Showing 15001 words to 18000 words out of 29550 words
Chapter 6 - A JININSA YAKE PDF BOOK 3 End COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt
na farko da Nusaiba ta dubi Abban Husna,
sam bata gaskanta idanuwan ta ba. Ta kara
duban sa da kyau, babu ko shakkar Ibrahim
ne.
Jikin ta duk yayi la'asar saboda al'ajabin sake
haduwar ta da Ibrahim, wanda tuni ta mance da
shi a duniya. Suna tafe Maman Husna na
fadin,"Sai yaushe ke nan?
Ta ce,"Ai ina hada layi na, za ki ji kira na. Ai ba
zan yi wasa da lambar da ki ka ba ni ba, dole ne
in kira Husna."
Suka yi dariya. Nusaiba yanke tabi wani
6angare,"Bari in jira su Antina a nan. Ta ce,"Ah!
Ba za ki sallama da Husnar ta ki ba." Ta ce kyale
ta, ta ga Abban ta, ta mance da ni." To shi
kenan, sai na ji ki." Ta wuce inda su Husna ke
tsaye da Abban ta, duk da cukuikuye shi, ta hana
shi sukuni.
Babban yaron dake tare da shi, ya rugo ya
rungume Maman su, shi ma zai kai shekara 6 ko
5 da rabi. Nusaiba na tsaye duk ta kosa Antinta
su zo.......Ta bar wajen. Don bata son Ibrahim ya
gan ta, kawai ji tayi Husna na rikota tana
fadin,"Zo ka gan shi Abba, Bebi mai kyau."
Gabanta ya fadi, ta waigo cikin tsarguwa, suna
hada ido da Abban Husna ya ji kamar zai fadi,
sbd faduwar gaba. Bai san lkcn da yayi zuru, ya
zuba mata ido ba.
Ta shiga dan yake, tana wa Husna magana,"Ke
wai ba mun yi sallama tun a jirgi ba?
Tsayuwayar Maman Husna wajen yasa Ibrahim ya
dawo duniyar daya tafi, yayin da Husna ke
fadin,"Abba na zai ga Bebi mai kyau.
Ka gan shi? Suka fara dariya, ya kar6e shi ya dan
daga sama ya ce,"Good day handsome Bebi!
>
Yayin da Nusaiba ta juya tana tambyara sunan
yayan Husna, ya ce,"Imran." Ta
ce,"Uhnmm..............Sunanka da dadi." Husna ta
ce,"Ni ma sunana da dadi. Ta kama habarta ta
ce,"Sosai ma, ke mai babban suna ma ba'a fadi,
shi yaya ake kiran ki Husna."
Dadi ya kamata har da yi wa Imran gwalo.
Ibrahin ya numfasa, ya dubi matar sa ya
ce,"Gaskiya wannan haduwa tana da ban mmk.
Ai dole ayi dalla-dalla. Wannan ita ce,"Nusaiban
da na ta6a ba ki labari. Nusaiba ga Madan din
na Sakina." Mamaki ya kama Maman Husna, take
nan kishi ya kulle ta. Ta dan daure fuskata ta
ce,"Ka ce min wacce ta kusan zarar min da
kai.
Nusaiba ma ta gyara fuska, ta ce,"Ki bar
maganar nan Maman Husna ta riga ta wuce." Ya
ce,"Sai zumunci ko? Yana da kyau, ina fatan kin
bata adires, kafin ta koma, za ta kawo mana
Ziyara."Sakina ta gyada kai tana yamutse
fuska,."Na dai bata lambar waya."
"Mts, ina ganin ya kamata mu wuce Abban
Husna, na fara gajiya wallahi."
Ya ce ,"Tunda ba'a zo daukan ki ba, why not ba
za ki bi mu, mu sauke ki gida ba? Sakina ta
kauda kai yayin da Nusaiba ke 'yar dariya, tana
fadin,"Ku bar shi Allah na gode. Ai na san za su
zo."
Ta mika hannu ta kar6i Ameer a hannun sa.
>
Ya maida hannaye aljihu, ya numfasa, amma bai
iya cewa komai ba.
Ta shashshafa kan su Husna ta ce,"Sai anjima ko
Husna!? "Bye-bye Bebi, sai ka zo gidan mu." Suka
yi sallama da Sakina, ba wata walwala a fuskarta,
ganin haka Ibrahim yayi gaba rike da hannayen
yaran sa.
Sakinta ta bi bayan su cike da kishin babu gaira
babu dalili.
Nusaiba na nan tsaye, duk takaicin al'amarin ya
dameta ta, kamar minti 5 da wucewar su.
Antinta ta iso,"Allah sarki Nusaiba, sorry,"Wallahi
sharrin mota ne, cak ta tsaya mana a titi da kyar
Direba ya gyara."
Yaranta mata duga guda 4, suka yayyame ta,
kowa son ya dauki Bebi yake yi.
Babu 6ata lkc. Direba ya kwashe kaya suka
rankya.
Tunda daga mota, har gida Antin Jordan ke
balbala tsiya akan abinda ya faru.
Dakin ta daban, aka ware mata ita da Bebin ta,
bayan an gama duk kayaniyar ganin juna har da
maigidan ya tofa na sa albarkacin bakin sa.
Sai dai nasihohi yayi mata akan ta aje hankalinta
waje daya, kar ta sa wa ranta damuwa.Daki ta
koma ta yi wanka, ta yi alwala ta yi sallolinta.
Gefen gado ta zauna tana tanunanin yanayin da
suka hadu da Sakina, fara'a kamar gonar
auduga, amma tashi guda ta sauya fuska, saboda
mijinta ya nuna ya santa.
Ta yi dan murmushi, ta ce,"Allah sarki Antina,
alkhairin Allah ya kai miki."
Ta sa hannu ta jawo jakar Bebi, ta daukko lambar
da Sakinta ta bata a rubuce, ta sa hannu ta
yayyaga, tana fadi a ranta,"Sa ran ki a inuwa
Maman Husna, kullum ni da mijinki haduwar
[Aiport] ce, rabuwar (Airport)." Ta matse a
hannun ta, ta wuce bayi ta watsa (Dosbin).
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Washe gari da wuri Naseer ya nufi Kaduna. Shi
kadai kuma ya tafi, wannan karon zuciyar sa ta
bushe, matar sa kawai yake son ta dawo.
Shi yasa ya kwashe duk wani tunanin dake ran sa
a game dake ran sa a game da tinkarar Alhj.
>
Yayi fakin, ya fito kai tsaye falon yayi
sallama.
Mariya dake goge-goge, ta amsa sannan, ta
durk'usa ta gaishe shi ya ce,"Hau sama ki kira
min Ummi." Ta ce,"Tana ma kicin, bari na kira
ta."
Ya zauna Mariya ta wuce. Jin kadan ta dawo ta
ce,"Ga ta nan zuwa." Ya share minti 5 nan, kafin
Ummi ta iso falon.
Ya mike kai sunkuye ya ce,"Sannu Ummi." Bata
tanka masa ba, ta wuce ta haye sama. Yayi tsaye
nan kirjin sa na harbawa.Bai sake ganin kowa ba,
wucewar minti 30 har ya gaji da tsayuwa ya
koma ya zauna.
Can Alh.Basheer ya tinkaro falon.
Ummi na rike da jakar sa suna maganganun
su.
Naseer ya kuma mikewa yayi tsaye irin na marasa
gaskiya. Ko inda yake Alhj bai kalla ba, jakarsa ya
karba. Ummi ta ce," A dawo lafiya." Ya ce,"Amin."
Ya fice.
Ummi na ta wuce kicin, ta ci gaba da hidimomin
ta.
Naseer yayi kamar ya nutse a kasa, jiki babu
kwari ya biyo bayan Alhj, amma kafin ya
karaso.
Alhj ya shiga mota. Deriba ya tayar. Haka ya
tsaya kamar dolo, yana kallo aka bude get.
Motar ta fice. Ya wuce ya shiga ta sa, ya bi bayan
sa.
Ofis ya ga sun nufa, shi ma ya bi su. Yana zuwa
zai wuce sakatare, ya ce,"Alhj ya ce ka dan jira
shi a nan tukuna."
Ya ce,"To." Ya zauna.
Shi kansa sakataran dauke da mamaki yake,
domin bai ta6a yi wa Naseer iso ba wajen
Alhj.
Yana nan zaune Alhjn ya kira waya, ya bada
izinin Naseer ya shigo.
Ya mike ya tura kofa, ya sjiga Alhjn na ta aikin sa
bisa (Laptop), bai ko kalle shi ba. Ya duka ya
gaishe shi, ya amsa a dakile.
Yayi shiru, haka shima Alhjn bai dube shi
ba.
A haka ya daure ya fara magana,"Abba, na san
babu abinda zan gaya maka wanda zai faranta
maka rai, amma duk da haka ina mai gurfanar
da kai na gare ka a matsayin mai laifi.Ka yanke
min duk hukuncin da ya dace dani, wanda zai
sanyaya maka rai, har ka huce ka ban Nusaiba,
in koma da ita.
Da sunan Allah na ke wannan rokon Abba, ka
taimake ni don son Manzon mu.
Yayi shiru. Shi kuwa Alhj sai a aikinsa yake
yi.
Kamar ba zai tanka ba, wucewar mintoci, kafin ya
ce,"Ka na iya tafiya, zan neme ka."
Ya durk'usa guiwa 2 ya ce,"To shi kenan, na gode
Abba.
Kuma ina k'ara neman afuwa akan kuskuran da
na yi.
Ka gafarce ni Abba."
Ya ce,"Ka je zan neme ka na ce."
Ya mike yana fadin,"Na gode, a tashi lafiya."
>
Bai amsa masa ba ya fice.
Alhaji ya sauke numfashi, ya dafe goshinsa, bai
san dalilin da yasa son Naseer yayi masa yawa a
zuciya ba, duk lokacin da ya gan shi kaunar sa
karuwa take.
Dole ce tasa ya yanke hukuncin nan, saboda ya
kar6o wa Nusaiba 'yancinta.
Ofishin su Yakubu Naseer ya nufa, can bargar
dawakai, amma wurin na kulle babu kowa, sai
mai ba dawaki abinci.
Bai tsaya 6ata lkc ba, ya damko hanyar dawowa
gida, yana tafe wasi-wasi ne fal cikin ransa, wata
zuciyar na saka masa zai yi wuya Nusiba ta dawo,
wata kuma na tabbatar masa za ta dawo ne,
tunda ya ce zai neme ka.,
Ai kai d'an gaban goshin sa ne. Daya iso shago,
ya tsaya wajen Sageer.
Bai dawo gida ba, sai karfe 1,abu na farko sada
fara gani, shine babu motar Nusaiba dake lullu6e
a wajen.
Gabnsa ya fadi, ya fito da sauri ya fada cikin
gida.
Zarah na zaune a barndar sasan su, tana ta
faman goge kwalla."Menene wai?
Ban ga motar Nusaiba ba a waje!
Murya na rawa ta ce,"An kwashe kayanta, ka ga
shi kenan ta faru, ta k'are, tuntuni na ke gaya
maka, ka je ka k'i................
Ya katse ta da masifa,"Don Allah isa haka, kar ki
kara 6ata min rai!
Ko yanzu daga ina na ke? Ya ce zai neme ni? Ai
shi kenan tunda baya son ta dawo!
Ya nemi waje nan ya zauna dabas, ya cire hula
zufa ta keto masa.
Zara bata iya kara komai ba, ta ma tashi ta bar
wajen.
Umma na jin sa, kanzil ba ta ce da shi ba.
Bayan sallar la'asar, yana kwance dakin sa ya
rasa abinda ke masa dadi, kamar an kwaso son
Nusaiba an kara cusa masa cikin zuciya, sannan a
'yan kwananin nan da bai ga Ameer ba, duk
kewarsa ta ishe shi.Gaba daya abubuwan sun
dagule masa, domin ya sani ba za su ta6a
daidaitawa da Abbansa ba, muddin Nusaiba bata
dawo cikin gidan nan. Ya runtse ido, ya dafe kai
kamar ya kwarma ihu. Zumbur ya mike ya
kwashi makullai, ya fice ko Zarah bata sani ba,
ya fada mota. Ya sake yi wa Kaduna tsinke. Yana
zuwa. Sakatare ya ce Alhj ya tashi.
Yana kokarin fitowa daga get. Motar Yakubu na
shigowa. Suka tsaya kowa ya fito gaba dayan su,
babu mai walwala a fuska. Yakubu ya fara
magana,"Ko ka ji abinda ya faru?" Ya ce,"Na
me ? Ya ce,"Na rufe (Dabai Riders) mana.
Alhj ya rufe kulob, yadda yake gaya min ma ya
sa dawakan a kasuwa har an samu masu siya."
Salati Naseer ya fara yi, kafin ya ce,"Saboda me?
Ya numfasa ya ce,"Wallahi ban sani ba, amma
tun faruwar wannan al'amarin na ku hankalin
Alhj a tashe yake. Iyaka kokari na, akan ya sauya
shawara, amma ya ce ra'ayin sa ne.."
Naseer ya k'ara tarus! Idanuwan sa suka kawo
kwalla, ya ce,"Yakubu ban san yadda zan yi ba,
dazun nan na zo na yi magiya gun sa, ya ce in je
zai neme ni, wai ina zuwa gida. Na tarar an
kwashe kayan Nusaiba kaf. Lambarta ba'a
samu.
Kuma ni na san rufe kulob din nan, duk baya
rasa nasaba da matsalar nan, wata kila yana
ganin ta dalililin Polo ya hadu da ni.Ban san abin
yi ba Yakubu? Ya ce,"Gaskiya ne. Magana kan ta
gama lalacewa. Ka san komai Alhj zai iya yi
saboda Nusaiba, kar ka manta ita ce 'yar sa
kawai. Sannan duk abinda ya faru, kai ka jawa
kanka, domin ba karamar asara ka yi ba. Sai ka
yi addu'a Allah ya sa hakan shine alkhairi. Gida
ka nufa?
Ya kada kai,"Ina nan sai na ga abinda ya turewa
buzu nad'i. Yakubu ya ce,"To sai ka
dawo,"Goodluck." Na gode." Naseer ya fice, shi
kuma ya karaso wajen sakatare, ya aje abubuwan
daya zo da su.
Gidan Naseer ya nufa. Alhj na tare da baki. Yayi
sallama ta gaishe su. Alhj ya bi shi da kallo. Ya ce
"Dama na zo ganin ka ne, bari in jira ka." Ganin
mutane a wajen yasa ya amsa." To ina
zuwa."Naseer ya fita, motar sa ya zauna yayi ta ji
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajinisa Yake3-04
Posted by ANaM Dorayi on 05:24 AM, 23-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Zan yafe maka komai, ya wuce har abada, amma
sai ka kawo min takardar Nusaiba."Kansa cikin
giuwa, ya girgiza kai, ya ce,"Ba zan iya ba Abba,
ka yi hkr." Ya ce,"Wannan ba hukunci na ba
ne.Nusaiba ce ta buk'ata ta kuma bar min
sallahu jiya kafin su wuce Jordan.." Ji yayi
numfashinsa ya shake gaba daya, yana neman
faduwa.
Ya kasa motsi, balle ya ce wani abu. Ya ci gaba
da cewa,"Na ba ka nan da jibi ka zomin da
takardar, daga nan zan maka bayanan wasu
abubuwa da suka kamata ka sani.
Ka na iya tafiya dare yana k'ar yi." Ya dago
idanuwa jajur! Ya ce,"Ummi ku taimake ni, ku ba
ni lambar ta mu yi magana, na san zata saurare
ni. Amma a raba auran a haka, abin babu
dadi.."Abba ya ba shi amsa,"Ban son dogon nace
Naseer, raina k'ara 6aci yake yi. Kwanciyar
hankalin na da kai shine ka kawo min takardar
Nusaiba. Yadda ba ka so, haka ita ma bata so,
shi kenan magana ta k'are babu lallai babu
tilas."
Ya sunkuyar da kai, yayi shiru. Ummi ta
ce,"Yakamata ka tafi, dare ya fara yi Naseer,
muna sauraronka."Yayi wawan ajiyar zuciya, ya
mike da kyar ya ce da su,"Sai da safe,gaba daya
suka amsa,"Allah ya kai mu, a gaida mutan
gidan."Bai k'ara komai ba, ya sakko a hankali ya
tafi.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Karfe 11 dare, ya shigo gida,. Zarah na zaune a
falo ta ci uban tagumi, ya turo kofar ya shigo." Ta
mike tsaye da sauri ta tarbe shi."
Yayana!
Kai kuwa ina ka shiga yau?
Bai tanka ba, ya wuce kujera ya zauna, ta bi shi
hannun kujerar ita ma ta zauna. Ganin yayi zuru-
zuru, yasa tausayinsa ya rufe ta.
Ta nunfasa ta ce,"Ina ka je yayana? Ya
ce,"Kaduna na koma." Ya aka yi to? Ya mayar
mata da abubuwan da Alhj ya ce,yayi shiru ta
rasa ta cewa. Ya kwanto da kan sa bisa
cinyoyinta, shi ma ya yi shirun Ta dafa kan sa ta
ce,"Kai yanzu me ka shawarta."Ya ce,"Na hukara
Zarah. Allah na gani na yi ikayar kokarina. Abinda
ya fi damuna maganganun da Alhj yayi. Ba
k'aramin dafa min jiki suka yi ba, sbd a zahiri
Alhj masoyina ne.Sai kin ga yadda ya cika hotuna
na a falonsa, kya rantse da Allah ni ne dan masu
gidan.
Ni dai na yi abin kunya, ban san ta yadda zan yi
in wanke kai na ba."
Ta ce,"Gaskiya ne, amma duk da haka ka tuntubi
su Umma ka ji ko za ta ce wani abu." Ya mike ya
wuce bayi, yayi wanka ya ji sanyi a jikin sa,
sannan ya kwanta.
Zarah na k'ara kwantar masa da hankali.
Da safe ya shiga wajen su Umma ya gaishe
su.
Abba bai amsa ba, ya tashi ya koma cikin
daki.
Daga can yana jin duk bayayin da yake wa
Umma.
Yana gamawa ta ce.
"To ne menene nawa a ciki? Duk abinda ka ga ya
dace, ka yi, tunda wannan 'ya ba ta mu bace,
k'arewa ma ka ce bata k'asar.
Ka ga da gaske Abbanta ya ke yi." Yayi dan jim
kafin ya mike, ya bar falon.
Umma ta bi shi da kallo, tausayin sa ya dan
kama ta, ta kada kai ta ce,"Kai ka jawo wa kan
ka."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sati 1 Naseer yayi yana sintiri Kaduna, wai ko ya
sanmi sauyin baki daga Alh.Basheer, amma sam
babu.
Yau daya je ma. Alhj cewa yayi yau ce rana ta
karshe daya ba shi, idan bai kawo takardar ba, to
kar ya sake zuwa gun sa, kuma duk abinda ya
biyo baya, kar ya ce yayi masa wulakanci.
Babu yadda zai yi, a daren ya rubuta takarda,
saki 1 ya sa a ambulan ya rufe.
Washe gari ya isa gida, ya sami Alhj yana shirin
fita.Bayan sun gaisa Alhj, na kallo irin ramar da
Naseer din yayi. Ummi ta zo suka gaisa. Yasa
hannun aljihu ya ciro ambulan, ya tsugunna ya
mika wa Alhj. Ya kar6a, ya buda, ya karanta, bai
ko karasa ba, ya rufe saboda irin lausasan
kalaman da ke cikin takardar.
Ya dube shi ya ce,"Magana ta kare Naseer, kuma
duniya da lahira na yafe maka abinda ka yi min.
Son ka a cikin jini na yake, na rantse da Allah ba
zan iya cire shi ba, saboda haka ka saki jikin ka,
kai da na ne.
Magana ta 2, ita ce,"Gida da motocin da na ba
ka, mallakin ka ne, ba na bukatar su. Abinda na
ke son ka da shi ne, ka dauki Zarah ku koma can
da zama.
Wannan umurni ne a matsayin na Babanka."Gaba
daya tsigar jikinsa suka tashi yar! Idanuwansa
suka kawo kwalla.
Ya zamo daga kujera ya ce,"Na gode Abba. Allah
ya saka da alkhairi."
Ya ce,"Koma ka zauna. Yanzu yaushe za ka
kammala karatun ka? Ya sunkuyar da kai, kunya
ta rufe shi, ya rasa me zai ce? Da kyar ya daure
ya ce,"Ai dama ban fara ba."
Da mamakinsa ya maimaita ,"Ba ka fara ba? To
da ka ce min ka na zuwa?
Ya sunkuyar da kai, kamar ya ratsa kujera ya
shige. Alhj yayi dan murmushi ya ce,"Allah da iko
yake, yanzu yaushe za ka fara? Kidimewa tasa ya
ce,"Gobe." Ummi ta ce,"Gobo kuwa? Ba dai gobe-
gobe ba, ai kuma sai an sake nema ko? Ko kuwa
ka na da "(Admission) ne a hannun ka?
Ya girgiza kai,"A'a.Duk sun lura a daburce yake,
saboda haka Alhj ya ce,"Shi ke nan, ka je ka yi
duk abinda ya kamata, idan ka sami ( Admission)
din ka kawo min." Ya ce,"To na gode Abba."
>
Ya kosa ya tashi saboda tsarguwa, zufa ce kawai
ke kwararo masa cikin riga.
Yana samu aka sallame shi, jikin sa na rawa yayi
godiya, ya fice.
Alhj ya dubi Ummi ya ce,"Kawai Allah ne ya dora
min son yaron nan, ba don haka ba, inda na ke
ma idan aka ce ya zo da kudi ba zai zo ba."
Ta ce,"Ya za'ayi, ga kuma zuri'a a tsakani, dole a
rage wani abin." Ya numfasa yana kada ambulan,
sannan ya mika mata,"Karanta ki ji bayanan dake
ciki." Ta kar6a ta karanta, ta yi dan murmushi ta
ce,"Allah sarki da alama ya saduda Alhj."
Ya ce,"Kyale ni da shi dai."
Ta ce,"Na kyale."
Kowa ya ji abinda Alhj yayi, sai ya sanya masa
albarka.
A hakikanin gaskiya Alh.Basheer mutum ne
wanda ba'a samun su a wannan zamanin, sai an
shekara ana bincike cikin mutanen kirkin da ake
wa zaton suna da halin mutan da can. Karshen
soyayya Alh.Basheer ya nuna wa, Naseer shi yasa
Naseer din ke k'ara nadama kan nadama, so da
kaunar Nusaiba ke k'ara dabaibaye
zuciyarsa.
Kewar ta ke jefa shi.
Nisan tunanin ta musamman lukutan daya samu
a asibiti yana jinyarta.Ya kan rink'a ganin kamar
wata sabuwar rayuwar soyayya ce suka yi a
tsakanin su, wacce yake mafarkin ci gaba da irin
ta.
Malam Balarabe kuwa kalaman godiya sun kare a
bakin sa.
Washe gari daya tafi Kaduna, ba tare da sanin
kowa ba, don nuna girmamawa ga Alh. Basheer.
Tabbas ya nuna halin girman, dole a jinjina masa.
Haka shi ma Alhjn ya roke shi akan ya daina
fushi da Naseer, tunda ya tuba, to ya kamata ya
karbi tuban sa, sbd fushin sa tamkar dafi ne a
gare shi.
Malam Balarabe ya amince, yayi farin ciki ya
kuma zubda kwallan