Showing 6001 words to 9000 words out of 22238 words
Chapter 3 - SAUYIN YANAYI Free pages -WPS Office.txt
Ahmad na cewa "insha Allah zamu samu ganinsa ai rana batai ba sosai duka sha d'aya yanzu".
Har suka fita daga gidan mutanan tsakar gidan ba wacce ta d'aga kai ta ce dasu sannu ko ya mai jiki, duk da sun san ciwon Salman ne ya tashi.
Suna tafiya Hajara ta saki wani murmushin mugunta tana cewa "aikin banza kawai, ai ko wannan ciwon ya hana d'iyarki auruwa wallahi, ai indai ina raye Hajiya baki ba jin dad'i ko walwala a cikin gidan nan".
Khadija data fito daga d'aki ta ce "hmm Mama ai kina min dai-dai abunda kike sa Abba yana masu. D'azo fa naje amso kud'in school, ta shigo d'akin karki so ganin yadda ta nuna bak'in cikinta da kud'in da Abba ya bani"
"Tayi ta gama, kad'an ma ta gani. Kuma d'iyarta ita da karatu sai dai idan anayi a lahira zatayi. Amma ni ce nan nasa Mlm ya toshema shegiya kwakwalwa"
Maryam ta zaro ido dake kusa da uwarta, ta dafa Hajara ta ce "kee Mama dama kice silar maida Salma marar k'ok'ari?"
Harara Mama ta banka ma Maryam ta ce "kee kiyaye ni, nasan halinki da shegen surutun tsiya, na sake naji maganar nan a bakin wani to wallahi sai nayi miki abunda baki tunani"
Zaro ido Maryam tayi tana sakin dariya kamin ta ce "haba Mama ya za'ai na tona miki asiri ai kema kin san bazai tab'a yiwuba, kawai abunne yaban mamaki"
Khadija ta kalli Mama ta ce "amma gaskiya Mama kin nakasata da yawa, kuma kin kyauta mana. Da yanzu shegiyar ta fimu komai wallahi dan daga gani ba k'aramar mai basirar karatu za'ai ba can"
Mama ta saki dariya ta ce "yo ai dama sai da Mlm ya ce min haka, ni ko na ce a dod'e kwakwalwata, ta daina gane komai, yo ina zaune zan bari tazo ta kere yarana ku biyu da nake dasu duk duniya ai bazan tab'a bari ba. Ita d'aya da kuke gani zata iya zama wani abu wadda ku kuna ku biyu ko kwatarta baza ku kamo ba, ni kuma ina ji ina gani bazan tab'a bari hakan ta faru ba".
Wani yaro ne yayi sallama yasa su duka suka bisa da kallo jin abunda yaron ya ce ne yasa Mama tashi tana cewa "kai mi naji kace?"
Yaro ya sake cewa "ance wai ana sallama da Salma wani mai mota ne yana waje"
Ai da sauri Mama ta ce ma yaron yaje gata nan zuwa.
Khadija da bakinta ke kyarma wajan magana ta ce "kan uba can. Mai mota ne yazo neman wancan yarinyar mai d'auke da cutar Sikila?"
Tashi Maryam tayi da sauri tana cewa "Mama kinyi shuru?",
"Kin san mi za'ai?, ke Khadija zan baki wani turare ki fesa sa kamin kije wajan wadda yazo neman Salma. Idan kika je ki tabbatar ya shak'i turaran. Sana ki b'ata Salma a wajansa, na tabbata zai dawo wajanki "
Maryam ta tab'e baki cike da jin haushin Khadija ta ce "haba Mama wai komai za'ai sai dai ace Khadija ni kuma fa?".
"Ke kinga ki kwantar da hankalinki kema naki na nan zuwa"
Duk da haka Maryam sai kunbure-kunbure take ta koma ta zauna kamar zata fashe da kuka, taso ace ita ce zataje taga waye ba Khadija ba. Dama ita ba wani samarin arzik'i ne da ita ba, duk na banza ne masu zuwa a soshale, a school d'insu.
Kamin a rufe minti biyar saiga Khadija an fito ance uban gayu ana taku dai-dai. Harara Maryam tabi bayan Khadija dashi, ji take kamar ta fisgota ta dawo da ita.
Khady na fita ta iske matashin saurayi a k'ofar gidansu. Jingine jikin wata mota sai kyalli take.
Ganin wata sab'anin Salma yasa ya d'anbi Khady da kallon mamaki. Tana idasa k'arasowa inda yake yaji wani k'amshin turare kamar na bori yayi masa sallama a k'ofofin hancinsa. Kansa yaji ya fara juya masa, da k'arfe ya runtse idonsa. Sak'on d'aya biyu.......
Ya bud'e su akan Khady sai ya samu kansa da sakar mata murmushi. Wani irin dad'i Khady taji ganin tarkonsu ya kama.
Sallama tamai cike da iyayi da jan hankali. Saurayin a zuciyarsa yake cewa "kai wannan fa tayi Alaji ko ita na samu ai nayi sa'a"
Bayan sun gaisa Khady cike da makirci ta ce "hmm naji ance wai Salma kake nema ko?"
"Wacce Salma kuma?, ai ni ke na ce a kira ba wai wata Salma ba",
Dariya Khady ta saki tana sake cewa "uhum kad'ai fad'i gaskiya, ai na d'auka Salmar kake son gani na ce baka da labarin bata da tarbiyya ko kad'an duk gidanmu itace zakka, gata d'auke da ciwon Sikila ba wadda ya tab'a zuwa da sunan yana sonta".
Tab'e baki yayi kamin ya ce "mubar maganar wata Salma, baga ki yanzu ba kin maye gurbin duk wata mace a waje na yanzu. Ni sunana Jafar kefa?"
"Ni kuma Khadija"
"Wow so nice name"
Sun dad'e suna fira. Zasuyi sallama ya bata wata leda daya ciko da kayan ciye-ciye da dai sauran su. Hannun Khadija har kyarma yake wajan amsa tana rafka masa godiya.
Sai da tasa masa number wayarta shima ya amshi tata. Kamin ya shige cikin motar ya tayar yayi gaba.
Juyowar da zatai ta koma cikin gida ta hangi Ahmad dayayi parking motar Abba yazo d'aukar katin Salma na asibiti da suka manta a gida. Ya baro su Salma na jiran ganin likita.
K'arasowa yayi inda Khadija take yana cewa "keee dan Ubanki ba Abba ya hanaku zance ba?, har sai kun gama karatu koba haka ya ce ba?".
Yadda ya daka mata tsawa yasa Khadija zabura tayi cikin gida da gudu.
Bin bayanta yayi shima yana shiga cikin gidan.
Ganin yadda Khadija ta shigo a hargitse yasa Mama tashi ta jawota tana tabbayar "ke lafiya?"
Wani kukan makirci Khadija ta saki tana nuna k'ofar gida tana cewa "Mama ba Ahmed bane daga ya ganni ina zance shine yazo a gaban saurayina ya mare ni, wai ba Abba ya hanamu zance ba"
Wata uwar ashar Mama ta dark'ara, dai-dai shigowar Ahmed cikin gidan kuma a kunnansa duk yaji abunda Khadija ta fad'a.
Nunasa Mama tayi da yatsa tana cewa "kaiiii Ahmad ka fita ido na rufe bana son hassada da bak'in ciki, yo idan ba bak'in ciki kake data samu mai abun hannu ba uban mi kake mata?, saboda ba'a ce K'anwarka bace wacce kuke uwa d'aya, y'an ubanci zaka fara nunama Y'ay'ana. Shine zaka disgata a gaban saurayi saboda baka da kunya?".
"Amma Mama kin sanfa Abba ya ce baya son ganinsu da samari tun.......... "Kai dakata na ce, ina ruwanka da rayuwar y'ay'ana K'anwarka ce wacce kuke uwa d'aya ita ce kake da ikon mata haka, amma banda su Khadija babu ruwanka dasu nama gaya maka. Idan kunne yaji gangar jiki ya tsira"
Zai sake magana saiga Abba ya shigo gidan. Ai ganin haka yasa Khadija k'ara b'are baki tana sakin kuka.
Hajara ma saita kama matse hawaye tana kama bakin zaninta tana fyace majina, alamar tasha kuka ta gaji.
Ahmad yana tsaye yana kallon ikon Allah, had'e da kallon makirci tsantsarsa wajan uwa da y'ay'anta.
Abba a d'an rud'e yake binsu da kallo kamin ya ce "mike faruwa ne?"
Khadija saita k'ara b'are baki tana cewa "yo Abba ba Ahmed bane daga na fita waje wani d'an ajinmu ya kawo min wani book nawa dana ara masa na makaranta, shine kawai ya kamani da duka wai zance nake, wai ka hanamu zance, kuma ni ba zance nake ba d'an ajinmu ne fa".
Ta k'are maganar tana matse hawaye.
Hajara ta amshe da cewa "kuma dan rashin kunya ina masa maganar miye tayi masa shine kawai ya kaima Khadija mari nima yana neman kai min marin, tunda dama ba kunya ce dashi ba".
Zaro ido Ahmad yayi kawai ya kama girgiza ma Abba kai, dake mai wani kallo na b'acin rai. Kai dama haka mata suke wasu?, haka suka iya kulla makirci, shi yanzu ko rantsuwa nawa zaiyi ma Abba to wallahi yasan bai isa ya iya kare kansa ba..... Tunaninsa ne ya katse jin saukar mari har biyu akan kumatunsa. Zaro ido yayi da mugun sauri ya dafe kumatun nasa. Yana kallon Abba daya sharara masa mari har biyu.
Cike da masifa Abba ke nuna Ahmed da yatsa yana cewa "wato uwarka ce ta turoka kayi ma mutane rashin kunya ko?, saboda kawai naki bata kud'in maganin Salma yadda zasu isa, shine kai kazo rasa kunya b'eran tanka, ka rama mata ko?. Ai ba'a kan Hajara da yaranta zaka sauk'e fushinka ba, gani ni ya kamata ka duka basu ba".
"A'a wallahi Abba ni Hajiya bata sanar dani komai ba, Allah ya baka hakuri".
"Idan nak'i hakurin fa?, bani key d'in motata"
"Abba suna asibiti fa suna jirana, kati nazo d'auka fa"
"Babu ruwa da inda kaje ka ajiye su, ka taro napep ku dawo kaja masu, bani key d'in motata kawai na ce"
Idon Ahmed jawur jijiyoyin kansa sun tashi tsabar b'acin rai, kawai ya mik'a ma Abba key d'in motar. Abba yasa hannu ya fisgesa da k'arfi ya juya ya fice daga gidan.
Yana fita Ahmed yabi su Khadija da kallo yadda suke sakin murmushin jin dad'i. Kwafa kawai yayi yana shigewa b'angaransu. Yana jin yadda Hajara ke sakin shewa da dariya tare dasu Maryam.........
*SAUYIN YANAYI*
Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*
*EPISODE* 4
*Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja Nigeria*
A hankali yake sakkowa daga matakalar jirgi. Gilas ne manne a idonsa, wata irin iska ya shik'a ta k'asarsa Nigeria, wata irin nutsuwa na saukar masa a zuciya.
PA dake janye da akwatunan su na kaya. Wasu jifga-jifga motoci ne suka zo d'aukar Salman sun kai su biyar a jere.
Gaba d'aya Airport d'in kallo ne ya dawo garesa. Mata y'an gayu wa'inda suke ji da kyau da kud'i ko wacce na binsa da kallo kamar idonsu zasu fad'u, ko wacce mace dake wajan ji take inama ita ce matar bawan Allahn nan.
Yazo giftawa ya shiga motarsa PA daya bud'e masa gidan baya na tsaye yana jiran k'arasowarsa. Yaji wasu y'an mata na rad'a a hankali suna cewa "kaii K'awata kinga wani gaye?, wow wayyo Allah na, wannan ka same sa gidan duniya ai ka gama samun komai"
D'ayar dake kusa da wacce tayi maganar ta harareta tana cewa itama "to nan da kike ganinsa ba wani cikakken mai hankali bane, idan ciwonsa ya tashi cewa akai ko waye a kusa dashi mugun duka yake sha, da kyar ake kwace mutum a hannunsa. Sana auransa ya kai uku ko wacce bata iya zama dashi saboda baya iya tsinanama mace komai, nan da kike ganinsa bai cika namiji ba da'aAllah".
Wani abu mai d'aci ne ya tukare ma Salman wuya idonsa ya kad'a yayi jawur danma a cikin gilas ne baka tab'a ganewa. Shi kad'ai yaji miye y'an matan ke cewa. Saboda Allah yayosa da mugun sauri jin magana, koda rad'a kuke zaiyi wuya baiji miye kuka cewa ba, indai tazarar ba wata bace. To yanzu ma a d'an kusa suke dashi koma a hakan wai rad'a suke suna galmarsa.
Shigewa kawai motar yayi PA dake tsaye ya maida murfin motar ya rufe. Yana tunanin mike damun Mai gidansa?. Da alama ciwonsa kwanakin nan na gaf da tashi dama a Nigeria indai zai zo to kuwa sai ciwon ya tashi.
*Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria*
"Kande ki tabbatar kin jera komai yadda ya kamata"
Kande dake wajan darning table ta d'an tab'e baki tana maganar zuci "kaji makirar mata, a waje ta Allah a zuci shaid'aniya. Yanzu Fisbilillahi duk wannan rawar kan da take akan Salman zai dawo da za'a bata wuk'a a b'oye zata iya hallaka bawan Allah ko?".
"Keee Kande ubanmi kike tunani ina miki magana?, kin mayar dani y'ar iska"
A tsorace Kande ta kai dubanta wajan Momy dake jefo mata kallon wulakanci bakinta na kyarma ta ce "kiyi hakuri Hajiya wallahi banji bane. An gama jera komai ai"
Tsaki kawai Momy tayi tana zama d'aya daga cikin kujerun parlon tana d'aukar wayarta. Wata number ta kira bugu d'aya aka d'auka.
"Kinga Asiya abunda kike so fa bai zai tab'a yiwuba"
Daga cikin wayar aka ce "haba Hajiya kinsan fa yarinyata Sakina tana mutuwar son Salman, mi yasa zaki ce bazai yuwu ba?. Bayan nasan komai na gidan Alhaji Bin Muhammad na k'ark'ashin ikonki ne"
D'an sauk'e lumfashi Hajiya tayi kamin ta ce "bana son rayuwar d'iyarki ta salwanta ne, bana so ta zama k'aramar bazawara ne, domin bazata iya zama da nakashashshan yaron nan Salman ba, abunda nake so dake shine Asiya ina so a samomin yarinya wacce iyayenta suke da son kud'in tsiya wacce a gidansu anfi tsanarta wacce bata da gata gaba da baya, irinta nake son k'ara aura masa, wacce zatayi sanadiyar nakasa masa rayuwa. Boka ya ce min dole a samo yarinya wacce bata da galihu shine kad'ai zai iya zama da ita wacce koya bigeta tasha wuya babu inda zata iya guduwa dole dai ta zauna dashi. Danni burina kawai ace yau Salman ya kashe matarsa dole yaje gidan yari, duk wa'inda yake aure ba sonsu nakeyi ba, saboda suna da galihu Y'ay'an masu hannu da shuni ne. Kuma dama suma ba dan Allah suke sonsa ba, dan kyansa ne da dukiyarsa ke rud'arsu. Dasun zo kuma sunga ya yake sai su gujesa".
Sauk'e goran lumfashi Asiya tayi dake cikin wayar kamin ta nisa ta ce "tabbas na gane ina kika dosa Hajiya, na gane nufinki kin iya taku gaskiya, komai a hankali kike binsa a sannu-sannu ta yadda wani mutum bazai tab'a gane ke muguwa bace, dole sai idan kice kikai niyar ya sani. Lallai na jinjina miki kuma insha Allahu a nan Hadejia zan bincika miki yarinyar data dace".
Murmushi kawai Momy ta saki tana sauk'e wayar bayan sunyi sallama.
K'arar tsayuwar motoci a cikin gidan yasa Momy tashi cike da fara'a kamar bakinta zai tsage tsabar makirci, harda fita k'ofar parlon gidan domin tarbar Salman.
Kande dake lab'e a kitchen tana lek'en Momy ta rake baki tana cewa a fili "keee duniya ina zaki damu?. Yanzu waye zai kalli matar can ya ce bak'ar muguwa ce?".
Ta idasa maganar tana kallon yadda Momy ta tarbi Salman ta rungumesa sai masa sannu da zuwa take, yadda kasan ta goyasa, baka tab'a kallonta lokacin d'aya kace ba d'anta bane.
"Ohhh My Son kasha hanya sannu kaji. Kaje ka watsa ruwa an gyara maka part naka, an had'a maka ruwan wanka ga abinci akan darning table kai kawai yake Jira".
Murmushi Salman yayi yana jin dad'in yadda Momy ke nuna masa so. Ya ce "Momy duk ni d'aya?. Ina Daddy ne?"
Murmushin itama ta sakar masa wadda bai kai zuci ba ta ce "Ohhh Daddynka yana wajan aiki, nasan yanzu haka yana kan hanyar dawowa domin ya san da dawowarka. Danma suna da wani mitin ai da harda shi wajan d'akko ka Airport ma".
Murmushi kawai ya saki yana juyawa ya nufi part nasa. Yana d'okin ganin Daddynsa.
Yana juya baya Momy tabi bayansa da harara. Tana maganar zuci "hmm haka kawai tunda na auri ubanka ko b'atan wata ban tab'a yi ba. Sai kawai na zuba maka ido ka gaje dukiyarsa, baccin kaima ga irin arzik'in da Allah yayi maka, wadda yama so yafi na uban naka. Ina ai bazan tab'a bari kaji dad'in dukiyar bama, bare ka tafiyar da ita yadda ya dace, saina ruguza rayuwarka Salman".
*8:00PM*
Zaune Daddy yake shida Salman suna cin abinci cike da hara da soyayya. Maganar kasuwanci suke da kuma kewar juna da sukai. Sai Momy dake zaune a gefensu tana ta k'ara zubama Salman duk wani abu da yake so tana ta washe baki kamar ta Allah.
Daddy ya kalleta yadda take ta nan nan d'ansa d'aya tilo abin sonsa ya ce "kai Momyn Salman anma manta dani kenan tunda anga Salman ya dawo ko?".
Dariyar yake ta saki tana cewa "yo ba dole ba, d'ana ya dawo ai dole na kasa zaune na kasa tsaye. Sai dai kayi hakuri Daddyn Salman wannan lokacin d'ana ne kawai".
Dariya suka saki a tare kamin Daddy ya aje cokalin dake hannunsa ya d'akko wayarsa yana cewa "abun y'ar hakane?. To shikenan kinci kyauta kawo account number naki yanzu kiji alart ai duk wadda ya kyautata ma Salman dole ne na basa kyauta"
Murtuke fuska Momy tayi tana b'ata rai ta ce "haba Daddyn Salman na d'auka Salman ai d'ana ne wadda nake d'aukarsa kamar ni ce na haifesa. Yanzu idan wani yaji ai sai ya d'auka dama ban isa haihuwarsa ba, ka nuna dama bani ce Mahaifiyarsa ba".
Da sauri Daddy ya ce "Ohh am sorry Momyn Salman ba haka nake nufi ba. Kyauta ce kawai zan baki, kin cancanta ne ba dan wani abu ba. Ni na isa na ce ba kece kika haifi Salman ba?".
Murmushin makirci ta saki tana sake cewa "Ohh yanzu naji bato koda na ce, to mun gode Daddyn Salman"
Dariya suka sake saki a tare Daddy na jin dad'in yadda Momy ke nunama Salman kulawa yana kallonta cike da so.
Bayan sun gama cin abincin kai tsaye part d'insa Salman ya nufa PA dake tsaye tare suka jera da wasu takardu a hannun PA d'in yadda yaga Mai gidan nasa na rik'e kansa yasa PA d'an shakkar rab'ar inda yake. Duk da PA na matuk'ar sonsa amma yana tsoro ciwonsa ya tashi yana kusa, ai kowa na tsoron abunda zai cutar dashi.
Sai dai addu'ar PA bata amso ba. Suna shiga parlon part d'in Salman kawai ba zato ba tsammani Salman ya zube a k'asa ba numfashi.
Wata irin zabura PA yayi yana waro ido waje tsoron tab'asa yake dan indai ciwon zai tashi dama haka yake, sai ya fara fad'uwa k'asa kamar wadda baida rai.
PA na tsaye a mugun tsorace shi bai fita ba shi bai idasa isa inda Salman yake ba.
Baiyi zaton tashinsa a d'an k'ank'anin lokaci ba, amma kawai idonsa ya gane masa Salman ya mik'e tsaye a haukace. Kalar idonsa ta sauya ta koma jawur kamar wuta. Wata irin kururuwa Salman ya saki kamar Zaki. Ya fara yaga suturar dake jikinsa, yana yagar fatar jikinsa kota ina kartar jikinsa yake, wasu irin farata zak'o-zak'o sun fito masa a hannu. Mutuwar tsaye PA yayi ido a waje jikinsa ba abunda yake sai kyarma.
Wani k'aton table dake gaban Salman ya wawuro, bai sauke sa a ko ina sai a akan PA wata irin zabura