnan yajawo pilet yana mai bud'e manyan food flask dake kan dining din masu kyau,duk da yaji bai amsa masa maganar sa sai ya furta sir mai za,a zuba maka,"Anything" ya furta atakaice
Tuwon semo ya zuba masa da miyar egusi da taji busasshen kifi,ya dora masa agabansa tare sa sanya masa spoon a ciki da zuba masa ruwa a karamin cup na glass da lemu,A hankali ya fara cin abincinsa,Aj da tun d'azu ya iso wurin yaga abunda yafaru yau Dr AA ne ya bari kuku ya zubamasa abunci...Yasan cewa bak'ar yinwa ce nanake da cikin sa shiyasa ya yadda amma da ba haka ba da kai tsaye zai dakatar dashi....


"Kansa kawai ya girgiza yana mamakin halin dan uwan nasa


"shima dai tuwon shinkafa da miyar wadda taji naman sa rago ya zaba,bismillah yayi cin abincinsa hankali kwance kamar ammar din,Muryar Dr ammar ce ta karad'e gurin yana mai furtawa sajidkhan "have me some water in a rubber"cikin calmly voice dinsa,ohk sir!ya furta, ruwan ya kawo masa aroba mai dan fadi


"hannunsa yacire dake kan spoon ya kada sa acikin robar ya ya wanke hannunsa sannna yasanya acikin filet din tuwonsa,Yunwar da yake ji bazata bar sa cin abin da spoon gani yake kamar yana bata masa time,domin shi mutunne da baya wasa da cikin sa,shiyasa ya cire spoon din yasanya tattausan hannunsa,mai da robar sajidkhan yayi kitchen ya maida robar ma,ajinta bayan yayi discard din ruwan..

Abincinsu suke ci hankali kwance,musamman dr.Ammar wanda kaikayi zaton manyan lomomi zaiyi daya sanya hannu sai dai ahanklai yake saka abincin adan karamin bakinsa cikin natsuwa kamar ma bai tauna tuwon..Yana gama cin semo dinsa yayima sajidkhan alamar akara masa,Sai yanuna masa na shinkafa,a wani sabon filet din ya cigaba da cin abincinsa hankali kwance..


Shikam Aj tuni yabar kan dining din yana waya wanda daga ji macece ta hanyar yadda yake mayar mata martani......


Shima dr ammar nagama cin abincinsa ya mik'e ahankali ya wanke hannunsa a sink din dake gefen dining din,lura da akwai aikin da mai aikin nasu yake yi akitchen din....




Wayar sa yadauka kawai yawuce warsa falo cikin tafiyar kasaita wadda sarauta tagama ratsa jikinsa,da zuwan sa yazube akan 2 sitter yana lumshe idanunsa jinsa yafara dawowa nrml da yunwar da ta dibesa, bayan kamar minti biyu ya lura da wayar sa aj din keyi,wanda koba,a fad'a ba yasan sumayya ce yake waya da ita wadda ke bima aj din,Amma anfi kiranta da sumy .....................................................………………


💫 Fa'eeh BG💫


Jin tambayar da yayima nacewa ina Auta husna ne yasanya sa kara tabbatarwa.


Ahankali ya kunna piano game yana bugawa cikin kwarewa da natsuwa,Maganar da aj yayi ce tasanyasa dakatar da game din,inda aj din ke furta wa sumy din kin raina ni ko sumayya tun yaushe nace kibar min wannna maganar amma bakya ji koh,yakai karshen maganar da yanayin hasala,cigaba da maganar yayi yana furta ki sani matsayi daya na dauke ku da ita,nace kibar mun maganar NISA domin kuwa itama kanwa ce agurina bayan wannnan babu komai,daga chan dayan bangaren naji ana furta sorry yaya aj,shiru yayi bai tankamata ba jin wata murya mai sanyi nakwala kiran sumy!sumy!wanda har sautin yake ratso kunnuwansa daga cikin wayar ..



Chanza firar da dayan bangaren akayi shi ya tabbatar yakara tabbatar masa da muryar da yaji,Ajiyar zuciya yasauke ab'oye ya makarnata ya furtamata kamar basu yi wannan gaisuwar ba inda take furtamasa ya aiki,lfylau ya furta itama tana furta karatu alhmdllh,Bayan jin ta amsa ma wadda ke kiran sunan nata,ta hanyar furta na,am nisa lafiya wannnan kira haka da murmushi a fuskarta ta furta kizo anfara shirin" imlie " dan suna matukar son shirin wanda starlife suke haskawa akullum mai dogon zango ,musamman nisa wadda sunan ta yake (yuhanisa)tana mugun son shirin dan ita takoyawa sumy sonsa,a cewar ta jarumin mijin imlie na farko yana kama da yaya aj dinta dan tana mugun son aj kamar ranta,sumy kadai tasan da maganar sai kuma wasu daga cikin kawayensu.......




Fahimtar da nisa tayi sumy waya take kuma da yayansu ganin yadda ta natsu,yasanya A hankali ta karaso kan gadon tana mai fadin allah yasa baiji ni ba tana rufe dan karamain bakinta,Murmushi ne ya subucewa dr.aj jin radar da tayuwa sumy,sannnan ya furtawa sumy bata wayar,A hankali sumee take mikamata wayar itama tana murmushi da addu,ar Allah yabawa kawartata ya yannasu ta yi wucewar ta falo...


A bangaren dr AA najinsan kuma yaciga da buga game dinsa,dan tun dazu Aj yamayar da wayar handsfree sanadiyyar rashin network na kirki da babu baiji sosai..
..........Shiru ne ya biyo baya bayan ta amshi wayar,A hankali tace yaya ina wuni murmushi yasaki yana furta kinmanta mu yanzu dare ne,laah ta furta tana rufe bakinta mai kama dana yayanta,tamboyi yamata game da kart tana amsa masa da alhmdllh cikin dan rashin sakewa dashi


Shiru ne yabiyo baya sai kuma ta katse shirun nasu,ta hanyar furta masa ina yaya Ammar ?
yana jin sautin Muryar kanwartasa sai dai yayi kamar baiji ba,duk da kallon da aj ke masa domin sarai yasan yanajinsu ...


Jin tana magiyar abatashi inyana kusa yasanya a hanklai yabaro kan kujera din sa yake yadaw kan hannun kujerar da aj kezaune,dan jin raunanniyar muryar kanwartasa tana rkon akan kawai taji muryarsa yasan duk laifinsa ne da baya cewa abasu waya inyakira,tunda basu da waya har yanzu basu bada izinin abasu ba wayan saboda kallon kananan yara da suke musu,ganin haryanzu basu gama secondry ba,a yanzu suna ss 3ne akarshen shekara zasu gama..




Hello!"yaya A ta furta tana sakin kayataccen murmushinta da hr aj dake kusa dashi yaji sautinsa dan yacire handsfree din bayan amsar wayar daga hannun aj..


Shima murmushin yasaki yasaki har saida dimple dinsa suka loba gwanin burgewa dama ayanzu duk kaga murmushinsa irin haka mahaifiyar sa ce ko kanwarsa wadda takasance ita ce autar su,suna mugun son juna datausayin junansu musamman Babban yayannasu da ayanzu yake abun tausayi...
hw are u ?fn ta furtamasa,ya schl da krt yakara tambayar ta ta furta masa Alhmdllh,Anbar doja koh tace ce eh cikin murmushi toh acigaba da kokari duk da bai yadda da maganar taba yasan su da rashin son zuwa makaranta tun suna kananan .


A hankali ya tsinkayi muryar ta tana tamabayar sa,yaya A yaushe zaku zo kugammu?murmushi yasaki yana fadin ashe kina gidan maaminah yayi hakan ne dan kawar da tambayar tata,ehh ta furta yau sati na daya,ohk!ya furta tare da tambayar ta inasu husnat da sumayya,"duk suna falo ta furta to ki gaidasu,toh ta furta cikin sanyin jiki jin yakawar da tambayar da tamasa don dama ta harbo jiginsa....
Yanzu dai je ki bawa maaminah wayan dan haka yake kiran kanwar ta mahaifiyarsa,mahaifiyar Aj,Hajiya husaina,kai yaya batasan andauko wayanta ba nima na isko sumy da itane,kuma yanzu intaga mundauko fada zatayi,murmushi yayi dan yasan halin mamin da bata daukar wargi duk da zaman ta nason barkwanc,kuma dama yasan basu fada mata zasu dauka ba,tunda yasan basuda waya,murmushi yakara saki yana mai fadin "to kudaina daukar mata bada izininta ba,babu kyau hakan,kurika tambayarta indai kungayamata ta "ya 'yanku zaku kira zata baku kunji koh"tau yaya in sha Allah ta furta.....


"in sha Allah inkuka samu result mai kyau a qualified exams naku zan siya muku waya mai kyau,murmushi tasaki mai hade da dariy tana fadin dagaske yayah ,kansa yadaga kamar yana gabanta yana furta eh,i love you so much yayah,proud of you the best brother in the world takai karshen maganar cikin farin ciki marar misltuwa domin dama sun matsu asiya musu wayoyi saboda mafi yawancin kawayen su na da ita,"me too ya furta cikin farincikin dayasamu kansa aciki Bye ki je ki aje waya yanzu kar taganku koh,toh yya tafurta tana masa godiya da sallama suna yanke kiran.........
Kowa ransa fess,cikin murmushin sa mai kara kawata fuskarsa ya juya ya dubi aj yana furta masa take your phone yana kara furta bari inje in dauro alwallah naga isha'i tagabato,da ohk kawai Aj ya bisa,shima yana mikewa yarage voluke din tv yana chanza tasha izuwa inda ake kira,ar qur'ani,ya wuce upstair shima tare da wayansa shaf shaf dukkaninsu suka dauro alwallah suka wuce masallaci don gabatar da sallar isha'i acikin jam'i....


Bayan dawowarsu aj kashe wutar falon da tvn kowa ya wuce nasa bedroom din dan yin bacci bayan sunyi sallama wannan kenan.........


BACK TO THE PRESENT .....
Murmushi kawai Dr aj yakara saki bayan gama tunano abunda yafaru kwana biyar da suka wuce yana mamakin hali irin na abokin nasa kuma dan uwansa.


Godiya bodyguard din nasu suka k'ara masa kafin suka koma gurin da dr .Ammar d'in yake tsaye shima suka kara masa godiya da basa hakuri,karbar jakar hannun sa daynsu yayi domin kaima sa office nasa.


Wanda shima bangaren dr aj hakance ta kasance agurinsa..
A hankali suka doshi hadadden hall din da yake cikin wannan katafaariyar asibitin ta mumbai wadda take da dubbanin tarihi na cigaban da ake samu ta hanyar kula da marassa lafiya shigarsu katafaren hall din daya tara dubbanin likitotah masu ji da kud'i da wanka,kowa yana zaune akan kujerar da take mallakinsa wadda ke dauke da sunansa.


A Hankali suka fara gudanar da taron cikin kwanciyar hankali,dama suna meeting din ne kan cases da ake yawan samu ne akan yawan mutuwar mata awajen haihuwa,suna son gano dalilin da silar faruwr hakan cikin alumma.......


..........................................
Kudai kucigaba da bibiyar 💞alkalamina…………A sannu zan warware muku wannan labari maicike sa tausayi,nishadi ilman tawarwa,soyayya,sarauta,cin amana,ga xumuncibugu da kari kuma ta,addanci wanda yakasance abunda yake ciwa alummar mu tuwo akwarya ganin yadda shuwagabbani suka zuba ido aalamarin da har yanxu ankasa samun mai yin katutu da al amarin,ganin kamar sunfi karfinsu wanda kuma ba haka bane,mu munsan addua bata bar komai insunfikarfinsu ai basu fi karfin ubangiji ba....sannnu bata hana zuwa sai dai adade ba,aje inji hausawa,dan haka karku sanya kucigaba bibiyar labarin....


NEXT PAGE TOMORROW IN SHA ALLAH
KUTAYANI SHARING BOOK DIN NAN PLS DOMIN AKWAI DARASI MAI YAWA ACIKI ...................




💫 A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️

💫P.E.W.A💫

Home of perfect writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️


pen 🖊️*Is mightier than the sword🗡️*
---------------------------------------------
TYPING📲📲📲




EPISODE1️⃣
FREE PAGE1️⃣7️⃣


WANENE DR.AMMAR(AA)
cikakken sunansa Abdulrashid Aliyu Ahmad,haifaffen garin Gusau,jihar Zamfara,Dane Ga sarki Aliyu Murai,sunan mahaifiyarsa hassana hamza wadda suke kira da unni,mama kenan ayaren (korea) mahaifinsa da mahaifiyarsa Auren soyayya sukayi,kuma auren zumunta,Mahaifinsa sarki Aliyu murai rikakken Dan kasuwa ne,wanda yake da kaloli kuma manyan kamfanona akasashen daban daban a duniya,A yanzu haka shine yake rike da sarautar ta zamfara A babbar masarautar murai ta Gusau'Ammar shine d'aa na farko ga iyayensa,sai mai bimasa hamza wanda yaci sunan kakansa na uwa,ana masa lakani da mahir,sai Auta yuhanisa inda taci sunan yayar kakarta ta uwa,suna kiranta da nisa,Ammar yana da shekara ishirin da takwas aduniya,mahir kuma yanada shekara goma sha biyar,sai nisa tana da shekara goma sha takwas aduniya,Mahaifiyar sa gimbiya hassana "yace ga wan mahaifin su sarki Ali Sarki,Hamza murai kenan,takasance yan biyu ita da mahaifiyar aj,sai autar su laila,sunan mahaifiyar su fateema suna kiranta Ammie,Ammar yaci sunan k'anin mahaifinsa Abdul rashid wanda shine autan su sarki Ali su uku ne maza,suna da mace daya mai suna khadija,suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login