Showing 3001 words to 6000 words out of 29550 words

Chapter 2 - A JININSA YAKE PDF BOOK 3 End COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt

06 Dec 2024

2071

faruwa ne Doctor? Ban
gane condition din yarinya ta ba! Shi ma ya
mike cikin sanyin murya ya ce,"Cool down Alhj,
zauna." "No I can't sit Doctor! Kullum yarinya sai
k'ara rikicewa take! Why? Wai ba anan ku ka yi
mata tiyata ba ne? Ya ce,"Alhj babu wata
maganar an ta6o mata wata jijiya. Infact, aikin
ta bai shafi ko'ina a jikinta ba, sai inda Bebi
yake. Ka zauna mu yi magana, Please! Da kyar
ya zauna, shi ma Lkita ya zauna." Dama kai na
ke jiran zuwan ka mu yi magana. Nusaiba ta
fada cikin matsananciyar damuwa, wacce har ta
sanya ta fizge-fizge, alhalin tana da ciki. Babbar
matsalar ce ga mai ciki idan ta sami kan ta a irin
wannan yanayin, domin ya kan kai a rasa su
duka. Shine za ka ga mutan kauye da suka
jahilci abin sai su ce bugun jinin ne, maimakon a
hanzarta kawo ta asibiti, don daukan matakin
gaggawa, sai a shiga hayaki da shafe-shafen
turaren aljanu. Daga karshe ka ga an rasa uwa
da Da. Abinda na ke so ka gane anan, damuwa
babu abinda bata haifarwa, amma ina son ku
natsu, za mu bicike da kyau, mu gano aininhin
abinda ke damunta. A halin yanzun muna
Expecting comma ta shiga, abinda muke magana
kenan da sauran Doctor." Alhj fa bai
yarda."Wannan ba comma bace, ta6in hankali
ne, sbd haka idan ku yi bincike a kwakwalwarta,
ko nawa ne zan kashe! Ya ce,"Wannan duk ba
matsala, yanzu zan rubutu gwaje-gwaje da
hotunan da za'ayi. Idan an rubuta kudaden, sai
aje a biya." Rubuta min, in je a biya kudin."
Yana zaune Likita ya rubuta duk binciken da
za'ayo. Tare suka fito, ya hada shida Yaron da
zai raka shi ofisoshin da za su rubuta kudaden.
Al'amarin Nusaiba kuwa ta rikita kowa, kuka
kawai suke yi. Shi kan sa Bebin kukan yake
tsalawa, yana jin yunwa, amma ta hana su yi
'yan dabara a lika shi, ya sha nono. Naseer ya
doso wajen, tun daga Nesa ya tsinkari muryar
ta. Da gudun sa ya karaso, yana tambayar
Zarah! "Me ya faru?, Murya na rawa ta
ce,"Nusaiba ta rikice Kai tsaye ya shiga dakin, ya
zube jakar da ke hannunsa, ya nufi gunta yana
fadin,"Ya haka Umma? Duk suka dare, suka ba
shi wuri, tana kyallo ido ta gan shi, ta zaburo
tana mika masa hannu, "Abba na! Abba na, ina
ta nemanka za su kashe ni? Bai san lkcn daya
rungumota ba,"Menene? Iye? Ba ki san akwai
ciwo a jikin ki ba? Allah da ikon sa, shiru tayi,
tana ajiyar zuciya,"Kai na ke ta kira Abba na, ka
ki zuwa, kai ma ba ka so na ne? Idanuwansa
suka cika da kwalla. Kowa yayi waje yana share
hawaye. Ya jima kafin ya ce,"Ai gani na zo, me
aka yi? Wa ya sanya min ke kuka? Ta zura masa
ido ta ce,"Antina suka kashe min, shine suka zo
ni ma suka danne ni, za su kashe." An ce miki
Antinki bata mutu ba, tsaya ki gan ta. Zarah! Ya
kira ta. Ta shigo, ya jawo hannayensu ya
hada,"Kin gan ta? Antinki ce. Ta fizge hannunta,
ta saka ihu,"Ba ita bace! Allah ba ita
bace,"Antina ta mutu
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
Ya rufe bakinta ya ce,"Shi kenan na ce, shi
kenan ba ita bace." Zarah ta yi sauri ta fice.
Sannan tayi shiru. Ya dube ta ya ce,"Abinda ki
ke yi, ba shi da kyau, ki na jin Bebin mu na
kuka, kin ki bashi nono, me ki ke nufi? Ta
ce,"Abba na ina naga Bebi kuma? Ga shi can a
waje, yana kuka."Ta ta6e baki ta ce,"Ban haihu
ba, Antina ce ta mutu. Ya kamo ha6arta ya
ce,"Dube ni, ki saurara da kyau, za ki ji kukan
Bebi. A kawo shi ya sha? Tayi shiru, tana
kallonsa. Ya sake kiran Zarah, ya ce ta kawo
Bebi,. Ta zo da shi a shawul, ya kar6e shi, ta
tsaya tana kallonta! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki
gani." Kyakkyawan kallo tai masa! Ya ce,"Yauwa,
dube shi ki gani, kyakkyawa da shi." Ta leko ta
dube shi,"Abba na wannan k'aton Yaron ai ya
girme ni." Ya ce,"Ban son shirme, ba shi ki gani,
idan bai sha ba, ki min duka." Ya dora mata shi
bisa jikinta, ta 6allo wa Zarah harara, sannan ta
dubi Naseer,"Abba na ka ce wa matar nan ta
fita, ban son ganin ta. Munafuka kawai, duk
sune suka kashe Antina." Hawaye suka kawo wa
Zarah, ta juya ta fita. Ya ce,"To ta fita, ba shi ya
sha. Ta ciro ta ba shi, ya kama sai tsotsa yake
yi, bawan Allah ya sha kuka, shi yasa bai jima
ba, barci ya kwashe shi. Naseeer yayi zuru,
yana kallon su, tsabar tausayinta yake ji, kamar
ya ce wayyo Allah. Ta ce,"Abba na ka daina
kallo na mana." Ya ce, "Ah! Ai kowa dole in kalle
ki, tunda ina son ki, kin zama abar kallona. Ko
kuwa? Ta sadda kai, tana dan murmushi. Ya dan
k'ara matso ta, ya ce,"Kin ga har yayi barci, to
ke ma ya kamata ki kwanta ki yi barcin, ki huta
ko?Ta yi hamma mai tsawo, yana rufe da
bakinta, kafin ta ce,
"Barci?"
Kin ga ni ban son shirmen nan na ce.
Kawo Bebin a kwantar da shi, ke ma ki kwanta
ki gani."
Ta ce,"Bar shi kawai, ya yi min dadin rikewa."
Hirar su kawai suke yi, abin ya ba kowa mmk,
har Alh.Basheer ya gama zirga-zirgar sa, ya
dawo. Ummi ce ta mayar masa da yadda aka yi,
ta yi shiru ta natsu.
Ya shigo dakin a hankali Naseer ya mike yana
masa sannu da zuwa, da ta fasa wata irin k'ara,
gaba dayan su gigicewa suka yi.
Naseer bai san lkcn daya koma gun ta
ba,"Menene? Idanuwanta rufe tana fadin,"Ban
son ganin sa! Ban son ganinsa!! Munafiki
ne.............
Ya rufe bakin ta, yayin da Alh.Basheer yayi waje
da sauri. Naseer ya ce,"Ban son abinda ki ke yi
Nusaiba, gaskiya ni ma zan tafi." Ta ce,"Na
daina Abba." Ta ci gaba da surutu k'asa-
k'asa,"Munafikin banza, munafikin wofi, ya wani
shigo wa mutane ko kunya." Yayi shiru, ya
kyaleta, kwalla suka zubo masa, ya share.
Wannan al'amari da me yayi kama? Kuma fa
duk shine sila ko?
Ya tambayi kan sa. Wasu hawayen sharshar!
Suka fito, ya sake gogewa. Alhj kuwa yana tare
da su Ummi, shi ma sai da ya share kwalla,
sannan ya mayar da yadda suka yi da Likita,
kuma nan ba jimawa, za so zo su tafi da ita
dakin hoto.
Jama'a sun sha Zagi da tsinuwa lkcn da aka zo
daukan ta, har da Naseer din da yake fada aji,
ya zama munafiki, tunda yana gani zai kyale a
tafi a kashe ta.
Dole Likita yasa aka kawo masa wata allura, da
kan sa ya zurkud'a mata.
Take nan ta wuce luuuu....!!!
Ba rai, ba dalilinsa.
Sannan da masu daukan ta suka gara ta wajen
hoto.Har aka dawo da ita, bata sani ba, nan
suka bar ta tana ta barci. Hankalin kam ba a
kwance yake ba. 'Yan dubiya na ta zuwa gaishe
ta, amma tana barci, da yawa daga cikin su
daga Kaduna suke zuwa. Haka Antin Jordan
kodayaushe sai ta bugo ta tambayi jikinta. Bizar
ta kawai take jira a gama, ta kamo hanya.
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Sakamakon duk gwaje-gwajen da aka yi mata
suka fito. Likita ya kira Alhj ofishinsa, shi kuma
ya kira Naseer, domin mijinta ne, hakkinsa ne
ya san halin da matar sa ke ciki. Kowanne ya ja
kujera ya zauna gaban Likita.
Shi kuma ya firfito da sakamako, ya ci gaba da
bayani."A gaba daya binciken da mu ka yi, babu
wata matsala a tattare da ita. Kwakwalwarta
lafiya lau, zuciya ma haka, k'oda lafiya lau, haka
jirin ta lafiya yake.
Saboda haka abin nan dana fara gaya maka
Alhj, shi din dai za mu ci gaba da kula da ita
akan shi."
Alhj ya ce,"Yanzu ka na nufin tsabar damuwa ce
ta jefa ta a wannan yanayin? Ya ce,"Kar ka yi
mamaki, damuwa tana sanya hawan jini, kuma
babu ga mai juna biyu.
Saboda haka za mu ci gaba da bata taimakon
daya dace, sannan daga wajen ku a matsayin ku
na iyaye da mijin ta, rarrashi ne kawai. A ring'a
lalla6ata, a kodayaushe, hanklinta ya zamana a
kwance yake tare da samun isashshen barci.
Insha Allah za ta warware, sai kun yi
mamaki."Alhj ya munfusa, ya dubi Naseer,"Ka ji
ko? Wannan aikin ka ne, ko dama kai kadai take
son gani, mu duk mun zama munafukai. Don
Allah ka yi hakuri da ita, sannan a rink'a had'a
mata da addu'a.
Idanuwansa cike da hawaye ya amsa,"Ya zama
dole Abba, Allah ya taimake mu."
Duk suka amsa da Amin."
Tun lkcn aka bar wa Naseer ragamar komai
ahanununsa, kowa ya koma gida, sai dai su zo
akai-akai su duba ta, shi ma ta, taga, idan har
idan ta 2, idan kuwa har ka ga wanin Naseer a
kusa da ita, tabbaci hakika barci take yi.
Zarah ma an sallame ta, ta koma gida, amma
kodayaushe zuciyar na asibitin, shi yasa bata iya
daurewa kullum ne sai ta zo, koda za ta wuni a
waje tana lek'en taga tare da renon Ameer.
Haka Likitocin ta ke iyakar kokarin su ba dare,
ba rana akan ta.
Magana ce ta kudi. Alh.Basheer kuwa ya saki
komai ya dace ayi mata, komai tsadar magani.
Shi kuwa d'an gogon, bai gajiya da yi mata
hidima, shi ne cin ta, shine shan ta. Kullum
yana like da ita, suna hiar shirme, domin kuwa
shirme ce, yanzun nan za'ayi magana dai-dai,
lkc guda sai ta ya6o shirmenta. Babu abinda ya
dame ta.Idan dare yayi kuwa tana barci, zama
yake bisa kujera ya zura mata ido, yana yi mata
addu'o'i. Idan ya tuna da bayanin Likita kuwa,
hawaye yake zubdawa sosai, domin ya tabbata
shi ya tara maya damuwar sa ta jefa ta wannan
mawuyacin halin.A haka so da k'aunar Nusaiba
suka zauna kwarai da gaske cikin zuciyarsa, har
yana mamakin kan sa."
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Sabon
shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
Kwanan ta 11 yau, ya gama kintsa Ameer, ya
kwantar da shi cikin (Net) din sa. Ya dube ta,
tana ta lissafin zucci, ya ce,"Za ki sha Tin ne
kafin ki kwanta? Ta ce,"Had'o Abba." Ya had'o
mata dai-dai wanda ta saba sha. Ya zo da shi
bakin gadon, ya zauna. Ya debo a cokali ya
ce,"Ungo, sha 'yar gidan Abbanta." Ta dube shi,
tayi murmushi," Miss you."Dariya ta ba shi, ya
ce"Za ki fara ko? Ai ni fushi na ke da ke."Me na
yi Abba na? Ya mika mata, ta kur6e ya
ce,"Batan kin kori kowa, mutane na son ganin
ki, amma kin hana, me yasa?
Hmm... Abba na kullum ina raba ka, amma ba
ka ji.
Me za'ayi da munafukai? Ya ce,"Na fa hana ki
ce musu munafukai. Haka dazu ki ka cewa
Umma, sa'ar ki ce?
Ta dan 6ata rai, tayi shiru, ya miko mata Tea ta
ki kar6a. Ya aje cokali ya dago ha6arta."Fushi ki
ka yi? Da ni ki ke fushi, shi kenan bari in zo in
tafi." Ta ce,"Yanzu saboda Allah Abba duk
wanda ya nuna baya so na, ba munafiki bane?
Yanzu dubi yadda ka ke k'aunar Naseer, amma
k'iri-k'iri ya nuna min, baya so na, yayi ta
wulakanta ni. Saboda Allah Abba me zan kira shi
ba munafiki ba, tunda ya munafunce ka."
Tunda ta soma mgn, gabn sa ya yanke ya fad'i,
yayi sukuiti duk jikin sa ya mutu, ya rasa me zai
ce? Ta zura masa ido, ta ci ga,"Abba ai dai ka
san na maka biyayya da ka ce min shi ka za6a
min, ban maka musu ba ko, Amma ka san Allah,
shi baya so na, wannan cikin na jiki na ma, ya
ce da shi zan koma gidanmu, baya so. Na ce ai
ban je da d'a gidan sa ba, ko fan fadi gaskiya
ba?
Hankalin Naseer fa ya yi mummunan tashi, ya
tabbata wata rana a surutanta za ta iya fadi a
gaban kowa. Idanunwan suka kad'a, ya aje Tea
bisa dirowa ya rufe.Ya kamo kafadunta 2, suka
yi wa juna zuru kafin ya ce,"Wannan maganar
bata dace ki na fadar ta ba 'yar gidan Abbanta.
Naseer masoyin ki ne, ni ya gaya min yana son
ki kwarai da gaske."
Ta girgiza kai,"Na rantse da girman Allah, karya
yake maka Abba. Naseer munafiki ne, ina gaya
maka maganar nan, ka yarda da ni Abba." Ya
sake ta ya kama kai.
Ta bi shi da kallo ta ce,"Mamaki ma ka ke yi?
Kai har yanzu ba ka san mutane ba, ka na dai
kallo aka kashe Antina, me za'ayi?
Yayi hucin zafi ya ce,"Duk na ji, amma kin san
abinda na ke son ki da shi ?
Ki kyale maganar nan, kar ki gaya wa kowa, ni
zan yi maganin abin. Kin yarda?
"ka dai gaya masa, idan na haihu zan aje Yaron,
shi zai maida shi cikin lemon
gwangw........................
Ya like bakinta,"Nusaiba na ce ki bar maganar
nan, zan fa tafi abi na." Ta ce,"Yi hakuri." To kin
yarda ba za ki gaya wa kowa ba? Na yarda,
amma ka san Allah, ka yi hankali da wad'annan
mahaukatan da suke zuwa 6arayi ne."
Yayi shiru yana kallonta, duk ta dagula masa
lissafi." Ba ni Tin mana." Ya dauko ya ci gaba da
bata, sai zuba masa surutu take, shi kuwa bakin
sa ya mutu har ta yi barci.
Yayi tagumi bisa kujera, ya rasa abinda ke masa
dadi.Ta dai ce ta yarda ne kawai, ba za ta sake
fadi ba, amma abin maras hankali, ai ba'a sirri
da shi. Dan saukin ta ma, bata kula kowa sai
shi. Daran nan bai runtsa ba saboda tunani.
Safiyar yau kuma daga ya ce, bude baki ayi
burosh, shi ke nan ta fasa kuka. Yayi rarrashin
dunuya, ta k'i yin shiru, ta k'i kuma mgn, a
haka ta shafe sama da mintu 30 ita da kan ta ta
yi shiru. Ta gyara kwanciya, ya sanya mata ido,
tana ta ajiyar zuciya, har barci ya sace ta.
A lokacin shi kuma ya fara na shi hawayen da
kyar ya iya tsaida su, saboda tsabar tausayinta.
Ko me yasa ta kuka?
Oho!
Ya tambayi kan sa, ya ba kan sa amsa.
Idanuwan sa suka kara ja, kamar garwashin
wuta, dama ga rashin barcin da bai yi ba jiya.
Yana nan zaune zuru, ya ji motsin Ameer, shi
ma ya farka. Ya tashi ya zuba masa ruwan dimi
a fida ya zuba glucose ya karkada, sannan ya
dauko shi suka fito waje, ya zauna a kujera yana
ba shi har ya shanye. Idon sa 2, amma baya
kuka, yana ta 'yan wasannin sa. Naseer na taya
shi.
Muryar Alhj kawai ya ji yana masa sallama, ya
dago da sauri yana amsawa. Tare suke da Ummi
da Antin Jordan. Ya mike yana masu sannu da
zuwa. AntIn Jordan ta kar6i Bebi tana
fadin,"Sannu Naseer, don kai ne abin gaisarwa.
Yaro duk ya rame." Yana murmushi ya
tsugunna, ya gaishe su.Alhj ya ce,"Mutuniyar
barci ta ke yi ne? Ya ce,"Eh. Ummi ta ce,"Yauwa
mun yi sa'a, shigo Fatima ki gan ta."Suka
dungoma cikin dakin, shiru suka yi suna kallon
ta kawai, don kar su yi surutu ta farka. Sun
kusa minti 10 a tsaye, sannan suka fito dan
koridon. Naseer ya baza darduma, suka
zazzauna. Ya koma gefe ya zauna, suka ci gaba
da tambayar sa yanayin jikin na ta?
Ya ce,"Da sauki, an gode Allah, amma ko dazu
ta sha kuka, kuma ta k'i magana, abinda ma ya
sa ta barci ke nan."
Antin Jordan ta goge kwalla, ta dubi
Alhj,"Gaskiya yaya idan babu wani ci gaba a fita
da ita waje kawai." Ya ce,"Wannan maganar na
rai na, akwai iiya kwanakin da na dibarwa
Likitocin nan din ne, idan sungaza, zan dauke
ta."
Ta ce,"Wannan tashin hankali da yawa yake." Ya
ce,"Jarabci ne, mun gode Allah, muna rok'onsa
sauki.
Kai Naseer ka yi ta hakuri, ka ji?
Ya ce,"Hak'uri na mu ne duka Abba."
Haka suka kasance tare, jama'a na ta zuwa
kamar kullum. Koda ta farka. Naseer ne kawai
ya shiga, ya kai mata Bebi. Allah da ikon sa
babu kuka, sai hira kamar ma ba ita ta sharari
kukan dazu ba.
Yayi mata burosh, ya bata Tea, ta sha. Abin
yana ta 6a Antin Jordan mmk har ta
tambaya,"Yanzu ina shiga, sai ta fara Ihu?,
Ummi ta ce,"Ko za ki gwada ne?
"Don daukan alhaki? Na gan ta ta taga, ya isa.
Allah ya yaye mata."
Ta ce,"Amin. Kwananta 7 ta koma Jordan.
Ranar da ta tafi, ranar Kausar ta iso da mijinta.
Bata 6ata lokaci ba, ta fadawa dakin, kanta ta yi
ta rungume ta sa kuka. Wani ihun da Nusaiba ta
yi, dole ta sake ta, tana kallo, jiki na rawa. Ta
runtse ido, tana zagi tana fadin.
"Ban son ganin su. Ban son ganin su! Naseer ya
rirrike ta. Mijin Kausar ya fito da ita, me za ta yi
ba kuka ba. Haka ta fada jikin Ummi, tayi ma
isar ta. Naseer kuwa da kyar ya shawo kan
Nusaiba tayi shiru, ta daina zage-zage. Ba
karamin Huashi Kausar ta bata ba, sbd ta6a tan
da tayi.Yini guda masifar da ta rink'a yi
kenan,"Wata munafuka ta zo ta cakume ni za ta
kashe ni! Sai bayan la'asar tayi barci. Kausar ta
je gun ta, tayi mata addu'o'i. Hawaye na zuba.
Da yamma lilis suka koma Kaduna.
Haka Kausar ta tafi da bak'in ciki, a duk lkcn da
ta tuna hawaye, ke zubar mata.
(Allah sarki Nusaiba


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100






Ajininsa yake 3-02
Posted by ANaM Dorayi on 08:53 PM, 20-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______



Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------


To shi kenan ya wuce." Ya kamo ha6ar ta, yi
dariya,"Yi dariya 'yar gidan Abba!

Ta fado kirjinsa, tana murmushi.

Ya rungume ta, ya runtse ido, wasu kwalla suka
yi masa caa, fadi yake a ransa, "Son ki ya kama
ni Nusaiba, ki yafe min don Allah.". (Hhhhhhh,
Anzo gurin, ammafaaaa...uhm! Maji ma gani)




Bai ko san ta kici-kicin tashi ba, sai da ya ji tana
kira,"Abba!

Ka shake ni!

Ya hanzarta sakin ta, yana goge kwallah. Ta bi shi
da kallo,"Wash!

Ka wani matse ni Abba, ai sai in mutu."Ya tashi
ya bata wuri, ya shige bayi ba tare da ya ce
komai ba.

Jim kadan ya fito, ya wanke fuskarsa, kwance ya
same ta, ya matsa gabanta ya ce,"Hirar ta isa
haka, ki yi barci ki huta." Ta amsa da ka, ya
duk'o ya sumbace ta, ya ja mata mayafi. Ya ja
kujera ya zauna, ya sauke numfashi,"Allah ka ga
iya kokarin da na ke yi. Allah ka taimake ni
yarinyar nan ta sami lafiya.

Ta ce,"Ka kwanta mana Abba." Ya ce,"Zan
kwanta, ke dai yi barcin ki." Ta rufe ido.

Tare da gyara kwanciya.

Da asuba ya fito bayi da alwalar sa, ya shimfida
sallaya, yayi sallah. Ya jima yana addu'o'i kafin
ya jiyo motsin ta.

Ya waigo yana kallon ta, ta tashi zaune, tayi mika
tana salati. Ta kalli can, ta kalli nan, bai ce da ita
k'ala ba.

Ta k'ura wa Bebin da ke barci cikin (Net)
ido.

Ta dago kai ta dube shi, suka yi ido 4.

Yayi murmushi, ya ce,"Kin ta shi?

Fashewa tayi da kuka, ya taso da sauri ya zauna
gefen ta."

Nusaiba, ke Nusaiba, za ki fara koke-koken nan
ko?

Tayi shiru tana tunaniin Antin ta.

Hawaye na ta ambaliya.

Ya rik'o ta, ta kwace jikin ta, kuka take tana
k'arawa.

Ya ce a ran sa,"Na shiga 3, yau kuma da kukan ta
tashi." Ya matso, ta matsa. Ya ce,"Ni Nusaiba, ni
ki ke gudu? Bata kalle shi ba, balle ta ce wani
abu. Ya sake matsowa, ta matsa. Ya ce,"Shi
kenan, bari in yi tafiya ta, in tafi ko? Ta amsa eh,
da kai. Ya ce,"Tabd'i! Da magana yau,"Cikin
ransa.Ya rasa yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login