Showing 21001 words to 24000 words out of 29550 words

Chapter 8 - A JININSA YAKE PDF BOOK 3 End COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt

06 Dec 2024

2074

fadi ba hujja
bace."

Ya bata tausayi kwarai, amma gaskiya ba za ta
iya aure yanzu ba, shi yasa haka suka tashi hirar
babu fahimtar juna, kowannan su ya koma cike
da tunani.Musamman Ibrahim da yake ganin
Nusaiba na son ta yi wasa da rayuwarsa, bayan
ya lashi takobin wannan karon, sai ya ga abinda
zai ture wa buzu nadi."

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Abubuwa da dama suke damun Nusaiba, ta kan
ji kamar ta tsero ta bar k'asar, domin Injiniya da
Antina sun tasa ta gaba, akan zancan Ibrahim,
kamar yadda shi kan sa ya addabe ta da
zuwa.

A hak'ik'anin gaskiya tana tunanin Istaharar ta,
kuma tana aji a jikin ta akwai maganar da Naseer
yake son gaya mata, dama ce kai bata ba shi
ba.

A wannan gwagwarmayar suka shafe shekarar
har ta yaye Ameer, yana neman wata 6 da
yaye.

Ibrahim bai hakura ba, ita kuma bata sakar masa
ba.

Anti kam har ta yi fushi ta daina yi mata
magana, kamar yadda Injiniya ya sa ido, abinda
ya sa a ransa shine wata kila Ibrahim din ne bata
so.

Shi kuwa Ibrahim har su Husna ya kwaso ya
kawo mata tabbacin cewa Sakina ta sani
kenan.

Wannan bai dami Nusaiba ba, domin bata san
irin bala in da ya sha a gida ba, akan hakan.
>
Ta fara riga ta ga duniya, babu wata yaudar da
Da namiji zai nuna mata.

Idan gaskiya ne, ya ce zai kai ta gun Sakinar
mana?

Bai ta6a gigi ba, sai dai ya kwaso mata su
Husna.

Kwatsam! Sai ga Alh. Basheer a Jordan, ba zato
ba tsammani. Kai murna a wajen Nusaiba, kamar
ta zuba ruka k'asa ta sha.Tana kewar sa sosai,
tunda ya zo take like da shi.

Shi kuwa Ameer ke zuciyar sa, ji yake kamar in
zai koma ya wuce da shi, ya zauna gidan sa.
>
Yaron yayi saurin girma kamar ba dan shekara 2
da watanni ba.

Suna zaune dare ya fara yi ga Injiniya ga
Antinta.

"Alhaji ya tambaya,"Wai 'yar gidan ta ku bata
fidda wani ba? Jin haka yasa Nusaiba ta tashi ta
bar falon.

Injiniya ya ce,"Ai mu Nusaiba ba mu san inda ta
dosa ba."

Kamar yaya?

Ya ce,"Wani yaro ke son ta kamar zai yi
hauka,

amma ba ka ga yadda take wahalar da shi
ba.

Ni Wallahi tausayi yake ba ni.

Yana da mata da 'ya'ya'yen sa 3.

Ibrahim sunansa, yana aiki da (Nijeriyan Embasy)
, yaro mai hankali, amma ta ki ba shi goyon
baya."

Ya ce,"Ibrahim?

Ni kuwa kamar na san sunan nan?

Anya kuwa ba yaron nan ba ne daya so auran ta
da?

Fatima ta ce,"Oho,"Nusaiba wani bayani za ta
zauna ta yi.

Yarinya da ka fara magana, sai kuka.

Ni dai yara suke gaya min wai a (Super market)
suka hadu, amma sun ga kamar dama can ya
san ta.

Ya ce,"Lalai Ibrahim din da na ke magana
ne.

Kuma da akwai alamun tana son sa, ni ne na
cusa mata Zancen Naseer.

To me yasa yanzu ba za ta aure shi ba?

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



----------------------------------------------------------------------------------------------






Zaharaddeen shomar
Whatsapp 08168575100








Ajinisa Yake3-05
Posted by ANaM Dorayi on 11:43 AM, 25-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Ta ce,"Ba zai wuce wannan yaron da ta
kwallafawa rai ba.
Ta shaku da Ameer ko alama bata son a raba su.
Ameer kuwa dole ya koma gidan ubansa, sanin
kan ta ne ba zai kyale mata shi ba.
Alh. Basheer yayi shiru, Injiniya ke fadin,"Nusaiba
manya,
abubuwanta dariya suke ban, na ga yadda za'ayi
wannan al'amari."
Alh. Ya ce,"Ku kyale ta, zan yi maganin
abin."Suka saki wannan shafin, suka kama wani,
dare yayi Alhj ya tafi masaukin sa.
Yana tunani tare ba tare da yayi wa Nusaiba
maganar Ibrham ba.
Koda dama bisa hanya yake, harkokinsa ne, suka
kawo shi, hanya ta ratso da shi nan.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Yana zaune cikin ofis a gida Nijeriya, misalin 11
rana.
Naseer yayi sallama ya shigo.
Ya amsa,"Lafiya lau.
Ya jikin na Zarah?
Ya ce,"An gode Allah.
Wannan karon dai Likita ya ce dole ta huta daga
wannan, saboda mahaifar ta ta yi rauni da
yawa.
Ya dan kada kai,"Ayya, gaskiya ya kamata ta
huta, saboda lafiyar ta, ayi hakuri da abinda
Allah ya kaddaro."
Ya ce,"Haka ne.
Dama tun jiya na zo in nuna maka Result.
Ya fito na kammala Diploma." Ya washe
baki,"Ah!
Lallai abin ba wuya a wurin Allah."
Yasa hannu ya kar6i takardu, ya duba,"Kai!
First class!
Gaskiya takardun sun yi kyau.
Yana 'yar dariya ya shafi keya, ya ce,"Sun ba ni
(Adimission ABU), Direct.
Next month za'a fara Rigistireshon.
Alhj ya miko masa hannu,"Congrat! Kai na ji
dadi., Allah ya bada sa'a."
Amin."
Ya fadi bakin sa ya ki rufuwa, ganin yadda Alhj
ke murna.
Ya mike yana fadin,"Zan koma Abba, na gaishe
ka."
Ya ce,"To na gode.
Zan tura ma da sako(Acconut) din ka, ba yawa,
sai ayi Rijistireshon ko?
Ya tsugunna yayi godiya.Alhjn ya jawo dirowa,
ya dauko farar ambulan ya mika masa,"Wannan
ma sakon ka ne."
Cikin mamaki yasa hannu ya kar6a ya kara
godiya ya fice.
Yana shiga mota da rawar jiki, ya buda
ambulan, don ganin me ke cikin su? Wasu
zaradan hotunan Ameer, ya rinka zarowa daya
bayan daya guda 24 kala-kala. Wasu tun yana
dan wata 4 a zaune, wasu yana rarrafe, da
yawa a tsaye yake.
Ya zura wa hotuna ido, kamar ya sume, saboda
doki da farin ciki.
Ya sumbata, ya rungume ya ma rasa inda zai
aje su.
Take nan ya kira wayar Zarah,"Kin ga yadda
Ameer dina yayi girma?
Ta ce,"A ina ka gan shi?
Hotunansa Abba ya zo min da shu, sai kin ga
yaron Zarah, kamar dan larabawa."
Ta ce,"Ka na ta sa min rai, yayana ka kawo min
in gani mana."
Ya ce,"Ki jira, yanzu zan baro Kaduna."
Ta ce,"Allah ya tsare."
Ya ce,"Amin.
Ya kashe waya.
Ya bi hoton hannun sa da kallo, can ya sauke
numfashi, ya sake sumbatar sa, sannan yayi wa
mota key, ya ya wuce.
Yana isa Zariya. Su Umma ya fara kai wa
hotuna suka gani.
Umma ta dauki daya.
Ya kai wa Inna ita ma ta za6i na ta.
Daga nan ya cilla Shika ya kai wa Zarah.
Wai ta ga hotuna kamar ta dauko Ameer yayi
motsi a gaban su.
Nan ya bar mata 2.
Fitowar sa asibiti a hanya ya shiga shagon sai da
(Gift) da (Frem) na sa Hotuna ya siyo kanana
guda 24.
Gaba daya hotunan sai da ya sa su cikin frem
har da na wajen su Umma da Inna.
Sageer an ba shi.
Yakubu ma, ya samu har da dakin Hajiyar
sa.Naseer B ma ya ce yana so a ba shi. Naseer
kamar zai hauka ce, saboda son Ameer. Bayan
kwana 2 daya koma Kaduna. Haka ya ga hoton
bisa tebur din Alhj gaba dayan firem din mai
kyan gaske.
Ba k'aramin dadi ya ji ba.
Shi yasa ya k'ara kaimi wajen addu'ar sa.
Allah ya dai-daita auran sa da Nusaibansa.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sati 3 tsakani, cikin Zarah ya k'i zama, wannan
karon ko wata 7 bai kai ba, watan sa 6. Dole aka
bi shawarar Likitan nan take aka juya mata
mahaifa, don ta huta da wahala, domin ba
k'aramar wuya take ci ba kafin ta haihu, ban da
jinin da take zubdawa.
Yaya za ta yi?
Haka Allah ya kaddaro.
Ubangiji yasa kaffara ce. Bayan ta gagije, lafiya
ta zauna mata sai Naseer ya neman mata F.C.E.
Ta samu a saukake, shi ya gama mata komai ta
fara karatu.
English/Islamic.
Asabar da lahadi ya fita da ita koyon mota, tun
tana tsoro har ta kware.
Cikin sati na 3, ita ke kai kan ta makaranta. Shi
ke nan ya sakar mata (Honda Civic) din sa.
Shi yana amfani da Jeep kawai.
Kasancewar Sageer zai tafi sabis din sa bana, sai
shagon dinkin sa yayi rauni. Ba sosai yake zama
ba, su Abbas ne kula masa da shi.
Idan ya taso makaranta yake zama ko ranakun
da babu karatu.
Kusan ace hankalin Naseer kwance yake, amma
Allah kadai yasan abinda ke damunsa a
dangane da son dawowa da Nusaiba gidan
sa.Ba shi da bakin magana ne kawai, ko kuma
mu ce babu wanda zai kai wa kukan sa balle a
share masa hawaye. Shi yasa wani lokacin za ka
gan shi a rame, wani lokacin kuma babu laifi.
Bayan wata 2 da dawowar Alh. Basheer Jordan
yana ta binciken halin da Nusaiba suke ciki da
Ibrahim.
Babu wani sauyi, kodayaushe nuna masa take
ba za ta aure shi ba, shine dai ya k'i hak'ura.
Jin haka yasa Alh.Basheer ya ce maza-maza ta
dawo gida Nijeriya ta yi aure anan.
Ta shiga shirin kaya, cikin bak'in ciki da 6acin rai
har ta rink'a jin kamar ta cewa Ibrahim ya fito,
don ta san tabbas Ibrahim na tsananin sonta.
Amma da ta tuna abinda Sakina ta yi mata a
filin jirgi, sai ta yi turus!
A tunanin ta da kyar Sakina za ta bar ta sakewa
gidan Ibrahim.
Saboda haka ta watsar da maganar Ibrahim, ta
ci gaba da shirinta ko gaya masa bata yi ba.
Ana gobe za ta dawo.
Alh. Basheer ya kira Naseer ya same shi a ofis.
Yana zaune, yayi shiru yana jiran ya ji dalilin
kiransa.
Alhj ya dan gyara fuska ya ce,"Gobe Nusaiba za
ta dawo maka da Ameer, saboda ta sami miji za
ta yi aure.
Shine nace zan gaya maka, idan sun iso, ka zo
ka kar6i abin ka, ka sa shi makaranta, tunda da
bakin sa.
K'iris ya rage ba'a zare ran Naseer ba, daga
inda yake zaune, domin ilahirin kwakwalwarsa
sa ta daina aiki.Yayi zugudun, kai sunkuye, bai
motsa ba, balle ya ce wani abu.
Alh. Basheer ya zura masa ido, jim kafin ya sake
fadin.
"Ka na iya tafiya, dama shi kenan sak'on, da
zarar sun iso, zan kira ka a waya."
Ya dago ya dube shi, ido cike da kwalla, sun
kada jajur, bakin sa dauke da magana, sai dai
ya kasa furtawa, sai ya ce to kawai.
Da kyar ya mike ya nufi kofa.
Alhj ya bi shi da kallo.
Goge hawaye yake da bayan hannu.
Yasa kofa zai buda. Alhajin ya kira shi.
Ya waigo a gigice, yana amsawa.
Yayi jim kafin ya ce,"Don Allah ka gaida min
Malama Balarabe da kyau."
Ya hadiye miyau, ya ce,"Zai ji Insha-Allahu."
Ya buda, kofa ya fice.
Ya shigo gida karfe 7 na magariba.
Kwanciya yayi a dakin sa ya rasa abinda ke
masa dadi a duniya.
Zarah ta yi tambayar duniya, ya kyale ta.
Ta yi mita har ta gaji, bata samu wata amsa ba,
duk ranta yayi mata k'unci.
Cikin dare ta farka, ba shi cikin dakin."
Ta fito ta biyo shi, yana falo zaune cikin duhu,
sai da ta kunna fitila sannan ta gan shi.
Ta matsa gaban sa ta ce,"Ikon Allah, watau
yayana she akwai wani lokaci da zai zo, wanda
ba dole ba ne in san me ke damunka? Gaskiya
ne..............
Ya katse ta,"Zarah ba wata magana bace. Ameer
ne za'a dawo min da shi. Nusaiba za ta yi
aure."
Ta numfasa ta koma dirshan ta zauna kafin ta
ce,"Amma yaya ka na da abin mamaki.
Nusaiba za ta yi aure, ba dole ta dawo maka da
danka ba?
Menene abin damuwa a nan? Yayi mata wani
mugun kallon da bai ta6a yi mata irin sa ba, ya
ce
"Babu!
Rok'ona gun ki shi ne ki koma ki sha barcin ki.
Please and Please!Ta bi shi da kallo, bata ma
san me ke bata mamaki ba.
Ta buda baki za ta yi magana, ya kwarara mata
tsawa,"Ki tashi na ce ko? Ban son jin komai
nace!
Idanuwanta suka cika da hawaye, ta tashi da
gudu ta nufi.
Sashin ta kuka kala-kala ta rink'a yi, kamar
yadda tunanin ta yake kala-kala. Lallai son
Nusaiba ya zauna masa, ko kuwa don yana
ganin ita bata aje masa da ba ne, shi yasa ya
fara yi mata kwakwazo?
To ai daga Allah ne, kuma bata bakin cikin
soyayyar sa da Nusaiba.
Me yasa zai juya mata baya yau? Kafin safiya,
idanuwanta sun kunbura.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Naseer na kallon ta, tana shirin tafiya
makaranta. Ransa ya k'ara 6aci. Tana ta wanke-
wanke a kicin ya biyo ta, bayan ta ya rungume,
ya sumbace ta, ya rada mata,"I'm sorry.
Jini na ne ya hau, kar ki yi fushi da ni sweet
Zarah."
Ta runtse ido, hawaye suka zubo, ya juyo ta ya
share su."
Ya isa haka, ai ya wuce ko? La66anta na rawa
ta ce,"Yayana ba na bakin ciki. Ko ka fara son
Nusaiba, kuma ina maku murna idan da za'a ce
gidan nan za ta dawo.
Amma menene na yi min ihu saboda na fadi
gaskiya? Saboda ban aje maka da ba ko?
Nan da nan idanuwan sa suka kada,"Kin san
abinda ki ke fadi kuwa Zarah? Kin maida ni jahili
kenan, ban san Allah ba? Ya juya mata baya,
ban ta6a zaton wannan maganar ba daga gare
ki Zarah."Take nan ta amsa laifinta, sai dai ka
fin ta mik'a hannu, ta kamo na sa, yayi waje ya
bar kicin din. Tana kokarin biyo shi, ta ji tashin
motar sa. Tana fitowa wajen Mai gadi na rufe
get, ya riga ya fice.
Ta koma falo ta zauna, tana mai nadamar
furucin ta.
Daga ita har Naseer babu wanda ya fahimci
karatun ranar. Shi kam Naseer caji 2 ke kan sa,
shi yasa ya kashe wayayinsa, baya son magana
da kowa.
Bai dawo gida ba sai bayan issha, yana shigowa
falo, ya ji ta a jikinsa, kiris ya rage ta kada shi.
Mafarin daya rike ta sosai kenan.
Ta ce,"Yayana na tuba. Allah na tuba ba zan
sake ba."
Yayi ajiyar zuciya mai karfi, ya kamo hannunta,
suka zauna.
Ya dube ta ya ce,"Magana makamanciyar
wannan kar ki sake min ita, idan ki na son farin
ciki na a duniya."
Ta kama kunuwanta 2, ta ce,"Ba zan sake ba
yayana."
Ya jawo kafadar ta, ta kwanto masa,"Ya wuce,
shi kenan."
Ta ce,"To yaya su Nusaiba, sun iso?
Ya ce,"Ni wayoyina ma kulle suke tun safe, ba
na son ya kira ni, so ban san halin da suke ciki
ba."
Ta ce,"Hakuri za ka yi yayana, su gani suke har
yanzu ba ka son ta ne."
Yayi shiru ya rasa me zai ce?
Ta dan dube shi.
"Zo mu ci abinci ko?
Ya ja hancin ta, ya ce,"Sure."
Suka tashi suka nufi tebur don cin abinci."A dai-
dai wannan lokaci Alh.Basheer da Nusaiba tare
da Ameer suka shigo gida.
Alhj ya dauko su daga filin jirgi.
Ummi ta tar6e su, murna kamar su lashe juna.
Duk da Ameer bai santa ba, ya saki jikinsa da
ita sosai.
Da yake shi ba mai bakunta ba ne.
Bayan sun ci abinci, an yi masa wanka yai barci,
ita ma ta kintsa, ta tafi kiran Abbanta, yana
falonsa kwance labarai yake kallo.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Tana shigowa ya tashi zaune yana fadin,"Zo nan
'yar albarka."
Tana murmushi ta zo gun sa ta zauna.
Ya ce,"Yauwa.
Magana za mu yi.
Kin tuna alkawarin da ki kai min a asibiti?
Ta dube shi,"Wane alkawari Abba?
Ya ce,"Lokacin da rigamar auran ki da Naseer ta
taso.
Ina ganin laifina ne, amma ki ka ce a'a, kuma
ko nan gaba na sake za6a miki wani mijin, za ki
aure shi.
Kin tuna?
Ta kada kai, ta ce,"Na tuna Abba."
To za ki iya ciki min shi?
Ta dan yi shiru, kafin ta ce,"Zan cika Abba na,
umurnin ka kawai na ke jira."
Ya rungumo kafadar ta ya ce,"Allah yayi miki
albarka.
Kafin nan na riga na gaya wa Naseer za ki dawo
masa da Ameer.
So kafin ya zo, ki tsaya ki duba wannan
takardar, wasika ce daga mijin da na sami miki."
Ina fatan za ki aje hankalin ki waje daya."
Ya sa hannu kasan filon kujera ya dauko
amblun, ya mika mata ta amsa jiki ba kwari.
Tashi ki je ki karanta, ki yi nazari akai, kafin
Allah ya kai mu gobe inji ta bakin ki."
Ta mike ta wuce babu wani ishashen kuzari a
jikinta.
Ameer ta tsurawa ido, ta fashe da kuka.
Shi ke nan za'a raba ta da shi.
Rayuwa kenan, abinda ya kamata ita da
Babansa su ba shi tarbiyar da ta tace
Hakan ba zai samu ba ko? Ta tambayi kanta,
gocewa ta sake yi da kuka.
Can wata zuciya ta ce,"Ba ga Antin ki ba? Ai za
ta iya rike miki shi tsakani da Allah. Ta goge
hawaye, ta ce,"Haka ne. Na san Antina za ta
iya."
Ta ci gaba da share hawayen, tana ajiyar zuciya.
Ta dauko ambulan din dake gefe ta jujjuya ta,
sannan ta farke ta, ta warware ta fara
karantawa, "Gaisuwa irin ta addinin Islama.
Kafin na ce dake komai, ina mai neman gafarar
tarin laifin da na yi miki. Da ace ki na cikin
hankalin ki a lokacin da na ke tare da ke a
asibiti. Da kin tabbatar da cewa na tuba, na
kuma fad'a cikin kaunar ki, son ki ya kama ni, a
lokacin da zaman mu tare ya zo k'arshe. SAKI
DAYA na yi miki ya ke ma'abociyar hakuri.
Amma ki sani, a duk bagun numfashin da zuciya
ta za ta yi a duniya, tare da bikon soyayyarki.
Da ace zan sake samun wata dama ta auran ki,
na yi rantsuwa da wanda ya halicce ni, zan
nuna miki za6i na gari Abba yayi miki. A karshe
ina addu'ar Allah ya raya mana Ameer, rayuwa
mai kyau cikin addinin musulunci. Mai son
kiNaseer Iliyas Balarabe!
Bata gaskanta idon ta ba, balle ta yarda da
abinda ta gani a rubuce. Ta sake maimaitawa.
Ta tsaya kasake tana sauke Numfashi. Me ke
cikin ranta wanda bata tantance shi ba? Kamar
farin ciki ne ya kamata, to me yasa hawaye ke
neman kubcewa?
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Gaba daya ta kidime. Ta sake duba takardar
bisa sunan mai ita Naseer Iliyas Balarabe! Ta
cicci6o Ameer ta rungume shi tana fadin,"Tare
za mu koma gidan Babanka! Allah na yafe
masa! Da kyar ta sami barcin kirki. Da safe ta
tafi gaida Alhjn, tun daga fuskarta ya shaida
tana cikin walwala, ba kamar dawowar ta jiya
ba. Bayan sun gaisa, ya ce,"Kin ga sak'on? Ta
amsa da kai, tana d'an murmushi. Ya dan dago
habarta, ya ce,"To yaya? Ya fito bazawarin? Ta
fado jikin sa ta kudundune fuska,"Kai Abba! Ya
fasje da dariya,"Shi ke nan, na bari, to tashi ki
ji." Ta mike ya ce,"Na san anjima zai zo, sai da
ba shi da labarin komai, illa Ameer da zai
dauka. Za'a ci kwalliya ko? Ta tashi da gudu, ta
bar dakin. Ya kama dariya yana kwanciya bisa
kujera,"Bebin Abba kenan 'yar albarka.," Karfe 9
da rabi Naseer ya iso gidan su, don gaida iyayen
sa kamar yadda ya saba duk ranar asabar da
lahadi. Yana shigowa. Malam Balarabe ya hau
fada,"Kai menene dalilin kulle wayoyin ka.
Alh.Basheer na ta neman ka tun jiya, bai same
ka ba? Ya ce,"Uhm.............Ba su da caji ne. Ya
ce,"Amma kai k'aryar ka ko hanyar masallaci
bata sani ba Idan babu Nepa, ba akwai jenareto
ba? Yayi shiru." Watau abin zai dawo ko? Da
sauri ya ce,"A'a Abba! Ya ce,"To mike maza!
Yana neman ka." Ya mike yana fadin,"Sai na
dawo. "Umma ce kadai ta amsa mashi. Ya wuce
babu kuzari.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sha daya yana ofis din Alhj ko zama bai yi ba,
yace ya ke can gida ya dauke shi, an riga an
gama kimtsa kayansa. Tafe yake kawai, amma
ko alama baya son ganin Nusaiba, kar kwadayin
dawo da ita ya taso masa. A haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login