Showing 12001 words to 15000 words out of 22238 words

Chapter 5 - SAUYIN YANAYI Free pages -WPS Office.txt

addu'a a ranta, sai kuma ta dawo da dubanta wajan Nanah data k'araso inda take yanzu.


Ta ce "bai dawo ba, nima nayi mamaki anayin sallar Asuba fa yake dawowa gida, indai sukai kwanan dajin nan"




Murmushin yak'i kawai Nanah ta saki, dan itama taji irin fad'uwar gaban da Inna taji kawai ta d'aure ne dan kar Inna ta fahimci hakan.


Auta ta jawo yasha Kokon kamin ta kama hannunsa zasu fice daga gidan taji Inna ta tsaida ita tana cewa "ke kuma fa bazaki sha kokon bane?"




Wani abu Nanah ta had'e a mak'oshinta kwata-kwata yau bata jin dad'i, bawai rashin jin dad'i na jiki ba, a'a kwata-kwata yanayin yau bata jin dad'insa.


Da kyar ta ce "a'a Inna na k'oshi, idan na dawo naci wani abu kawai"


Itama Innar bata sake magana ba, har su Nanah suka fice daga gidan. Kawai saita samu kanta da tagumi hannu biyu-biyu ta rasa mike mata dad'i itama.




Tafe suke kan hanya ita da Auta zasu dawo gida bayan an taso daga Islamiyar, Auta sai tsaida ita yake yana y'an wasanninsa.


Tsawa ta daga masa tana cewa "wai kai Auta mi yasa baka da natsuwa ne?, muna tafe kan hanya ka natsu mana muje gida"


Auta daya firgita da tsawar da Nanah tayi masa, yasa ba shiri ya natsu yana binta da kallo kamar ba itama ba, bata tab'a masa irin wannan tsawar ba. Kodai bata da lafiya ne?.


Sai kuma ta kamo hannunsa suka cigaba da tafiya.


Sun shawo kwanar gidansu kawai taji Auta na cewa "lahhh Nanah dubi k'ofar gidanmu cike da mutane"




Kan Nanah a k'asa yake ai da sauri ta waiga inda k'ofar gida nasu yake. Wata wawar bugar zuciya ce lokaci d'aya ta riski Nanah had'e da wata fad'uwar gaba. Tunkan ace mata mike faruwa ta fara hawaye kawai domin jikinta ya bata ba lafiya ba.




Da gudu Auta ya warce hannunsa da Nanah ta rink'e yayi cikin gida.


Nanah ma ta tsakiyar mutanan ta rab'a ta wuce yadda taga sai binta suke da kallon tausayi, an shinfid'a tabarma ga Liman yazo wasu na alwala duk jikin mutane a sanyaye.


Da sassarfa ta idasa shigewa cikin gidan. Tana shiga abunda idonta yayi mata tozali dashi shine Gawar Baba shinfid'e a har an gama shiryata duk jini ya b'ata jikin likafanin. Wata irin razananinyar k'ara Nanah ta saki a haukace ta nufi inda gawar Baba take wata irin wawar runguma tayi masa, kawai ta fashe da wani irin kuka mai zuma zuciyar mai saurare.




Auta dake jikin Inna shima sai kuka yake duk da bai san mutuwa ba amma yasan idan aka tafi ba'a dawowa shikenan kaida mutum har abada.




Da kyar aka b'anb'are Nanah da har sumewa tayi a jikin Gawar Baba sai da aka shafa mata ruwa bayan an fita dashi.




Matsuwa Nanah tayi jikin Inna tasa kanta akan k'afad'ar Inna tana hawaye tana magana cikin muryar kuka ta ce "Inna miya faru da Baba?",


"Nanah y'an Ta'addar nan ashe dajin dasu Babanku suke b'uya sun gane cewa dama b'uya suke subar matansu. Wani d'an lek'en asiri suka turo ya kwana a garin shine yaje ya sanar dasu komai har inda su Babanku suke. A daran sukai ma wajan dirar mikiya sun kashe da yawan mazan dake wajan hatta Balah shima sun kashe sa Ibro ne kad'ai ya tsira shima sunji masa mugun ciwo"


Kuka kawai Nanah ta saki tana tsinema y'an Ta'addar nan a zuciyarta yafi a k'irga sai tsine masu take tana jawo masu bala'in duniya dana lahira.




Gaba d'aya garin Gurbi ya zama shuru da yawan mutane a ranar basu k'ara kwana a garin ba, a hankali garin ya fara zama kamar ba gari ba. Duk wadda ka kalla a cikin garin bashi da natsuwar zuciya kullum da tashin hankali suke kwana suke tashi. Dan yanzu har tsakiyar rana y'an Ta'addar shigowa suke.




Tsaye Inna take yau kusan wata d'aya da mutuwar Baba tana shirin saida gidan da suke ciki ta tattara y'ay'anta su koma cikin garin Jibia da zama, ko sun samu kwanciyar hankali, duk da taji Jibiar ma shiga suke idan sunyi niyya, amma ai gara can da yawan mutane a garin.




"Yanzu Inna waye zai siya wannan gidan da daraja a garin nan?"


Inna ta kalli Nanah dake mata magana. Inna ta nisa ta ce "na dai aika Auta gidan Saminu dallali, yaji idan zai iya siyan gidan nan, dan bana ma so mu k'ara wasu kwanaki a garin nan gaskiya"


"To Allah yasa ya siya d'in, kin san yanzu tsoron siyan gida ake a garin nan ma"




"Yo Nanah ba dole aji tsoron siyan gida a garin nan ba. Ai dan a zauna ake siyan gida, to k'iri-k'iri idan ka siya zai gagareka zama indai a cikin garin nan ne.........
*SAUYIN YANAYI*






Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*




*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*




*EPISODE* 6






*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*






"Kaiii Ismail tsaya na ce"


Juyowa Ismail yayi yana duban Hajara data masa tsawa, rik'e k'ugunsa yayi yana kallon Hajara kawai.


Wani duba take mai cike da mamakin yaron ta cije baki kamin ta ce "kai dan ubanka, ni ce zan aike ka kaje kayo min shirme?"


"Mama bafa shirme nayo miki ba, haka kike ce na sayo miki Sigari"


Dafe k'irjinta Mama tayi ido a waje take nuna Ismail tana cewa "na shiga uku Sigari?, ni ce nace ka sayo min Sigari?"


Wani irin kuka ta fashe dashi na makirci. Tana matse hawaye


Da sauri Maryam ta fito daga d'aki tana kallon Mama cike da mamaki take cewa "Mama lafiya na ganki tsaye da yaron nan dangin marassa kunya?"


Mama ta dubeta ta ce "bari y'ar nan, yanzu ni wannan yaron zaima shirri?, wai ni ce zance yaje ya sayo min Sigari ni?, yanzu kamar wannan yaron d'an haka dashi ya iya k'ulla shirri?".


Wani kukan kura Maryam tayi sai gata agaban Ismail batai wata-wata ba, ta tsinka masa mari. Wani ihu Ismail ya saki yana dafe kumatunsa.
Duk da haka Maryam sai da taci kwalar rigarsa tana zare masa ido, a tsawa ce take masa magana.


"Kaii dan ubanka, uban waye ya had'a maka wannan tuggun da har ka iya had'a munafurci, dan kaja ma Mama shirri kana yaro da kai?. Zaka fad'a min ko sai na faffasa maka baki?, ka tab'a ganin Mama nashan tab'a dan uwarka?"


Hajiya ce da Salma suka fito a hargitse jin kukan Ismail.


Ganin yadda Maryam taci kwalar rigarsa yasa Salma zuwa da k'arfi tajawo Ismail tana bin Maryam da kallo na mamakin miye yayi mata haka?.


Mama ganin Hajiya ta fito, yasa dan d'aukar magana ta saki wata shewa tana cewa "yo idan banda abunki Maryam, ai uwarsa ce zata gaya masa yaje ya sayo Sigari domin kawai ya b'ata min suna, dama bata san zamana a gidan nan. Tota Allah bata mutum ba wallahi, duk wani munafurci uwarsa ya gadu ai".


Wani murmushin manya Hajiya ta saki tana kallon yadda Hajara ke tujara. Batai niyar tanka taba amma jin maganar data keyi yasa Hajiya cewa "ke kin san y'ay'ana basu iya munafurci ba. Kuma ko kin d'auka kowama irinki ne?, kin d'auka duk wani makirci da mugunta da kikeyi a cikin gidan nan, kin d'auka duk mutane kalarki ne?".


Maryam zatai magana Hajiya a tsawace ta nunata da yatsa ta ce "Kinga ke baki isa nayi ceceku ce dake ba, da uwarki nake bada ke ba, ke ba sa'ar yina bace kin gane?".


Hajiya ta juya inda Salma take da Ismail ta nuna masu hanyar shashinta alamar su wuce ciki, wucewar su Salma yasa Mama hayayyak'o ma Hajiya kamar zata dake ta.
Hajiya bata k'ara magana ba, tayi shigewarta abunta tabi bayansu Salma.




Rik'e baki Maryam tayi tana cewa "kan uba, Mama wai wannan matar mi take nufi ne?"


"Yo mi kuwa take nufi nidai nafi k'arfinta wallahi, kuma bari Abbanku ya dawo wallahi saina sanar dashi abunda shegen d'anta yayi min"

Sallamar Khady ce ta mantar dasu maganar da suke kanyi.


Ganinta nik'i-nik'i da k'aya cike da leda, yasa ba shiri suka jata sai cikin d'aki.


"Yanzu Khadija duk wannan uba-uban kayan Jafar d'in ne ya siya miki?"
Cewar Mama, tana yi tana fiddo kayan dake cikin ladar, kayan ciye-ciye ne kala-kala harda su chocolate.
Maryam ma data fasa wata alawa tana tauna a baki ta ce "amma daga gani Jafar d'in nan yana da kirki sosai, daga gani yana da abun hannunsa"


Dariya Mama ta saki tana cewa "yo daga gani ai, ba sai an gaya miki ba"


Khadija ta saki murmushi tana d'aukar wata chocolate itama tana b'are ledar chocolate d'in tana cewa "wallahi kuwa Mama, ai harya fara min maganar turo manya a ciki, domin yana sona sosai nake gaya miki. Wai Mama kinga gidansa kuwa da yake ginawa har k'ofar gidan ya kaini, kai aljanar duniya".


Zaro ido Mama tayi cike da zumud'i ta ce "ke dan Allah bari, har can kuka je?"

Khadija ta amsa mata chocolate cike da bakinta ta ce "wallahi kuwa Mama karki so ganin gidan. Danma ban tafi da waya taba, na barta a nan gida, da ai har hoton gidan zan d'akko ku gani".


"Na yarda, kuma insha Allahu suzo gida kawai ayi a wuce wajan. Dan jiran ya huce shike kawo rabon wani"


Khadija ta zaro ido tana cewa "Mama kin manta ban gaba karatu ba?"


"Shin wai ba saura shekara d'aya ki idasa bane?"


"Eh Mama"


"Yawwa ai dai-dai kenan, asa rana ayi komai asa ranar dai-dai lokacin da zaki gama school, a lokacin a ranar sai kawai a d'aura auran"


"Kaii Mama nama manta da wannan dabarar fa wallahi, hakan za'ai ma kuwa zan masa magana ya turo manya kawai su gana da Abba"






*Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria*


Auta ne ya shigo ciki gidansu da gudu tare da taya yana garawa.


Inna ta kalli Auta ta ce "yawwa Auta na, kaje aiken dana yi maka kuwa?"


Auta ya aje tayar da yake garawa zaiyi magana Nanah ta rigasa tana cewa "Allah yasa yaje d'in, ya fad'i sak'on yadda ya dace, baiyi shirmen daya saba ba".


"Kinga kibarsa ya gaya min ko?"


Shuru Nanah tayi tana kallon Auta itama, tana son jin miye zaice.


Auta ya ce "Inna naje ya ce zaizo gidan da kansa kuyi magana zuwa dare"


"Yawwa Auta na, Allah yayi albarka"


Gaba d'aya suka amsa da amin shida Nanah.


Kamar yadda Auta ya ce, saiga Saminu dallali yayi sallama a k'ofar gida.


Koda ga jin sallamarsa Inna data idar da sallah ta kalli Nanah ta ce "kije ki shigo dashi zaifi muyi magana a cikin gida"


Da to Nanah ta amsa tana sa hijab d'inta ta nufi waje.


Inna kuma ta baza tabarma a tsakar gidan ta dawo ta zauna akan sallayar data idar da sallah.


Da sallama a bakin Saminu ya shigo gidan Nanah na gaba, tamai iso.


Sun gaisa da Inna ta nuna masa wajan zama.
Bayan ya zauna Inna ta nisa ta ce "abunda yasa na kira ka Saminu shine, ina so na saida wannan gidan ne, da muke ciki, ina so zamu koma Jibia da zama gaba d'aya".


Saminu ya gyara zamansa ya ce "to wani hanzari ba gudu ba, yanzu dai gaskiya babu wadda ke zuwa ya ce zaisa gida a garin nan, na cikin garin ma tashi suke suna guduwa daga cikinsa. Danni kaina yanzu haka shirin tashi muke nida iyali na"


Shuru ya d'an gifta na wasu sak'onni kamin Inna cike da tashin hankali ta ce "yanzu Saminu ba yadda za'ai a shigar da gidan nan?, wallahi nima garin tsoro yake bani baya ma ace dare yayi"


Saminu cike da tausayi ya ce "gaskiya nima ban san yadda za'ai ba, amma zan miki taimako d'aya, zan ara miki kud'i idan kunje Jibia sai ki kama haya dasu. A nan kuma zansan yadda za'ai a shigar da gidan, idan ya so ana saida gidan sai na d'auki kud'ina"


Girgiza kai Inna tayi, domin Allah ya sani bata son bashi ko kad'an, tana tsoron ace yau gobe ta mutu da bashi akanta.


Ta ce "a'a Mlm Saminu bazan amshi bashinka ba, ina da wata sark'a tunta aure na, kuma ina da tabbacin zatai daraja, zan baka ka saido min a cikin birni zuwa gobe. Domin can baya naso na sayar da ita amma Babansu Nanah ya hana, gara na siyar da ita mu tashi kawai".


Gyada kai kawai Saminu yayi yana binsu da kallon tausayi.


Tashi kawai Inna tayi ta shiga d'aki ta d'akko sark'ar ta kawo ma Saminu.
Amsar sark'ar yayi yana jujjayata kamin ya ce "kai ai kuwa sark'ar zatai daraja domin za'a iya siyanta dubu d'ari biyar harda y'an kai ma"


Murmushi Inna ta saki danta san zata kai hakan itama.


Sallama yayi masu inda yake cewa sai goben insha Allahu zai shiga birni ya saida ta........


*SAUYIN YANAYI*






Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*






*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*






*EPISODE* 7








*Garki Hospital: Tafawa B'alewa Way, Area 3, Garki, Abuja Nigeria*


"Daddyn Salman please ka samu ka zauna zai samu lafiya fa insha Allah"


Daddy dake safa da Marwa a harabar asibitin da aka kawo Salman, da kyar wasu Maza suka danne Salman aka kira Doctor ya danna masa wata allurar bacci. Duk da haka sai wasu irin surutai yake, jikinsa na sauyawa kamar maciji.


Daddy fuskarsa cike da damuwa ya ce "bazan tab'a samun natsuwar zuciya ba, har sai naji ya yanayin jikin d'ana yake"


Momy zatai magana saiga doctor ya fito daga d'akin da aka kwantar da Salman. Da sauri suka tarbeshi, sai dai ya d'aga masu hannu yayi masu alamar su biyo shi Office kawai. Shima kansa doctor d'in wata zufa ce yake sharewa, domin abunda ke damun Salman d'in yasha masa kai.


PA dake tsaye baiyi gigin binsu Office d'in doctor d'in ba. Yana tsaye hannunsa d'auke da wayoyin Salman dake ta aikin ringing tun d'azo. Wani dogon tsaki yaja tana mitar cewa "wai su mutane mi yasa basa da hakuri ne?, sun kira sau d'aya ba'a d'aga ba, basai su hakura ba"


Wayar dake hannun damansa ce tayi fara ringing wacce iya y'an uwa, da wadda suke da mahimmanci ne a rayuwar Salman kad'ai ke iya kira ta cikinta.


Hakan yasa PA duba mai kiran, ganin Faruk Galadima rubuce akan wayar yasa shi d'auka.


Sai da suka gaisa Faruk yake tabbayar ina Salman?.


PA ya nisa kamin ya ce "wallahi yanzu haka muna asibiti jiya ne kawai ciwonsa ya tashi, dan gaskiya wannan karan yafi ma tsamari"


Hankali a tashe Faruk ya ce "Subhanallahi, ya yanayin jikin nasa?, shi yasa tun jiyan nake neman wayarsa tana shiga ba'a d'auka"


"To jiki dai sai dai ace Alhmdllhi, amma har yanzu dai sai a hankali"


Sun dad'e suna tattaunawa daga k'arshe sukai sallama.


A Office d'in doctor kuwa suna zama, Doctor ya dubi Daddy da Momy ya ce "gaskiya abunda ke damun Salman bana asibiti bane, saboda munyi iya yinmu amma abun yaci tura. Yanzu fa da nake gaya maku kalar jikinsa ce ke sauyawa tana komawa irinta jikin maciji, jikinsa na sab'ulewa yadda kasan shida kansa Macijin ne"


Zaro ido Daddy yayi zuciyarsa na halbawa da k'arfi kamar zata faso k'irjinsa ta fito, tsabar rud'u da tashin hankali.


Da kyar ya samu magana ta fito daga bakinsa ya ce "doctor maciji fa ka ce?".


"Kware kuwa Alhaji, zama ku iya zuwa ta bakin window da aka kwantar dashi kuga halin da yake ciki. Mafita d'aya ce a samu wani Malami na addini ya rink'a masa karatu ko wasu taimako haka dai".


Momy tana jin haka tayi wuf d'in cewa "haba Doctor ba wani Malamin da za'a kira, kuma ni ban yarda d'ana ba ciwon asibiti bane, saboda baida wani abokin fad'a bare har a samu mai masa asiri"


Shi kansa Daddy ya yarda da abunda Momy ta fad'a. Domin iya saninsa Salman baida wani abokin fad'a ko d'aya.


Shuru Doctor yayi duk yadda yaso fahimtar dasu amma ina, daya d'akko nan sai Momy ta toshe can. Dole tasa ya kama bakinsa yayi shuru.


Fitowa sukai daga Office d'in, Daddy na niyar zuwa inda aka kwantar da Salman, Momy da makirci da wayo ta hanasa zuwa, bare ma ace ya yarda da abunda doctor d'in can ke fad'a. Ai ina bazata bari
Ya rusa mata shiri, wadda ta dad'e tana shiryasa tun tsawon shekaru.


Saima ta jasa suka koma gida, wai zuwa anjima zasu dawo, zata taho da kayan buk'ata, suka bar PA a nan da wasu masu tsaron d'akin da aka kwantar dashi.


Suna zuwa gida ta haura sama da sauri tana wurgar da jakarta ta lalubo wayarta ta dannama Asiya kira.


Tana d'auka ba gaisuwa ta fara cewa "Asiya na jiki shuru fa?"


"Hajiya kiyi hakuri, ina d'an jiran wani abu ne, amma nama samo yarinyar, ina jiran wani abu ne ya faru a gidan su yarinyar ne, zanje kuma za'a bamu ita insha Allah"


"Haka nake son ji, yana can kwance rai hannun Allah"


Dariya suka saki a tare kamin Momy ta tsinke kiran.


Wata dariyar ta sake kecewa da ita, kanta a sama tsabar dariya har wasu hawaye ke zuba mata a fuska.


Rayuwarta ta can baya take tunowa, da abunda ya maida ita muguwa, abunda yasa ta tsani Salman shida uwarsa, wacce tana kawosa duniya Momy tayi sanadiyar barinta duniya.


*Shekarun baya da suka wuce*




"Yanzu Didi Alhaji Bin Muhammad aure zaiyi?, kuma yasan ina bala'in sonsa, haba Didi kiyi wani abu mana"


Didi ta kalli Aysha dake kuka bil hakki da gaskiya. Duk da tasan Alhaji Bin Muhammad d'an uwa ne a garesu to amma tunda yaje ya d'akko bare yaya zatai dashi?, tunda yak'i y'ar uwarsa k'iri-k'iri ma ya nuna Hakan.


"Kinga ki kwantar da hankalinki, indai ina da rai to sai kin auri Alhaji, kima sama kanki ruwan sanyi"


Share hawayenta Aysha tayi, duk da taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login