Showing 30001 words to 33000 words out of 55607 words
yar dubar domin ruwa bazai sanyu ajikinsu saboda yadda suka chanza kamanni,sai dai gwargwado abunda gawar zata iya dauka,riko hannun d'an uwan nasa yayi mai kama da kwarangwal yana hawaye yana tofa masa Addu,a,A lokacin baiga zoben a hannun sa ba,sai maganar mahaifinsu tafad'o mai arai.......Zoben baijin wuta...
Tou Amma ina zoben yashiga da suka k'one k'ila yafita tare da naman jikinsa,touh ina zoben yashiga acikin gidan?sai maganar mahaifin su ta fado masa arai inda yace "koda wuta ta tab'a zoben zai zauna hannun maishi ne,sai idan ancire sa da dubara",Alokacin tunani barkatai ne sukayi ta zomasa arai,duk sai ya watsar dasu saboda tashin hankalin da suke ciki alokacin.....
Abu daya ne yatsaya masa arai maganar rashin samun gawar norah ko wata alama ta nuna akwai ta awurin....
Maganar gimbiya hassanat ce tadawo dashi daga firar zuci ko ince tunanin dayake "Cin abinci ko wanka zaka fara ?sannan insa Akawo ma nan?ganin yafada duniyar tunani....
Murmushi ya dajin jerun tambayoyin da ta jero masa,Cikin kara yin murmushi " har yanzu yarinya kike komawa,hassnat duk wayenn nan tambayoyi yanzu amsa suke nema,murmushi tasaki tana mai d'aga masa kai tare da gyara daya,murmushin yakara saki mai hade da dariya ganin yau rigima take ji,itama karamar dariyar tayi,furta mata ya afara hada mun ruwan wanka,nabiyu abinci da adining zanci tareda "ya "yana...
Murmushi tayi tana furta kamanta yau akwai school mahir yatafi itakuma yuhanis taana gurin husaina,murmushi yasaki yana shafa gemunsa wanda yafara tara yar furfura ooh hakane fa kinga na manta da auta na kusa yau da anga rigima cewa zatayi namanta ta ta baki daya tunda har namanta cewa tana gidan husaina...
Murmushi unni tayi tana furta aiko dai sarkin rigimar ka sai kai
Murmushi yakaryi yana furta toh akawo mun nan gimbiyata,murmushi tasaki jin furicinsa,har tajuya ta tsinkayi muryar sa yana furta shin kunyi waya da mai sunan Autan maza?
Chak ta tsaya domin abazata taji domin anyi shekara bai mata magaanarsaba saboda fushin da yake yi dashi,Akan kafewar sa,wanda har ita sai da abun yashafa sarki yashareta nawata daya kanta saka bakinta ya bar mganar tunda baiso wanda kuma kullum cikin bincikar yaron nata take koza'a dace tunda shima kaifi daya ne kamar mahaifinsa....
Idan bazata manta ba yau shekara da wata takwas ko ma tara za,ace da sarki Ali baiyi maganar Ammar din agabanta ba duk da abaynta yana bibiyarsa,ta email wanda kosun tura sakon baya dubawa,yana boye mata ne gudun kar ta ga kamar ya karaya shiyasa bai bata damar yimasa maganar sa agabansa ba...
Murmushi ne yasubuce mata.....
Nima anan zan dakata sai gobe in Allah yakaimu
Inkunyi comment da yawa zaku samu long page gobe ,zanbiyaku bashi ne kawai na jiya alhamis da bakusamu ba
Kunsan weekend bana typing ranar hutu ce
Like pls comment share
DAGA ALKALAMIN ✍️
💫FA'EEH BG💫
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊
Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣3
TYPING📲📲📲
Juyo wa tayi a hankali tataka inda yake zaune ta kafesa da idanunta,jin idanunta akansa yasanya sa kawar da kansa Yana mai lakace tsinin hancinsa,irin yadda Ammar yakeyi inyana cikin yanayi mai kyau
Hannayensa ta rik'o tana furta Alhamdulillah aranta,A hankali ta bud'a bakinta tafurta nayi magana dashi shekaranjiya,yana lafiya shida d'an uwansa,tambayar ta yak'ara yi har yanzu yana kanbakansa duk da yana da labarinsa,Amsa tabashi cikin d'ar d'ar "eh amma ina nan ina kokarin janyo tunaninsa izuwa garemu da fushina...
" Dan duk lokacin da mukayi waya dashi ina nuna masa fushi na inbarsa cikin zullumi nasan cewa baison damuwar d'ai daga Cikin mu,ko sharekan da yayi nasan kai kafara nuna masa taurin kai irinka naka,Allah kad'ai yasan yanayin dayake ciki ayanzu,zuciyarsa akar ye take,ni nasan waye Ammar cikin sa da bayansa,kuma nasan waye mahaifinsa...takai karshen maganar cikin jin tausayin yaron nata wasu hawaye ne suka zubo a idonta..
Murmushi sarki Ali yasaki jin kalamin ta na k'arshe..
"A hankali ya furta na janye maganar bashi sarautar,ayanzu inaso su dawo kusadamu gaba d'aya
Ayanzu haka nakusa kammalla Gina masu babbar asibitinsa domin sudawo su rik'e ta shida d'an uwansa su kula da ita....
Farinciki ne mai yawa ya bayyana A fuskar gimbiya hassana,rungume sa tayi tana zubarda hawayen farin ciki da godiya ga Allah,daya nuna mata wannnan rana data dad'e tana mafarki
Shima rungume ta yayi cikin farin cikin dayasamu kansa a cikin cigaba da maganar sa yayi " nasan cewa Ammar yana da kud'in da zai Gina wannan Asibitin,Amma na zab'i inginata masa ita dakaina saboda inason yarike ta da mahimmanci idan yatuna wannann kyautar mahaifinsa ce a garesa,kuma A duk lokacin da akayi ceton rai acikin Asibitin nasan cewa ladar zata je garemu kobama Raye muda sauran iyayenmu...
In sha Allah wannnan Asibiti zata zamo Abin Alfahari acikin wannna kasar mu tana Nigeria dama sauran kasashen...
'Murmushi da dariya ne yake fita akan fuskar gimbiya hassana a lokaci d'aya k'ara rungume sa tayi acikin jikinta,
Murmushin ne shima yake yi na farincikin ganin yalwataccen farinciki a akan fuskar matar tasa,Wanda tada d'e batayi ba, Wanda tun bayan da yafara maganar murabus,juya mulki ga Ammar d'in,Wanda alokacin anti tak'addama sosai dan yakafe yace baiso mulkin shiyasa mai bai cika kawo musu ziyara tun da yaji anfara maganar,sai dai tawaya su gaisa shida mahaifiyarshi da "yan uwansa,Dan har wayar sarki yabar kira tun lokacin da akayi rigimar yakira mahaifin nasa yafi missed call ishirin bai d'aga ba,domin alokacin yana fushi dashi mai tsanani,saboda maganar da sukayi inda yake sanar masa kar yak'ara kiransa da mahaifinsa indai bazai karb'a ba,shiyasa daya kirasa bai d'aga ba domin yasan ba maganar da yakeson ji d'aga bakin sa bace zai furta masa...shiyasa shima sai yasharesa bai k'ara Neman saba tun lokacin duk da dukkansu suna azabtuwa,Amma zuciyar d'ayace,kowa kafiya da taurin rai..
Sarki Ali yatsinci kansa sosai cikin farinciki sanin da yayi Ammar d'nsa zaiyi farinciki fiye da nasa jin wannan labari....
Wayarta tadauko dasauri bayan mik'ewarta d'aga jikinsa,muryarsa ta tsinkaya yana furta karki sanar masa sai ankammala komai har janye maganar basa mulkin,b'ata fuska tayi,tana furta "saboda me adili"? "
Murmushi yayi ganin yadda tayi kamar wata k'aramar yarinyar,yana furta inaso ne kawai yazame masa Abun kamar A MAFARKI ne murmushi tasaki,tana furta hakan yayi, Amma dai bari insanar wa sister wannan abun farincikin sai muyi farincikin tareπ
"Murmushi yayi yana furta to ki kwatse ta koh kar ta kirasu ta sanar da Al Amin,Amsawa tayi cikin k'aramar dariya ai ko haka za,ayi......
Ruwan wanka ta had'a masa a cikin k'aton bahon wankan na silver mai kyau,dake a cikin had'ad'den k'aton toilet din dak'in nata Wanda yaji kayan k'yalk'yali ta ko ina......
Bayan yashiga yayi wanka tafito masa ta da kayan da zai sanya,sannan ta fita domin Bada umurnin akawowa abinci a turakarta,A falon da na biyu kamin kashiga uwar dakin nata,Abincin suka jera cikin tsari mai kyau akan wata had'addiyar carpet din dake malale afalon,Alokacin duka ma'aikata sun gama ayyukansu na rana...
Kuyi hakuri da wannan ba nida isashen chaji ne
Shinko kuna ganin Dr.Ammar zaiyi farinciki?
Kuma zai baro k'asar India?
Shin ko akwai sanadin da yakai sa k'asar India karatu,ko ko dai Ra,ayin kansa ne?.......
Jama'a ina labarin Halee nasan wasu harsun manta da ita ......
A gobe in sha Allah zamu lek'a rayuwar Halee baiwar Muji a wani hali take sannan wace irin rayuwa take fuskanta ne ayanzu shinko Baba Asabe ta shafa mata lafiya ganin idanun Baba Asabe ko kodai tacigaba da muzguna mata......
Wacece ita?
Mekuke tunani game da rayuwar Halee?
Mu had'u a comment section dan jin hasashen kowannenku.......✍️✍️
Shin tsintacciyar ce dagaske kamar yadda Baba Asabe ke yawan furtama taa?
Shin waya bada Amanar Halee da har Baba Adee yakirata da Amana?
Sannan waya bada Amanar ?
Waih........🤭
Nima fa kaina ya kulle 🤔
Kudai kawai kucigaba da bibiyar Alkalamina✍️✍️domin Warware muku wannan labari mai cike da darussa...
Kuyi sharing kuyi comment
💫 FA'EEH BG💫
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥
*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*
*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........
*+2348069059746*
*+2348084504630*
----------------------------------------------------------------
*💫A MAFARKI NASANTA*💫
*2023 novel is the story of an innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA KO MASU MUKAMIN *MENE DASU DA HAR ALKALAMINA YA KIRA SU MANYA KASA*....
*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA*
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊
Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣4️⃣
TYPING📲📲📲
*INDIA*.....
wata kyakkyawar yarinya ce mai zubin asalin larabawa fara tass da ita ta isko sa zaune abakin ruwa,itama sai ta zauna akusa dashi,ba yanzu ne yafara ganinta ba bare ya damu Akullum tana zuwa wurinsa suyi fira wata rana ma fad'a,ta bud'a bakin ta kenan Tana furta D'an uwanah sai ga wasu mutane masu bak'ak'en kaya sunzo wurin da zuwansu suka yi kan wannan yarinya suka daddafeta tana kuka tana rok'on karsu cutar dashi,wanda shima wasu sun rirrik'esa kasancewar su majiya karfi sai yaakasa kwatar kansa agaresu bare itama yataimaketa,haka suka sanya bindiga suka harbeta yana kallo ga kukanta da yake ji har tsakiyar kansa zuciyarsa har wani b'al b'al take na tashin hankali,suna gamawa da ita duk sai suka gudu har wayenda suka rik'esa suna masu furta masa kaima zamu dawo kanka,baibi takansu ba sai yadda zai ceto ranta yakeyi, sai ma Rungume wannan yarinya da yayi wadda har yanzu baian sunantaba Amma yasaba da ita sosai har sonta yashigesa baisani ba duk da yana kokarin b'oyewavzuciyarsa hakan
Kuka yake kamar wani k'aramin yaro yana jijjigata wanda take mayafin dake kanta yazame wanda yabbayanar da lallausar doguwar sumar ta har yarufe mata rabin fuskarta saboda yadda yabarbazu,ganin ta fara nisa ne Alamar mutuwa zatayi yayi ga jininta yana ta zuba,yasanya vail dinta yad'aure mata inda suka harbetan aciki ganin jinin yak'i tsayawa ne kuma yasanya sa cikin rud'u yak'ara sanya handkerchief d'insa yana k'ara danne wurin harbin,kuka yake cigaba da yi yana girgiza kansa alamar no cikin rud'u lallausan gashin kansa duk ya hargitse,sungumar ta yayi kamar wata jaririya yana yi yana kallon kyakkwar fuskarta ganin yadda take fitar da numfashi na wahala,
Takawa yafara yi daniyar bata agajin gaggawa acikin gidan nasa sai yaga hannayenta sun saki yaraf Alamar ta mutu kenan,wata uwar k'ara yasaki yana girgizata a matuk'ar rud'e yana furta "nooo karki tafi kibarni",ganin bata motsaba yakara furtawa cikin fitar hayyaci "karki tafi ki barni" Yana kuka kamar karamin yaro ..........................
Misalin karfe 3 :00 na dare
Kwance yake akan had'adden gadonsa juye juye yakeyi akan gadon kamar wanda ke cikin wani yanayi na damuwa,ya had'a zufa duk da karfin a.c dake a bedroom din nasa da sanyin da gari yake dashi na watswar hadari Dr.Ammar kenan.......
Bayan kamar minti hud'u ya farka agigice cikin fitar hayyaci yana furta "karki ki tafi ki barni",A hankali yafara yadawo wa cikin natsuwarsa Addu'o'i yayi na neman tsari Akan mafarkin dayayi,take mafarkin da yagama yi yafara dawo masa akai kamar ayanzu abun ke faruwa duk da yasaba yin mafarkin sa da wannan yarinya,Ammana ya yau yabashi tsoro..
Tagumi Ya rafka bayan gama tunano da mafarkinsa wanda yasha banban da sauran mafarkan nasa da yarinyar,Dan shin ruwa da yaji akwar min idonsa ne yasanya shafo kyakkyawar fuskarsa da lallausan hannunsa guntun hawaye ne yaji sun gangaro suka zubo acikin idanun nasa bisa beauty face dinsa big sparkling eyes nasa sai suka kara haske da shining na ruwan hawayen da ke cikinsu curly eyelashes nasa suka k'ara cure wa waje d'aya...
Tambayar kansa yayi shin yanzu dagaske sun kashe masa ita?kuma suwane ne wad'an nan mutane da har suka yi masa barazana?,me ta musu?meye had'inta dasu,?yana jin badadi aransa zuciyarsa tayi d'aci mafarkin nasa na yau abun yatab'a shi duk da yasan mafarki ba gaskiya bane,Amma yasaba da yarinyar tana tayashi fira abakin swimming fool nasu shiyasa akodayaushe yake yawan zuwa bakin ruwan ko zai ga koda fatalwartace ....
Tambayar kansa yak'ara yi wacece ita da har ta iya kiransa da D'an uwanta? duka wayen nan tambayoyi suna tayawo ne acikin kwakwalwarsa,rasa mai basa Amsoshin tambayar sa ne yasanya shi tashi yayo alwallah,ya zura jallabiya fara mai taushi,akan short d'insa,ya shimfid'a sallaya ya raya darensa sannan yayi karatun alqur'ani mai girma acikin zazzakar muryar sa domin kuwa Dr ammar akwai kira'a yana da hizif talatin akansa ne,
Addu'o'i yayi na Allah yasa mafarkinsa ba gaskiaya bane,sannan yanemawa kansa kariya da wannan baiwar Allah da haryanzu ko sunanta baisani ba,sannan yayi Addu'a ga k'anen mahaifinsa da nora da na Allah yajik'ansu da rahama,yakuma bayyanar da takwaransa lafiya,sannann kuma yana Addu,a da fatar Allah mahaifinsa yasauko daga fushinsa,sannan yayiwa Al ummar musulmi addu,ar zama lfya, ire iren wayen nan Addu'o'in sune yayi sannnan yacigaba da kira'ar sa har yaji ankusa tada sallar asuba,fitowa nasa d'akin yayi yana k'wankwasa ma Aj kofa A lokacin shima Aj ya shirya suka d'unguma sai masallacin unguwar su....
*NIGERIA*
*BUNGUD'U ZAMFARA*
Halee ce ta mik'e zaune daga barcin da take yi tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un,khady ce itama ta mik'e zaune tana tambayarta lfya?,
A hankali ta bud'a bakin ta cikin rashin kuzari da tsoro ta furtawa khady cewa "mafarki nayi",dafa ta khady tayi tana tana furta kamar wane kalar mafarki kenan..Shiru tayi mata tana jin zuciyar ta ba dadi,sai kuma ta fara bata labarin mafarkin nata 'wasu mutane ne suka zo kasheta sai ga wani mutun mai kayan sarauta ajikinsa yazo yataimake ni sai dai banga fuskar sa ba saboda rawanin dayarufe fuskartasa,ahaka yayi iya kokarin yakare ni sai dai Allah bai nufa ba sai suka kasheni,sannann kuma kafin in mutu naji suna furtamasa saura shi shima zasu dawo kansa,dukkaninsu jikinsu yayi sanyi musamman Halee dake bada labarin tanaji kamar abun zai faru dagaske ne,kasheta d'in da maganar da suka furtama wannan bawan Allah,Khady ce cikin kwantar ma Halee da hankali ta furta karki saka damuwa Halee mafarki ba gaskiya bane,ni wai ma kinyi Addu,ar kwanciya kuwa?ta tambayeta ne duk da tasan Halee bata wasa da Ibada,tasan awasu lokuttan ma ita ke shafeta da Addu, a in bacci yadauke ta batayi ba,ta tambaye ta ne kawai domin kawar mata da tunanin da ke shirun addabar ta,d'an kallonta Halee tayi cikin damuwa tana langab'e wuyanta kyakkaywar fuskarta takara kyau,kara furta mata khady tayi ganin bata bata amsa ba,aikin shed'an ne kawai may be kinyi kuskure awurin yin Addu,ar ne musakeyin Addu'ar ta furtama Halee da ke ta Kallonta,murmushi tayi tana furta mukawana lafiya bayan gama Addu,ar tasu suka gyara kwanciyar su,Amma ita kam Halee har Asuba tayi bata runtsa ba,tunani ne barkatai ke zomata...
A hankali ta mik'e daga kan katifarsu zuwa toilet nasu ta dauro alwallah,raka'atanil fajr ta gabatar sannan tayi Asuba tagabatar da Addu'o'in ga wannan bawan Allah,wanda ko da ace tagansa afili bazata iya ganesa saboda rawanin da yayi k'awanya wa fuskarsa,sannan tayi Addu'ar Allah ya had'a ta da iyayen a Aljanna idan har sun mutu..
Inkuma suna raye Allah yabayyanar mata dasu,Byan tayi karatun alqur'ani acikin zazzak'ar muryar,dogon hijab dinta na sallah ta cire ta lunke,sannan tasanya d'an k'araminta na tsakar gida komawa tayi kan katifar su d'an runtsawa kafin gari ya waye taje yin ayyukkanta basai Baba Asabe tazo tashinta ba,saboda weekend ce babu makarantan boko sai ta islamiyya,gashi Baba Adee ya koma mafara gurin aikinsa tun satin da ya wuce.....
Bayan ta kwanta baccin yagagareta tunanin mafarkin da tayi take
Hawaye ne ke silala a idonta wanda bata san dalilin su ba,ko na tausayin wannan bawan Allah ne ko na tausayin rayuwarta ne,shesshekar kukanta ne yasanya khady bud'e idanunta tar akan Halee bayan jin shesshekar kukan nata,wadda tunda takoma barcin bata tashi ba saboda tana fashin sallah...
Leka kyakkyawar fuskar Halee tayi dan ta tabbatar indagaske ne kukan takeyi duk da tasan kuka bai wa Halee wahalar yi,sharkaf taga kyakkaywar fuskar Halee da hawaye batace mata komai ba tabarta tacigaba da shesshekar kukan ta sai da tayi mai isarta ko zuciyarta zata samu salama,domin yin kukan ma wata rahama ce ga d'an Adam...
Bayan ta tsagaita da yin kukan sai kuma bacci yakwasheta daga nan kishingiden da take......
Halee baiwar Allah
Koda ta farka har khady tayi wanka tahad'a mata musu abun da zasu karya dashi sannan ta gyara ko ina na gidan har jidan ruwa ma tagama A murtsatse.
Kallonta kawai Halee keyi wadda tafarka cikin zullumi tuna wa dayau batayi aikintaba,kafe khady tayi dake zaune akan d'an madaidaicin mirron d'akin nasu ta shiryawarta cikin doguwar riga ta atamfa, da manyan idanunta da tambayoyi barkatai aranta, khady lura da kallon datake mata ne yasanyata yin murmushi tana furta madam ki tashi kiyi wanka mu karya sai kiji komai,Murmushi itama Halee tayi har sai da fararen hak'oranta suka Bayyana tana mai mik'ewa tazuro fararen kafafun ta sannan takama hanyar