Showing 15001 words to 18000 words out of 22238 words

Chapter 6 - SAUYIN YANAYI Free pages -WPS Office.txt

dad'in maganar Dad'i tayi, to amma idan ta tuna dole fa su biyu zai aura koda ya amince da auran nata, sai taji zuciyarta tayi bak'i wani irin kishi na rufe mata ido.


Tashi tayi ta shiga d'akinta tana zarya so take ta samu mafitar ruguza auran Alhaji da waccar Hafsa d'in, ta tsane ta, ita ba y'ar gidan kowa ba, amma tana son bata matsala. Ji take ko wuk'a aka bata zata iya yanka Hafsa wallahi.




"My hayat ka tsaya mana tun d'azo nake fa faman gwala maka kira fa"


Tsayawa Alhaji yayi yana bin Aysha da kallo, shi harga Allah bata birgesa. Yanzu ma abunda ya kawosa gida yazo wajan Dad'i ne shine take masa maganar dole ya had'a auran Aysha ya auri mata biyu, idan ba haka ba kuma bata yafe masa ba. Sun kasance Dad'i ita ce Kakarsu kuma ita ce kad'ai ta rage masu a duniya daga shi har Ayshar, itama Iyayenta sun dad'e da rasuwa, a wajan Dad'i take zaune, kuma tun tana k'arama take dak'on son Bin Muhammad.


Ita kam Aysha dake kallonsa kamar zata cinyesa. Tun shigowarsa taji, ta sakko da gudu domin ganinsa kawai da jin muryarsa yana sata farin ciki.


Ganin ta tsaya ita bata ce masa komai ba yasa shi cewa "kefa nake jira ina inda zani, kuma waje ne mai mahimmanci a rayuwata"


Bakinta bata san sadda ya furta cewa "wajan wa zaka daya fi nan mahimmanci?"


"Hmm wajan My Hafsa mana"
Ya fad'i hakan yana shigewa Motarsa ya data yabar mata saurin k'urar motar a fuskarta.


Rufe idonta tayi tana jin wani tuk'uk'un bak'in ciki na tokare mata wuya.


Fad'awa tayi kan gadonta bayan ta shigo d'akinta da gudu. Tana fashewa da kuka.can Kuma saita tsayar da kukan tana tuno k'awarta kuma Aminiyata Asiya.


Da sauri tajawo wayarta ta dannama mata kira.

"K'awata yau kune da kanku kuke nemanmu?"


Bayan Asiya ta d'auki wayar ta ce haka.


"Kinga akwai matsala wallahi ina cikin damuwa ne"


"Subhanallahi mike faruwa ne haka?"


"Kinga maganar bata waya bace kawai kizo ina son ganinki"
Daga haka ta katse kiran.


Zuwa can da yamma Asiya tazo gidan. Zaune suke a d'akin Aysha. Asiya ta kama hannun Aysha bayan ta gama jin duk abunda ke damun k'awar tata.


Ta nisa ta ce "tabbas idan baki d'au mataki ba, haka za'ayi auran, ki koma y'ar kallo, ki koma yi masu shara da wanke-wanke"


A zabure Aysha ke kallon Asiya, cikin b'acin rai Aysha ta ce "ai wallahi hakanma bazai tab'a yiwuba ba, kin san wacece ni ai?"


"Na sani duk da haka saifa kin mik'e tsaye kin kwato ma kanki y'anci"


"Ban gane miye kike son cewa ba Asiya"


"Kawo kunnanki kaji"


Wani abu Asiya ta rad'a ma Aysha, wata dariya suka saki a tare had'e da tafa hannu. Aysha ta tashi tsaye cike da murna ta ce "kin tabbata idan muka je wajan Malamin nan zai min aiki Alhaji yaso ni kamar Hafsa?".


"Harma yafi na Hafsa, ai aiki yake kamar yankan wuk'a wallahi"




Duk wata hidimar biki cike da kuzari Aysha da k'awarta Asiya suke yinsa.
Hatta Dad'i ganinta saki ranta itama ta d'auka ko Alhaji ne ya fara nuna ma jikar tata kulawa.


Bayan an d'aura aure har yanzu basu je wajan Malamin ba, Asiya ta ce mata ta bari sai bayan bikin tukunna da kanta zataje mata kuma za'ayi aiki yadda ya dace.


Bayan biki da wata d'aya, Dad'i ta rasu, abunda ya dakatar da Aysha kenan zuwa wajan Malaminsu danta ce da kanta zataje Asiyar ta raka ta. Domin kuwa har yanzu babu abunda yake shiga tsakaninsu da Alhaji sai kallo kawai, amma a wajan Hafsat kuwa soyayya take ganin yana nuna mata sosai.


Aysha tasha kukan rashin Dad'i dan har saida aka kwantar da ita asibiti. Amma duk da haka mutuwar Dad'i bata sa Aysha saduda da duniya ba, domin tana samun sauk'i suka wuce wajan Malamin da Asiya ke fad'a mata.


Bayan Malamin ya koro masu jabin cewa Hafsa na d'auke da cikin Alhaji na tsawon sati uku. Yasa Aysha rud'ewa zuciyarta a bushe ta ce "Mlm babu yadda za'ai cikin ya zube?"


"Akwai yadda za'ai mana. Ga wannan maganin ki tabbatar kinsa mata shi a cikin abinci, sana wannan k'ullin kuma ki tabbatar Alhaji ya tsallaka sa, to komai sai abunda kika ce shine za'ai a gidan".




Sosai Aysha taji dad'in hakan, ta zube masa kud'i masu yawa wadda bata sanma iya adadin nawa taba Malamin ba.


Kamar yadda Mlm ya ce haka komai ta aiwatar dashi yadda ya dace.


Kuma an samu nasara Hafsa taci abincin, Alhaji zaije kiran Aysha ganin yadda Hafsa ke juye-juye tana rik'e da cikinta, ga jini sai zuba yake mata duk ya b'ata mata jiki. Suna zaune daga cin abinci yaga ta fara haka.

A rud'e ya nufi sama inda d'akin Aysha yake, a nan wajan ya tsallaka maganin, dama kuma tasan zaiyi wuya baizo sanar da ita ba, kawai saita yanke shawarar sasa a hanyar d'akinta.


Ai ko yana tsallaka maganin yaji kansa ya juya kamar wani abu ya shige masa tunani.


Yadda taga Alhaji ke mata magana cike da kulawa da soyayya tasan aikinta yayi, hak'arta ta cimma ruwa.


Itama cike da makirci ta sakko k'asa hannunta cikin na Alhaji.
D'aukar Hafsa sukai aka nufi Asibiti da ita.


A sadda Doctor ke sanar da Alhaji cewa cike ne da Hafsa na tsawon sati uku, cikin yaso zubewa ne, kuma kamar wani abu tasha shine ya kawo mata hakan, amma Allah ya tak'aita abun, domin cikin na nan bai fita ba.


A lokacin Aysha ji tayi kamar ta shak'e Doctor d'in nan. Tun lokacin duk wani makirci ta rink'a had'ama Hafsa. Hafsa tayi bak'i ta lalace ga cikin jikinta na matuk'ar bata wahala, haka ta d'aure ta cije take zaune a gidan. Yanzu ita da Alhaji sai dai kallo domin ko d'akin kwananta Aysha sai taga dama zata ce yaje ya kwana.


Babu irin abunda Aysha bata yi ba, domin dai cikin jikin Hafsa ya fita amma ina Allah yayi al'k'awarin sai yazo duniya.


A ranar da zata haihu a ranar Aysha ta koma wajan bokanta, a ranar aka had'a wani mugun asiri data dawo gida a bayan gidan ta binnesa. Asiri kuma shine wasu bak'ak'e aljanu aka turama Hafsa su shafi jariran data haifa, ita kuma su kasheta.


A dai-dai lokacin data binne asirin a dai-dai lokacin kuma nak'udar Hafsa ta tashi gadan-gadan, gashi ita d'aya ce a d'aki sai wahala take tun d'azo.


Koda Aysha ta shigo gidan tana iya jiyo ihun Hafsa da neman taimako da take, saima ta samu waje akan kujerun parlo tayi zamanta.


Hafsa tasha bak'ar wahala ta shafe awanni kamin Allah yasa ta haifo d'anta namiji, sai dai tana haihuwa bata ga abunda ma ta haifan ba, taji kamar an shake mata wuya tana shure-shure har rai yayi halinsa.


Sai da Aysha taji kukan jariri ya karad'e gaba d'aya gidan, ta daina jin matsin Hafsa, hakan yasa da gudu tayi cikin d'akin da Hafsa take.


Wani mugun farin ciki ne ya lullub'e Aysha ganinfa Hafsa an tafi, tafiyar da babu dawowa.


Cike da makirci, ta kira Alhaji tana wani irin kuka tana sanar dashi Hafsa ta haihu amma ita Allah yayi mata rasuwa.


Shima hankali a tashe duk da dama an kauda hankalinsa daga gareta kwata-kwata, amma mutuwar ta shigesa dan har kuka yayi a sadda yaga za'a fita da ita.




Tun lokacin ya dawo da soyayyar da yake ma Hafsa akan abunda ta haifa. Tun lokacin da Hafsa ta haihu Aysha taga namiji ne, nanma ji tayi kamar ta shak'e jaririn, amma wata zuciyar na gargad'inta da hakan, tunda ta tuna shima fa ta gama da rayuwarsa, zai taso ne kamar mahaukaci, ba mai cikakkar lafiya zai taso ba.




Aysha taso ta kauda hankalin Alhaji daga Salman tun yana k'arami amma hakan ya gagara. Dole tasa ta yada makaman yak'inta, ta rink'a jawo yaron a jiki kamar wacce take sonsa Dan Allah. Shi kuma Alhaji ganin yadda take basa kulawa yasa ya k'ara jin sonta a ransa. Dan har idan zatai wani abu ko tana son amsar kud'i a hannun Alhajin sai kiga tana k'ara ririta Salman kamar ta maida sa ciki.
Tunda Salman ya tashi ya bud'e ido ya gansa tare da Momy Aysha duk zatonsa ita ce ta haifesa. Sai dai ita da kanta ta fad'a masa cewa Mamarsa ta rasu wajan haihuwarsa. Domin Allah ya sani ta tsani yaron kamar yadda ta tsani uwarsa. Koda rab'arta yayi ji take kamar ta shak'e sa ya mutu haka nan take danne zuciyarta tana nuna masa soyayyar k'arya.


Tun yana shekara goma, abunda Momy ta masa tun yana ciki ya fara tashi. Haka kawai sai aga yaro ya fad'i kamar mai farfad'iya, yayita fashe-fashen abubuwa, duk da k'ananun shekarunsa idan mutane sunzo rik'esa duk sai ya watsar dasu, ko kuma ya kama mutum saiya ji masa ciwo ko ya sumar da mutum.


Alhaji ya shiga tashin hankali, ba inda baije ba domin neman magani har k'asar waje ansha fitar da Salman, amma abun yak'i sakinsa. Momy kuwa ita tak'i bari aje wajan Malaman Addini bare har a gano miye yake damun Salman d'in na ainafi.




Sai dai duk da abunda tasa rayuwarsa a ciki hakan baisa Allah yak'i basa sa'ar rayuwa ba. Tunda ya fara karatu bai tab'a samun matsala ba, gashi da farin jinin jama'a. Kota ina ana ji dashi, komai zai tab'a sai Allah yasa masa albarka a ciki. School d'in dayayi da kansu suka d'au nauyin karatunsa aka turasa k'asar waje ya ci gaba da karatunsa.


Yana gama karatunsa, bai jira wani aikin Gwamnati ba, kona Daddynsa, ya kama sana'ar saida motoci da gidaje, da kud'in da aka basa kyautar su a school d'in daya gama, yaci kyaututuka kala-kala iri-iri daban-daban. Hatta k'asar daya gama karatu sunso d'aukarsa aiki amma ya ce shi so yake ya tsaya da k'afafunsa.


Cikin ikon Allah nanma Allah yasa masa albarka dandanan ya bud'e kanfanin k'era motoci. Companynsa kusan biyar a k'asar waje, harda na k'era Abayoyi irin na K'asar Dubai, da atanfofi da dai sauran su.


Momy abunda ya k'ara sa mata tsanar yaron kenan, bata da wani buri yanzu saina ganin bayansa....




Sauk'e lumfashi Momy tayi tana zama akan gadonta bayan ta gama tuno gaba d'aya rayuwar data wuce baya....


*SAUYIN YANAYI*






Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*








*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*






*EPISODE* 8






*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*




"Wallahi Abbansu Maryam k'iri-k'iri yaron nan Ismail, ya nemi min rashin kunya, saboda uwarsa ta d'aure masa gindin yayi ma mutane rashin kunyar"


Mama ta idasa maganar tana hararar Hajiya dake gefe, sai Ismail dake gaban Abba. Dawowar Abba kenan gidan, Mama ta kai k'arar Ismail.


Abba da b'acin rai ya aika a kira masa Ismail, shine Hajiya tajawo hannunsa suka shigo a tare d'akin Abban.


Abba ya kalli Hajiya yana cewa "wato na ce yazo shi d'aya shine ke mai d'a, zaki kwaso k'afa ki biyosa ko?"


"Amma Mlm abunda kake fa bai dace ba ko kad'an"


Cewar Hajiya tana kallon Abba, dake masifa an tab'a masa mata.


Rik'e baki yayi yana kallon Hajiya, sai kuma ya kama kunnan Ismail ya murd'e. K'ara Ismail ya saki yana ba Abban hakuri.
Abba ya k'ara murd'e kunan Ismail yana cewa "dan k'aniyarka, miye ya had'aka da ita?"


Ismail cikin muryar kuka ya ce "wallahi Abba, ita ce ta ce naje na sayo mata Sigari, shine fa dana dawo take cewa ita ba itace ta ce na sayo mata ba"


Dafe k'irji Mama tayi ai kawai saita fashe da kuka tana nuna Ismail tana cewa "kaji irinta ko?, yanzu haka ita ta jashi d'aki saida ta shirya masa abunda zai fad'a, idan an kawo k'ararsa wajanka dama. Wallahi wannan maganar fad'a masa ita akai, wannan d'an yaron dai bazai iya shirya magana har haka ba. Yanzu tsakani da Allah Abbansu Maryam na tab'a sha maka Sigari a gida fisbilillahi?".


Kamin ma ta rufe baki Abba ya kaima Ismail wani mangari a k'eyarsa. Yana cewa "bata hakuri dan ubanka, kuma ka tashi kabar wajan nan, marar kunya kawai"


Zuciyarsa Ismail na zafi ya duk'a har k'asa yaba Mama hakuri, ciki-ciki ta amsa tana binsa da mugun kallo.


Duk abunda ke faruwa Hajiya na kallo bata sa baki ba, zuciyarta na zafi, ta taushi zuciyarta ne kawai dan a zauna lafiya.


Ismail na fita Mama ta kalli Abba ta ce "yawwa dama ina son magana da kaine, akwai maganar da nake so mu tattaunawa mai mahimmanci"


Abba ya kalli Hajiya da bata da niyar tashi ya ce "maganar tamu kad'ai ce ko kuwa?, sai an bamu waje?".


Murmushin jin dad'i Mama tayi ganin yadda Abba ke gayama Hajiya magana.
Cike da makirci ta ce "a'a kowaye zan iya fad'a a gabansa, tunda mutum baida wuta baida Aljanna bare ya saka ni".


Gyara zama Abba yayi yana bata hankalinsa, domin indai maganar samu ce ta kud'i to Abba yana gaba-gaba a wajan.


Mama ta gyara zama itama tana cewa "yawwa abun arzik'i ne yazo har gida. Khadija dai ta samu miji, kuma da alama mai kud'i ne, baya ma so bikin ya d'auki lokaci da yawa, tunda kaga ta kusa gama karatun ta, yana son shigowa gida ne asan dashi, idan yaso akasa ranar auran sai asa dai-dai lokacin da zata gama karatunta. Koya kake gani Mlm?"


Cike da farin ciki Abba ya washe baki yana cewa "kai Masha Allahu, haka ake so, kinga ita ta tsaya tayi karatunta kuma ga miji ta samo dai-dai ita, ba irin su O'a ba"


Murmushin Hajiya dake gefe ta saki, batayi niyar tsoma masu baki ba, amma jin abunda Abban ke cewa ne, yasa Hajiya bazata iya hakura ba ta ce "karka manta Mlm dukansu fa Y'ay'anka ne, kuma komai lokaci ne dashi. Itama baccin kak'i ai da yanzu Salma ta dad'e da yin auranta"


Girar Abba ce ta had'e waje d'aya, kamin ya dubi Hajiya yana cewa "Hajiya kima daina wannan maganar, domin kuwa Salma gata can ma tayi karatu, ke wai wani ya hanaki yin karatun ne?, ba da iliminki na ganki ba, miye karatun bokon baiyi miki ba, hatta aikin hajji da kika je, ba ta dalilin karatun bane?".


Ganin maganar naso tayi tsayi yasa Hajiya tashi domin tasan ko kwana zatai tana gaya masa gaskiya tofa ba yarda zaiyi ba.


Tashi tayi tana cewa "Allah ya baka hakuri, amma gaskiya ka rink'a kamanta adalci a cikin y'ay'anka"


Tana idasa fad'ar haka ta fice daga d'akin.


Wani tsaki Mama taja tana cewa a zuciyarta "kinyi ki gama Hajiya, amma Salma ba ita ba auran wani wadda zata huta a rayuwa, sai nasa ta auri wadda zai ida nakasa mata rayuwa, wannan al'k'awari ne wadda na d'aukarma kaina"


Abba ne ya katse mata tunani, suka ci gaba da maganar Khadija da Jafar yadda komai zai kasance.




Washe da safe. Salma ce ta fito daga d'akinsu tana k'ok'arin shiga babban kitchen d'in gidan. Fitowarta ta hangi su Maryam da Mama dake zaune k'ofar nasu d'akin.


Fitowarta taji tsakin da sukai mata. Mama ce ta kunna redio, kawai taji suna karanto wani littafi waishe KADDARA CE, abunda ya k'ara hargitsa ma Mama da Maryam kwakwalwa shine yadda sukaji wacce ta rubuta book d'in.

Salma duk da taji abunda yasa su firgita sai tayi shigewarta kitchen d'in ta nuna kamar bata ji ba. Duk da tasan book d'inta ne, to amma cikin gidan nasu babu wadda yasan tana rubuta book's daga ita sai y'an d'akinsu. Ita kanta bata san gidan redio na karanta book nata ba, amma taji dad'in haka.


A rud'e Maryam ta ce "wai baku ji wane suna naji ana kira bane?"


Dariyar rainin wayo Khadija ta saki tana cewa "naji mana, zai wuce wata ce can sabuwar marubuciya akai, dan naji wani book ma abokiyar hira ta karanta na marubuciyar yadda kaddara taso, duk ita tayi shi".


Maryam ta ce "to amma ya akai sunan marubuciyar yake kama dana wancar Salman"


Mama ta tab'e baki ta ce "ke kuwa Maryam da abun dariya kike, idan banda abunki ina Salma ina iya rubuta wani littafi, yarinyar da bata san komai ba, sai jakanci kwakwalwata babu komai ciki sai dusa"


Dariya suka saki tare Maryam da Khadija har suna tab'awa. Dai-dai lokacin da Salma ta fito daga kitchen d'in.


Duk taji abunda suke cewa, sai kawai ta girgiza kanta tana murmushi ta shige d'aki.


Tana shigewa Mama tabi bayanta da harara tana cewa "yo yama za'ai hakan ta kasance, ai da nayi kukan bak'in ciki kuwa, ai insha Allah haka zaki k'are a gantale Salma keda uwarki"


Bayan kwana biyu Mama na zaune kan gadonta taji Maryam ta tab'a ta, ba shiri ta tashi zaune tana kallonta.


Ganin kamar gulma ta kawo mata yasa ta tashi da sauri tana cewa "ke lafiya na ganki haka?, kamar wacce aka biyo tayi sata"


Maryam tama kasa zama, ta had'e hannayenta waje d'aya, sai kuma ta kama baki cike da tsananin mamakin abunda kunnuwanta suka jiyo mata a k'ofar d'akinsu Salma, sakin bakin tayi ta dafe kanta. Mama ganin cewa kamar fa Maryam d'in a kid'ime take yasa ta jawota ta zaunar da ita a kusa da ita.


A hankali Mama ta waiga k'ofar d'aki wai ko wani abu ne ya biyo Maryam d'in, daya sa ta zama Haka.


Ganin babu alamar komai yasa Mama cewa "wai minene naga fuskarki ta cika da mamaki?"


Sauk'e wani goran lumfashi Maryam tayi kamin ta ce "yo ba dole Mama ki ganni a haka ba, ashe duk littatafan da muke ji a redio da You tub channel, wadda abokiyar hira take Karantawa, ashe duk na Salma ne, mu duk d'aukarmu ai suna ne kawai yazo d'aya ba ita ba ce, ashe kuwa Salmar gidanmu ce ba wata ba"


A zabure Mama ta mik'e tana cewa "keeee Maryam bana son maganar banza kinji"


"Na rantse miki Mama ita ce"


"Ke ta gidan Ubanwa kika sani to?"


"Mama ki natsu dan Allah kaji"


Jawota Maryam tayi ta zaunar da ita tana cewa "Mama nazo shiga ban d'aki ne, kawai kamar ance na matsa k'ofar d'akin su Salma, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login