Showing 6001 words to 9000 words out of 29550 words
Chapter 3 - A JININSA YAKE PDF BOOK 3 End COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt
zai yi, dole ya sa mata ido,
tayi ta kuka. Can kuma ta tashi ta fito koridon ta
zauna, bisa kujera. Shi ma ya biyo ta nan ya
zauna, yana gadin ta.
Jim kada ya ji kukan Ameer.
Ya mike ya ce da ita,"Ga Ameer can ya tashi, in
kawo shi ya sha? Ta kyale, bai ma ishe ta kallo
ba, ya shige ciki ya dauko shi, ya tsugunna
gabanta,"Yauwa, 'yar gidan Abbanta kenan, dubi
Bebin mu kuka yake yana jin yunwa, dan ba shi
ya sha." Ta dauke kai, tamkar bada ita yake
magana ba.
Abu fa ya gagara, dole ya dauko wa Ameer fida
ya tura masa, yayi ta tsotson ruwa da
glucose.
Kullum karfe 7 nan take masu. Alh.Basheer suna
nan zaune kuwa, sai ga su.
Naseer ne ya fara hango su, ya mike ya nufo
su.
Su ma tsayawa suka yi cak, ganin Nusaiba a
zaune wajen.
"Yaya dai? Alh.Basheer ya tambaye shi, yayin da
Ummi ta kar6i Ameer a hannun sa.
Ya ce,"Ai yau ko Ameer ta k'i ba shi nono.
Kuka kawai take yi,"Ya ce,"Likita ya zo?
Ya ce,"Ka tsaya nan, kai kuma koma gun ta, bari
in nemo Likitan." Ya koma wajen ta.
Alhj ya zaga ya wuce, ita kuwa Ummi ta
lafe.
Jimawa kadan suka dawo da Likita. Abin ya ba
Naseer mamaki daya ga Lkita ya zo, ya tsaya
gabanta bata zage shi ba.
Ya ce,"Nusaiba, tashi mu shiga ciki, mu yi wata
magana." Kai tsaye ta mike ta wuce. Naseer ya
saki baki, shi ma ya taso ya biyo su. Ta zauna
bakin gado, ya jawo kujera ya zauna ya
ce,"Kukan me ki ke yi?
Ta ce,"Antina ta mutu ko?Ya ce,"An gaya miki
bata mutu ba, Antin ki na gida." Ta runtse ido
wasu hawayen suka tsunke mata, ta sa hannu ta
share. Ya ce,"An ce kin ki ba Bebin ki nono,
saboda me? Haka za muyi da ke saboda Allah?
Ta dube shi da kyau ta ce,"Doctor ka yi min wani
taimako don Allah, lambar Abba na zan ba, ka
kira min shi." Idanuwan Naseer suka k'ara yo
waje, ya koma da baya da baya ya fito waje. Shi
kuwa Likita k'ara tsura mata ido, ya ce,"Abban
ki? Ta ce, eh. Ya ce,"Ina zuwa." Ya leka yayi kiran
Alhj da hannu. Ya taso daga inda yake zaune ya
zo. Likita ya kamo hannun sa, ya shigo da shi a
hankali. Kan ta na duke ya ce,"Wannan Abban
naki ki ke nema? Tana yo ido hudu da shi, ta
mike hawayenta suka yawaita, ta ce,"Abba! Wani
tsananin farin ciki ya kama Alhj, dole kwalla suka
cika idon sa, ya ce,"Bebin Abba! Ta rugo da gudu
ta rungume shi. Tuni Ummi ta fado dakin ta hade
su ta rungume, kuka suke saboda murna. Haka
Naseer ke sharar kwalla. Amma ya rasa abinda
zuciyar sa ke sakawa game da wannan al'amari.
Tabbas Nusaiba ta warke, to me zai biyo baya?
Da alamun zai shiga magana, yanayin da ta
nuna. Yayi ta maza ya shigo. Alhj Basheer ya
rungume shi, suna wa juna barka. Likita ya fita,
ya bar su cikin farin ciki da murna maras
misaltuwa.Bayan sun natsa. Ummi ta dubeta,
duk ta rame ta ce,"Sannu Nusaiba, Ubangiji Allah
ya k'ara karewa." Ta ce,"Amin. Ta miko mata
Bebi ta ce,"Kin ga Bebin da aka ciro miki? Ta dan
dube shi, tayi murmushi , ta dauke ido,"Na gan
shi Ummi ta. Kwalla suka taru fal a idonta, ta
kasa shanye su, sai da suka zubo. Abban ya
rungomu kafadunta, ya ce,"Yi hakuri daina kuka,
komai ya wuce Insha-Allah." Ya ce,"Allah ya
yarda Abba. Bari in yi sallah." Ta mike ta wuce
bayi ta jima bisa sallaya, tana yi wa Allah godiya
daya dawo mata da rayuwarta dai-dai. Ta dawo
gefen gado ta zauna kusa da Abban ta. Ya jawo
ta jikin sa, ta dan numfasa ta ce,"Abba lokaci yayi
da zan gaya maka wata magana, ina fatan za ka
gafarce ni." Naseer na jin haka, ya mike ya bar
dakin. Abba ya ce,"Babu komai Bebina, gaya min,
me ke da mun ki? Ummi ta sa masu ido tana
kallo. Ta k'ara gyara zama ta ce,"Na san za ka yi
mamaki, idan na gaya maka cewa tun aure na da
Naseer, babu kwanciyar hankali tsakani na da
shi. Ai kuwa Alh ya sha mamaki, ba shi da kadai
ba har Ummi da take zaune. Ya kara dubanta,
baki sake, ya tambaya, "Saboda me? Ta
ce,"Abinda na fahinta,"Abba, shine ya kar6i aure
na ne kawai don ka cika masa ido, ba zai iya ce
maka a'a ba. Amma a hakakin gaskiya Naseer
baya so na, kuma ya nuna min kiyayya, ba don
Antyna na tsaye ba, ina ganin wuyar da zan sha,
ba 'yar k'arama bace.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Shi yasa na ke son ta, domin tayi min komai,
kuma tayi iyakar kokarinta wajen jawo hankalinsa
zuwa gare ni, sai dai haka bata samu ba, saboda
babu sona a zuciyar sa." Ransa ya 6aci kwarai, ya
ce,"Me yasa tuntuni ba ki gaya min ba? Ta
ce,"Saboda kai ne Abba. Ba na son wani tashin
hankali ya shiga tsakanin ku. Kuma ina ganin ai
ya girmama ka ne, tunda ya kasa fitowa fili ya
nuna maka baya so na. Shi yasa na yi ta kokarin
zama da shi shekara daya da rabi, sai da Allah ya
kawo rabon wannan Yaron, sannan ya shiga daki
na. Daga baya na yi tunanin bai kamata mu
zauna muna cutar da juna ba, shi yana jin haushi
na, ni ma ina jin na shi. Sai na same shi a daran
da wannan abin zai faru, na yi masa magana.
Abba cewa yayi idan na k'ure shi, zai 6atacciya,
dole in koma gidan mu, har d'an baya so, ya bar
mana...................!!! Tana shiru. Ummi ta
cafe,"Ina, inda kuma yayi karya kenan. Ai ba mu
kai masa ke da Da ba." Alh.Basheer yayi shiru,
zuciyar sa na tafasa, abin kamar a mafarki yake
ganin sa, domin ko alama bai ta6a mafarkin
Naseer zai ci amanar sa haka ba. Ya dubi Ummi
ya ce,"Har hada mata kayan ta mu tafi." Ta mike
tana fadin,"Ashe ga damuwar da ta kusan hallaka
rayuwarki Nusaiba, kenan. Yayi wa kan sa. Kuma
sai Allah yayi miki sakayya." Nusaiba ta kada
kai,"Ba haka bane Ummi ta, ba laifin sa bane,
kar ki manta soyayya, gamon jini ce, laifin sa 1,
shine daya danki amanar da ba zai iya rikewa
ba."Alhj ya ce,"Duk laifin iyayen sa............ Tayi
saurin katse shi."A'a Abba, iyayen Naseer ba su
da laifi kuma ina mai tabbatar maku yadda ya
yaudare ku, haka ya yaudare su. Ba su san komai
ba a game da zaman mu. Sun rike ni tamkar 'yar
cikin su. Idan na ce ga abinda su kai min, na yi
masu karya, sai Allah ya tambaye ni. Abba, rokon
da zan maka daya ne, don Allah, don son Annabi
kar ka k'ullaci kowa akan maganar nan, ni ce
baya so, to ka dauki 'yar ka. Ai shikenan, an
gama magana." Ya ce,"Haka ne Nusaiba, ki yi
hkr, ni ma na gane kuskure na, ni na jawo miki
duk abinda ya same ki." Ta ce,"Ban ta6a ba ka
laifi ba Abba, ba kuma zan ta6a ba ka ba. Ai kai
alheri ka k'ulla, sai dai ka san a wannan zamanin
ba kowa yake son ayi masa za6in abinda ya
kamace shi a ruywar sa ba. Ya fi son abinda
ra'ayinsa ya ba shi. Ka ga kuskuren da aka samu.
Ina alfari da kai Abba na, kuma ko a yanzu ka
sake za6a min miji. Wallahi zan aure shi. Bai san
lkcn da ya rungume ta, ya fara kwalla ba. Haka
Ummi ke ta share hawaye, tana sawa Nusaiba
albarka. Ta mike ta shiga hada kaya. Hayaniyar
hama'a suka jiwo gaba daya jama'ar Naseer ne.
Zarah ma kayan barci ne ajikin ta, ta dora zani ta
sa hijabi. Suka doro cikin dakin. Zarah na
fadin,"Amarya!Ta zaburo da gudu, "Antina! Suka
rungume juna, sun sha kuka, sai da Umma ta
raba su ita ma, ta rungume ta. Daga nan ta
matsa ta gaida kowa. Su Malam Balarabe, Malam
Umar. Ya gaisa da Sageer da amayar sa. Bayan
an gama gaishe-gaishe. Malam Balarabe yasa aka
yi addu'a, kowa ya shafa. Aanan suka lura babu
Naseer tun shigowar su. Inna ta fara
magana,"Jama'a wai ina dan Inna ne? Malam
Umar ya ce,"Kai wai dama babu Naseer a wajen
nan? Sageer ya amsa,"Ai kuwa baya wajen nan,
tunda muka zo? Malam Balarabe ya ce,"Ah to ina
ya je? Ya fadi, yana kallon Alh.Basheer. Ya
ce,"Gaskiya ban san inda ya je ba. Kuma dama
ina son ganin ka, idan ba za ka damu ba." Ya
ce,"Bismillah Alhj, ba damuwa." Suka fito waje,
yayin da Zarah da Nusaiba ke like da juna suna
maida yadda abubuwa suka faru. Alh.Basheer ya
kebe da M.Balarabe, ya kwashe bayanin da
Nusaiba tayi masa kaf, ya gaya masa. Tun da ya
soma magana, gaba daya jijiyoyin jikin Malam
Balarane suka tsinke, jiri ya fara dibar sa. Allah
yasa a zaune suke, da babu abinda zai hana shi
faduwa. Tabbas ya san Naseer baya son auran
nan, aka yi shi, amma ko alama bai ta6a sanin
rashin mutunci da wulakancin da ya rinka
aikatawa ba. Ya jima kafin ya ce,"Alhj wannan
magana ta ban kunya, kuma Wallahi tallahi ban
san komai a game da zancan ba. Nusaiba bata
nuna mana ba, balle ta furta da bakin ta. Don
girman Allah ka yi hakuri Alhj. Ya ce,"Ai magana
ta k'are, tunda baya son ta, ni ina son abata
kuma zan tafi da ita, ba tare da 6ata lkc ba.
Amma D'a, ban sako mata shi cikin gara ba, sbd
haka nan za ta aje shi ko ya kashe ko ya bar shi
da rai, duk ya rage nasa. A karshe, ka gaya masa
na gode. Allah ya saka da alkhairi. Kan
M.Balarane yayi gingirinn! Kunya kamar ya nutse
kasa. Idanuwan sa suka cika da kwalla, ya rasa
me zai ce wa Alhj? Kawai sai ya juya ya dawo
dakin, gaban kowa ya daga murya ya
ce,"Nusaiba, don me za ki min haka???Akan me
za ki zauna sama da shekaru 2 cikin wulakanci da
bak'in ciki, amma muna tare, ki kasa gaya min?
Ba ki min adalci ba Nusaiba, domin da kin gaya
min da tuni na yanke hukunci, sai dai ya nemi
wani uban, ba ni ba! Kowa yayi tsuru-tsuru.
Nusaiba kuwa tuni ta fara kuka. Ya matsa gadabn
Ummi ya tsugunna." Hajiya ki yi wa girman Allah,
ki yi hakuri. D'a ne ka haife shi ba ka haifi halin
sa ba. Ko alama ban san halin da suke ciki da
matar sa ba. Ga mahaifiyar sa nan a zaune, ko
ita da ke zama tare da su munafikin Yaron nan
bai ta6a barin ta gane wani abu ba, balle ni da
ban zama cikin gida. Maganar tafiya da Nusaiba
kuwa kun yi dai-dai, domin ko ni ne hakan zan
yi. Saboda haka kowa yayi shaida. Ni Balarabe na
tsame hannu na akan komai daya shafi Naseer,
duk abinda ya ga dama yayi rayuwa
ce................ Ya fashe da kuka, jikin kowa yayi
sanyi, matan da ke wajen ma tuni suka soma
taya shi, musamman Umma da ta ji abin kamar
saukar aradu. Sageer ma waje yayi kirjin sa na
bugawa, ga ranar da yake jin tsoron zuwanta,
kullum yana gaya wa Naseer. Amma kunnuwansa
iskar duniya ta dode masa su. M.Umar da Alhj
suka riko M.Balarabe,"Ka yi shiru haka,"Malam
Balarabe, kar zuciya ya kwashe ka, ka yi masa
baki." Ya dube su ya ce,"Ni Naseer yayi wa tijara
haka, Babu komai, rayuwa ce!Ya dubi Umma ya
ce gaba,"Ke dauko masa D'ansa mu tafi, ki kai
masa kayansa, idan ya ga dama ya jefa shi bola!
Malam Umar ya ce,"A' ba'a yi haka bane, duk ku
zauna a sasanta magana. Ai in rai ya 6aci, hankali
ke nemo shi. Alhj ka yi hakuri, mu zauna da
Naseer mu ji ta bakin sa, don girman Allah kar ku
yanke hukunci kai tsaye haka." Alhj ya kada
kai,"Ban k'i taka ba. Amma Naseer ya riga ya
k'are magana, sai dai hukuncin daya yanke ne
ban yarda da shi ba, d'a kan ba na mu bane, na
shi ne. Don haka anan za'a bar shi. Iya magana
kenan." Malam Balarabe ya ce,"Magana tayi dai-
dai Alhj, ku bar masa shi, ya san uwar da za ta
shayar masa D'an shi. Ki dauko shi mu tafi, na
gaya miki, idan kuma ki na nan, ni na wuce! Yayi
waje. Malam Umar ya bi shi. Umma ta dubi
Ummi, ta ce,"Don girman Allah Hajiya kar ku yi
wa Yaron nan haka, shi bai san komai ba, ku
tausaya masa." Tayi shiru, ta rasa me za ta ce?
Yadda Alhj ya fusato, babu mai sa shi dukan
D'an nan. Haka Zarah ta rike Nusaiba,"Amarya
kar ki ta fi, don Allah ki taimake ni. Idan ki ka
tafi da wa zan zauna? Suka k'ara fashewa da
kuka. Ita dai Fa'iza ba baki, sai ido. Bata fahimce
komai ba, take ta faman kuka. Alhj ya fice ya bar
su nan, suna ta faman magiya. Jim kadan ya
dawo tare da Likita. Shi dai ya ga ana ta koke-
koke, a zaton sa duk na murna ne, yayi abbuwan
da zai yi, ya gama ya ba su sallama tare da
takardar magunguna da za ta ci gaba da sha na
tsawon kwana 7.Alhj da kansa ya rink'a dibar
kaya yana kaiwa cikin mota, har ya kwashe su
duka. Ya kamo hannun Nusaiba, ya wuce da ita.
Ummi ta biyo bayan su, suka bar Umma da jariri
bisa gado, yana ta faman barci. Ta k'ara fasa
kuka. Inna ta kamota tana rarrashi. Haka Zarah
ke durk'ushe, hannu 2 bisa kai.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Daga inda Naseer ke 6oye, yana hango su Alhj
suka zo suka wuce a moTa. Yasa hannu ya goge
hawayen da ke kuncinsa. Jimawa kadan ya hangi
su Umma. Inna na dauke da Ameer, suka shiga
motar da ta kawo su. Direba ya ja suka bar
asibitin. Wasu hawayen suka sake zubo masa,
yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Ya nufi inda
ya aje motar sa, ya shiga haka ya dawo gida,
baya gani wuri sosai. Ya rasa inda zai je, sai yayi
fakin kofar shago, ya shiga ya sallami su Abbas
ya ce duk su tafi gida. Ya kulle kansa ciki, ya rasa
abinda ke masa dadi a duniya. Cikin gidansu
kuwa kamar anyi mutuwa, shiru ba ka jin motsin
kowa. Jim kadan Zarah ta fito da jakar kayan ta,
ta lallabo zuwa sasan su Umma. Ta leko a
hankali, ta ga babu kowa, ta cire takalmanta ta
wuce sadaf-sadaf kamar 6arauniya. Tayi waje kan
ta tsaye tayi gidan su. Inna ta zura mata ido,
kafin ta ce,"Ke kuma fa? Ta shige uwar daki da
gudu. Inna ta biyota,"Na ce ke kuma fa? Kin
shige da gudu. Menene na ce? Ta ce,"Allah Inna
ni ma ba zan zauna ba. Haba ai wulakancin yayi
yawa, ko alama yayana baya jin magana. Ta
balbaleta da fada,"Laifin waye? Ai duk ku na
sane, aka rasa wacce za ta gaya wa manya, don
ayi maganin abin, sai yanzu da zance ya lalace,
za ki ce Naseer ne baya jin magana? Maza dauko
jakar nan, ki koma inda ki ka fito, tun kafin
Babanki ya k'araso gidan nan, ya sameki." Ta
6arke da kuka, tana fadin,"Ba inda za ni Inna,
idan har na koma gidan nan, to yayana ya dawo
da Nusaiba. Kuma ku matsa min ku gani. Wallahi
tafiya ta zan yi." Inna tasa mata ido tallafe da
baki. "Ki ka ce me? Lallai wuyanki ya isa yanka,
to zan ji idan kke ki ka haife mu." Ta yi zamanta
bakin gado, har Inna ta gama babatun ta, ta
fice." Na rantse da Allah ba zan koma ba, ya je
ya ci kan sa a gidan, tunda shi ba'a gaya masa
ya ji." Koda Malam Umar ya dawo, babu yadda
ya iya yi da ita, ya gama fadansa da barazanarsa
ko gezau zuciyar Zarah bata yi ba, kuma ta
rantse ta maya, muddin suka bari ta bar nan, ba
za su sake ganin ta ba. Shi yasa da ta dauko jaka
ta fito. Inna ta dauko muciya ta kora ta daki, ta
ce,"Koma daki marasa kunya, idan Naseer din ya
zo ya dauke ki! Ta maida jaka ta yi zamanta cikin
dacin rai da takaici tare da tausayin Nusaiba da
karamin goyonta.
Sageer ma da ke zaune a dakinsa, babu abinda
ya fi damun sa irin dan karamin yaron da aka
aje. Alhalin bai san komai ba. Fa'iza ta
ce,"Yakamata ku taimaka wa yaron nan a maida
shi wajen Maman shi,"Wallahi shi ne abin
tausayi, ba ka ji yadda na ke ji ba, kamar inyi
tsuntsu kai shi wajen ta." Ya ce,"Shirun nan da ki
ka ga nayi. Ameer kawai na ke tunani." Yayi
hucin zafi, ya dauko waya daga aljihu ya nemo
lambar Naseer. Ta dan jima tana bugawa kafin ya
dauka, ya ce,"Ka na ina ne? Murya dishe ya
amsa,"Shago." "To ina zuwa." Ya kashe waya, ya
dubi Fa'iza,"Wai yana shago, bari in je in same
shi." Ta ce,"To ba za ka dan ci komai ba? Ya kada
kai, bari dai in je in dawo. Ya fice, tana fadin a
dawo lafiya. Ya kwankwasa kofar shagon, ya zo
ya bude, suka koma ciki tare. Daga kallon Naseer
kawai. Sageer ya gane yayi nadama, gaba daya
ya jeme ya fita hayya cin sa. Ya dube shi a
sanyaye ya ce,"Ka ga irin abubuwan da na ke
gaya maka ko? Yanzu ina ribar wannan abu?
Kullum ina gaya maka yi wa iyaye biyayya ibada
ce, duk kuma mai yin sa ba zai ta6a ganin 6acin
rai ba. Amma Naseer na ka ji, ni ban san abinda
ke damun ka ba. Dan yaro jariri an ajiye maka
shi, ina amfanin sa? Iyayen ka na ta kuka saboda
kai, wacce irin masifa ce wannan? Ka farka daga
bacci Naseer, kai ba yaro ba ne."Ya dube shi
kwalla suka zubo ya ce,"Ban san abinda zan ce
ba Sageer, domin ni kaina na san mai laifi ne,
saboda haka duk hukuncin da aka yanke min,
yayi dai-dai. Sai dai babu wanda ya san cewa na
dade da yin nadama, sannan in na ce ba son
Nusaiba yanzu, na yiwa raina karya. Shi ya sa na
dage ba dare ba rana wajen kula da ita tare da
rokon Allah ya bata lafiya, don in samu in nemi
gafarar ta, na kuma nuna mata iya so da kaunar
da na ke mata yanzu. Allah da ikonsa sai ta sami
sauki, hankalinta ya dawo jikin ta, a lokacin da
iyayen ta ke wajen, sannan bata 6ata lokaci ba,
ta zayyane masu komai. Ka yarda da ni Sageer?
Ka taimake ni, domin ni yanzu ban san yadda zan
yi ba." Sageer yayi shiru, yana kada kai
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Tabbas ya yarda da maganganun Naseer, saboda
yana daya cikin masu mmkin yadda Naseer ya
rinka kula tare da ririta Nusaiba, sai dai a lokacin
ya dauka saboda halin da ta shiga ne, kuma bata
son kowa ya kusance ta, sai shi. Ya nisa kafin ya
ce,"Yanzu tinkarar Abban, tashin hankali ne ba
karami ba, kuma dole ne aje a same shi, tunda
shine jigon komai. Abin yi shine, ka taso mu je
wajen sa, ayi ta ta kare ko kashe mu zai yi." Ya
kada kai,"Gaskiya Sageer ba zan iya ba.ka je kai
kadai tukuna, ni na fi kowa sanin halin Abba." Ya
ce,"Shi ke nan. Za ka jira ni a anan