Showing 123001 words to 125146 words out of 125146 words

Chapter 42 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete writing by Nimcey Sarauta .txt

25 Nov 2024

4833

ɗin da take ciki ba, bai ci ace sun juya mata baya ba, suna bawa jama'ar gari damar d su faɗi duk abinda sukai niyya akan Majeederh, Mami cikar imanin mutum shi ne yadda da ƙaddara cikakken mumini shi Ubangiji yake jarabta ko dan tabbatar da imaninsa, wallahi ba gama garin mutane Ubangiji yake nunawa jarrabawa da ƙuddirarsa akan su ba, mu yarda ne bai kawowa Majeederh mijin aure ba, mu yarda jinkirin aure ta samu" Mami ta ce "Idan mu mun yarda jama'ar gari fa?" Latifa tayi shiru can kuma ta ce "Mami mutum tara yake bai cika goma ba, a jikin ko wanne mai rai akwai zuciya ita take saƙa masa komai, to at this point ba zaka taɓa hana mutane abinda sukai niyyar faɗa ba, haka halin ɗan adam yake, baka da gadonsa yana da gadon maganarka, wani ma bai sanka ba bai san ya kake gudanar da rayuwarka baz bai san komai game da kai ba, ji kaiwa zai yi mutane suna magana ya ara ya yafa ya ɗora nashi akai, sbd kawai baya ƙaunarka ko yana baƙin ciki da abinda kake ko yadda yake gudanar da rayuwarka, wani kuma haka halinsa yake da haɗa ƙanzon kurege haka mutum yake, The world is big, the challenges in it are many, the people in it each have their own character" Latifa tayi shiru tana goge hawayen idanunta ta ce "Human nature is difficult to deal with, whether you do well or not, you will never stop a person from saying what he intends, kinga kenan babu yadda za mu yi, let them says lokacin su ne watarana za su daina, Mami banga aibun auren yaron daka raina ba, tunda bakai ka haife shi ba, ba kuma na nufin rainon yaran da ba kai ka haifa ba illa ne ko haramun ne, amma da Abbu ya bawa Abraham dama nasan dole zai musulunta" Cak Majeederh ta miƙe jiri na ɗaukarta. Washegari gari ta yiwa asibiti tsinke ta nufi wajan Dr Jamal ya gudata ya shaida mata kawai stress ne na gari ya bata magani. Bayan ta koma gida ta samu Abbu da Mami a parlour Mami ta ce "Me Dr ya ce? Akan zazzaɓin?" Majeederh ta ce "Wai stress ne" Mami ta ce "Oh Allah ya ƙara sauƙi" Abbu daman tuni ya zame hannunsa daga kan Majeederh ko gaisuwarta baya amsawa Family ta daina shiga kowa iyaye yake mata akan yana da aure gorin aure ake mata babu ji babu gani, ji take kamar ta mutu ta huta da sauri kuma take Asstagafirullah. Shiru tayi haka kurum tunanin Abraham ya faɗo mata gani take tafi kowa laifi, mai yasa idanunta ya rufe a lokacin ta kasa fahimtar da gaske ba ita ta haife shi ba? Me ya sa take sake masa har yake taɓa jikinta? Bayan tasan ya haramta a gareta, kenan ita ce wacce ta bashi da dama har ya ji ya fara sha'awarta. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku, Allah na tuba Ubangiji ka yafe mini, ban taɓa tunani hakan ba" Tun daga ranar take neman yafitar Ubangiji da yardar shi, tana jin kamar ta ci amanar addinin musulunci ne, Tunanin Alpha ya faɗo mata haka nan taji tana son saka shi cikin addu'a, shi ma ya riƙe hannunta amma gwara shi yayanta ne, Sai Ajlaal kuma bashi da kunya dama daga gani yafi ƙarfinta ko wanne a riƙe hannunta mistake ne bada gangan ba Abraham kai ta sakewa yanzu kuma tayi ladama kullum cikin neman yafiyar Ubangiji take tana hora kanta da raya dare tana sallah da azumi.....
After a year da ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal nan ma ya shaida mata lafiya take. Lokacin tana da shekaru 34 ta jingine komai a gefe, ta ƙaddara Abraham baya ƙasar ba labarinsa babu na Gang team. Lokacin data shiga shekaru 35 farkon shekarar sai ta ji kamar gilamar abu a cikinta ta ɗauka kawai irin abin nan ne da ake kira macijin ciki. Nan ma ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal ya dubeta yana murmushi ya ce "Wai mai Malama Majeederh ke tunani ne? Gashi dai har scanning da X-ray duk nayi amma ba komai lafiya lou kike" Ta ɗan yatsuna fuska ta cikin liƙab ta ce "Kawai ban san yin ciwo" Ya jinjina kai ya ce "You're right, ni kam na tambayeki mana" Ta jinjina masa kai ya ce "Me muhimmancin saka liƙab da hijabi ga mace ne?" Ta kalle shi ta ɗauke kai ya ce "Wlh masu saka liƙab da hijabi na mugun birgeni, na taɓa ganin wata ina sonta amma tayi mini kwarjini" Sai a lokacin Majeederh ta ce "A duk sanda kaga mace ka ji sha'awa to ba kai ne mai laifi ba ita ce zata ɗauki zunubi, ita ta baka damar ganin abinda zai sanya ka ji sha'awarta, to me liƙab sirri ne, hijabi mai taraba ne ga ko wacce mace, abu uku zuwa huɗu yake fara jan hankalin namiji ga ƴa mace, na farko da namiji yaga mace idanunta yake fara kalla, a wannan kallon wani zai iya samun matsala, daga nan sai baki, daga nan sai wuya, abu na gana kuma murya, daga nan kuma bayan mace namiji yake gani, to idan zaka saka hijabi ka saka liƙab ka rufe jikinka babu wani ɗa namiji da zai sha'awarka balle ita macen ta ɗauki zunubi, liƙab da hijabi alama ne da tarbiyyr mutum, masu sakawa a fassara mu su da Allah, idan ka duba larabawa za kaga ko wacce da liƙab ɗinta, me ya sa ƴan izala suke sawa matansu suna sakawa? Ka yi tunanin su ɗin suna da kishi kuma sun san amfaninsa" Zai yi magana ta miƙe ta ce "Thank you Dr Jamal" kwanci tashi Majeederh ta ji cikinta ya fara girma tsoro ya kamata har aka ɗauki wata biyar Mami kallonta kawai take. Tana zaune kamar daga sama taga Uncle Isma'il da Uncle Bello "Saka hijabi hospital zamu" Bata ce komai ba ta miƙe suna zuwa asibiti a gabansu akai mata komai da komai Dr ya ce "Lafiya lou take, gaskiya ko da wata cutar mu dai bamu gani ba, ga photon komai na cikinta ai kuna gani" Uncle Bello ya sauke numfashi Uncle I ya ce "Mu je wani hospital ɗin" suna zuwa wani the same abinda aka faɗa musu shi ne suka sake ji, Uncle Isma'il ya saka akai mata medical check up nan ma the results is good dole suka dawo gida. Latifa ta dinga bawa Aliyu labarin halin da ake ciki akan Majeederh shiru kawai yake mata ta ce "Don Allah don Annabi ba danni ba ka duba girnan Allah dana mahaifiyarka Hajia ka amince da auran Malama Majeederh" A hankali yana miƙewa tsaye ya ce "Accepted" ta kurma ihu ta rungume shi. Lokacin data jewa Majeederh da maganar fata fata sukai ta ɗauke mata huta. Tafiya tayi tafiya har Majeederh tayi wata tara cikin shekarar data shiga na 35 haka kurum ta ji hankalinta yaƙi kwanciya, musamman da cikinta ya yi wani irin mahaukacin girma ƙafarta ya kumbura sosai ta buɗe tai wata ƙiba, hijabi ta saka ta ɗauki waya da jaka ta fito, Mami na zaune a a parlour tare da Raihana da Ruma da Aaliyah hadda Sahar data zo ta fito da ƙyar, tunda ta fito Mami ke kallonta ta ce "Wai kinga ganki kuwa? Anya likita ba ƙarya ya yi miki ba? Ji bi ciki kamar wacce akaiwa ajjiya? Majeederh ta ce "Mami ko jiya sai da Uncle Isma'il ya tisani a gaba wajan likita asibiti biyar muka je Mami ki tambaya ki ji" Ta ce "To Likitocin me suke cewa?" Kanta a ƙasa ta ce "Cewa suke lafiya ta lau, ba su ga komai ba" Ta jinjina kai ta ce "Allah ya kyauta" Ta ce "Zani wajan Dr Jamal na kirasa yanzu ya ce yana cikin asibiti kawai zuwa zan" Mami ta ce "To Allah ya kiyaye" Raihana dai kallon Majeederh take tun daga sama har ƙasa tana tuntsirewa da dariya, da ƙyar Majeederh ta ja ƙafarta zuwa waje ta nufi gidan Latifa ta sameta zaune ta ce "Plx ki yi dropping nawa hospital Latifa i can't drive myself" Ta ce "Ok, amma yau kin fi bani tsoro akan kullum wannan kamar wata mai cikin tagwaye?" Ta miƙe ta ɗauki key ta mayafi ta ce "Sweetheart ya fita zan masa yawa idan mun je" Mota suka shiga Latifa na driving Majeederh a gefe idanunta rufe ta cure waje guda sbd wani irin sanyi da aka tashi da shi yau ga wani masifaffan hazo na tashin hankali, tunda suke tafiya kuma bata ce komai ba rawar sanyi take Latifa ta ɗaga Glasses ɗin motar ta kashe komai na sanyi, amma duk da haka sanyin shiga jikin Majeederh yake tun kuma data shiga motar kanta ke sunkuye, Latifa na lura da damuwar da Majeederh ke ciki, kuma ta yau tafi da ko yaushe, ta ƙara sauri domin su yi su ƙarasa Aminu Kano hospital ɗin amma ina daidai by pass na first bank go-slow ya riƙe su...... _*(A page 1 za a ga ci-gaba daga nan)*_


Continuation..
Shassheƙar kukanta His Excellency Abu-turab yake ji har tsakiyar kansa ya ɗauka kukan farin ciki ne, da Allah ya bata shi a matsayin mijin aure, wanda ya ji tausayinta na ƙaddarar daya faɗa mata ya aura, amma sai ya ga kukan tsananin baƙin ciki da damuwa ne a hankali ya ce "Ya isa haka Jiddo"
Ta zame jikinta daga na shi da sauri duk da babu hijabi a tsakaninsa yanzu mijinta ne shi kuma matarsa ce, amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. His Excellency ya watsa mata rinannun idanunsa cike da zallar so ya ce "Mene na kuka?" Ta yi masa shiru ya miƙa hannu zai riƙo nata tayi saurin barin parlourn ya bita da sauri ta shige bedroom ta banko ƙofa tare da murza key tana sulalewa jikin ƙofar tare da rushewa da wani irin raunataccen kuka. *END OF BOOK 1*






Allahamdulillah! A nan na kawo ƙarshen BOOK1 wanda suka labari ne, akan yadda aka samu cikin Khalil da kowa ke cewa ɗan shi. I hope yanzu zaku fahimci labarin daidai idan mun ɗora... Da yawa za kuga kamar Malama Majeederh ba ta yi achieving komai a rayuwarta ba sai baƙin da ƙaddarori da suke ta rige-rigen faɗa mata. Ba zan iya cewa kun ji daɗin BOOK1 ko aka asin hakan ba... Abu ɗaya na tsani tsagwaron labarin yana BOOK2. Akwai wasu ƙalubalen tunda mutum a karan kansa bai taɓa dauwama da farin ciki ba, to rayuwa haka take yau fari gobe baƙi, yau zuma gobe maɗaci. Duk macen da zata buɗe baki ta ce tunda tayi aure da mijinta zaman daɗi suke basu taɓa samun matsala ko saɓani ba, tuni na bugi ƙirji na ce ƘARYA TAKE. Allah ya taɓa zuciyata na fahimci komai na gane komai kuma ina fatan zaku biyoni domin kuma ku fahimta...


1. Wacce rayuwa Majeederh za ta yi a gidan Abuturab?


2. His Excellency zai yarda ya saketa ko ya ya? Zata haihu da shi ko ya ya?


3. Abraham zai dawo kamar yadda ya yi al'ƙawari? Idan ya dawo ya samu labarin Majeederh na gidan mijinta me zai faru? Zai haƙura ya barta tayi rayuwa da mijinta ko ya?


4. Ina fatan baku manta da General Alpha Bello khan ba? Shin bayan ya gudu sbd baya son auren haɗi tsakaninsa da Majeederh ina yaje? Yana raye ko ya mutu ne? Yana cikin hankalinsa ko hauka yake? Zai bar Majeederh ko ya?


5. Aliyu ya ce idan har bai auri Majeederh ba to mutuwa ya yi, shin ya zata kaya? Zai haɗa su kishi da Latifa ne?


6. Kuna ganin Abbu zai yi aman shi ya lashe? Wacce magana Fulani zata faɗawa Majeederh amma bata samu dama ba sai Abbu ta faɗawa.


7. EHEM🤓 WAYE AJLAAL SULTAAN Mr ji dakai masu taƙama da rawani, kuna ganin zai dawo Nigeria a karo na biyu? Waye zai yi SACRIFICE a cikin zataran mazan? Su waye zasu haƙura da Majeederh wa kuma kuke ganin ya dace da ita matsayin miji na gari?.


WANNE IRIN ZAMA ZA A YI TSAKANIN MAMI DA ƊAN RAINONTA?🤣 BILLAHI DRAMA CE BABBA WANDA BAI BIYONI A BOOK2 BA BABU RUWANA... KUN TAƁA GANIN INDA MATA TAKE GUDUN MIJINTA?😂DUK MAI SON SHIGA GROUP 2 ZAI BIYA #500 BABU YAWA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER6850917335
Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616 ayi maza a cika group wanda bashi da 500 kada ya karanta na sata yazo na yi masa Discount sbd Allah shi ya taɓa zuciyata ba ruwana. Ina ƙaunar masoyana na amana da gaskiya da duk mai karanta littafina. Ubangiji yabar zumunci da ƙauna Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira ya sadaku da dukkan alheri yayi muku albarka🥰Ya hure muku kuɗin siyan MIJIN MALAMA 2 thanks for the love and cares thanks for patronize me 🤞🏽kune ni da bazarku nake taƙama kune kuke sawa asan da zamana 😘😘😘😘 Nimcyluv sarauta's love you👑💋❣️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login