Showing 6001 words to 9000 words out of 24998 words

Chapter 3 - MATAR UBA HAUSA NOVELS BY MRS ALKALI.doc

26 Oct 2025

377

acikin bukkan ko sallama babu , wani kyamusheshen tsohone fari amma kanaganinsa kaga bafukatani yana sanye da rigar saki da hula malafa irin ta fulanin jeji akansa , gefensa wasu turarukane masu warin tsiya ga kwarya da faifayi agabansa da wani katon madubi awajen,
Murmushi yayi yace maraba da qawayen junah ku qarasu yanunamuasu gabansa ,
Haka su inna su kazube sunamasa barka da lokaci yace meyake tafe dasu donyasan ruwa baya tsami banza.


('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*

Page 9??

Malam aikin dakamin akan mijina ne nakeso aqara qarfin aikin ajikinsa dan naga yanamin katsalandan a wasu al amurana , sannan maganar yarsa shatu inason asamasa tsanarta aransa kuma duk abunda zanmata karyayi magana akai ma'ana inason arufemin bakinsa ,
Inason asa ta lalace tafara bin maza yadda zatana kawomin kudi don yarinyar akoi surah kyakkyawa ce sosai za ta dau hankalin maza ,
Sannan yata habbi ina son adubamin meyake damunta don batada saurayi ko guda daya,
Malam jafaru yace toh ba matsala haka yajawo kayan aikinsa yafara dube, bayan yagamane yace , lallai mijinki yanada taurinkai jikinsa akoi tsari shiyasa wancan aikin be kamasa sosai ba Amma akoi aikin da zanmasa wadda da wuya ya tsallake hakan , sannan bazai iya tsanar yarsa har cikin zuciyarsa ba amma akoi abunda za za amasa duk wani abu dazaki mata bazai iya yin maganaba koda abun baimasa dadi a zuciyaba , sannan babu karuwanci a qaddaran shatu , saidai inkin yarda za a samata bakin jinin da saita gwammaci mutuwa da shi, yarki habbi bakin iskane yake damunta shiyasa maza basa gabanta kuma shi yake hana samari zuwa gurinta, inkinyarda sai afara aikin,
kallon juna inna rabi da aminiyarta sukayi , inna larai ne tamata alama da ta amince , haka tace malam na amince ,yace ba matsala zaku iya tafiya ladan aiki sai buqata tabiya , haka sukayi godiya suka taho gida , sai dab da magariba suka qaraso duk sun riga da sungaji, Inna Rabi ne tace naso ace shatu tafara bin maza kinsan bakaramin kudi za asamu da yarinyannanba dudda batagana zama budurwaba , don yanzu shekarunta 15 yakike gani inta goge a harkar ainikam kakata ta yanke saqa , dudda haushin yarinyar nakeji amma naso na nemi kudi da ita ,hmm aini bantaba ganin yarinya mai kyauba kamar shatu saikace yar aljana, Inna Rabi tace shiyasa naqara tsanarta duk tafi su hannatu kyau yarinya sai kace jinin larabawa,
Amma ai da babu gara ba dadi tunda ba bin maza a qaddaran ta , aigara asamata bakin jinin kawai , dariya sukayi Inna larai tace bari nazo nawuce kafin mijinki yadawo, haka sukayi sallama inna larai ta tafi.

('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*

Page =??

Tundaga wannan rana rayuwa tasake yiwa boddi zafi , wata irin rayuwa akeyi agidan malam adamu wato baffah, sai abunda inna rabi ta fada akeyi,

Shikanshi baffah abun yana damunsa yadda gidansa yadawo sai dai baya iya magana akai ga azaba da Inna Rabi ta ganawa shatu amma baya iyamata magana kuma yanajin zafin abun azuciyarshi amma bakinsa baya iya musata,ga su hannatu kullum cikin fita yawo da samari kuma sai tsakar dare zata dawo nanma bai isa yace uffan ba,
Tabangare habbi sai abunda ya qaru don ahalin yanzu takoyawa qanwarta mairamu neman jinsi wato lesbian, habbi da hansai awaya sukafara kallace kallacen videos din lesbian a hankali abun yana shiga zuciyarsu haryakai ga sunfara aikata hakan a tsakanin su gashi har sun koyawa mairamu batare da Inna Rabi tasaniba, ita dai malam jafaru yace bamata bakar iskane take damun habbi shiyasa bata da samari,
Inna Rabi, duniya tamata dadi komai natafiya yadda takeso , ahalin yanzu har ansa ranar auren hannatu da alhaji issaqa, sai shirye shirye akeyi , komai ya kankama,
Zokaga murna wajen inna rabi yarta zata aure mai kudi sai rawan kai takeyi ita da aminiyar cin mishenta wato inna larai,
Rayuwa tayiwa shatu zafi , ahalin yanzu tana SSS 3 sunashirin zana jarrabawar karshe wato neco,duk yadda Inna Rabi take takuramata , bai hanata zuwa makaranta da isilamiyaba dudda asha ruwan tsuntsaye takeyi ba kullum take zuwaba ,
Shekarunta 17 a halin yanzu , suranta na yammatanci duk sunfara baiyana amma ba sosai ba sha'anika da jikin fulani,
Shatu tana da tsayi amma ba sosai ba fiskanta dan dedai ne ba mai fadiba gata da siririn hanci wanda ya sauka harkan bakinta gashine kwance asaman goshinta yan kanana bakake sunyi luf luf dasu gwanin sha'wa tana da wasu irin idanu manya masu daukar hankali zaka dauka bacci takeji amma bahakaba haka hallitan idanun suke , dudda wahalan da takesha awajen inna rabi bai hana fatanta kyau ba dan haka Allah ya halliceta, wannan shi ake kira da natural beauty,

Biki ya kankama yau ake daura auren hannatu da angonta alhaji issaqa, bayan daurin aure ne anata shirye shiryen kai amarya dakinta , inda kawayenta suke ta shiga da fita domin karban kudin fidda amarya,
Shatu ne take zaune rakube a gefen dakin inna rabi, inna larai ne ta dubeta tace ke Shatu ke bazakije kai amarya bane kowa nata shiri kekinrakube saikace wata bare,ai kya shirya kije kema ko kyasamo mana wani alhajin acikin abokan ango, shewa Inna Rabi tayi tace inbanda abunki,kema larai ina shatu ina abokan ango ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke kintabajin anyi sallama agidannan ance Shatu tazo , ai shegen bakin jinine da ita tayi gadon uwarta kinsan haka uwarta tayi saida akabama malam adamu sadakanta sannan ta auro, dariya sauran matan sukayi wata acikinsu tace sai shegen kyau kamar jinin larabawa, amma ba mashinahine wannan ai shine kyan dan maciji,
Qawayen Inna Rabi ne sukasa shewa Inna Rabi tace ai ita da aure sai dai taga anayi, haka sukayita maganganunsu,
Shatu ne ta tashi tashiga dakin su fashewa da kuka tayi tana tuna innar ta Hajjo mutuwar inna tana dawomata sabo,
Ita kanta abun yafara damunta tunda take bata taba saurayiba bawanda yataba cewa yanasonta , Amma tasha jin yanmatan ajinsu suna yaba kyanta harcewa akeyi duk makarantan su ba wadda tafita kyau,
Kuma yawanci anbada yanmatan ajinsu kusan ma duk itace tarage batayi engagement ba ,
Qara fashewa tayida kuka mai stuma zuciya , tashi tayi tafita tayiwo alwala tazo ta fara sallah don nemawa innarta gafaran ubangiji,

('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*
Page 1?? 1??

Ankai amarya hannatu dakinta anwatse anbar amarya tana zaman jiran angon ta,
Ango ne yashigo ko sallama babu yana sake da babbar riga tun na daurin aure taci uwar sukuizin , fiskarna sai sheki takeyi duk maiko,
Hannatu ne ta daga kai tana kallon angon nata jin motsin mutum ,haka tayi arba da bakar fiskarahi ga katon tumbinshi agaba kamar mai shirin haihuwa, don alhaji issaqa irin mazan nanne masu kiba ga tumbi kuma gajeru , haka tasauqe ajiyar zuciya da ta tuna ai kidinsa ta aura to ita ina ruwanta da muninsa,
Zuwa yayi ya zauna a gefen gado yace amarya ansha kyau , murmushi tayi tace alhaji na kenan kaima ai kasha kyau duk kyauna ai ban kaikaba , murmushin jin dadi yayi jin yadda amaryarsa hannatu ke yabonsa ,yace Hannah kenan akoi ki da dadin baki tace badadin baki bane alhaji haka zancen yake, miqa yayi yace wlh duk agajiye nake kinsan abunka da hidimar biki akoi gajiya.
Tashi yayi yacire babbar rigansa ya ajiye a gen gadon hawa kan gadon yayi yaja pillow guda daya ya kwanta ko minti biyu baiyi da kwanciyaba sai munsharinsa hannatu taji saikace wani rago,

Dudda sun sha sheke ayarsu a waje kafin ya aure ta Amma batayi zaton haka darensu na farko zai kasance ba don ita tazaci zaiyi ta rawarqafa akanta amma saitaga yabuge da bacci ,
Haka tatashi ta tube kayan jikinta tasa na bacci ta hawo kangadon tafara shafashi, cikin bacci alhaji yaji ana tabashi juyi yayi yadan bude idonsa yace amarya lafiya kuwa , hannatu ne tace haba alhaji, ka konta baka chanza kayan jikinkaba sanna saikace bayau bane daren farkonmuba,

Tsaki yayi yace kajimin wata magana awajenki , to wani dare ne jamage bai ganiba kina zancen daren farko inzaki konta kizo ki konta inbakya jin bacci nidai kibarni don bacci nakeji,

Haka alhaji issaqa ya juya yaci gaba da baccinsa ,
Wani takaicine yakama hannatu azuciyarta tana cewa saikace wani abun arziki yakemin baisan maleji nakeyi dashiba, yanzuma nasan ba gamsar dani zaiyiba saidai inrage zafi ,amma shi har magana yake fadamin ,inba don kudinsaba me zanyi dashi ,hmm zaisan yayi da yar halak, haka taja pillow ta matsa jikin alhaji ta konta ko second biyu batayi da mannuwa ajikinsaba yatureta gefe, yajara kwanciyarsa yacigaba da munsharinsa.
Toh pha amaryar alhaji maimanja asuba ta gari>?#?>?#?>?#?

('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*

Page 1?? 2??
"GOMBE STATE" Federal low-cost

Wata matashiyar mata ce dazata kai kimanin shekaru 45 zaune acikin katafaren falon , wanda yagaji da kyau ,kallo daya zakayiwa fallon kasan ankashe kudi , lallai kudi sun koka awajen
Kyakkyawa ce amma ba sosai ba dudda ahekaru sunfara ja amma kallo daya zaka mata kasan tana kula da jikinta yadda yakamata ,
Tana zaune bisa kujera ta daura kafa daya kan daya ,sanye take cikin wani hadedden leshi mai uban tsada wuyanta da hannunta sun sha sarka da awarwaro da zoben azurfa,
Inka kalleta sai ka sake kallonta dan zaka zata gasar kyau ko kolliya na duniya zataje don fiskarnan tata tasha powder da jambaki harda jagira irin na yanmatan zamani dasukeyi tayi, sai kamshi take bazawa,
Ajima tadaga kanta takallah agogon da yake manne asaman parlourn nata kamar dai akoi wanda take jira,
Alamar tafiya taji ,ko daga kai batayiba sabida tasan bawanda take zaman jiran sa bane,
Jitayi an zauna kusa da ita sai alokacin tadaga idonta ta kalleshi,
Wani dottijone me kimanin shekara 65 , bakine , amma irin baki mai kyau dinna wanda ake kira black beauty, kana kallonsa kasan baya cikin wahala dan jindadin da yake ciki ya boye ainihin asalin shekarun sa, dafa kafadarta yayi fiskansa dauke da damuwa shima, yace bana son kina saka damuwa aranki haka , ko so kike nima damuwar ta hadu tamin yawa, ajiyar zuciya ta sauqe tace badole nashiga damuwaba ace danmu kwaya daya munkasa magan ce masa matsalan da take damunsa haba alhaji inna ce maka abunnan baya damuna namaka karya.
Hakane hajiya luba amma ya zamuyi haka qaddarar sa take ,.amma dai alhaji bazamu zuba masa ido haka ba yakamata ,aduba lamarin, hakane hajiya luba Allah ya shige mana gaba.
Qaran bude gate ne yasa sukayi shiru da hiran da sukeyi , hajiya luba ne ta tashi da sauri , ta nufi window tadaga labule tana lekawa, alhaji saleh ne yakalleta yana girgiza kai, yana mamakin yadda hajiya luba take damuwa da lamarin tilon dansu ,dudda yagirma ya mallaki hankalin kanshi amma kulawa na musamman takebashi,
Aharaban ajiye motocin gidan yayi parkin wata bakar mota wadda kallo daya zakayiwa motar kasan bata yarabane dan anzuba kudi wajen sayan,
Bude marfin motan akayi , wani kyakkyawan kafa aka zuro daga cikin motar sanye yake da wani kyakkyawan takalmi na maza dudda kafar baki ne amma bai hana takalmin haska kafarsaba, yakai kusan minti biyu sannan mamallakin kafar ya fito, ya Allahu , wani matashi ne mai kimanin shekara 35yrs, bakine ba sosai ba fatarsa tana sheki , yanada dogon hanci ,girarshi yana da cikar gashi baki kamar yanda kansa yake dauke da bakin gashi koncecce, irin na fulani, idonshi qanana ne masu daukan hankalin me kallonsu,yana da tsayi, kallo daya zakamasa kagane ya na motsa jikinsa sabida yadda jikinsa yake murde,
Kyakkyawa ne ajin karshe zakace shi yayi kansa fitowa yayi daga parkin space din hannunsa dauke da brief Case dinsa ,
Fiskarnan tasa a hade take tamau zaka ce baisan wani abu ba mai suna dariya , yahade fiskarsa tamau, baba maigadi ne yakemiko gaisuwa , alhaji qarami sannu da dawowa , hannu kawai yadagawa baba maigadi batare daya ce masa uffan ba ,wucewa yayi hanyar main parlour yanufa,
Hajiya luba dake jikin window idonta a lumshe tana shaqar sassanyan kamshin danta dake bugo kofar hancin ta.

('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*

Page 1?? 3??

Cikin parlour yashigo bakinsa dauke da sallama kasakasa inba kallon sa kakeyiba bazakace yayi sallamar bama, alhaji saleh ne ya amsa yana mai fadada fara'ar sa , yana cewa kaga likita bokan turai har andawo, sassauta fiskartashi yayi jin abunda dady yafada ,matsowa yayi kusa da dadyn yadan duka yace dady barka da gida, yace yauwa barkanka dai, ya aikin ,yace lafiya qlu alhmdullah,
Juyawa yayi wajen da hajiya luba take tsaye tana kallon sa fiskanta dauke da murmushi kai kace ba ita ne ta hade fuskarna tata dazu ba.
Zama yayi kan sofa yace momy barka da gida, murmushi tayi tace barka dai my son andawo lpy, yace lpy qlu momy.
Mikewa yayi da brief Case dinsa a hannu yanufi stairs, momy ne tayi magana tace son bazaka tsaya kaci abinci ba tudazu
na hadamaka da kaina, bai fasa tafiya ba ciki ciki ya amsa da mom I'm okay naci abinci da Dr mahmud,mom bata sake cewa komai ba sabida inda sabo tasaba da halinsa na miskilanci tarasa kabeer wani irin yaro ne , yanada wuyar sha'ani,ita kanta kabeer na bata wahala da shegen miskilancinsan nan saikace ba itane mahaifiyarsa ba,
Dady ne yace wanna dannaki ai sai ke mutum kullum fiska ba fara'a, haba sai kace wanda akayiwa saqon mutuwa,
Alhaji kenan kafi kowa sanin halin da alhaji qarami yake ciki dole ko bai fada mana ba abun yana damunsa, kawai dai don yana da zurfin ciki ne ga ciwon dayake fama da ita ace abu yaqi ci yaki ci yaki cinyewa, kullum da abun nake kwana nake tashi, amma kanaganin zamuci gaba da zuba masa ido yazau na haka ,
Jikin dady ne yayi sanyi , wani tausayin dansa ne yaqara shiga zuciyarsa, murya asanyaye yace hajiya yakike so ayi kina ganin wa zaiyadda yabawa alhaji qarami auren yarsa bayan wannan lalura dayake dauke da ita.
Hajiya bazan boyemiki ba wlh koni na tsorata da lamarin alhaji qarami kawai dai bayaddana iyane,
Shiru mom tayi tace alhaji yakamata ace ansake masa wani auren ko Allah zaisa adace amma baza mu zauna muzuba masa ido yaci gaba da zama a hakaba shekarun sa tafiya suke , duk sa'anninsa sunyi aure daga mae yaya biyu sai mai yaya uku , shi har yanzu ya gagara ajiye matarma,
Dady ne yace kina ganin wazai basa auren yar sa agarinnan , ni kaina bazan iya tinkaran wani dasunan nemawa alhaji qarami aure ba, don bakisan yadda maganarsa ta bazu bane a cikin gari ba,
Shiru mom tayi chan tace haka ne alhaji, Amma me zai hana aduba ko da a kauye ne kaga su basusan ma waye shi ba bare asan abunda yake faruwa da shiba, inyaso sai mu jarraba ko Allah zaisa adace,
Hajiya kina ganin ba wata matsala yin hakan , alhaji inaga ba matsala dady ne yace to nabarmiki wuqa da nama a hannunki hajiya ta murmushin Jin dadi Mom tayi tace baka da matsala alhaji na.
Bayan ya haura sama wani kofar daki ya nufa yasa key ya bude , wani sassanyan kamshi ne ya ke tashi aciki sallama yayi ciki ciki dudda yasan ba kowa a dakin amma hakan dabi'ar shi ce ,takalmar kafan shi yacire sannan ya qarasa shiga cikin dakin parlour ne ma dai dai ci asaman ba wani tarkacene aciki ba amma ankashemasa kudi wucewa yayi cikin bedroom dinsa , toilet yanufa dan yana buqatar ya watsa ruwa don yau yagaji sosai soyake ya konta ya huta, bayan yafito daga toilet din daure da towel a jikin sa yana goge leman da ke jikinsa,
Gaban dressing merro yatsaya yadau turare ya goga ajikinsa sannan yajuya yanufi gadon da towel din yakonta , bacci yakeson yi , rufe idanunsa yayi yanatunanin rayuwarsa

SHIN WAYE DR. KABEER...?


SHIN WANI LALURANE YAKE FAMA DA ITA.....?



ME YASA MOMY DA DADY SUKE SON NEMAMASA AURE A KAUYE......?

SHIN MOMY ITACE TAHAIFI DR. KABEER.....?

KUBIYONI DAN JIN AMSOSHINKU.....!!!


('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*


Page 1?? 4??

Dr. Kabeer Maina Saleh shine ainihin sunansa, babban likitana abangaren mata a babbar asibitin jahar GOMBE, yana daya daga cikin likitotin da ake ji da su awannan asibiti, sabida kwarewar sa da kwazonsa ,
Da deya tilo awajen alhaji maina Saleh shaharerren maikudi ne acikin jahar GOMBE yanada gidanen mai, da manya manyan plaza, ba a cikin garin gombe kadaiba.
Yana da mata daya hajiya zulai itace mahaifiyar dr kabeer Allah yamata rasuwa tun Dr kabeer yana shekara hudu a duniya.
Bayan rasuwarta ne dady ya auri hajiya luba itama bazawara ce saidai bata taba haihuwaba, tadau son duniya ta daurashi akan kabeer inba wai fadamaka akayi ba baka isa kace ba ita ta haifeshi ba.
Dr kabeer tunyana dan shekara 25yrs yafara fiskantar matsala, yanada karfin sha'awa wanda idan abun yatashi yake fita daga hayyacin sa , da farko momy da dady basu dau abun serious ba sai daga baya ne abun yafara tabasu anyi maganin asibiti abun yaki sannan anyi na gargajiyan ma shiru , shine dady yanke shawaran masa aure, dudda momy ta hana sanda suka kai ruwa rana kafin ta amince , haka dady ya nema masa auren yar abokin sa safiyyah randa aka kawo safiya gidan washegari sai gawarta akasamu , bayan angama zaman ba kwai ne mahaifin safiyyah yace ma dady ga kanwar safiyyah mai suna sultana haka aka daura aure ta tare , kazalika itama washe gari sai gawarta aka dauka, wannan abu ya matuqar tada hankalin mutane musamman su Mom da dady, haka aka hakura aka fawwalawa Allah komai,

Bayan wani lokaci ne ciwon kabeer sai gaba gaba yakeyi, haka dady yasake kawo shawaran yimasa wani auren ko Allah zaisa adace awannan karon MOMY ta amince dan itama ciwon nasa yana damunta, haka dady yasake nema masa yar makwabtar su itama randa ta tare washegari sai gawarta aka dauka , wannan abu da yafaru shiyasake daga hankalin jama'a anata yamadidi da zancen wasu suce shiyake kashe matansa wasu suce aa aljana ce ta aure sa ,
Shi kansa kabeer ya girgiza da wannan lamari sai dai bayanda zaiyi da lamarin Allah, shidai baitaba jin yana son wata ya maceba duk matansa zabin abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login