Showing 45001 words to 48000 words out of 55607 words
Ali Bayan dawowarsu da wannnan mummunan labari labari hankalinsa yak'ara tashi sosai sun sanar masa wata mota ce ta tsaya ta shiga gabansu kuma sai ta lalace,....maimaraba sarki Ali baice musu komai ba face umurtarsu dayin reverse sukama hanyar Gida ( fada).
Abunda yafaru Alokacin da Baba Adee yake tafiyar sa hankali cikin rashin kwanciyar hankali ganin hadarin da ya had'u yana so ya isa gida lafiya batare da yasha kashin ruwa ba... sai dai kuma baima lura da motar da ke bibiyarsa Abaya ba, kuma Alokacin da suka bi bayansa kad'an saboda d'an cunkosan da akasamu sai dai suna hangosa kad'an yana tafiyarsa akan babur d'in kasancewar sa bama gudu da abun hawa bane,wata katuwar mota ce jif bak'a wulik mai tinted glass tashiga gaban motar fadawan atsiyace,wanda dukkaninsu sai da suka razana yadda motar ta kutso agabansu bayan barin guraren da cunkuso yake,abun haushi kuma wanda ke cikin motar ne yak'i fitowa duk da jin k'arar horn d'in da fadawan ke ta sakar masa,d'ai daga cikin fadawan ya fito cikin yanayin masifa yana kwankwasa gilas d'in motar,A hankali glass din motar yake zugewa izuwa k'asa wata matashiyar kyakkyawar budurwa ce da taji bleaching ta bayyana a driver seat d'in wanda da alama ita kad'ai ce acikin motar yanayin ta kamar arazane Amma bai hana ta taunar cingum d'inta ba.
'Magana bafaden yayi cikin nuna bacin ransa"meyasa zaki tare muna hanya kinsan aikin da ke gaban mu ne,Alamun kuka ta fara cikin kissa tana furta masa motar ce fa ta kucce mata kuma she try to control it but takasa sannan ta daura da basa hakuri,sannann kuma yanzu taki tashi ma,Cikin d'an yanayin gamsuwa bafaden ya furta bakomai yan mata amma akara kulawa da irin gudun sa za'ayi domin mafi yawancin haka mota ta kufcewa mutun to ta iya yuyuwa mugun gudu yakeyi da ita ko kuma d'an koyo ne,kai ta d'aga masa cikin kara yimasa godiya,tana mai kara gwada tada motar da farko bata tashi ba na biyu ma sai a na uku ta tashi cikin murna tad'ago tana ma bafaden murmushi da yabata umurnin ta tada motar akaro na biyu taga ko zata tashi,Hannu tad'aga masa cikin sakin fuska sannan ta fisgi motar tana yin gaba abunta,suma fadawan da basu fahimci komai ba suka juya ganin tabbasa Baba Adee ya kubce masa basu ga ko ku'rar sa ba Yasa suka koma gurin sarki domin isarda sako...
©°•••••••••••••••••••••••••••••••°©
Gudu motar tayi kamar na barin Duniya sai gata a wani tangamemen gida,Bayan wangale mata k'aton gate d'in inda ta shiga aguje suna parker motar a inda yadace maimakon mace ta fito sai wani saurayi ne yafito a driver seat din wanda daga ninsa dai kaga d'an hau,dariya kad'ai yake tik'a yana furta ashe dai lawisa zaki iya sana'ar film wannan acting haka kinga yadda kikayi kuwa wallahi kad'an yarage dariya ta tafito fili a bayan nan da nake kwance. budurwar da naji ankira lawisa ce ta fito a extra seat itama tana ta tik'ar dariya harda rik'e ciki ashe ma itace budurwar da tashiga gaban motar fadawan sarki...
💫FA'EEH BG💫
FIRST LADY🙌
"Muryar tace take tashi tana furta kace kaso katona mana asiri jimmy sugane da gan gan muka shiga gabansu takai k'arshen maganar tana dariya,tak'ara furta jimmy Amma fa nima naso in d'an kwafsa dan namance kwata kwata inbar taunar cingum dinan tana mai kara yin wani k'aton kwai da cingum d'in,dasauri saurayin da aka kira jimmy ya furta wallahi kuwa taunar cingum d'in nan naki yaso yabadamu dan naga kamar bafaden nan yana miki wani kallo duk da nasan bai fahimci komai ba,dariya tayi tana furta yau da aikin mu baiyi kyau ba da oga ya hana muna na sharholiyar mu na kusan sati gashi yau muna da party a club takare maganar da shewa hannayen su suka bige irin na jin dadin nan.
'Jimmy ne yak'ara furta a wanchan karon makinsan anso samun matsala da sai sunga juna tun lokacin,kuma kinsan oga yace da sunyi magana shikenan komai zai lalace shiyasa ma nakara sanya su gaja su su kara saka mana ido kan wanchan tsohon,dana rasa dalilin da yasanya oga bai bada damar akashe masa shi ba na rasa dalilin da yasanya yasa ake kular masa da shiga da ficen tsohon cikin garin nan,duk da ni bazan iya wannan kasadar ba....
Firar su suka cigaba dayi suna lakkame da juna har suka shiga kofar Babban shigarsu su acikin tangamemen falon tabani damar kare musu kallo,lawisa dai irin karuwan nan ne masu lasisi dan tundaga shigar jikinta zaka gane hakan yadda kana nan kayan jikinta sukayi tieting din ta babu inda ba,a gani najikinta abun ba kyan gani,ga uban attach da zuba akanta da nail zago zago kamar wata horanya farace tass kalar farin bleaching,shima jimmy dai da ka gansa kaga d'an wanka ne kuma rikakken d'an shaye shaye bakinsa yayi bak'i alamar shan taba da sauran kayan maye tundaga yanain maganar sa zaka gane,shikam dai bak'ar fata ne irin tamu bakamar lawisa mai bleaching ba.
Su lawisa anji kunya💁 domin ba,a godewa Allah ba shine aka koma neman kyaun kanti🙅.
*gareku "yan matan mu kuji tsoron Allah kudaina fita tsirara kuna sakin siffar jikinku ga mutanen kan hanya,domin kuwa Allah yatanadar da azaba mai tsanani ga masu irin wannan shiga,Dan Allah arage yin irin kayan nan masu matse jiki,iyaye kuma hakkin ku ne ku hana ya yanku saka irin wannan sutura domin ko zunubi suka samu a danaku kason indai dasanin ku suka sanya,teloli kuma kuji tsoron Allah kudaina yiwa yayan mutane dinkin da kuka san bazaku iya barin ya yanku da k'annenku..Allah yasa mudace yakare mu daga sharrrin shaid'an dana zuciya *🙏🙏
©°•••••••••••••••••••••••••°©
Hayaak'i ne ya turnek'e falon inda nakai duba na a tsakiyar falon inda na hangi jimmy da lawisa manne da juna,Ance mannau😁Nida cingum..
suna zukar shisha hankalinsu kwance,hannu jimmy d'aya akan kirjin lawisa daya kuma rik'e da tiyo mai kyau nashisha,kar'ar wayar sa ce dake a hannun kujera yasanyasa cire hannun nasa akirjin lawisa yana duba mai kiran nasa sunan oga yabayya akan screen dinsa dasauri yayi picking call yana karawa akunnensa,A ad'ayan bangaren oganne yake furta jimmy inata kiranku shiru inji in aiki yayi kyau,cikin muryar maye maye jimmy ya furta ya oga na ka kwantar da hankalinka ai kasan ko yaushe mune da nasara indai tawanann fannin ne yakai karshen magaanar cikin sakin dariyarsu irin ta yan hau,A bangaren oga shima dariyar yayi yana furta nakasa zaama tun d'azu yanzu hankali na yakwanta domin tin lokacin da yashigo akasanar mini yakara furta kace yau akwai party kenan aikin ku na kyau zakuji alert din miliyan biyar yanzu yanzu shewa jimmy yakeyi lawisa na tayasa da duk taji komai tare da furta godiya mukeyi oga sannan suka datse kiran,dasauri lawisa ta mike cikin farinciki ta kwaso kwalaben giya dake kan dinning ta tile agabansu da kwayoyin maye,
*SAY NO TO DRUGS ABUSE🚭🚭
.*YAN UWA MUGUJI TA AMMALI DA MIYAGUN KWAYOYI DOMIN ILLANE GA RAYUWARMU*💡💡
A hankali suke bin kwalaben da'i dai suna shanyewa tare da kora wasu kwayun da ga su ga kamar ko kyan kallo baabu,take dukkaninsu suka sake rikicewa kai yad'au chaji kamar wasu mahaukata haka suka kara had'ewa da juna suka fara masha'ar su da suka saba cikin maye kamar wasu dabbobi
( wal iya zubillah )Nidai ganin haka yasa na fece kar inyi mugun gani.
Allah kashirya muna zuri'ar mu🙏
Allah yakare mu daga kusantar zina🙏
A ba'ngaren sarki Ali kuwa tunda yakoma gida hankalinsa yagaza kwanciya ko fada bai je ba sai safa da marwa yakeyi akatafaren dakinsa dake sashen unni kuma kuma ya hana kowa yashigo masa sashen duk da yasan gimbiya hassanat da Amintacciyar masarauta kadai ne sai yan yansa ke iya shigo masa kai tsaye. k'arar wayar sa ce ta tsayar dashi da zagayen da yakeyi uwar dakin nasa daukar wayar yayi dan ganin mai kiransa khadijan hajiya yagani yabayyana a screen d'in,bakowa bace wannan khadija sai autarsu dake aure a kano picking call din inda cikin d'an tashin hankali take masa bayani bayan sun gaisa...
"(Hajiyar safkare) ce gimbiya halimatu. mahaifiyarsu Suce dake wurinta ta tada hankalinta sai tadawo zamfara yau saboda mafarkin da tayi na Abdul rashid dinta yadawo gida....
Hankalinsa Ne yakara tashi sosai sai dai bai bayyanar afili ba gudun kara tashin nata hankalin,A yanzu ma tana masa bayanin ne kamar zatayi kuka domin hajiya ta sako ta gaba,lallashinta yayi tare da bata umurnin taje tabawa hajiyar waya...
tafiya kadan tayi zuwa hadadde d'akin da hajiya take bayan tayi sallama an amsa mata wayar ta makala mata a kunne A hankali yar tsohuwar dake kan sallaya tana ta jan charbi tasanya hannunta ta dafe wayar da mama dije ta daura mata sunan da yaran ke kiranta dashi kenan.
Muryar Sarki ali ce ta doke kunnenta sai ta fashe da kuka wanda dama haka yake fama da ita kullum indai zai kira ta,ta dalilin abu guda biyu muryoyin su umar da Abdulrashid take tunowa a duk lokacin da tayi taji muryarsa Takance Ali Allah kabayyanar da haske acikin duhu dan haka take kiransa..
Dama dalilin da yasa tazabi tadawo wurin mama dije da zama shine sanadin tun lokacin da aka nemi Abdul rashid aka rasa taji masarautar ta ta isheta da ma jihar har zuwa lokacin da umar yakone da iyalansa alokacin da mama dije tayi Aure a garin kano sai tanemi takoma gurin ta da zama babu yadda sarki Ali da rashin yan uwansa yadamesa zaiyi haka yabar ta ta koma chan da zama sai dai aka rufe sashen ta domin yafahimci kamar hankalinta zaifi kwanciya chan, kuma duk abunda mahaifiyarsu keso shine abun da suke so tun suna yara.
Kuka take sosai cikin jin radadin abunda baka da yadda zakayi dashi sai dai fatan Allah yayi maka mafita yakawo maka karshen komai,acewar ta muryoyinsu duka iri d'aya ne tun suna yara shine dalilin kukan nata sai aduk lokacin da suka yi magana dashi.
Ta bangaren sarki Ai shima hawayen kawai yake zubarwa na tausayin mahaifiyarsa dake cikin damuwa cikin raunin ta da yafara bayyana wanda take kokarn boyewa na shekara talatin da takwas dan ma Allah yasa hajiya macece mai tawakalli dasai hawan jini yakamata da wasu cututtukan.
Bayan tagama kukan yakara lallashinta yana furya Umma kiyi hakuri inaji ajiki na komai zai bayyana in sha Allah kuma komai yakusa zuwa karshe wanda duk suke da sa hannu akan cutar damu Allah zai tona musu asiri,kanta kadai take iya d'aga masa cikin kara jin natsuwa na saukar mata,mama dije dake zaune bakin gado itama taci kukan ta dan yau dukkaninsu abun yadawo musu kamar sabo sai kallon mahaifiyar tata takeyi cikin tausayi...
hakuri yakara bawa hajiya tabar tafiyar sai gobe za,a turk private jet yadauko ta saboda ynzu baisauko ba yana kasar paris da wakillan kasuwancinsa sukaje taro na manyan yan kasuwa da suka wakilcesa,Amma zai sauka da daddare.
©°••••••••••••••••••••••••••••••••°©
FIRST LADY🙌
A bangaren hajiya kuwa tacije tsaf bata son jirgin a mota take so tazo dole ba yadda ya iya Ya amince maata da zuwan ta mota sallama sukayi ta mikawa mama dije wayar tare da sakar mata haraara na kiran sarki Ali da tayi taso ace sai dai aganta tsididit a masarautar,wayar mama dije takarba tana mai sunkuyar da kanta cikin d'an sakin murmushi domin tasan dalilin hararar da tasamu D'akin ta fice cikin d'an rashin gaskiya..
BAyan fitar tane sai ga wani kiran na sarki Ali yana mai sanar mata zai turo mota biyu yau gobe tunda sassafe sai su taso tunda bata son tabiyo jirgin,ki shirya mata kayanta touh Hamma tace,tambayar ta yayi ina inayah?tana makaranta tabasa amsa dayake ma yau suke yin hutu shiyasa bata dawo da wuri ba,kigaishe ta ya furta cikin kulawa sallama sukayi tana furta zataji
Tare da yanke kiran...
💫Fa'eeh Bg💫
FIRST LADY🙌
kai amma fa nayi kokari yau babatun manaji duk da bani lafiya kunsamu long page.. Kusanya ni a addu'ar ku ina fama zazzabi ne.
Kuyi sharing pls.
Kuyi muna like,da comment...🙏
https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free book* 📙
EPISODE1️⃣
PAGE3️⃣4️⃣
TYPING📲📲📲
*BUG*
©°•••••••••••••••••••••••°©
A bangaren Baba Adee ya isa gida lafiya inda ya tarar da su Halee sun dawo makarantar boko har sun chanza kaya izuwa na gida saboda ba,a islamiyya yau alhamis,khady na ma Halee fira itakuma tana ta wankinta na kayan Baba Asabe dake zaune agefen barandar tanashan redion ta...
Sallamar sa ta mik'ar da Baba Asabe daga zaunen datake tana kame kame,domin ita ko karar babur dinsa bataji ba,turus yayi ganin abunda baiyi zato ba waton dai har yanzu bata bar cutar Da yarinyar nan ba ya furta acikin zuciyarsa,
su Halee ne dake masa sannu da zuwa ne suka dawo dashi dai dai daga maganar zucin da Dayakeyi Amsa musu yayi yayi cikin d'an sakin fuska sannan dakin sa bayan ya ajiye ledar da yashigo musu da ita.
'Baba Asabe da batayi tsammanin dawowar sa yanzu bane tasha jinin jikinta tana masa sannu da zuwan da yak'i Amsa mata,Baba Adee ne bayan shigar sa dakin nasa ya kwala kiran Lauratu ! Lauratu ! Amsa masa tayi jiki Amace dan tasan yau ta k'ara ballo ruwa, aiko shigar ta dakin kenan yahau ta dafad'a dan me zata bar Halee cikin wannan uwar rana rana wanki gashi tasan bata isasshiyar lafiya,take ana jikinta zai iya chanzawa sai kuma ankoma yawon ganin likita.
Shiru tamasa shikuma yacigaba da fadansa yana furta kiji tsoron Allah Lauratu yarinyar nan kinsan cewa Wata babbar Amana ce agurin mu karki bari ubangiji yakama ki da laifin cuta mata dan bata miki komai ba hasalima akoda yaushe cikin kyautata miki take.
nasha fada miki irin son da nake wa yarinyar nan batun yau ba tabbas inajin ta Araina kamar yar da na haifa tawa tajini na,domin nafi jinta araina fiye da khadija saboda maraicin ta,yanzu ko dan ni baza ki rike ta Da gaskiya ba kamar yarcikin ki.
Baba Asabe dake jin fadan nasa a cikin kunnuwan ta kamar ta saki ihu take jin ya had'a da yakeyiwa Halee dana Khady ranta ya mugun b'aci sosai sai dai ba halin nunawa, A hankali kamar zancen yashiga kunnenta ta fara basa hakuri tana furta ai Halimatun ce tace inbata zatayi ka tambaye ta kaji,ta furta hakan ne domin tasan Halee bazata tab'a karyata taba.
murmushin bakin ciki yasaki tare da girgiza kansa domin ya fahimci manufarta tanason kare kanta ne A hankali ya tunda kince ita tace kije ki karb'i wankin ki iyar da kanki ko kibawa khadija ko kira almajiran da kewankin.Amsa masa tayi da toh,sannan ta fice daga d'akin tana guna gunai kasa kasa cikin ranta afili kuwa badamar fitarwa,Dai inda Halee ke duk'e cikin rana tana wanki wanda bayan fakon idon na Baba Asabe khady ta taso ta rika mata dan kayan nada yawa,jin motsin fitowar tane daga d'akin Baba Adeen ne yasanya khady runtumawa aguje zuwa d'akinsu wanda har sai da Halee tayi d'an murmushi duk da yanayin da take ciki na kuncin zuciya,domin kuwa khady bata mance da kashedin da tamata ba na inta sanya hannunta cikin wankin sai lakad'amata na jaki.....
ooh ni fa'izatu ke kam wannan Baba Asabe anyi futinanniya,har da yar son taki ma baki ragawa to kenan koni mai kwaso rahoton baza ragawa in ankamani kai aiko bari inyi takaina inkara boye kaina.😝
"ke ta furta bayan tsayuwar ta gaban Haleen ki Aje wankin nan ki kira min su idi suzo su idasa shi takai karshen maganar tana sakar mata harara Kinyi arziki Amma ko yanzu akwai wata rana zamu hadu zaki idasa aikin ki takara furwa Halee kasa kasa,A hankali Haee tajawo dogon hijab d'in blue dake mak'ale a igiya tasanya adan karamin dake jikinta cikin dan yanayin sanyin jiki tafice gidan wanda sai da takai zagayen gidan sannan wasu hawaye masu zafi suka samu damar silalo mata tana sharar zufan data tara acikin ranar mai kyaifi da tasha,share hawayen take da gefen hijab dinta aranta tana Addu,ar Allah yabayyanar da iyayenta in suna raye da ahalinta baki d'aya,sannan tafice bayan tsai da hawayen nata.
Wasu yarane guda biyu daKe zaune achan gefen barandar masallacun dakE unguwar tasu ta kyafato da alamar su zo,biyota sukayi har cikin gidan Alokacin Baba Asabe duk ta hada musu kayan dan fita dasu idi almajiri zasuyi ,direct bohol din unguwar sukayi Domin idasa wankin bayan kwasar kayan.
Halee dakinsu ta wuce achan ta tarar da khady na assignment din da aka basu,dashigar ta d'akin ta fad'a toilet dan yin wanka wanda kuma achan cikin bayin ne ta darji kukanta kamar ranta zai fita gwanin tausayi khady tayi tayi tabud'e kofar ta lallasheta ta yi banza da ita hasalima da ta murd'a handle din arufe kofan yake ansanya sakata dole takyale ta tayi mai isarta..
Wankan ta tadauro tare da dauro alwallar la,asar bayan ta lallashi kanta
'karar bud'e kofa ne yasanya khady bud'e idanunta dake rufe wanda dama tsumayin fitowarta takeyi bare datas
Ji shiru.kyakkyawar Halee ta kalla datayi jawur da ita sosai