Showing 18001 words to 21000 words out of 29550 words

Chapter 7 - A JININSA YAKE PDF BOOK 3 End COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt

06 Dec 2024

2262

bakin cikin rabuwar auran
Naseer da Nusaiba.

Ba 6angaran su Malam Balarabe kadai bakin cikin
rabuwan auran ya dama ba, ita kan ta uwar
gayyar, yau ta tsinci kanta cikin wani yanayin da
bata gane masa ba, a tun lokacin da sako ya zo
mata ta waya daga Nijeriya cewar ta fara iddar
ta.

Zaune take dirshan bisa gado, ta takure kanta,
tunanin yayi mata yawa.

Tana tambayar kan ta, ita kuma haka Allah ya
kaddaro mata? Mutuwar aure ita ce matsala ta
farko da ke ci mata tuwo a kwarya, a
rayuwarta.

Ta tsani, ace anyi aure ya mutu, sai ga shi yau ya
tabbata akan ta.

"Kaddara!

Ta fada a ranta hawaye, suka kubce.

Ta dawo tana zargin kan ta,"Watakila Naseer ya
so ya gaya mata wata magana lkcn da ta wayi
gari ta gan shi tare da ita asibitin, amma ta ki ba
shi dama.

Yi hakuri ki ba Bebinmu nono. Haba 'yar gidan
Abba."

Tabbas rarrashin ta yake yi, amma ta dauke kai,
ta nuna bata san abinda take yi ba.

Alhalin ta warke, hankalin ta ya dawo jikinta.
>
Da kenan amarya, amma, a yanzu ina mai
tabbatar miki yayanmu yayi nadama, ko bai gaya
min da bakin sa ba, ni na yi imanin yana son
ki.

Ba ki ga yadda ya fita hayyacin sa ba.

Lokacin da lalura ta kama ki, kuma ya kula dake
yadda ya kamata!

Ta toshe kunnuwanta ta daga kai.

Idanuwanta tamau a rintse, hawaye suka ci gaba
da sauka.

Istaharar ta ta tabbata gaskiya.

Bata sami isashen barci ba, sbd a yanzu take
tunanin ya kamata ace ta ba Naseer dama shi da
ita sun yi magana.

Yanayin daya suka kwana ita da Naseer, domin a
ranar suka koma Hanwa. Yayi sintiri a sashin ta
iya yadda ya ishe shi, wanda a da bai ta6a shiga
cikinsa ba. Tun Zarah na taya shi sintirin, har ta
hakura ta sakar masa. Daga ranar ya daukar wa
kan sa alkawarin zama lafiya da kowa, zuwa
k'arshen rayuwarsa.

Idan ba shi gida, yana shagon dinki ne, daya
samu Abba ya fara amsa gaisuwar sa, kuma bin
sa yake sau da kafa.

Komai bai zartarwa sai abinda ya ce. Haka yake
bin Alhj, bai ketare umurinin sa. A haka aka
share watanin 2. Mamakin sa 1 shine. Alhj ya ki
dawo da wasan Polo, shi kuma yana jin nauyin yi
masa magana.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


A 'yan tsakanin ne. Fa'iza ta haihu da namiji
k'aton gaske mai kama da Babansa. Ranar suna,
ya rada masa Mohammad. Zarah gidan sunan ta
wuni duk da ta wayi gari baya jin dadi.

Tun daga ranar jikinta ya k'i yi mata dadi,

tsoro ya fara kamata, sbd fargaba daukan
ciki.

Lalurar ta ta fara bata tsoro.

Lalai kuwa, abinda take wa tsoron ne ya
samu.

Shi kan sa Naseer tausayi take ba shi, shi yasa
wannan karon murnar sa raggiya ce.

Zarah na tsakiyar laulayi, aka biya kudin
jarrabawar (External)

Naseer ya biya duka WAEC da NECO.

Daga nan Sageer ya shawarce shi daya fada
makarantun bada (Lesson), don ya k'ara wanke
masa kwakwalwa.

Babu musu, ya nema ya shiga guda 2, yana
zuwa.

Ranar da za'a kai Zarah daurin mahaifa, ranar ce
suke da jarabawar farko. Hankalin Naseer ba'a
kwance yake ba, babu yadda zai yi.

Haka nan ya hakura suka tafi tare da su.

Umma da Inna Sageer ya kai su a Jeep din
sa.

Shi ya tafi jarabawar sa da Civic.A saukake yayi
jarabawar sa, duk da ba shi cikin nutsuwa, babu
tambayar da ta gagare shi amsawa.

Yana tashi ya wuce asibiti abin sa, ya duba
Zaraha, sannan ya dawo shago yayi ayyukansa.
Can yake zama su ci su yi hira, zuwa karfe 9 ya
dawo gida.

Zaman sa shi kadai yana kara taso masa da
kewar Nusaiba, a lkc irin wannan can baya, duk
da ta san baya maraba da ita cikin dakin sa, ta
kan shigo har ta tambaye shi ko yana da bukatar
wani abu.

Shi yasa ya dauki filo ya nufi sashin ta cikin dakin
barcinta, ya jefa pilo bisa kafet ya kwanta.

Nan ya kasance wajen barcinsa, kodayaushe,
yana laluben inda zai ji motsinta.

Watannin 3 sakamakon jarabawarsa ta fito.

Allah da ikon sa gaba daya sakamakon Naseer
masu kyau ne.

Yayi matukar sa'a.

Allah ya kubutar da shi daga sharrin hukumar
jarabawa da yanzu abin yake neman zama
kasuwanci.

Ko ma ince ya zama din."

Magidanci na fama da kansa, duk da haka ya
dage da karma-karma ya biya zunzurutin kudi,
sai jarabawa ta fito, ace yaro bai ci ba, alhali da
kokarin sa da komai.

Sannan ya dage wajen neman taimakon
makarantun (Lesson), tunda daman makarantun
gwamnati sai a hankali.

Ba duka (Syllabus) ake (Covering) , ba, balle yaro
ya san makamar jarabawarsa.

Allah ya sawwake.

Ilimi ya zama wahala ga 'ya'yanmu talakawa.Shi
kam Naseer yayi sa'a kamar yadda Allah ya
halicce shi, shi mai sa'a ne a rayuwarsa.

Da rawar jikinsa ya kai wa Alh. Basheer takardun
ya gani.

Yayi murna kwarai, daga nan ya shiga neman
makaranta, don samun (Admission).

Sageer na taimaka masa.

Ba jimawa ba, ya sami Poly ta hannun Sageer
din, Babu kudin kirki a hannunsa a wannan 'yan
tsakanin, sbd zaman Zarah a asibiti.

Ya zauna yana tunanin yadda za'ayi.

Ba tare daya takurawa kowa ba.

Abin mamaki yana zuwa Kaduna, ya nuna wa
Alhj,("Admission) din, kamar yadda ya umurce
shi, cewar da ya samu ya kawo masa ya
gani.

Take nan ya ware dubu 50 ya ba shi, ya ce ya je
yayi hidimar makaranta.

Allah mai iko.

Tun daga ofid har ya dawo gida, godiya yake wa
Alhj cikin ransa.

Ya kawo wa Abbansa, suka sa albarka shi da
Umma, balle Zarah da take jin tausayin sa, sbd
hidimar da yake sha a asibiti, ga kuma makaranta
ta kunno kai.

Lallai Alhj ba karamin taimako yayi ma su
ba.

Ciki lafiya, ba ka lafiya, ya kama karatun sa a
(Poly Computer Science) yake karantawa, kamar
almara yake ganin abin.

Lokacin kuwa cikin Zarah ya shiga wata 7.

Zullumi ya ishi kowa, musamman ita mai dauke
da cikin.

Kusan kullun da ciwon mara take kwana.

Bata dai yin magana ne kawai.

Saboda ciwon ba wai ya tsananta ba ne.

Sati 2 da fara karatunsa, abinda ake gudun ya
faru.

Ta haifi da namiji.

Aka sanya shi a kwalba kwana 7. Ya ce ga garin
ku nan kuma shi ya ci sunan Alhaji, watau
Mohammad Basheeeeeeeeeeeeerrr­
rrrr!!!!!.......

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Labarin haihuwar Zarah har Jordan, amma da
aka ce ya koma. Jikin Nusaiba yayi sanyi, ta dubi
Ameer yana ta rarrafen sa, yayi k'atob gasket,
dauki da nishi jajur, ga suma baka wulik! Kamar
kan Babansa.

Tausayin Antinta ya kama ta, ta yi tagumi ta ce a
ranta,"Allah sarki Antina." Ta numfasa, Ameer ya
rarrafo gun ta, ya dafa ta ya mike, ta sa hannun
ta dauke shi ta rungume.

Tabbas ta sani dole Naseer ya sa Ameer a
ransa.

Ta k'ara matse shi jikin ta, tunanin ta wai ace
Naseer ya tada k'ayar baya, dan sa yake so a ba
shi. Abinda ba zai samu ba kenan, yadda ta
shaku da Ameer.

Ai mai raba ta da shi, sai wanda ya bata shi. Ta
yi dai yi masu addu'ar Allah ya ba su mai
albarka."

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


BAYAN SHEKARA DAYA

Shekara guda da rushe(DABAI RIBERS),sauran
kolub-kolub din wasannin polo sai kawo wa
Naseer takardun gayyata suke, suna neman ya
koma kungiyoyinsu.

Gayyata har da Ghana, Kamaru, Benin Republic,
da sauran kasashen makwafta, wadanda suka
san Naseer, suka kuma san irin rawar daya taka a
wasan tsern Polo.

Amma sam ya ki amsa kiransu, duk da ya san
dumbin alkhairin da zai samu a can. Sam-sam
zuciyarsa ta fita daga wasan Polo tunda Alh.
Basheer ya bar harkar.Hakan ya gaya wa Yakubu
ranar da ya same shi da wata takarda da ta zo ta
hannun sa daga Sakkwato. Magana ta kawo
magana, suna hira tsakanin Yakubun da
Alhj.

Shi kuma yake ba shi labari.

Saboda haka Alh.Basheer ya kira Naseer yayi
masa magana. Baya ketare umurinin Alhjn,
amma wannan karon Naseer kad'a kai yai ya
ce,"Abba karatuna ya fi min wannan wasan,
kuma ban jin zan iya wasa da wani (Polo club) a
halin yanzu.

Alhj ya bi shi da kallo, tsaf ya kasa ganeme yake
nufi.

Yayi dan murmushi ya ce,"Shi kenan tunda ka
kawo zancen karatu. Allah ya bada sa'a."Ya
ce"Amin. Alh.Basheer ya dade yana nazarin
maganganun Naseer kuma yana tausaya masa,
domin ya saba da Polo.

Yana sha'awarsa, bugu da k'ari wasan Polo A
JININSA YAKE.Abinda kuwa daka saba da shi zai yi
wuya ya fice maka a rai, sai dole. Alhjn bai yanke
hukunci ba, tukuna, amma yana nan yana nazari
a kai.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Al'amarin Nusaiba kuwa a birnin Jordan, ba yabo,
ba fallasa a yanayin jikinta. Ta kasa samun
natsuwa a ranta, saboda yawan zancen aure da
Antin Jordan ke yi mata, tunda Ameer yayi wayau
sosai, yana gudun sa ko'ina gwanin
sha'awa.

Kullum amsar ta ita ce bata da wani bazawari
tsayayye ko a Nijeriya, balle kuma a nan Jordan
da babu wanda ta sani kasancewar ba fita take yi
ba.Idan ba (Shopping) ba tare da yaran gidan da
Direba. Ta damu kwarai domin ba ta san dalilin
da yasa Antin ta damu da yin sabon aurenna
taba. Shekara 1 kacal da mutuwar auranta.

A yammacin yau (Shopping) din za su da yaran
gidan.

Kowace ta shirya cikin dogayen kaya kala daban-
daban.

Direba ya aje su katuwar (Super market) din da
suke saba zuwa.

Suka shige kowa, yayi na sa wuri, yana neman
abinda yake so.

Nusaiba na jaye da Ameer cikin kwandon
Shopping din ta saka shi, don kar ya rink'a bata
wahala, yana gudu, tana kamo shi.

Bata ko lura da mutumin dake tsaye 6angarn
kayan abincin yara ba, sai da ta ji yana
fad'in,"Ameer!

Haka ka yi girma?

Ta waigo da sauri ta dube shi.

Ibrahim ne ke wasa da habar Ameer.

Bai kalle ta ba, ya ci gaba da cewa,"Ka ba Husna
kewa, kullum maganar ka take."

Ameer washe baki yake yana dariya.

Ita kuwa Nusaiba jikinta rawa ya dauka, ta tsura
masa ido.

A hankali ya dago, ya dube ta yayi dan murmushi
ya ce,"Hajiya Nusaiba."

Ta yi yake, tana fadin a ranta, "Ibrahim ko maye
ne?Kafin ta ce ,"Ya ku ke? Ina su Husna da
Mamanta? Ya ce,"Lafiya lau suke.

Amma ba ki da kirki? Ta gyara fuska,"Da aka yi
me?

Shekara 1 ki na garin nan, ki kasa kawo mana
ziyara, ba ki yi alkawari ba.

Sakin ta ce min ta ba ki (Phone Number), amma
ba ki kira ba." Lambar ce ta 6ace. Ka gaida min
Husna."

Ta fadi tana tura keken (Shopping) tana ci gaba
da kiran yara,"Sumayya ina ku ke? Ku zo mu tafi!


Ya dan sauke numfashi, ya biyo ta a hankali.
>
Suka hadu da yaran a wata kwana,"Anti ba mu
gama ba,"Inji babbar cikin su Sumayyah.

Dai-dai Ibrahim na tsayuwa wajen.

Ta ce,"Gaskiya ba zan jira ku ba, gobe Direba ya
sake kawo ku." Yayi fit yasa masu baki,"Haba
Anti, bai kamata ba, ki kyale su su gama."

Duk suka bi shi da kallo.

Ya juya kan sa,"Ga Sumayyah ko? Ke fa? Ya nuna
mai bi mata, ta ce,"Khadija."

Ke fa? Ta ce,"Mahadiyya." Ya duka ya kamo 'yar
kamar ,"Ke fa? Ta ce,"Zainab." Ya runtse ido ya
ce"Wash! Uwa da magani. Sannu Husna.

Mahadiyya ta cafe,"Ba husna sunanta ba ZEE
AFLAN! Ta kai mata duka, suka kwashe mata da
dariya. Takaici ya ishi Nusaiba, ta tura keke ta yi
gaba.Ta bar shi yana rabon fada, wa ya radawa
uwa ta ZEE AFLAM? Lalai ba zai sha (Ice-cream)
ba yau."Mahadiyya ta ce,"Ba ni bace. Anti
Sumayyah ce."

Ya kada kai,"Ba ki kyauta ba.

To ku tsaya in tambaye ku, yaushe Anti Nusaiba
ta zo nan? Sumayya ta ce,"Ta dade, tun Ameer
na jariri." Baban Ameer yana nan garin ne? Ta
ce,"A'a yana Nijeriya." Wai ko ba za ku zo mu tafi
ba ne?

Yau na ga yara.

Nusaiba ta leko tana kiran su.

Sumayya ta wuce da saurarinta. Khadija ta biyo
bayanta. Ya kamo hannayen su. Zainab tana
tambayar sa,"Kai ya sunan ka? Ya dube ta ya
ce,"Suna na mai son Anti."

Suka kwashe da dariya,"Wannan suna, ban ta6a
jin irin sa ba."

Inji Mahadiyya,"Ya ce,"Ga shi yau kin ji. Ko a gida
aka tambaye ki, ki ce mai son Anti, sunana."
>
Ta ce,"To."

Ya debo kwalayen cakulet 2 da biskit 2, ya mika
ma su. Suka yi godiya.

Wajen biyan kudi, suka same su, duk cin
maganin Nusaiba sai da Ibrahim ya biya
kudin.

Suka shiga mota, yana tsaye yana tunanin ta
yaya zai binciko gaskiyar lamarin? Sun bada baya
kadan, ya manta bai ma tambayi inda gidan su
yake ba.

Ya zabura da sauri, ya fada motar shi, ya bi
bayan su.

A haka a hankali yake bin su.

Nusaiba na jin Mahadiyya na tambayar su,"Kun
san sunan mutumin nan? "Wai mai son
Anti."

Gabanta ya fadi, ta zaro ido.

Sumayya ta ce,"Ah lallai ma wannan.

Antin Nusaiba, wai kin san shi ne? Ta ce,"Ina fa
na shan shi, ku da ganin mutum kun tsaya ku na
surutu da shi." Ta ce,"Anti ba ki san shi ba, shine
ya san sunan ki da na Ameer? Ta ce,"To saura in
ji maganar a bakin Anti, sai na murje bakin
yarinya." Sumayayya ta kwa6e fuska, ta dubi 'yan
uwanta, suka kama dariya,

suna toshe baki.A haka suka iso gida, yana biye
da su. Yana kallo suka shiga get, yana kallo duk
suka wuce cikin gida.

Farin cikin ya kama shi, domin ya san mai
gidan.

Injiniya Ahmad Kaita.

Abokin ogan sa ne a ofis, kuma yana aiki da
(Internet Global Services Jordan) ne."

Suna da manya rassa a Potugal, Iraq, Swedan,.
Hedikwatarsu na birnin New-York. Hamdala yayi,
sannan yayi ribas ya koma, farin cikin zuciyar sa
ya dawo sabo ful!

Washe gari karfe 9, yana (Internet Globar
Services). Ofishin Injinya Ahamd Kaita.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------
a

Bai sha wahalar ganin sa ba, saboda dama sun
saba gaisawa idan ya zo wajen ogan sa.

Bayan sun gaisa, yayi masa bayanin abinda ke
tafe da shi. Nan take dadi ya kama Injiniya,
domin ya san Ibrahim mutumin kirki ne, ogansa
ma na yabon sa.

Nan take yayi maraba da shi, ya kuma ba shi
kati, ya ce idan ya zo ya kira wannan
lambar.

Yayi godiya, ya fito.

Ofishinsu ya wuce yana mai murna da farin ciki,
babu abinda yake hangowa, sai an daura auran
sa da Nusaiba.

Wai! Yaya zai ji ranat? Yayi sauri ya dafe kirji,
dadi zai kashe shi.

Injiniya na koma wa gidan kan sa ya kira
Nusaiba, ya gaya mata anjima za ta yi bako,
kuma yana rokon ta, don Allah ta ba shi hadin
kai, domin mutumin kirki ne.

Ta amsa da to.

Ta koma dakin ta, ta yi iya tunanin ta, amma ta
kasa gano mai neman dama mata lissafi. Su
Sumayya da sun rantse sun maya ba su gayaea
Ibrahim gidan su ba, balle ya san mai gidan.
>
To ko hadin Injiniya ne? Ta tambayi kan ta. Ta
runtse ido takaicin duniya ya isheta.Dan ta
karami, an dame ta da maganar aure.

Ita kuma ba shine a gaban ta ba, tana son
isashen lokaci, don kula da dan ta.

Ta sallaci isha'i. Bayan cin abinci.

Wankan ma ta ki yi, balle ta gyara jikinta.

Yadda take tun safe, haka take zaune tana tana
jiran ta ga dan rigimar dake neman auranta.
>
Bata gama tunanin ta ba.

Zainab ta zo da gudu ta gaya mata sako, inji
Abbanta.

Ta kura wa Ameer ido dake barci, sannan ta
wuce ta fito.

Zuwa karamin falo, inda aka ce bakon yake.

Kai,"Inna-lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un!

Haka ta fada lkcn da ta yi ido 4 da Ibrahim.
>
Ya ce,"Dole ki yi salati, kin ga mayaeb zai cinye
ki."

Ta ce,"Saboda Allah menene na bn diddigi? Ya
girgiza kai,"Ba ki ma sani ba?

Lallai yau ne na gane cewa da hadin bakin ki
Abba ya hana ni auran ki."

Ta dan yamutsa fuska,"Allah ne,Abba bai isa ya
hana ka ba."

Kin di ni baki Nusaiba, kuma hakan yana k'ara
min son ki.

Wannan karon da alamun nasara, ki dubi tsawon
tazarar dake tsakanin Najeriya da Jordan, amma
Allah ya ce je ki Nusaiba mijin ki na can." Ta yi
dan murmushi, ta rasa me za ta ce da shi."

Ba karamin dadi murmushi ta yasa shi ba.

Ya dan langwabar da kai, ya sake fadin,"Kamar
an fama min gyambo Nusaiba, tun ranar da na
sake ganin ki tare da Sakina, kodayaushe sai mun
yi hirar Ameer ni da Husna, shi yasa har yanzu
bata mance da shi ba.

Da gangan ki ka batar da lambar da Sakina ta ba
ki, saboda ba kya son in san komai game da ke?


Ta ce,"Tabbas haka ne, na kuma kar6i lambar ta
ne kafin in san ko ita wace ce, da na zo na sani,
sai na kiyayi kai na, saboda tunanin me zai je ya
dawo?

Ya jinjina kai,"Kin yi gaskiya, amma da yake
Ibrahim mai sa'a ne sai ga shi abinda ya je, ya
dawo din.

Ko ba haka ba? Saura a ban dama, ayi ta ta
kare"

Ta ce,"Yaro na karami ne, ban ko yaye shi ba, da
dai............

Ya katse ta,"Ki na nufin Ameer? Je ki ji yadda yayi
suna a gida na, balle kuma ki kawo min shi, gaba
daya zai zama da na.Ta ce,"Ban tsara masa
hakan ba."

Ko?

Ta ce,"Tabbas."

Yayi dan shiru, kafin ya ce,"Ba kya so na dai ke
nan."

Ta ce,"Ban fad'a ba."

Ya ce,"Idan ba haka ba,"Ameer ne kawai zai
hana ki k'i aure na? Ta nisa kafin ta ce,"Har da
matarka, domin na lura Sakina na son ka da
yawa, bai kamata in shiga tsakanin ku ba.

Mun yi hira sosai da ita a jirgi, amma ka na
zuwa, ka nuna mata ka sanni, shi ke nan ta
sauya min fuska.

Ka ji dalilin yaga lambar da ta bani, don ba na
son tashin hankali."

Hankalinsa ya tashi kwarai, ya ce,"Ba ki fahimce
ta ba ne Nusaiba.......

Ta ce,"Haka ne Wallahi, ai ka ga lokacin ba ta ma
san halin da na ke ciki ba.

Ta ganni da Bebi, ba ita ba, kai kan ka ka yi
zaton ina gidan mijina.

Quite O.K a lokacin ba mu rabu ba, sai daga
baya.

To ina ga ace ga shi za ka aure ni?

"Babu abinda zai faru. Haka Sakina take, bata iya
rufe kishin ta, amma bata da fada, idan ku ka
fahime juna za ki gane tana da hakuri."

Ta ce,"Na ji."

In turo kenan?

"Ai na gaya maka ba yanzu na shirya yin aure
ba."

Ya runtse ido, dafe da goshi ya ce,"Nusaiba ba
kya so na.

Please!

Ki je ki yi shawara, abinda ki ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login