Showing 3001 words to 6000 words out of 22238 words
Chapter 2 - SAUYIN YANAYI Free pages -WPS Office.txt
mazauni bane, yana harkar kasuwancinsa k'asashe-k'asashe. Kuma koba wannan ba ai yana da dangi a Nigeria, ko baki san haka ba?, to zaije ganin gida ne".
"Hmmm PA kenan ba kaine sa'an yina ba, wadda ya ajeka shine dai-dai ni"
"Duk wannan haukan da kike hakan bazai sa Mai gida ya aureki ba. Saboda kyansa kika gani da dukiyarsa kike rud'e haka, amma ba dan Allah kike duk wannan haukan ba. Kuma na baki shawara Jasmin?. Mai gida koda yana da niyar aure yanzu to bazai tab'a auranki ba, domin baki dace dashi ba. Dube ki, dubi jikinki dubi kayan dake sanye a jikinki kwata-kwata kamar ba d'iyar hausawa ba. Kawai danki girma a ture sai akace ki yada al'adarki?".
Jikin Jasmin tsabar b'acin rai har wani rawa yake so take ta gaggaya ma Fahad magana itama amma wani abu ya tsaya mata a wuya.
Ganin bata da bakin magana yasa Fahad wucewa yana murmushi dan yasan ta shak'a iya shak'a. Ai wallahi baya fatan Mai gidansa ya auri irinsu Jasmin ai sai su lalata masa rayuwa gaba d'aya ma.
*Canada Studio Faruk Galadima*
Zaune yake a studios yana sauraran wak'ar da ya gama rerawa yanzu cikin harshan turanci. Dafasa akai ne yasa shi cire abunda ke manne a kunnansa yana duban Henry daya dafa k'afad'arsa.
Henry ya ce "Ohhh Faruk, you should rest like this and work hard today, I see that your phone is being called and you should check"
Sauk'e goran lumfashi Faruk yayi yana lumshe idonsa yana d'an murza dogon gashin kansa. Wadda daka kalla zaka san irin na Fulanin asali ne.
Muryarsa a gajiye ya mik'e yana cewa "by God, I'm also planning to leave the studio and go home. I know, Amma I'm waiting for me".
"You should do it because today we are working on this song"
Computers guda biyu ya d'auka sai wasu y'an abubuwa yana shirin barin wajan yaji Henry na cewa "yawwa kaga nama manta babbar mawak'iyar nan tazo nemanka wai tana so tayi wak'a da kai"
"Wa kenan?"
"Enisa mana"
"Ohhh, but I'm just singing, I don't release the video of the song, but some people sing my song if we sing normal, but honestly I won't sing, I can't sing"
"Faruk na fad'a mata wannan duk da taso ku hau wak'ar tare amma ta amince zaku rera wak'ar kawai"
"Okay yayi ba bamuwa ita ce ta rubuta wak'ar ne?".
"Eh ita ce yanzu hakama taban wak'ar a rubuce zuwa gobe zata dawo domin ganinka.Then decide when you think you will sing the song"
"Ba damuwa zuwa goben ma idan aiki bai min waya ba, zamu iyayinta kawai".
Ficewa yayi daga studion yana fata yasa face mask ya rufe fuskarsa, gudun mutane suyo kansa, duk da dare ya tsala amma garin kamar safiya ce. Dan duk inda ya shiga a k'asar Canada to ansan sa ansan waye Faruk Galadima shahararran mawakin dake tashe a duniya. Ya fara wak'a tun yana k'araminsa da sun cikar burinsa na son zamowa mawaki. Kuma Amma ta basa goyin baya, sai dai duk da haka baisa ya manta shi d'in waye ba. Mahaifiyarsa kad'ai ta rage masa a duniya. Sunsha wahalar rayuwa acan baya amma wak'ar daya ke tasashi d'aukaka, d'aukakar da zato bai zata ba. Shi kansa baiyi tunanin zai zama wadda duniya take alfahari dashi kamar haka ba, it's a good thing for everyone to join him wherever he goes or where he goes.
Abunda ya maido sa zama Canada shida Amma bayan wak'a yana aiki a wani kanfani na k'era wayoyi da computers da dai sauran na'oruri daya danganci electric. Yasan takan waya da computers duk idan sun samu matsala zai iya gyara maka a d'an k'ank'anin lokaci. All companies are proud of Faruk Galadima.
Katse tunaninsa yayi dai-dai yazo gaban wata Mota mai d'aukar ido. Bud'e gidan baya yayi yasa abubuwan dake d'auke a hannunsa, bayan yasa ya rufe bayan ya dawo ya shiga ya tada motar yabar cikin studion, da shima mallakinsa ne yanzu, mawak'a wadda basu kaisa ba suna zuwa sosai domin su buga wak'arsu a studionsa ba tare da ka bada ko sisi ba. Da yawan mutane abunda ke k'ara sawa su soshi kenan sunansa yayi zarra a k'asar Canada, kai harma da makwaftan k'asashe.
Wani ma dai-daicin gida wadda ya gaji da had'uwa yayi parkin d'in motar tasa kamin ya bud'e ya fito yana danna wani madanni dake hannunsa nan take get d'in gidan ya bud'e, shi kuma ya koma cikin motar ya data ita, ya idasa shigewa harabar gidan. Wajan aje motoci yayi parking.
Fito yayi daga motar ya d'auki kayansa dake bayan motar ya nufi cikin gidan.
Yana shiga babban parlon gidan ya iske Amma dake zaune zaman jiransa.
Ganinsa ya dawo k'alau yasa Amma sauk'e ajiyar zuciya. Har saida Faruk yaji yadda ta sauk'e ajiyar zuciyar.
Murmushi ya saki yana ajiye kayan dake hannunsa yazo kusa da Amma ya rungumeta yana cewa "Ohhh Amma idan na fita sai kace wani k'aramin yaro, wadda idan ya fita akesa ran bazai iya gane gida ba?. Amma nafa girma yanzu"
Kumatunsa Amma taja tana cewa "kaci gidanku Faruk, yaushe aka haifeka ma da zaka wani ce ka girma yanzu?, ni a waje na kai yaro ne".
Murmushi ya sakar mata ya ce "hakane fa Amma, ai kin san ina kan hanya gashi na dawo kuma lafiyata lau".
"Kaji ja'iri baccin ka gama tada min hankali, ka kalli k'arfe nawa ne yanzu kuwa?"
Da sauri Faruk ya kai dubansa akan tsintsiyar hannunsa dake d'aure da agogon hannu. Waro ido waje yayi yana cewa "Ohhhh sorry Amma sha biyu saura ashe na dare. Mi yasa baki kwanta ba?, aiki ne yau yayi min yawa wallahi"
Shafa kansa tayi tana cewa "nayi tunanin hakan, amma kasan idan ba dawowarka na gani ba bazan iya bacci ba. Kaida kota ina mutane nemanka suke ya za'ai kullum hankalina bazai tashi ba idan zaka fita?".
"Amma nemana mutane suke amma ai soyayya ce tasa hakan ba wai cutar dani zasuyi ba"
Murmushi Amma ta saki irin na manya ta ce "har yanzu kai yaro ne Faruk, ai cikin hakan ake samun mak'iya, wad'anda basa son ci gabanka, kai dai kawaii Allah yayi mana tsari da su. Allah kuma ya k'ara k'are min kai a duk inda kasa gaba"
Kiss ya kai mata a goshi yana amsawa da amin.
Yana niyar tashi Amma ta ce "abinci fa?"
"Bana jin abincin nan zai shiga yanzu Amma"
"To miye kaci yau?".
"Na d'anci wani abu a studio"
"A'a bazan yarda ba saifa kaci abinci, nasan ba wani abinci kaci ba, yanzu haka Chacolate d'in daka saba ci kayan zak'i sune kayita sha. Kazo ga abinci nan akan darning table kaci"
D'an tab'a cikinsa Faruk yayi sai yanzu nema yaji lallai yana jin yinwa, dan rabonsa da abinci tun safe da zai fita aiki. Sai Chacolate d'in da sha.
Shigewa yayi d'akinsa dake sama. Yana shiga toilet ya fad'a ya watsa ruwa, bayan ya fito yasa wasu k'ayan bacci. Yana d'aukar wayarsa dake ta aikin ringing tun d'azo.
Wayarsa ta gida wacce y'an uwansa na kusa da friend's nasa ne kad'ai ke kira ta cikinta yaji ta fara k'ara.
D'aukan kiran yayi yana k'arawa a kunne.
Cike da kulawa yake yin wayar wani lokacin yayi dariya daka gani kasan da abokinsa yake waya.
Can ya ce "Okay kuna gaf shiga jirgi?. Ni banso ka koma Nigeria ba yanzu friend, miye zakai a Nigeria ne?, kasan kuma ciwonka yafi tashi idan kana can".
Daga cikin wayar aka ce "to ya zanyi ina son k'asata kuma Daddy ya kirani yana son gani na nima nayi kewarsa sosai kasanfa rabona da Nigeria zanyi shekara biyu, tun sadda naje Momy ta matsa nayi aure, akayi a daran aka samu matsala dole na saki matar tun lokacin na bar k'asar"
Faruk cike da kulawa ya ce "Salman ya kamata fa asan miye asalin mike damunka gaskiya ba yadda za'ai ka zauna ba aure"
"Abunda bana so kana min maganarsa kenan Faruk ka sani. Nigeria is the only thing I don't want to come to where I went and Daddy pressured me to get married, kuma bayan yasan bazan iya zama da kowacce mace ba a haka"
"Insha Allahu Salman komai zai wuce zamuyi waya idan ka sauka. Wai ina Jasmin ne taka?"
"Kai ko? Bana son wannan zancan, ko kasan Jasmin bata da kamun kai?, kai kwata-kwata ma bata cikin jerin matan da nake so. Kuma duk fad'a take duk sadda a gaban idonta ciwo na ya tashi wallahi a ranar guduwa zatai"
"Hakane aboki ai da yawansu badan Allah suke son mutane irinku ba"
"Harda kai ma ai Faruk kaifa sele ne"
Dariya Faruk ya saki yana cewa "kai Salman na kaika ne nifa wak'a ce ta d'aukaka ni kaifa tsaye kake da k'afafunka kaine ka kafa kanka da kanka, ai matsiyin da dabanne"
"Ka cika wasa Faruk wallahi"
Sun dad'e suna waya kamar kar su daina sai da jirgin su Salman zai tashi tukunna sukai sallama..........
*SAUYIN YANAYI*
Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*
*EPISODE* 3
*Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria*
"Ance wai ana sallama da Babansu Auta"
Inna dake tsakar gida ta dubi yaron daya shigo ta ce "kaje kace gashi nan zuwa"
Juyawa yaron yayi ya fice daga gidan.
Inna ta kalli Nanah dake cin abinci ta ce "Nanah shiga d'akin Babanku kice ana sallama dashi k'ofar gida"
Tashi kawai Nanah tayi ta shiga d'akin Baba ta sanar dashi.
Ba'a jima ba Baba ya fito ya fice daga gidan ya nufi waje.
Nanah ta kalli Inna ta ce "wallahi Inna gidan su D'an Liti mai shigo tashi fa zasuyi daga garin nan"
Inna ta aje redion dake hannu wacce take shirin kunnawa ta kalli Nanah, kamin ta d'an nisa ta ce "ai banga laifin su ba wallahi"
"Da mukaje da Auta yi masu jaje wallahi sai had'a kaya suke gaba d'ayansu gidan wai zasu koma katsina"
"Allah sarki ni kinga tun ranar dana je masu jajen ban gani ba, ashe barin Gurbi zasuyi. Kai wa'innan mutanan suna d'aukar alhakin al'umma. Haka kawai kana son garinka amma ya gagareka zama".
A k'ofar gida Baba yana fitowa ya iske su Ibro da Balah duk abokansa ne. Ganinsu hankali a tashe yasa Baba k'arasowa da sauri yana mik'a masu hannu, gaisawa sukai kamin Balah ya ce "Baban Nanah akwai fa matsala a garin nan"
Cikin Baba saida ya bada wani sauti kulululuuuu da kyar ya had'e miyau ya ce "ban gane ba Balah?"
"To yanzu dai y'an Dabar nan dake yawan shigo mana gari masu satar mutane had'e da kashe su, sana su d'ibi dukiyarmu da muke nomawa sun waiwayo kanmu"
"Subhanallahi wai kana nufin wadda suka so data garin nan baki d'aya?"
Ibro ya sauk'e lumfashi yana mik'a masa wata farar takarda ya ce "kaga wannan takadar sak'o ne daga wajansu suka aiko wai suna nan shigowa garin muma shirya. Sana sunce duk abunda muka noma mu tabbatar mun barsa a gonakinmu domin suna zuwa zasu d'ibesa su k'ara gaba, kai harda kud'in haraji ma suka sama kowa dake cikin garin nan"
Baba dake kallonsu ido a zare ya ce "wai wa'innan mutanan miye suke sone damu?, so suke su maida mu bayinsu kenan?".
Balah ya nisa ya ce "kuma abunda ke k'ara tada min hankali ma shine, Gwamnati ta kasa kawo mana d'auki. Kun tab'a ganin wani shugaban Gwamnati ya k'ara zuwa cikin garin nan da sunan yazo yaji miye yake damun talaka?".
"Inafa muka sake jin d'uriyarsu, ai tun gabannin zab'e da suke so muje mu dangwala masu k'uru'a. Sunci zab'en sun manta damu. Daga su sai iyalansu, ai wata shara'ar sai dai a lahira wallahi"
Cewar Baba da duk jikinsa yayi sanyi.
Baba ya sake kallonsu ya ce "to yanzu miye abunyi?"
Ibro ya ce "nidai gaskiya yanzu haka naba matata kud'in mota ita da yara na ce taje garinsu, mugani kamin garin yayi lafiya. Dan yanzu haka dangin D'an Liti mai shigo suma, sun tashi daga garin nan gaba ki d'ayansu"
Cike da tsananin tausayin kansu Baba ya ce "ashhsha yanzu muna ji muna gani garin nan zai dawo kamar mak'abarta?".
"Toya zamuyi gara mu matsa mu basu waje, domin tsira da rayuwarmu".
Cewar Balah. Baba ya ce "nidai gaskiya bani da inda zan kai Iyalaina wallahi, addu'a kawai zanyi Allah ya k'aremu gabaki d'aya. Sana yau can wajan gari zamuje mu kwanan?".
Balah ya ce "Baban Nanah yo ni nima ai babu inda zan kai nawa Iyalan. Kwana wajan gari kuma mu maza ai ta kama mu, domin kasan can baya indai suka shigo gari suka taradda namiji a gida kashesa suke nan take, shi yasa gaba d'ayanmu yau ba'a gida zamu kwana ba".
Ibro ma ya ce "Mai gari kuwa shi tuni ya kama gabansa shida Iyalansa an sai masa gida a cikin garin Jibia"
"Yanzu dan Allah miye wannan?, ace Mai gari guda na b'uya shida garinsa an hanasa zama a cikinsa"
Sosai suka tattaunawa kamin suyi sallama Baba bai koma cikin gida ba saida yaba su Balah kud'in harajinsa da y'an Dabar suka sa masu kowa saiya biya...
*Unguwar Dubantu Hadejia, Jigawa State Nigeria*
K'udundune take akan gado zazzafan zazzab'i ya rufeta. K'asusuwan jikinta sai kwankwatsa suke. Sosai take rawar sanyi yadda taji k'afarta na mata ciwo sosai, da cikin k'ashinta tasan ciwonta ne na Sikila zai tashi, hatta cikinta wani irin ciwo yake mata.
Hajiya ce ta shigo d'akin ganin halin da take ciki yasa hankalin Hajiya tashi ba shiri ta rungumo Salma tana cewa "haba Salma mi yasa tun d'azo baki sanar dani ciwon ki zai tashi ba?"
Da kyar Salma ta bud'e baki ta ce "Hajiya nima kawai ji nayi k'afata ta fara ciwo daga nan sai kwankwatsar k'ashi"
"Subhanallahi tashi yanzu nasa a mik'a mu asibiti bari nayi ma Abbanku magana Ahmad ya mik'a mu"
Hajiya na gama maganar ta fice daga d'akin.
Hajiya na fita tsakar gidan ta iske yaran gidan su Maryam tare da uwarsu Hajara duk sun dabaibaye ta tana rabon abincin rana. "Yara kamar wasu mayu". Cewar Hajiya a zuciyarta.
Wani kallon Mmn Maryam ta aikama Hajiya tare da su Maryam suna sakin shewa.
Duk da Hajiya tasan da ita suke hakan baisa yau ta tsaya ta maida martani ba, domin abunda Salma ke fama dashi ma kad'ai ya isheta.
B'angaran Abba ta shiga yana zaune yana jin redion sai Khadija dake zaune kusa dashi tana masa maganar kud'in karatunta, danta kusa komawa school. Hajiya na gani ya fiddo kud'i masu yawan gaske yaba Khadija, ta tashi rafka godiya take, ko kallon Hajiya bata yi ba, bare tasa ran gaida ita.
Hajiya cike da tak'aici ta kalli Abba ta ce "Fisbilillahi Abban yara kana ganin yarinyar nan ta ganni na ganta amma ta wuce bata gaida ni ba, saboda ban isa ba?, dama uwarsu ta gama hure masu kunne akaina yaran Hajara gaba d'aya sun raina ni a cikin gidan nan. Amma ni nawa yaran suna bata girmanta a matsayinta na matar Ubansu"
Abba dake danna y'ar k'aramar wayarsa bayan ya ajiye redion sai kuma ya sake aje wayar itama ya dawo da dubansa wajan Hajiya "Hajiya ya kike so nayi ne wai?, na tabbata akwai abunda ya kawoki, ba wannan ba ina sauraranki"
Wani abu mai d'aci Hajiya ta had'e a mak'oshinta ta cewa a ranta "lallai Rabe wato ma babu abunda zaiyi, yara sun gama rainata suna taya uwarsu kishi, ai ko wallahi zata san matakin da zata d'auka, bazata zauna yara y'an cikinta suna raina ta ba wallahi bac........ Abba ne ya katse ma Hajiya maganar zucin data keyi.
Ta kallesa cike da damuwar rashin lafiyar dake damun Salma ta ce "Abban yara, Salma ce ciwon nan nata ya tashi, shine nake so ka bamu key d'in motarka Ahmed ya mik'a mu asibiti"
"Wato danta ji anyi maganar karatu shine zata wani ce ciwonta na Sikila ya tashi kenan?".
Kallon tak'aici Hajiya tabi Abba dashi kamin ta ce "ban gane miye kake nufi ba?. Ciwon y'arka ya tashi wadda kasan tana d'auke dashi, kuma dama akai-akai yake tashi zaka ce kuma wai danta ji ana maganar karatu zata ce bata da lafiya, kana nufin k'arya take kenan?".
"Ni bance ba, amma ta sani ko mutuwa zatai sai tayi karatu. Domin ita yanzu wannan ciwon da take fama dashi duk wadda zai aureta sai an sanar dashi, ba kowa ne zai iya auranta da ciwon nan ba".
Wani dogon salati Hajiya taja tana kallon Abba. Ita yanzu abunshi ya daina bata mamaki sai dai tsoro. Kwata-kwata an gama dashi duk Y'ay'anta bai damu da damuwarsu ba, sai dai Y'ay'an kishiyata Hajara. Ahhh lallai Hajara ta dace Bokaye, yo idan ba aikin Boka ba ko Mlm tasan haka nan dai kawai Uba ba zai k'i Y'ay'ansa har haka ba.
Shuru kawai Hajiya tayi tama kasa magana kwata-kwata. Ganin haka Abba ya mik'a mata key d'in motar kawai yana niyar tashi ya fice yabar mata d'akin. Da sauri Hajiya ta ce "baka bada kud'in magani, da za'a sai mata ba. Domin duk magungunan da take sha sun k'are gaskiya"
Dubu biyar ya mik'o ya bata. Amsa tayi tana bin kud'in da kallo kamin ta dawo da kallonta garesa ta ce "haba Abban yara, yanzu wa'innan kud'in miye zasu siya a cikin maganganun Salma?. Kasanfa magungunan data ke sha masu d'an tsada ne, saboda lafiyarta fa ake saya, wannan kud'in ai ko ganin likita da siyan kati bazasu isa ba bare ace ajega magani"
"Toni dai iya abunda nake dashi kenan"
"Amma naga kaba Khadija kud'i masu yawa, saboda ita boko zata ko?, ita koma Salma ta mutu kenan kake nufi?".
Ganin tana son sashi b'acin rai yasa ya idasa ficewa daga d'akin ya barta tsaye sake da baki.
Hajiya dake jin wani abo ya tokare mata mak'oshi, kwafa tayi kawai ta fice daga d'akin itama.
Tana shiga b'angaranta ta iske Ahmed rik'e da Salma. Da sauri Ahmed ya amshi key d'in yana kallon yanayin Hajiya fuskarta kamar akwai b'acin rai ya ce "yanzu haka Abba ya b'ata miki rai ko Hajiya?".
"Hmm Ahmad ai kasan duk sadda ciwon nan na Salma zai tashi to irin haka saita faru tsakani na da Mahaifinku".
"Kiyi hakuri Hajiya insha Allahu wata rana komai zai wuce. Nima yanzu nake shigowa na iske Salmar bata jin dad'i shine take gaya min kinje wajan Abba ya bada mota zan kaiku asibiti".
Hijabi Hajiya tasa tana amsar Salma daga hannun Ahmad ta ce "eh muje ko mun samu ganin likitan".
Suna tafiya