Showing 51001 words to 54000 words out of 55607 words

Chapter 18 - A MAFARKI NASANTA BY FA'EEH BG FIRSTLADY .txt

28 Dec 2024

3826

yi dad'i A hankali suka shek'e da dariya wadda sai da duka su Unni dake firar yaushe gamo suka juyo suna kallonsu,kai kawai Ummi ta girgiza itada hajiya suna masu fad'in Aikin ku kenan Haijya ce ta furta waisu wayen nan yaran yaushe zasu gama boko ne,Murmushi Unni tayi tana furta Hajiya boko ai ba,a gama sa sai dai kai iya yinka, kyab'e baki hajiya tayi,Ganin reaction d'inta sai Unni tayi murmushi ta furta shekarar nan ne ai Hajiya,to ai kam dasun gama makaranta zan zauna da iyayensu amusu Auren sai ahade da inaya itama,kallon hajiya kawai su Unni keyi dan sun san su nisa ko samarin basu dasu bare akai ga fira duk da basu sani ba ko duk suna da wayenda suke so,Dan D'an yau ba'a shaidar shi...


Unni ce ta furta to ai shikenan hajiya ita sumayya yar gida ma za,ayi inaga tana dariyar jin kunyar maganar tata,basu dai tambayeta dawa ba,Amma ita kam Ummi tagane tunda har Unni kejin kunyar maganar toh da mahir take nufin za,ayi yar gidan Murmushi ne yasubuce mata cikin farin ciki sai ta girgiza kai kawai. Muryar Hajiya ce ke furta itama Inaya kamar akwai nata hadin anan dan naji wadanchan ja'iran na maganar wai akalli Inayah da Abdullahi sun dace sun zata banji su ba murmushi dukkaninsu sukayi suna furta Allah yatabbatar da Alkhairi acikin wannan zur'i a tasu Ameeen nikam nace harda mu...


Muryar hajiya ce takara furta da yanzu takwarata NORAH tana duniya da harda ita sai a had'ata da bak'in likitan turai Ammar take nufi haka take cemasa Shikuma Aj bak'in likita.


A hankali takara furtawa cikin sanyin jikin da yasameta Allah yajik'anki da rahama Sadiyaa keda iyayenki,Dukkaninsu suka Amsa cikin yanayin damuwa,sannan suka cigaba da Firarsu har zuwa lokacin da sarki Ali yadawo shida Husnat bayan fitar su falon.
"Inayah ce ke harara su Sumy taana furta gulmaAjali in ba'ayiba a mutu tana mik'ewa daga zaunen datake kan dinning suma mikewar sukayi suna dariya k'asa k'asa suna mata gwalo,falon dukkaninsu sukayi suka jone dasu hajiya aka cigaba da firar yaushe gamo wanda hardasu mahir dasuka fito yanzu aka cigaba dasu.




💫 A Mafarki Nasanta💫
Daga Alkalamin Fa'eeh BG
FIRSTLADY🙌


©°•••••••••••••••••••••••••••••••••••°©


*INDIA MUMBAI*
*AMDAVAD*


Amdavad unguwace Babba tana d'ai daga cikin manyan unguwanni agarin mumbai kasancewar ta tara manyan masu muk'aman gwamnati masu fd'a aji.Babban gida ne wanda yake flat katon gate ne golden inda naga wata mota ta shara ro da gudu tana buga horn mai gadin dake gadin gate d'in ne ya wangale mata gate din inda motar batayi tsinke ako ina ba sai a parking space na gidan ko dai daita parking d'in motar ba'ayi ba wata kyakkyawar yarinya ce yar kimanin shekara goma cikin shigar jeans da t shirt masu kyau ta fito da gudu a bayan motar tana kuka,tana nufar kofar dazata sadaka da babban falon gidan dasauri itama wata yar matashiyar budurwa wadda bazata wuce 16yrs ba ta gaban motar a extra seat tana k'wala kiran Lubna! Lubna! Amma ina yarinyar tuni yarinyar ta shige cikin falon.


"Ziyadah k'yaleta kawai naji an fad'a daga bayanta inji yaron da yafito a driver seat shima dai kyakkyawan yarone fari tasa kamar dai yarinyar da aka kira da ziyadah da kuma Lubna,shima dai bazai wuce 16yrs kamar ziyadah inaga yan biyu domin kamar su daya hatta tsawon su sai dai banbancin shi ya d'an fita zama Babba saboda Banbancin jinsi.
Juyo tayi cikin yar damuwa ta furta Ziyad kasan fa halin yarinyar chan yanzu zata iya zuwa tagayawa Appah da Aunty laila karya da gaskiya yadda ranta yake bace din nan, yaron da takira Ziyad ne shima A hankali ya furta manta da ita kawai twin sis ai nasan Dukkanin su sauraren ta kawai zasu yi tunda sun san Lubna da karauniy,kuma ma ta tafi tafad'i fad'a ne kawai Appah zaiyi mukam babu ta yarda za'ayi mu yarda tabi mutumin da bata sanshi ba muma bamu sansa ba,bamu tab'a ganinsa ba sai yau.Har sun fara tafiya Ziyadah tace kaga tasa mun manta ma da icce cream namu amota juyawa tayi dasauri tabude bayan motar tad'auko wasu hadaddun shoprite bags sannan ta rufe motar.


Sallamar su ce wata matashiyar kyakkyawar mata da shekarunta baza wuce talatin da biyar ba fara tass da ita kamar balaaraba,gaidata sukayi da yaren indiyanci inda itama ta amsa musu da yaren sannaan ta musu sannu da zuwa.


Tambayar ta sukayi ina lubna bayan sun zazzauna aka tafaren falon dayasha kayan armashi komai na falon milky and white colour manyan hotuna ne makale akaton falon da fuskar wani farin dattijo wanda shima dai bazai wuce 57yrs ba a hoton shida wannana kykkyawar matar tare da ziyada da ziyad agefe da gefensu sai kuma lubna dake zaune ak'afafun tsohon dakuma wani karamin hoto na zane wanda ke d'auke da wata itama kyakkyawar yarinya yar shekara daya duk da azane ne amma duk tafi su ziyad kyau lubna ce mai d'an kama da ita ma,rik'e a hannun kyakkaywar matar nan,yarinyar na murmushi a hoton gwanin burgewa a happy family 👪wanda dukkaninsu suma murmushin sukayi,sai nasu kowa shikad'ai,sai na zanen yarinyar kuma wanda ahoton bazata wuce shekara daya ba da yan watanni ita kad'ai hotunann dan duk nata sunfi yawa wani tana rarrafe wani tana dariya wani tana rarrafe,wani kuma ta wangale d'an karamin bakinta ta had'a hannayenta Alamun tafi gwanin burgewa....


Muryar ziyad ce tadawo dani daga kallon tsaf din danake yiwa hotunan yarinyar mai saurin shiga rai,Anty laila ina Appa? Murmushi kyakkaywar matar dasuka kira Aunty laila da alama dai mahaifiyar su ce,A hankali cikin cikin murmushi ta furta yana nan yana bedroom dinsa naga lubnar dakuke tambaya tashigo tana kuka mai kuka mata?kallon juna sukayi tsakanin ziyad da ziyaada suna masu sunne kansu kasa A hankali ta matso garesu ta zauna garesu ta zauna atsakanin su tana mai sanya hannayen ta ta rike nasu cikin sanyinta ta furta kugayamun zan fahimceku kunji "ya"yana,muryar ziyad ce cikin d'an damuwa ya furta Aunty laila ina lubna take tana gurin Appah ku tana shigowa chan tayi tsinke tabasu amsa ziyad yakara furta kinga Aunty laila sai da kikace kar mufita yau mubar tafiyar nan sai gobe saturday,Amma wacchan uwar rigimar ta matsa sai da muka fita,Uhmm Aunty Laila ta tace tana kara fadar na sani kufito direct kufad'a kugayamun ziyadah,ziyad sai yan kwane kwane yakeyi,Ahankali ziyada tafara bata labarin abunda yafaru bayan fitarsu siyen icce cream din..Maimaita maganar kawai Anty laila keyi aranta har inda ziyada take furta AUnty laila yana kama da didinmu fa harda muma sai dai shi chocolate skin garesa kuma shima baki ga yadda ya rike lubna ba kamar kar yasaketa....✍️✍️


ko wane ne wannan da Lubna ta lik'e??
Su kuma wayen nan daga ina ????


Chakwakiya to bari dai mubi yarima musha kid'a adai juri zuwa rafi...✍️✍️


Next pge tommorrow


Naji sauki sosai ina godiya da Addu'o'inku wayen da suka nuna kulawa dama wayen da basu nuna ba,Allah yabar zumunci.Ameen ✍️✍️


pls Like share and comment...
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


FIRSTLADY🙌
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*


*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*


*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*


*Pen🖊️ is migthier than the sword 🗡️*


*Free Book*📙


EPISODE1️⃣
PAGE36




TYPING📲📲📲


<><><><><><><><><><><><><><><><><>


........Koda muka zo inda yake rik'e da ita Baki ga yadda yake ta kallon mu ba har muka gaisa.. tambayar kanta ta k'ara yi Shin wane ne wannan wanda yake kama da Norah d'inta da kuma lubna wanda har lubna zata iya kiranshi da BAYYA Indian lang,( yaya) har take son sai yakaita gurin DIDIN SU(DIDI indian lang YAYA MACE) da ahoto kad'ai taganta ta tab'a ganinta,Muryar kyakkyawan tsohon ce take ratsa tsakiyar falon inda yake furta meyasa kuka k'i barinta ta bishi?,D'ago manyan idanun su sukayi irin na mahaifiyarsu har ita Anty laila d'in suka kallonsa dan son tabbatar da indagaske yakeyin maganar dan sun san Appah yana yawan goyawa lubna baya..


Zama yayi A falon tare da Lubna da ke ta tsiyayar da hawayenta yayi lallashi har ya gaji tun bayan shigar ta bedroom nasa d'in .akan d'ai daga cikin manyan rugs d'in falon ya zauna kara jawota yayi jikinsa ya rungume yana shafa lallausar sumar kanta data sha gyara ba,ayi kitso ba kamar dai yadda indiyawa keyi.


Murmushi kawai Aunty Laila tayi tana mai tasowa daga kujerar da take ita dasu ziyad,hannu tasanya bayan ta zauna a gefan Lubnah dake hawaye har yanZu ta rik'o hannunta tana furta "Nima haka nace musu meyasa basu barta tabi ya" y"anta ba tana yin maganar tana kallon Lubna me matso hawaye harda na dole..."Ko zai kaita gurin didinta,Murmushi tsohon yayi afakaice,har dasu ziyad ma Aunty Laila ce tacigaba da magana,Yan zu ke Lubna baby in inbanda ke ya za,ayi ki gane didinku wadda a zane kad'ai kika santa kika tab'a ganinta tana murmushi kuma har kika iya yarda yana tare da didinku,didinku da take Nigeria,Dasauri Lubna ta bud'a baki Tana Furta Allah Aunty Laila nikam na yarda dashi tana maganar cikin sakalci dagani kasan yarinyar akwai wayau "ai shima yana kama da mutanen kasar, Aunty black ne fa shima ni shiyasa ma nak'ara lak'esa ai dan ya tabbatar mun zai kaini gunta tunda yasanta baki gansa ba fa Aunty Laila wallahi kamar sa da didin sosai yakeyi Amma shine su Aunty ziyadah suka hanani binsa da yanzu naga didi na ni na matsu naganta.... kuka Ne yakara kubce mata bayan gama furucinta na karshe.


Sukam su ziyad sunyi zugum suna kallon mahaifiyar tasu da kanwar tasu jin yadda take ta zaro zance kamar an rera shi acikin kanta,jin mahaifiyartasu tana lallashinta Lubna din ne yasanya ziyad furtawa lubna ai sai ki shirya Gobe ma sai mukai ki in Appah ya yarda ya furta hakan ne ganin signal d'in da Appah yamasa domin yasan hakan ne kawai zai kashe wutar domin kuwa ya k'agu yaji komai gun Aunty Laila domin haka kawai tun fara bayanin na Lubna wanda achan duk bata masa shi ba yaji gabansa yana mugun faduwa hankalinsa ya dugunzuma gaba d'aya..


Ai ko da jin furucin ziyad take lubna ta share guntun hawayen ta wanda har yafara kafewa cikin farin ciki ta kalli Appah kallon bani AMsa kai yad'aga mata shima cikin murmushi dukkaninsu murmushi sukayi.


Bayan samun saukowar tane suka wuce nasu dakin itada ziyada don yin fresh up shima ziyadah ya wuce nasa dake farkon nasu.


©°•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••°©


A falo kuwa Bayan wucewar nasu ne Aunty Laila takamo hannun mijinta dan son tabbatar da yanayin da yashiga A hankali ta furta ABBAN NORAH !!!!
D'ago rinannun idanuwansa yayi wayenda suka sauya tun bayan da aka ambaci nigeria yaji wani k'olon mashi yachaki zuciyarsa na bakin ciki,da kuma yana yin tausayin norah da yazame musu jiki akoda yaushe.


A hankali itama Aunty Laila ganin yanayin nasa sai taji hawaye sun taru a idonta natausayin tilon yarsu dasu kansu basu san a ina take ba,a wani hali take sai dai hope dasuke dashi kasancewarsu iyaye suna fatan ace yarsu lafiya lau take, cikin gargada muryar kuka ta k'ara furta Abban Norah lokaci yayi da zamu bayyanar da kanmu ga ahalinnmu lubna tana son ganin ahalinta haka ma su ziyad wayenda ma suka fita wayau ada mun boye musu norah amatsayin yar uwarsu da muka fahimci hakan bai da amfani munsanar musu matsayinta agaresu duk da bakomai muka sanar musu ba, ni ina ji ajiki na wannan wanda Lubna suka gani jinin mu ne.


Dasauri Appah yak'ara d'ago rinannun idanunsa cikin razanar jin furucin matar tasa,kai ta d'aga masa cikin tabbatarwa,' wanda su Lubna suka gani jininsu ne to wanene wannan kenan?nanata kalmar yayi wurin sau uku ko fiye ma daga karshe babu mai bashi amsa,A hankali Aunty Laila ta bashi labarin dasu ziyad suka bata,ganin shock din da yashiga yahasa yin wani motsi sannan takara masa da wanda Lubna tafadi yanzu wanda ta san hardashi ne yasanya kansa yin zafi damuwar ta mishi Yawa ganin lubna kiri kiri ta nuna tana son ganin yar uwarta wanda sauran maganar tata duk shirme yadauketa a farko sai yanzu da aka bude masa komai....



Kallonta yakeyi kamar yasamu camera bako kyaftawa cikin shock din da k'ara shigarsa,bayan na farkon da yashigesa tun lokacin da tafara basa labarin maganganun ne ke dawo masa akai kamar gabansa akayi komai hango yaron yakeyi a idanunsa,musamman inda tace sunce yana kama da Lubna da Norah mamaki ne yak'ara kamasa sosai yau tsawon shekara talatin da "yan kai basu tare da yan uwansu akan zaluncin wasu azzaluman mutane suna ta b'oyon kansu a wannan k'asa yau gashi rana daya Allah zai nuna nashi iko akansu dama mutanen dake kokarin b'oye su ga ahalin nasu wanda basu san dalilinsu ba nayin hakan duk da taimakon da suka musu na farko wanda kuma su shaida ne ba mutanen Ba Azzalumai bane na kirki ne.


A hankali cikin wani farin ciki da ya mamaye zuciyarsa ya furta tabbas wannan wanda suka gani bakowa ba ne face jinin......................................




Yaya Aliyu!!!!!!!!!!!! Ne


Dan tunda suka ce wanda sukagani ba fari bane tabbas daga tsatson d'an uwana ne domin shine baki acikin mu,sannan in na chan ka Ammar ne suka gani domin shine mai irin fatar yaya,dan mahir fata nace daasshi zance ko taki sai kuma jaririyar da muka bari bamu san yadda a takoma ba.


Yau yaji labarin da yamasa dadi tun bayan na norah din,Kurumm yana Cikin maganar dariya ta subuce masa hadi da murmushi harda guntun hawayen da yadade baiyi ba na hango nesar su ta matso kusa mahaifiyarsa yake so yagani ruwa ajallo yana begen yaga ahalinsu a haka ma shidayake namiji mai karfaffiyar zuciya inaga Aunty Laila wadda kullum sai tayi kuka aboye bakowa ta kwallafa rai akan son gani ba sai yar ta nora wadda bata san a ina take ba tadai san tana cikin nigeria...


Allah sarki uwa mai dad'i
Allah yasaka ma iyayen mu da aljannar fiddausi.Ameen!


Itama Aunty Laila dariyar take yi had'i da murmushi na farinciki musamman da taga yana yin mijin nata yau da yafara komawa asalin walwalarsa,ikon Allah take ta nanatawa aranta kenan Ammar d'inta ne suka gani yau sai kuma tayi murmshin ta mai kyau tana kasa boye farin cikinta itama....


A hankali ta furta " Allah sarki Norah ko a wane hali take yanzu yata girma shekara ishirin da d'ai da yan watanni ai nasan yanzu duk inda take sun mata Aure takai karshen maganar cikin d'an sanyin jiki yadda ta kwallafa rai da norah sai gashi ashe batare zasu rayu ba kaddara ta rabasu..


Muryar Appah ce ke magana yana furta"wannan bawan Allahn ya tabbatar muna da tana hannun kirki ni nayarda dashi domin ke kan ki shaida ce da taimakon Allah da taimakon sa muke rayuwa to dan haka karki saka damuwa aranki kinji oum norah da nur yakai karshen maganr da yin murmushi itama murmushin tayi cikin farin cikin datakara tsintar kanta jin yahada harda sunan Ammar wanda Unni ke kiransa dashi sai kuma ita a wasu lokuttan.


Cigaba da magana yayi "kuma da ace an mata Aure da ya sanar muna fatana kawai Allah yakara mata lafiya,ya tsare muna ita..Kuma ya bayyanar muna da Autan maza kafin mu koma nigeria ko don farin cikin hajiya yadawwama,kuma ya tonawa wayenda suke da hannu gurin cutar damu sukayi sanadiyyar rabamu da ahalin mu kasar mu,Ameen Aunty Laila ta Amsa.


Fitowar su ziyada ne da lubna sun chanja kaya izuwa na hausa Atamfa chiganvy jaa da bak'i dogayen riguna A shape sun masu kyau gwanin burgewa,da veil baki masha Allah kamar yan nigeria masu zama acikinta,shima ziyad yafito tsaff cikin shigar maroon colour yadi mai taushi harda hular zannan bukar bak'a mai daukar ido kamar wnda zaije gasar kyau.Dama duk ran friday shigar mu ta hausawa sukeyi saboda yadda iyayen nasu suka sabar musu Masha Allah Aunty Laila ta furta tana mai k'ara gyara ma lubna d'aurin ta irin na zahra buhari wanda ziyada tamata wanda Aunty Laila takoyamata.


Shaf shaf shima Appah yaje yashiryo cikin yadi maroon irin na ziyad,suka fice zuwa masallaci dan gabatar da sallar juma,a cikin jam'i har da ziyada ma Aunty Laila kad'ai aka bari tana cigaba da aikin gidan da bawani aiki bane girki ne kad'ai Sai yan gyare gyare dan ko ina tsaf kamar ba yara agidan.


FIRSTLADY🙌


*AMDAVAD*
> >>>>>>>>> >>>>>
Yau indian dishes ne agaban Amma shi yakasa tab'a koda wani gefe na abin cin dake kan dinning din,tandori chicken ne da pani puri sai kuma pakora sai tashin kamshi sukeyi yaushi ne abunda kukunsu ya girka domin shine a list na girkin yau na rana,DR AJ ne yasanya pock da knife ya yanko tandori chicken sai turu ri takeyi na kamshi bakinsa yakai yana kallon Dr.AMMAR da tambayoyi abakinsa,d'auke kansa yayi daga kallon da yake masa,yadauki pani puri d'aya yakara cusawa a bakinsa yana mai furta "narasa gane maka tunda mukaje shoprite d'in nan har yanzu baka dawo dai dai ba kamar akwai abunda yayi shocking naka agurin,tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login