Showing 9001 words to 12000 words out of 29550 words

Chapter 4 - A JININSA YAKE PDF BOOK 3 End COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt

06 Dec 2024

2078

din ne? Je ka
dawo ina jira. Ungo key din mota don ka yi sauri.
Ya kar6a ya fito a sukwane, ya fada mota, yayi
gidan su Naseer. Yayi sallama falon Abba, a
lokacin Umma tana goya Ameer ta fito ta siyo
masa madarar jarirai, bayan ta nemi Zarah ta
rasa a cikin gidan, don bar mata ajiyar yaron
kafin ta dawo. Shi yasa zuciyan Abba ke kara
tafarfasa, ya sani babu makawa ita ma tafiyar ta
ta yi. Da kyar ya amsa sallamar Sageer. Ya shigo
a darare, ya nemi gefe ya makure, ya ce,"Sannu
Abba." Ya ce,"Me aka yi Sageer? Ya ce,"Abba
Naseer ne................Ya dakatar da shi da
hannun sa kafin ya ce,"Tashi ka tafi! Sannan idan
ka je, ka gaya masa ita ma wacce yake son ta tafi
abinta, saboda haka ya zo ya kwashe kayan sa,
ta bar min gidana in huta." Ya tashi ya durk'usa
Abba................Ya runtse idanuwansa,"Sageer ina
ganin mutuncinka, don Allah, don son Annabi ka
tashi ka tafi. In dai akan maganar abokinka ne,
na riga na datse magana, na yi rantsuwa Naseer
ba zai sake sani kaffara ba. Saboda haka ka je ka
gaya masa, shi 'yantacce ne, kar ya dami kan sa.
Tashi, kanzil ban ka kara fadi ba, idan har ni ina
isa in gaya maka. Idan kuma ban isa ba, to
kacigaba da zama. Sageer ya shiga 3, Abba ya
daddaure shi, ga magana bakin sa babu damar
fadi, yana ji, yana gani, ya tashi ya fice. Yayi
tsaye jikin mota ya rasa tudun dafawa. Ga wata
sabuwa, kuma ita ma Zarah ta yi gaba. Duk da
dai yana ganin na ta mai sauke ni, amma ba
dadi ace ita ma tana gidan su.Ya fi minti 5r a
tsaye, sannan ya bude mota zai shiga. Ya hango
Umma tafe. Ya tar6e yana mata sannu da Zuwa.
Ta amsa za ta wuce cikin gida, ya ce,"Umma ku
taimaki ni Naseer na cikin wani hali, komai za iya
faruwa da shi. Ta ce,"Shine me? Sai aka ce
karshen Umma ya zo? Ya ce,"Ba haka ba ne
Umma. Wallahi Naseer yayi nadama, tun ranar
da ta sami kan ta cikin wannan yanayin, kuma ba
shi da wani buri daya wuce idan ta ji sauki, ya
bata hkr akan abinda yayi mata. Sai kuma aka
sami akasi, komai ya yamutse. Ta yi dan
murmushin takaici ta ce,"Yaro man kaza. To
yanzu da ka zo nan ka na ta dogon bayani, akwai
Nusaiba a nan ne? Tana fa Kaduna, a gaban Ka
Babanta ya dauke ta. Ba sai ya je can ba, ya roke
ta. Menene abin zafi? Ya durk'usa bisa guiwa, ya
ce,"Ku yi wa girman Allah Umma ku yafe masa,
ke ma kin san duk abinda ki ka fadi, ba zai yuwa
ba. Sai da goyon bayan ku." Yana sa aya Abba na
tsayawa kofar zauran, bai ce wa Umma komai
ba, ta wuce cikin gida. Shi ma ya bi bayan ta.
Sageer ya sauke numfashi, ya tashi ya fito ya
tafi.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Yana shiga shagon zama kawai yayi, ganin haka
Naseer din ma yayi shiru, ya san babu nasara.
Sun dau minti goma a haka, kafin Sageer ya
ce,"Wai Zara ma ta tafi gidan su."Ya dube shi da
sauri." Me na yimata ita kuma? Kashe ni suke so
su yi ko? Shi kenan." Ya goge kwalla. Wayar sa ta
hau bugawa, da kyar ya dauka. Yakubu ne ke
kiran sa. Ya rasa ta yadda zai yi ya dauka. Ya
dubi Sageer, ya ce,"Zo mu je gidan Yakubu." Ya
tashi suka tafi. Ya maida masa bayanin komai.
Yakubu yayi masa fada kamar zai ari baki, shi
kansa ba karamar kunya ya ji ba lokacin da Alhj
ya kira wayarsa, yana gaya masa Naseer ya ci
amanarsa. Duk da haka yayi masa alkawarin
shiga maganar, sai inda karfin sa ya kare. Shi
kuwa Naseer B ana maganar, yana kallon kowa a
dage, zuciyar sa gwanin haske, har yana addu'ar
kada Allah yasa su shirya. Amma bisa fuskar sa,
ya fi kowa nuna damuwa kamar yayi kuka. Daga
gidan Yakubu, wajen Zarah suka iso, misalin
karfe 1 na rana. Sun shigo gidan. Inna na kwashe
abinci cikin kula. Ta daga ido ta dube su, tana
amsa sallamar su. Gaban ta ya yanke ya fadi,
ganin yadda Naseer yayi wanu duhu lokaci guda.
Ta ce,"Dan Inna! An gaishe ka da aiki. Ku shiga
gani nan zuwa." Ya wuce simi-simi. Sageer ya bi
bayan sa, suna zaune. Inna ta gama abinda take
yi a kicin, ta bi su dakin. Zarah ta leko daga bayi
ta ga Inna, ta shige sai ta sadado ta aje buta, ta
suri hijabin Inna dake shanye bisa igiya ta yi waje
ta bar unguwar. "Sannu dan Inna, ka sha aiki
Wallahi, ya gajiya? , Ya sunkuyar da kai Sageer ya
ce,"Inna kuskure ne, kin kuma san ajizanci irin na
Dan-adam. Amma a yau ya gane, har ya
tuba........ Ta katse shi, tuban mazuru? Sau nawa
Naseer ke cewa ya tuba a gidan na ma kawai,
wanda na sani? Ai ba zan iya fadi ba. Yanzu wa
gari ya waya? Babu abinda ba mu gaya maka ba
D'an Inna, tun kafin ayi auran nan. Bayan anyi
kuma, ba mu fasa ba, sai dai in kafar ka bata
shigo da kai gidan nan ba, amma ba ka ji. A
fuska lafiya lau ka ke, halin ne kawai ka kasa
gyara shi, su yi dai-dai da fuskar ka. Me yasa? A
yanzu wa ka ke ganin zai iya tunkar Alhj? Babu
abinda za mu iya gaya masa, ya yarda, saboda
ka riga ka rushe ginin tun ranar zane. Naseer ya
ce,"To Inna shi kenan, haka za'a sa ido, auran ya
kare kenan? Ta ce, "Eh mana, ta riga ta gayawa
Babanta ba ka son ta, wa ka ke zaton zai je ya
ce, karya ne? Ya ce,"Gaskiya Inna ban yarda ba,
na san ana zuwa biko Inna. Sai dai in ba za ki je
min ba ne kawai

Ta yi dan murmushin dole ta ce,"Dan Inna
manya, ga laifi, ga saurin tuba. To shi kenan, ka
bari Baban na ku ya dawo, za mu san yadda za'a
yi." Ya numfasa ya ce,"Wai ita ma Zarah don ta
kara min hawan jini shine ta bar gida ko? Ina
take, sai ta ci dan banzan duka yau, in ni sa'an
ta ne, za ta gaya min." Dariya suke da Inna da
Sageer, kafin Inna ta ce,"Yanzu ta shiga bayi, za
ta yi alwala ta yi sallah." "Ina nan ina jiran ta ta
fito,." Inna ta mike,"Bari in kawo maku abinci
Sageer. To Inna. Sageer ya amsa. Ta fice,"Sageer
ya ce, "Na ciro maka wayar Rediyon can ne?, Me
zan yi da ita? Dukan mana harka mance? Tsaki
yayi ya dauke kai. Inna ta shigo da abinci ta
ce,"Ka fa ci. Sageer ka matsa ma sa ya ci. Ya
ce,"Ai zai ci Inna." Ta yi waje ta koma daki. Shiru-
shiru Zarah ta ki fitowa daga bayi. Inna ta fito da
wannan mamakin, tana tambayar kanta,"Ita
wannan zaman me take yi a bayi?" Tana sa aya,
ta aje ido bisa buta a gefe. Ta leko dakin ta
ce,"An gama dukan?" To ai ban ji kuka ba, bata
daku ba kenan." Suna dariya ya ce,"Ai bata shigo
ba Inna.." Ta gintse fara'a ya ce,"Ban gane ba?
Ga shi ta aje butar a waje. Ta juya ta fito tana
kwala mata kira, yayin da dukkansu suka aje
cokula suka fito. Kamar wasa, babu Zarah acikin
gidan. Mamaki ya ishi Inna. Ta kama baki, tana
kallon igiya babu hijabin da ta shanya. Sageer ya
ce,"Wai ita Zarah da gaske take yi? Inna tayi
shiru abin ya girmi shekarun ta. Naseer ya
numfasa ya ce,"Inna ki gaya mata, idan ta ji ina
asibiti kar ta sake ta zo guna. Zo mu je Sageer.
Ya yi waje. Sageer ya ce,"Inna ki ce Allah ya bata
hakuri. Sai anjima." Da kyar ta iya amsawa,"Allah
ya ba mu alkhairi." Shi ma ya wuce. Inna ta ja
kujera ta zauna, yau na ga zamani ni A'isha. Kiri-
kiri yarinya ta ban kunya? Suna tafe a mota
Sageer, ya ce,"Yanzu ina muka nufa? Ya
ce,"Gidan za ni, duk ayi ta ta kare, idan ma
yankana ni za su yi, su yanka. Ba shi kenan ba?
Idan kowa yayi min, ai bai kamata Zarah ta yi
min ba. Duk saboda wa na shiga wannan halin?
Ba saboda sonta ba ne? Duk ba ta ga hakan ba."
Ya furta. Sageer yayi shiru domin ya lura abokin
sa ya zare gaba daya, kar ya tofa wani abu, ya
kara masa zafi. Ya ci uban birki a kofar gidan, ya
fito yayi cikib gida, bai ko saurari Sageer ba. Sai
dai yana shigowa ciki ya tsinkayi Ameer na ta
tsala kuka. Nan da nan ya yi turus, guiwa sa ta
kwa6e, a salu6e yai sallama falon. Umma na
kokarin goya Ameer a lkcn Abba kuwa na zaune
gefe iya wuya yake. Kuma yana ji da kowa, duk
wanda ya kuskura yi masa wata magana akan
Naseer. Yana shigowa. Abba ya mike ya debi
takalman sa ya bar gidan. Naseer ya bi shi da
kallo, ya kasa cewa da shi komai, har Umma ta
gama goyon, ta sa hannu ta dauke gwangwanin
(Prisso-cream) din da ta siyo ta dora bisa firij, ta
dauki fidar ta yi waje. Ita ma ya bi ta da kallo,
sannan ya bi bayanta. Tana famfo tana wanke
fidar da soso da omo. Ya bi ta, ya tsaya a gefen
ta ya sanyaya murya,"Umma!Ji ta yi tamkar ya
watsa mata wuta. Ranta ya ci gaba da k'una
kamar ta rufe shi da dukan fitar hankali. Ya
durk'usa ya mika hannayen sa gaba gare ta.
Idanuwansa dauke da kwalla. "Umma, ki yi wa
girman Allah ki amsa min. Umma ki dube ni ki
saurari rokona. Na yi laifi Umma, amma tuni na
gane kuskure na, ku ba ni dama ta karshe
Umma. Da yardar Allah ba zan sake saba maku
ba, Umma ki taimake ni." Ta gama dauraye fida,
ta yarfe ruwan, ta juya ta koma daki tana
daddaure su yadda suke. Naseer ya nemi wuri
nan ya zanau dirshan! Sageer ya matso zai masa
magana, yayi sauri ya riga shi." Je ka gidan abin
ka Sageer. Na gode." Ya yi dan jim, yana kallon
sa,"Ka ta fi na ce, babu komai, sai mun hadu."
Ya numfasa ya ce,"Shi kenan, Allah shi kyauta."
Ya juya ya fice, ba tare da Naseer ya sake cewa
wani abu ba. Nan yayi ta zama har ya tuno, bai
yi sallah ba. Yayi alwala a nan famfon, ya wucce
sasan su, yayi Sallah a falo ya ci gaba da zama
nan bisa sallaya. Babu abinda zuciyarsa bata saka
masa ba. Zarah kuwa bata dowa ba, sai bayan
sallar la'asar, ba shakkar komai. Ta yi sallama ta
shigi ta wuce Inna a tsakar gida ta shigo daki.
Inna ta tafa hannu ta ce,"Da izinin wa ki ka bar
gidan nan? Ina kuma ki ka je? Kai tsaye ta
amsa,"Inna ai na gaya maku ba zan koma ba. Kin
zaci wasa na ke yi ko? Ta ce,"To ba kuwa zama a
gidan nan ba, bari baban na ki ya shigo. Na lura
so ki ke ki kawowa mutane raini. Ta juya ya bar
dakin. Zarah ta matsa inda kulolin abinci ke aje,
ta buda ta zuba ta hau ci. Karfe 5 M.Umar ya
shigo gida, Inna ta feshe shi. Ya jinjina kai ya
ce,"Wai Zarah da na sani ki ke fadi? Ta ce,"Ka na
wasi-wasi kenan? Shiga tana nan a daki." Tunda
ya baro dakinsa yake balbala masifa har cikin
dakin."Ki hada kayan ki, ki koma inda ki ka fito!
Ta ki motsi, M.Umar har da barazara duka,
amma ko alama Zarah bata motsa ba, sai sharar
kwalla take yi. M.Umar ya cika da al'ajabi, yana
haki, ya koma dakin sa. Inna ta yi zuru tana
kallon sabon salo. Fadi take cikin ranta,"Zarah ta
kangare." Haka kowa ya kwana a wannan dare.
Babu barcin kirki.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Washe gari bayan sallar asuba. Nusaiba ke zaune
bisa gado, tunani bisa tunani. Tun jiya take cikin
wannan yanayin. Musamman da ga Abbanta ba
shi cikin sukuni kuma tun isowarsu gida, babu
inda ya sake fita. Tashin hankalinta ya k'ara
tsananta, tun daga lkcn da ta ga nononta ya cika,
har ya fara tsiyayewa a banza. Bakin takaicin
dake cinta kenan, a halin yanzu bisa gado, ta
rasa inda za ta tsoma ran ta, ta ji sanyi sbd
tunanin dan kyakkyawan dan ta. Ta tabbata yana
can yana kukan neman nono, ga shi nan yana
zubewa a iska. Farkewa ta yi da kuka, sbd
tausayin rayuwar da Naseer ya je fasu ita fa dan
ta,. Ji ta yi an riko ta. Muryar Umminta ke
fadin,"Nusaiba! Daina kuka, ki yi hkr. Ta fado
jikin Ummi ta rungume ta. Ummi ta shafa kanta
ta ce,"Ki yi shiru na ce. Allah ne ya kaddaro miki
wannan al'amari. Yanzu dago fuskar ki ki ji. Ta
dago, Ummi ta sa hannu ta share mata hawaye,
kafin ta ce,"Abinda na ke so da ke Nusaiba, ki yi
hakuri mu je a dauko yaron nan.Bawan Allah ne
shi, bai da laifin komai. Sannan shayar da shi da
za ki yi, shine yake sanya shakuwar uwa da
danta, soyayya tare da jin kai.Ki sani Nusaiba
Ubangiji ne kadai ya san dubun ladan da uwa
take samu tun daga daukan ciki, haihuwa, raino
tare da bada tarbiya, ga 'ya'yan da Allah ya
bata,kar ki bari wannan gara6asar ta wuce ki
Nusaiba. Ki dauko dan ki ya shaku da ke, ya san
cewa ke ce mahaifiyar sa.

Ta yadda zai ji kan ki, a cikin zuciyar sa, idan
Allah ya raya shi. Na yiwa Abban ki magana, na
rarrashe shi, na kuma yi nasara, ya amince,
yanzu yardar ki na zo nema, domin ya ce shi ba
zai matsa miki ba, duk abinda ki ka za6a shi
za'ayi.

Shi kuma Naseer din muna nan muna jiran sa, ya
kawo miki takardar ki.

Yanzu me ki ka ce?

Ta goge kwallan da suka dararo mata, ta ce,"Ki je
ki dauko shi Ummi, babu komai."

Ta tallafo fuskarta ta ce,"Yayi kyau. Allah yayi
miki albarka.

Amma ki tashi ki shirya Direba zai kai mu, don ki
kintso kayan ku a natsa.

Tashi ki daina kuka, ba na son ki na damuwa, kin
kuma san Abbanki hankalin sa ba zai kwanta
ba.

Ta goge hawayenta sarai,. Umma ta kama ta ta
riko, ta raka ta hanyar bayi, sannan ta fice ita
ma, don shiryawa.

Abban ke kwance a falon sama bisa kujera, shi
kadai yake kallon silin yana lissafon halayyar Dan-
adam mai abin mamaki.

Nusaiba ta shigo cikin shirin tafiya.

Kamar mai ciwo yake kwance, bai motsa ba har
ta zo gun sa, yana kallon ta.

Ta tsugunna ta kwanto kanta jikinsa, ta yi
shiru.

Ya daka kanta ya ce,"Bebina, ki je ki dauko dan
ki, ki shayar da shi.

Allah zai ba ki lada, kin ji?Ta amsa da kai. Ya
ce,"Mike ku tafi, na ga Ummin ki ta gama
shiryawa.

Allah ya kiyaye hanya." Ta ce,"Amin Abba na." Ta
mike ta wuce ya bi ta da kalllo, ta kai kofa, ta
waigo suka hada ido, yayi dan murmushi yana
mata (bye-bye) da hannu.

Ita ma ta yi masa, sannan ta sauka, lkcn karfe
7:30am. Ummi ta matsa mata ta dan ci kayan
karin safe.

Karfe 8 Direba ya dauko su, suka damk'i
hanya.

Karfe 8 din dai-dai. Naseer ya shigo falon,
Umma, don gaishe su ko ba za su amsa masa
ba.

Umman kadai ke falon,

tana ta faman gyangyadi.

Da alama Ameer ya sami barci, domin cikin dare
yana ta jin kukan sa.

Bata kalle shi ba, ya durk'usa gaban ta, ya
ce,"Umma ina kwana?

Kamar za ta kyale shi, sai wata zuciya ta ce,
amsa.

Bata kalle shi ba ta ce, lafiya.

Farin ciki ya lullube shi, ya ce,"Na gode
Umma.."

Ta kyale shi.

Yayi dan jim yana kallonta, kafin ya ce,"Umma
ina Abba?

A fusace ta dube shi, ta yi masa tsawa,"Ga shi
nan a baya na a goye!

Tabatacce maras kunya.

Ka sake zuwa ka tambaye ni, ina Abba ya ke, sai
na ci mutuncin ka!

Yasa hannu ya dafa guiwoyinta ya ce,"Yi hakuRi
Ummana, ba zan sake ba.Dama Zarah ce ta ce
ba za ta dawo ba, sai Nusaiba ta dawo, shine
nace ko za ki sa baki ta yi hkr ta dawo kafin a
shawo kan Alhj?

Kai tsaye ta dube shi, tsakar ido ta ce,"Ban
zuwa." Kar mu yi haka dake Ummana. Wallahi na
yi nadamar abinda ya faru, ku sa ke ba ni dama
ku gani zan rike Nusaiba iya rayuwata.

Ta dube shi a dage ta ce,"Bakin alkami ya riga ya
bushe maka Naseer, domin jiya da daddare su
M.Umar da M.Lawar sun zo. Amma Abbanka ka
ya rantse, ya masu, babu ruwan sa a cikin
maganar ka.

Haka ni ma bai lamunce min ba.

Saboda haka ka makara, dabara kuma ta rage wa
mai shiga rijiya. Ina fatan ka gamsu. Yayi zuru
kafin, ya numfasa ya dube ta ido sun kawo
kwalla.

"Shi kenan Umma, na gode. Abinda na ke son ki
rokin min Abba, shine, don Allah yayi hkr, idan
na gaishe shi ya rinka amsawa. Ni zan fita, ga
wannan koda Ameer yana bukatar wani abu." Ya
ciro dubu 2, ya aje bisa hannun kujera ya tashi
ya fice.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~­
~~~~~~~~~~------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Karfe 9 ta gota kadan Jeep din su Hajiya Zulai ta
yi fakin kofar gidan su Naseer. Suka fito Ummi na
rike da hannun Nusaiba. Ummi ta yi sallama
tsakar gida. Umma ta amsa daga falo, a lkcn
kuwa ta kammala shirya Ameer tsaf!Yana ta
tashin kamshin hoda. Bata dauki murya sosai ba,
don haka ta ce,"Maraba, ku shigo mana." Ummi
ta yaye labule. Umma ta mike baki har
kunne,"Hajiya!

Ah!

Nusaiba!

Sannun ku da zuwa."

Suka zauna a kujera Umma ta mikawa Ummi
Ameer, ta karbe shi. Sai ta wuce firj za ta dauko
kayan sha.

"Dama kin bar shi, kin san safiya ce." Duk da
haka ta kawo da Jus din kananan kwali da kufuna
2.

Bayan sun gaisa, Umma ta tambayi Alhj? Sai
Ummi ta ci gaba da cewa,"Ba wani abu ya kawo
mu ba.

Ameer mu ka zo tafiya da shi, ya zauna wajen
uwar sa ta shayar da shi. Ko dama 6acin rai ne
yasa aka aje shi."

Kwalla suka cika idanuwan Umma ta ce,"Gaskiya
ne kuwa, na ji dadi, domin a gaba daya wannan
al'amari Ameer shine abin tausayi.

Shi kuma wancan sakaran, ai kyale shi ya gasu,
duk da cewar ya ce yayi nadama." Ummi ta yi
dan murmushi ta ce,"Ai ba'a soyayya dole, mu
ma mun san haka shi yasa Alhj ya ce a gaya
masa, tana jiran takardarta, ko zuwa jibi. Insha-
Allah za mu turo mota akwashe kayan ta a dauki
motar ta."

Umma ta goge kwalla ta ce,"Ba laifi, ki yi hkr
Nusaiba kin ji? Allah ya amfana miki dan ki. Ta
dan sadda kai ta ce,"Ba komai Umma.

Idan kuma na yi miki wani laifi, ki yafe min." Ta
girgiza kai,"Baba abinda ki ka yi min Nusaiba,
Allah yayi miki albarka."

Ta ce,"Amin." Ummi ta ce,"To bari mu je, za ta
debi wasu kayan kafin a zo kwashewa." Umma ta
ce,"To bari in kawo maku wani makullin, ya fita
da na hannun sa."Nusaiba ta ce,"Ina Antina
Umma?

Ta ce,"Ita ma ta tafi."

Suka dubi juna, kafin Ummi ta tambaya,"Saboda
me?------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login