Showing 54001 words to 57000 words out of 125146 words

Chapter 19 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete writing by Nimcey Sarauta .txt

25 Nov 2024

4822

daga cikin bedroom ɗin duk da ya sa key amma ita ta riga data mance, kafin ta ƙarasa wajan ƙofa Alpha ya ƙara yi mata wata mahaukaciyar tsawa wacce bai bata taɓa jin irinta ba, hakan ya sa ta rikice ga ƙirjinta da ya yi mata nauyi a hankali ta fara gani dishi dishi, sama-sama kuma take jin muryar Alpha daya riƙe kafaɗunta yana girgizata tasan ta faɗa jikin mutum kuma ya rungumeta daga nan bata sake sanin komai ba.... A hankali yake tafiya a cikin wrld ɗin hannunsa zube cikin Aljihu, yana sanye da wani floral jacquard one button suit, black colour sai necktie ɗin daya kasance red, ƙafarsa cikin Loafers mai kyau, sai fidda ƙamshi yake a nutse yake sauraran Latifa Omar dake gefensa tana cewa "Wallahi ban san meya sameta ba, ni ina gida ita kuma taje sallama yanzu nake samun labari wajan Aaliyyah ina ƙoƙarin tafiya kuma kace na jiraka, ashe hadda su kwanciya asibiti??" Aliyu ya fesar da iska ya ce "Allah sarki" Daga haka bai sake cewa komai ba, Aaliyyah Latifa ta kira ta fito zata nuna musu inda aka kwantar da Majeederh, su kaci karo a hanya ta durƙosa har ƙasa ta gaida Aliyu-haydar, ya bita da kallo yana yabawa da nutsuwarta, ga sahihin kyan da take da shi, ya fara tunanin ko ya Majeederh take? Idan babu wannan abun na fuskarta? Ya yi saurin cire tunanin a ransa har suka ƙarasa ƙofar room ɗin suka samu Anti,da Mami, sai mahaifiyar Alpha da kuma Uncle Isma'il da Ruma, Aliyu ya durƙosa har ƙasa ya ce "Ina yini Uncle ya mai jiki?" Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Jiki Allhamdulillah, sallamarta ma za ayi" Ya jinjina kai ya ce "Allah ya ƙara afuwa" Ya juya ya gaida sauran jama'ar wajan, Anti sai kallonsa take sbd abinda ta gani kwance akan fuskar shi ta ce "Aliyu ka shiga kaga jikin nata mana, Latifa raka shi" Latifa Omar ta yi jim ta ce "Ba kowa a ciki?" Uncle Isma'il ya ce "Da kowa ba kowa, Soja ne yayanta Alpha shi kawai a ciki" Latifa Omar tayi kamar karta shiga haka kurum jininta bai zo ɗaya dana Alpha Bello khan ba, baya kulata ko gaishesa ta yi, sai kuma ta miƙe tsaye daman tuni Aliyu ya miƙe tayi gaba ya bi bayanta a hankali ta murɗa handle ɗin Ƙofar tare da shiga bakinta ɗauke da sallama, ta matsa gefe Aliyu ya shigo idanunsa ya sauka akan Majeederh da kanta ke cinyar Alpha sai kuka take rusa masa mara sauti wanda ya fi ko wanne cin rai, yadda idanun Alpha ya yi jajir zai baka tabbacin kukan na Majeederh yana taɓa masa zuciya. Aliyu ya dinga kallon yadda Majeederh kewa Alpha kuka kana gani kasan kukan data jima tana tarawa a zuciyarta ne, ya rasa kukan na mene? Hannunsa ya sauka akan hannun Alpha da yake ɗan shafa kan Majeederh da sauri Aliyu ya juya har yana birgewa da ƙofa jiri na ɗaukarsa ya fice daga room ɗin, Latifa ta biyo bayansa, Uncle Isma'il dake tsaye shi da Dr ya dubi Barrister Aliyu ya ce "Badai har kun gaisa ba?" Ya daure murya can ƙasa ya ce "No, zan dawo" Yana faɗin hakan ya nufi harabar asibitin tare da shiga mota ko Latifa dake kiransa bai saurara ba yaja motar da gudu yabar asibitin...
Alpha ya ɗago Majeederh ya kasa cewa komai can ya sauke numfashi ya ce "It's okay, stop crying" Ta kasa daina kukan harda shassheƙa daman kuma Alpha ne kawai ke iya jin zurfin cikin na Majeederh tun tana yarinya, ya sa hannu ya riƙo fuskarta ya kalleta ya ce "What again? Kina so ni ma na shiga damuwa ne?" Ta girgiza kai ya ce "Gashi kina ta kuka, 20 yrs kamar yarinyar goye" Ya sa hannu ya share hawayen fuskarta a hankali ya cire hannunsa ya yi shiru, Majeederh ta ce "Kada ka faɗawa kowa abinda nace please" Ya kalleta kawai ta ƙara marairaice fuska ta ce "please" A hankali ya ce "Ok" kasa ci-gaba da ganinta haka ya yi a hankali ya fice daga room ɗin yana jinta tana wani kukan. Anti ta tsare Alpha da idanu ta ce "Har yanzu bata ce maka komai ba? Na yi mmki" Maman Alpha dai kallonsu kawai take da idanu dake magana bai dameta ba, Uncle Isma'il ya ce "Lallai al'amarin babba ne tunda har ta kasa cewa Alpha komai" Alpha bai tsaya ba ya nufi wajan Dr ya biya bills na komai kana ya dawo ya ce "Uncle zamu iya tafiya" Anti ce da kanta ta shiga wajan Majeederh ta bata hijabi ta zura kanta a ƙasa suka shiga motar Alpha kai tsaye kuma Gidan Abbu ya nufa, lokacin Abbu yana zaune saman kujera yana duba littafi Anti ta yi sallama hannunta riƙe dana Majeederh sai Maman Alpha, Uncle Isma'il da Aaliyyah da sauran napep suka shiga shiyasa tafiyar bata yi daidai ba. Bayan sun gaisa da Abbu suka nufi ciki har kan gado Anti ta kwantar da Majeederh ta ce "Ki kwanta ki huta sosai, Kinga ace 7 jirgin naku zai ta ce" Ta juya ta kalli ɗakin ta ce "Kin dai gama haɗa komai?" Majeederh ta ce "Na ji sauƙi fa, na gama" Ta ce "To Allah ya ƙara afuwa, bari ni ma duk na gaji kwana biyun nan" Mami ta yi musu godiya suka samu Alpha zaune da Abbu Maman Alpha ta ce "Kai fa?" Ya ɗan yatsuna fuska ya ce "Momi kuje kawai, ga kuɗin napep" Ya zaro dubu biyu ya bawa kowa duba ɗaya suka tafi, Abbu da Alpha suka ci-gaba da magana har aka kira Magriba suka nufi masallaci a tare. Mami na haɗa abincin dare Alpha ya yi sallama ya shigo parlourn Mami ta ce "Soja mazan fama, sai da ranka akan na wasu" Ya shafa kai kawai bai ce komai ba ta ce "Ga abincin dare zauna ka ci" ya ware idanu ya ce "No thank you, am full" Mami ta haɗe fuska ta ce "You're always full dama" Ta ƙara cewa "Tana ciki ai" Ya nufi ɗakin Majeederh ya sameta zaune saman ladduma tayi wanka ta sauya kaya kanta a ƙasa, shi kuma ya tsareta da idanu kamar zai magana sai kuma ya ajjiye takeaway ɗin hannunsa tare da fita.
Har aka kira sallar Issha Majeederh na zaune tana azkar, turo ƙofar ɗakin aka yi Mami ce ta shigo ta kalli Majeederh ta ce "Kizo inji Abbu" Tana faɗin hakan ta juya tabar ɗakin, sosai gaban Majeederh ya faɗi ko sunan Abbu aka kira sai ta ji faɗuwar gaba, gudun kada ta yi laifi ya sa ta ajjiye azkar ɗin ta nufi waje ta samu su Raihana a parlour suka dinga yi mata sannu, ta samesa a zaune yana wanke hannu zai ci tuwo ta yi sallama ya amsata ta nemi waje ta zauna. Cikin ɓacin rai ya ce "Ni mahaifinki Majeederh zaki tuzarta? Sbd ki nunawa duniya forcing naki nayi zuwa Misira kika kwanta ciwo? Na haifi yarinyar da zata haɗa da ƴan-uwana Majeederh ni zaki saka ciwon zuciya? Sbd na nemi alfarma a wajanki? Ko riƙonki nake ban cancanci ki wulaƙanta ni ba irin wulaƙantawar da ki kai mini yanzu ba, babu komai ki je na soke tafiya Masar ɗin" Majeederh ta zube akan ƙafafuwanta ta shiga girgiza kai idanunta cike da hawaye ta ce "Ka yafe mini Abbu, na tuba na bi Allah na bika, wallahi ban san na faɗi ba gani na kawai nayi a gadon asibiti, kuma bance bani da lafiya ba, bance kai kace naje karatu ba, ni nake son karatu nina zaɓi tafiya Egypt ba kai ba, na shiga uku idan kalamanka su ka yi tasiri a gareni, ka yafe mini na tuba na bi Allah na bika Mahaifina, ka yi mini komai yanzu ya kamata na baka farin ciki gwargwadon yadda zan iya" Abbu ya haɗe rai ya ce "You surprised me, as your father you will humiliate me, ni Majeederh? Har kin yi girma hakan? Ba zaki iya sacrifice akaina ba?" Jikinta duk rawa yake ta gigice da kalamansa wani irin kuka take kamar zata haɗiye zuciya ta ce "Ka yafe mini don Allah, ni mai laifi ce na yi alkawarin zan yi karatu zan yi aiki duk acan ƙasar, har sai mutuwa ta riskeni ko ka bani umarnin dawowa?" Abbu ya sauke numfashi ya ce "Kin yi mini alƙawarin zaki aiki a can?" Ya jinjina masa kai sbd kuka ya ci ƙarfinta ya ce "Allahamdu lillahi, idan ki kai hakan kin gama mini komai Allah ya yi miki Albarka maza jeki kwanta kada ki makara" Ajjiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tabar ɗakin ta nufi nata tana jin kamar zuciyarta ce zata faɗo......
A can Darmanawa a rikice Aliyu ya shiga cikin haɗɗen gidansu lokacin Hajia da Almustapha da Papa suna zaune a parlour Almustapha ya ce "Papa amma Gwamnati mai ci a yanzu tana ƙoƙari, na ji ɗalibai wajan ɗari biyar aka ɗauka scholarship shi, hadda allowances every month" Papa ya ajjiye remote ɗin hannunsa ya ce "sosai ga hukumar jakadanci ta jiha ta saka hannu, haka na tsaro, hukumomin fikira, da tawaga ta musamman duk an zuba idanu akan ɗaliban gudun samun matsalar rikicin ƙabilanci, ko wani abu" Almustapha na ƙoƙarin yin magana Aliyu ya shigo babu ko sallama hannunsa riƙe da kansa, Hajia ta miƙe da sauri ta ce "Zakina Lafiya? Baka da Lafiya ne? Meke damunka?" Aliyu ya kasa cewa komai sbd parlourn dake juya masa a hankali ya ce "Hajia lulluɓeni san yi nake ji" Hajia da bata jure rashin lafiyar yaran nata gabaɗaya ta rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Aliyuna mene ya sameka yanzu ka fita lafiya lafiya fa?" Papa ya kalli Almustapha ya ce "Kira Dr" Almustapha ya juya da sauri zuwa ɗakko waya, Papa ya kama Aliyu ya kwantar saman duguwar kujera sai rawar sanyi yake idanunsa rufe jijiyoyin kansa duk sun fito, Hajia ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku mayu sun kama mini yaro, yarana kwaya biyu kacal a duniya shi ne za a ga bayan ɗayan?" Papa ya dinga kallon Aliyu shi kansa ciwon ya bashi mamaki, Aliyu dake cikin ciwo ya kama hannun Hajia ya riƙe ya ce "Ki danna mini ƙirjina Hajia, zuciyata zata fito waje" Hajia ta ƙara saka kuka, daidai nan Almustapha ya dawo babu jimawa Dr ya zo allura ya yi masa tambayar duniya ya faɗi meke damunsa amma yaƙi. Suna zaune har bacci ya ɗauke shi a cinyarsa Hajia yana sauke numfashi a wahale..
Har gari ya waye bacci baiga idanun Majeederh ba, ana kiran sallah ta tashi tayi wanka tare da yin Sallah ta jima tana addu'a sosai kafin ta shirya cikin wata duguwar riga Maroon tayi rolling kanta. Tana tsaye Latifa Omar ta shigo idanunta ya yi jaa taci kuka son ranta ta ce "Wai ki fito ba lokaci" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Haka aka damu dani? Irin wannan kuka" Latifa ta sake fashewa da kuka, bata hanata ba don dai itama taiwa kanta al'ƙawarin daina kuka ne, da babu shakka sai tayi nata kafin ta tafi, safiya ce amma ƴan-uwa sun cika gidan Abbu kowa yana son ganin tafiyar Majeederh, tafiya ce wacce ba lallai a sake ganin juna ba, inma ita ta mutu inma su, kanta a ƙasa ta fito daga nan suka rankaya airport, anan sukai ta ganin ɗalibai masa da mata, kasancewar a makare suka ƙarasu wajan yasa ta shiga sallama da mutane ta ƙarasa wajan Abbu ta ce "Abbu na tafi ka yafe mini don Allah" Ya ce "Babu komai, Allah ya bada sa a" haka ta dinga bin mutanen wajan tana zuwa wajan Aaliyah ta rungumeta, a can gefe ta hango Alpha yana tsaye rungume da hannunsa, uniform ɗin sojoji ne a cikinsa amy colour ta nufi inda yake ya kalleta bai ce komai a hankali ta ce "Na tafi" Ya gyara tsaiwa ya ce "All The best, ki kula" Za ta yi magana ya yi saurin shigewa mota, sai a lokacin hawaye ya taro a Idanunta ta nufi cikin wajan har tayi nesa da su kai tsaye jirgin ta shiga sai da ta zo matattakalar ƙarshe ta ɗago kanta ta kalli ƴan-uwanta kamar ance ta kalli gefe idanunta ya sauka akan Aliyu hannunsa maƙale da carnoner...




MIJIN MALAMA
08119237616
Uhm get ready...... Yanzu zamu fara🥹26
Majeederh ta sake kallon Aliyu, she saw that he had changed from the way she knew him, duk da ba wani mugun sani ta yi masa ba, ta ɗauke kai ganin yadda ya kafeta da idanunsa da suka janye, a hankali ta juya idanunta cike da hawaye ganin Khan's family maza da mata yara da manya suna ɗaga mata hannu. Jikinta na ƙyarma da ɓari na rashin sabon tafiya ita ɗaya ta ƙarasa kujera ta zauna tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, wani rauni ya mamaye dukkan zuciyarta fargaba da tsoran abin da zata tarar a ƙasar daba tata ba ya wanzu a zuciyar Majeederh Abdul'aziz Khan. Ya za ta yi a garin da babu uwa ba uba? Garin da ba wa ba ƙani? Garin da babu idon sanin? Garin da babu mai kwaɓarta? Ya za ta yi idan abu ya faru da ita wa kuma zata tunkara? Rashin sanin wanda zai bata amsar tambayoyinta ya sanya ta ƙara tura kanta wani mahaukacin kuka na kwace mata ta yi saurin rufe bakinta. "Assalamu alaiki" Wata murya ta sauka cikin kunnenta a hankali ta goge hawayen idanunta tas ta ɗago kanta bayan ta gyara zaman liƙab ɗin fuskarta. A hankali ya daidaita tsaiwar shi ya ƙara cewa "Assalamu alaiki" Su take ta amsa amma harshenta ya yi mata nauyi ta ɗaga kanta suka haɗa idanu, yana tsaye ya rungume hannu ɗaya a ƙirjin fuskarsa maƙale da face mars, ya ƙara zuba mata idanu ganin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya ya ce "Ki duba number seat ɗin ki" Sai a lokacin ta duba taga a number 35 take zaune number ta kuma 34 ne, ta langwaɓar da kai alamar ban haƙuri kana ta tashi a hankali ta zaune a number dake window. Ya nemi waje ya zauna yana danna airplane mode a wayarsa tare da ware jarida ya shiga dubawa, yadda Majeederh ke sauke numfashi a wahale ya sanya ya juya ya kalleta tare da cewa "Are you okay?" Ta jinjina kanta.
"Are you sure?" Ta ƙara jinjina kanta ya bita da kallo kafin ya ce "Okey"
Sanarwar aka fara kowa ya shirya jirgi zai ta shi, a hankali ta jawo ballet ta ɗaura a jikinta.
Jirgi ya fara juyawa a ƙasa tsayin wasu daƙiƙo zuwa mintuna, Majeederh ta rufe Idanunta tare da ƙanƙame jikinta waje guda, lokacin da jirgin ya yi katantanwa zai tashi ji tayi kanta yana sarawa amai na shirin zubo mata. A taushashe ya ce
"Sorry" tana cikin wannan yanayin jirgin Emirates Airplane ya ɗaga da ɗarorun ɗalibai. Ta sauke ajjiyar zuciya ya ɗauki ruwa ya miƙa mata ta girgiza kai, har lokacin bai ji maganarta ba.
"Please bear with the interruptions, is this your first time on a plane?"
"Uhm" ta furta a yanayin da ba zai iya haddace muryarta ba.
"I see, sorry" Ya mai da hankali zuwa ga jaridar dake hannunsa deep down na zuciyarsa he was thinking ko dai bata jin magana, kurma ko bebiyya? Only God knows... Majeederh ta rufe Idanu yayinda da dukkan wani farin cikinta ta barshi a jihar Kano, ƙasar Nijeriya.
Aliyu ya zame idanunsa daga kan jirgin su Majeed wanda ya gama shigewa cikin gajimare, ji ya yi kamar da zuciyarsa ta tafi tare da nutsuwarsa ya sauke numfashi yana ƙoƙarin buɗe murfin motar shi ya ji an ce. "Hi"
Ya tsaya ta buɗe motar ya juya idanunsa ya sauka akan Alpha wanda baya jin zai iya mance yanayin daya gansu shi da Majeederh. Bai ce masa komai, Alpha ya gyara zama ce ya ce
"Alpha Bello khan my name, Captain, It is the highest rang in Tactical troops organization"


"Good" Aliyu haydar ya ce murya kuma can ƙasa, Alpha ya gyara tsaiwa ya ce "Sunanka Aliyu Sufyan Alhassan, ɗan Jarida a matakin farko na fara aiki, Kayi karatu a Al'ƙalam University, daga nan ka shige Cairo ka ɗora da karatu, a gida anso ka karanci ɓangaren politics Democracy, kai kuma ka ce Law ka ke so, mahaifinka Alhaji Sufyan Alhassan shi ne Commissioner for education, ku biyu iyayenku suka haifa, yayanka Almustapha shi ne Manager a Bua campaign, mahaifiyarku tana ji daku sosai shi ya sa bata jure dukkan ɓacin ranku, wannan dalilin ya sa bata takura ku akan maganar aure duk da akwai ƴan mata a familynku amma kuna jin kun girmi ajin su" Alpha ya yi murmushin gefen baki ya zuba hannu a aljihu ya ce.
"Idan har a kwana ɗaya zan iya sanin waye kai, to karantar zuciyarka ba zaiwa Alpha wahala ba, bayan kasanceweta soja ina aiki a hukamar fikira ta jiha ka kiyaye, kada ka fara abin da ba zaka iya ba, kada ka sanya zuciyarki cikin ramin da zata kasa fitowa, kada ka yi ƙullin da zaka saka cikin kejin kaza, kasan kaza uwar tune-tune ce, stay away from her, Ina nufin Majeederh Abdul'aziz Khan she's my sister"
Bar Aliyu Sufyan Alhassan dake jingine da jikin lafiyayyiyar motarshi ya ɗan miƙe hannunsa mai ɗauke carnoner ya ɗaga ya shafa kansa ya ce "Anzo wajan"
Ya dubi idanun Alpha dake kwance cikin nasa idanun kai tsaye ya gane me launin idanun yake nufi domin a yawan karatun English Novels da yake da literature daya karanta yasa fahimtar hakan bai masa wahala ba "Uhm"
Sai kuma ya ce "Me ya sa zaka nuna maitarka a fili? Kada ka manta nan fa ba filin yaƙi bane ko dajin sambisa Captain Alpha Bello khan, a tsare rayukan jama'a kafi ƙarfi, amma ba zaka nunawa Babba lauya fahimtar waye mutum ba, by the way, who are you talking about? Stay away name? Please open your heart ƙilan na fahimta sosai"


"Ka janye jiki daga gare ta, baku dace ba?" Cewar Alpha. Cike da rainin hankali irin na Lauyoyi Aliyu ya ce "Wai wa kake magana? stop

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login