Showing 111001 words to 114000 words out of 125146 words
Chapter 38 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete writing by Nimcey Sarauta .txt
ma ya nufi part ɗinsa, ƙarar data kuma yi ya ya jawo hankalin Mama da mai aikinta suka shigo parlourn a guje jinin dake malala a ƙasan Maysoon ya sanya Mama rikice Maysoon tuni ta fara kokawa da ranta, Mama ta fara kuka sbd tausayi cikin ikon Allah kuma suka fara jin kukan jariri da sauri Mama ta ɗaga Maysoon ta matsar da babyn Salati Maysoon take tana kiran sunan Abuturab tare da yin wata jijjiga idanunta na rufewa, Abuturab Mama ta shiga ƙwalawa kira yana ji ya yi shiru ganin numfashin Maysoon na tafiya baya dawowa yasa Mama fara kalmar shahada,idan ta kira sunan Maysoon sai ta faɗi kalmar shahada cak numfashinta ya tsaya jikinta ya saki idanunta ya yi sama rai ya yi halinsa Maysoon died.
Ban yi Edited ba.. bear with meDa hannun bibbiyu Abuturab ya riƙe kansa yana kallon ƙyakƙyawar jaririyar da matarsa ta mutu ta bari. Mama dake Kallonsa tayi jigum ta ce "Ka yi haƙuri, ko wanne mai rai mamaci ne, damuwata har yanzu ban san mene ya samu Maysoon har ya yi sanadin Ajalinta ba" Abuturab ya yi shiru yana jin wani iri a ransa. Kallonsa kawai Mama take kafin ta ce "Na yarda da kai na aura maka ƴar mutane ta zauna dakai a yadda ta sameka, Ali wallahi muddin ka saɓawa yardar da na yi maka Ubangiji ba zai barka ba, zaka samu jarrabawa ta yadda baka yi tsammani ba, gwara tun wuri idan akwai wani abu ka faɗa mini" A hankali Abuturab ya ce "Are you accusing me, Mom?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zarginka nake ba, kawai dai tunatarwa na yi maka" Ya jinjina kai ta ce "A sakawa jaririyar sunan uwarta Maysoon" Da sauri ya ce "No Mama" Ta ce "Why? I don't think it's a crime to inherit her mother's name, no matter what, we'll always remember her" Cikin rauni da siga ta tausayi ya ce "Mama zan dinga jin kamar zata dawo gareni ne, ni kaɗai na san abinda ke damuna, ko a saka sunanta ko ba a saka ba, she's always be on my mind, she's a kind and nice person da ban taɓa ganin irinta ba, so Please Mama ki yi haƙuri kada a saka sunan Please" Mama ta tsora masa idanu kafin ta ce "To wanne sunan kake so?" A hankali ya ce "Hawwa'u, we can call her Jidderh" Mama ta ce "Hawwa'u?" Ta tambaya da mmki ganin ka kaf Familynta babu mai irin sunan ya yi shiru. Ta ce "Ubangiji ya rataya, ya bata haƙuri irin na mahaifiyarta" Miƙewa ya yi zuwa part ɗinsa sbd jin muryar ƴan gaisuwa duk da ya hana zaman makoki for no reason. Kwanciya ya yi yana lumshe idanunsa tun auren su da Maysoon bai samu nutsuwa ba, gani yake kamar ya ci amanar wacce zuciyarsa take so da ƙauna da muradin kasancewa da ita, yanzu kuma wani irin sauƙi yake ji da nutsuwa ko babu komai she's pass away frm his life,She was out of his life, He will live without constraints, he will live from him only what his heart wants. Ajjiye babyn ya yi yana jin son yarinyar har ransa musamman idan ya tuna sunan data mallaka. Wayarsa ce ta fara ringing a hankali ya duba ganin mai kiran ya sanya ɗauka. A nutse ya ce "Barka" Daga cikin wayar aka ce "Ka duba news kaga meke faruwa?" Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce "Bana ce ba, kasan am not in the mood" Mutumin ya ce "Motar ƴan boarding school dake tafiya zuwa wani abu na makaranta aka cinnawa wuta, ɗalibai sama da 500 sun ƙune ƙurmus ga kabari mutane wajan goma da aka tune aka kwashe gawarwakin an rasa waye, Hon ina jin tsoro baka tunanin jam'iyyar hamayya ta aikata wannan abun sbd kawai taci mulki? Ko wani asiri suke ki tsubbu?" Miƙewa Abuturab ya yi zufa na yanko masa ya ce "Yanzu Sir al'amarin har ya kai sbd son mulki a sanwaltar da rayukan al'umma wanda basu ji ba basu gani ba? Me ake son zama ne?" Mutumin ya ce "Calm down Hon, ina tunanin we can do something about that" Ya ce "Kamar m" Ta cikin wayar aka ce "Mu je makarantar mu jajanta lamarin mu bawa iyayen ko wanne yaro haƙuri da kuma ɗan wani abu, tare da al'ƙawarin yin bincike idan jam'iyyarmu ta samu mulki" Tattaunawa sukai kana suka sauka akan layi.
After 1weeks
Majeederh na zaune tana duba wasu files da aka turo mata na Human rights akan wani cases da ake son ta taimaka kamar daga sama taga Abbu ya shigo cikin sauri ta ɗago kanta ta dube shi jikinta duk rawa yake ta kasa cewa komai Abbu ya ce "Hawwa'u me ya kai ki Bristol Palace Hotel?" Wani irin bugawa ƙirjinta ya yi ta ce "Hotel Abbu?" Hannu ya ɗaga ya zabga mata mari ya ce "Are answering my questions with a question? How dare you?" Yatsunsa ya fito sosai akan fuskarta sosai idanunta ya shiga fitar da hawaye ta ce "Abbu ban taɓa zuwa Hotel ba, don Allah..." Wani marin ya kuma sauke mata idanunsa sukai jajur kamar zasu fito waje yama kasa magana sai pointing ɗinta da hannu da yake "Ban haifi yarinyar da zata ɓata mini sunan family da nawa ba, kin yi kadan zaki san cewa ni na haifeki ba kece kika haifan ba wallahi lokaci kawai nake jira" Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta ce "Why should i do that Abbu? Wallahi ban taɓa zuwa Hotel ba mene ribata bayan nasan illar hakan don Allah Abbu...," Hannu ya ɗaga ya ƙara sauke mata wani marin kafin ya ce "Idan ba ki ki Hotel ba to wace wannan? 1week ago wacce ta je gidan ƙartin maza? Past week's waye ya dinga hauro mini gida yana shiga ɗakin ki? Ko shi ma bake bace baki san anyi ba? Shekaran jiya kin ce mini zaki wani meeting a Abuja daga nan mene ya kai ki Lagos?" Wani irin kuka take sosai bakinta na rawa ta ce "Abbu zan maka bayani wlh ba abinda kake tunani bane" Jin hayaniya ya saka Mami fitowa Main parlour, Raihana ta fito itama da sauri Mami ta ce "Meke faruwa ne?" Da hannu Abbu ya ce
"Hawwa'u zata saka mini ciwon zuciya, tana sane ta ƙi yin aure take yawo tarbiyyar dana baki kenan? Na yarda dake na amince miki shi ne zaki aikata mini haka? Kin san bana iya bacci sbd damuwarki, burina kawai na ganki a ɗakin mijinki kamar sauran ƴan uwanki amma abin ya ci tura, ashe haka zurfin ilimi ke jawowa?" Mami ta ce "Take ur heart please Alhji baka da lafiya ka dinga bin komai a sannu Please, kada ka yanke hukunci ba tare da bincike ba" Abbu ya ce "Wanne irin bincike bayan wanda na yi? Komai nake idanuna yana kan Majeederh bani da cikakkiyar nutsuwa private Investigators nawa na saka akanta?" Da wani irin tashin hankali Majeederh ta ce "Zargina kake Abbu? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un na shiga uku, wallahi Abbu ban taɓa aikata sabon Ubangiji ba, ba zan taɓa cutar da tarbiyyarka ba da nayi haka gwara mutuwata, taimakon al'umma musulmi kawai nake" Wata zabgegiyar bulala ya ɗakko ya nufi Majeederh zai daka da sauri Mami ta shiga tsakani idanunta na zubar da hawaye ta ce "Haba Alhaji idan rai ya ɓaci nutsuwa ake samu, hankali ke nemo shi, idan ka yarda da Majeederh tun farko bai kamata ka zargeta ba yanzu, zargi haramun ne a musulunce wlh" Yana huci sosai ya ce "Leave, Asabe ki matsa daga nan ko na haɗa dake" Mami na kuka sosai ta ce "Wlh sai dai ka dake mu tare, na fara gajiya wanne irin mutum ne wai kai? So kake a zageni ace sbd bani na haifeta ba? Ka sassautawa zuciyarka, kabi komai a sannu faɗa baya magani idan ba kangarar da yaro ba, ko ƙaddara ce fa ta faɗa mata dole ka zauna da ita ƴarka ce jininka ce hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar" A wannan karan hatta Raihana sai da ta ji tausayin Majeederh, babbar mace mai shekaru ilimin addini dana boko kuɗi hankali nutsuwa amma ita ake doka kamar Ƴar shekara biyar. Zubewa Abbu ya yi dafe da kansa dake juya masa yana jin kamar zuciyarsa zata fashe, shigowar Abraham cikin main parlour ya sanya Abbu miƙewa da sauri ya ce "Ban hanaka shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara tsafta me yawo da datti ya dinga shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara gata da ƴanci wanda bashi da mara da almajirin kan titi shigo mini gida ba?" Abraham kallon Majeederh dake durƙoshe yake wacce gefen bakinta ya fashe, ta kasa ɗago kanta ta kalli Abraham sbd gujewa ganinsa da take rabon data ganshi ma ta mance ta rufe duk wata hanya da zata haɗata da shi ba da son ranta ba. Abbu ya ce "Da kai nake magana?" Abraham ya zame idanunsa ya kalli Abbu, sauyin idanun Abraham ya kaɗa hantar cikin Mami. "What brought you into my house?" Gently Abraham ya taka har gaban Abbu ido cikin ido ya ce "Ƴar ka nake so" Hatta Mami ta jijjiga da wannan maganar ta Abraham, Abbu kuma ji ya yi zuciyarsa ta tsaya na wani lokaci cikin rashin fahimta ya ce "Me ka ce?" A takaice Abraham ya ce "Zan auri Mamina" Abbu ya ce "A sbd kai Mahaukaci ne?" Shortly ya ce "Akan ta, ni Mahaukaci ne Grandpa ya turo ni wajanka just to ask ur permission na aurenta" Abbu ya juya ya kalli Majeederh wacce kanta ke sunkuye sai numfashi take da ƙyar ya dawo kan Abraham ya ce "Ka zo gidana, a gabana ka kalli cikin Idanuna ka ce kazo auren ƴata?" Abraham ya ɗan watsa kafaɗa tare da fito da Teller ya ce "Daga 1m zuwa ko nawa ka faɗi kuɗin da kke buƙata yanzu ka bani ita mu tafi" Mami ta ce "Son ta kake?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "I don't know, kawai ina son auren ta" Abbu ya ce "Mara addini kamar ka shine zan bawa auren ƴarta? Wanda bashi da gata, Ahhali mai yawo da ƴan iska suke fashi da bindigogi zan bawa auren ƴata? Mai Shaye-shaye da yawo da mata wanda yake gidan kansa maimakon na iyayensa shi zan bawa auren ƴata?" Abraham kallo Abbu kawai yake ba tare daya damu ba ya ce "Yanzu ma kuɗin auren nata ai fashin su na yi" Majeederh dai ta kasa motsi zaka iya ɗauka bata cikin hayyacinta ne Abbu ya ce "Ban yi mamakin hakan ba, bari na faɗa maka abinda baka sani ba, wallahi tallahi dana aura maka ƴata gwara naga gawarta, dana aura maka ƴata gwara ni na mutu, dana aura maka ƴata gwara duk me zai sameta ya sameta, dana aura maka ƴata gwara naga ta zube mini shego gwara ko wacce ƙaddara ta faɗa mata" Da wani irin tashin hankali Majeederh ke kallon Abbu sbd jin furucinsa wanda ya gigita ta ya sauya mata lissafi tunaninta ya tsaya, kalmar shego ta nemi tarwatsa mata zuciya da sanya wa ta jita kamar matacciyya. Mami ta ce "Alhaji kasan me kake cewa kowa? Kada ka jawa Majeederh masifa da bakinka" Abbu ya ɗagawa Mami hannu ya ce "Ki daina saka mini baki cikin maganata Asabe" Mami ta zaune tana rushewa da kuka. Abraham jijiyoyin kansa suka fito tare da yin raɗa raɗa saman goshinsa silently ya ce "Ohk, ka shirya ganin babies" Yana faɗin hakan ya juya tare da ficewa daga cikin gidan a hanya suka haɗu da Latifa dake shigowa Murmushi tayi masa ta ce "Our son kana ta girma abinka wajan Mamin taka ka je?" Ko inuwarta bai kalla ba balle ya bata amsa shi duk duniya da Majeederh kawai yake duguwar magana. Yana zuwa mota Taj ya buɗe masa ya shiga gidan baya, Salamon na gaba shi kuma Taj ya nufi mazaunin driver bayan sun fice daga cikin gidan Taj ya ce "Bad boy ya amince?" Abraham ya yi shiru Salamon dake danna waya ya ce "What did i miss?" Taj ya ce "Bad boy ya je neman auren Mami" Da wani irin sauri Salamon ya juya ya kalli Abraham dake bayan mota idanunsa rufe ya dunƙule hannayensa ya birkita sumar kansa ya dawo da ganinsa kan Taj ya ce "Shawarar wace wannan?"Taj ya ce "I, to me zai zauna jira kawai ya aureta" Salamon da wani irin yanayi yake kallon Taj kafin ya ce "Wai mene ruwanka da rayuwar Abraham ne? Me yasa kake sawa ya aikata abinda bashi kenan ba? Daman haka ake neman aure a musulunci? Kawai ya tunkari mahaifin Mami ya ce he wants to marry his daughter ko me?" Taj ya ɗaga shoulder ya ce "Is just a suggestion, kawai na duba yanayinsa baya bacci cikin kwanakin nan kullum kiran sunan Mami ni kuma i can't take it anymore" Salamon ya ce "U can't take it a matsayinka na ubansa ko uwarsa ko kuma me?" Taj ya ce "A'a kada ka zageni bafa fini son Bad boy kayi ba, ina yin komai sbd farin cikinsa da kwanciyar hankalin sa ai shi ya sani idan kai baka sani ba" Tuni zuciyar Salamon ta fara kaiwa ƙarshe ya ce "Farin cikinsa ko kuma ɓata shi? Ka bashi ƙwaya ya sha ka saka masa maganin felling da burin ya yi wa Maminsa Fyaɗe Allah ya taƙaita, ka kirata har gidansa ta da burin ta ganshi kwance da Debeka, ka haɗa plan da Engagement, yanzu ka sanya ya je wajan mahaifinta wai ya bashi aurenta are you mad....," Da ƙarfi suka ji Abraham ya ce "Stop the car" Taj ya tsaya bakin titi cikin ƙara ji Abraham ya ce "Salamon get out of the car, bana son ganin fuskarka har abada" Murmushi kawai Salamon ya yi yana kallon Taj ya ce "Wannan shi ne abinda kake buƙata?" Taj bai ce komai ba, Salamon ya buɗe ƙofa ya fita tare da matsawa can gefe da gudu kuma Taj ya ja motar sai Club. Wine yake tsiyayawa Abraham yana zubawa cikinsa sai da ya sha ya yi tatul kafin Taj ya ce "Bad boy ni zan tsaya maka ko kowa zai gujeka ka mini halacci a rayuwa, Salamon son Maminka yake" Sai a lokacin Abraham ya buɗe rinannun idanunsa ya kalli Taj wani irin kallo yake masa kafin can ƙasa ya ce "I'll kill you Salamon" Taj ya ce "Ganin yana son ta shi ya sa nace bari kawai mu fara da neman auren amma tunda Abbu yaƙi kawai ka tafi gidan Uncle Isma'il yanzu kafin Abbu ya bata auren wani a daren nan" Cak yaga Abraham ya miƙe yana tangaɗi daga shi da three quarter ya zari key ya nufi hanyar fita daga cikin Clun ɗin da ƙyar, murmushi Taj ya yi ya ce "Well-done Abraham Daniel David"
Uncle Isma'il da Uncle Bello sai Abbu na zaune a compound na gidan Uncle Isma'il su kaga an buɗe gate wata dalleliyar mota ta shigo, gabaɗaya suka kalli motar banda Abbu da kansa ke ƙasa, Abraham ya buɗe murfin motar da ƙyar ya fito yana layi da tangaɗi ko idanunsa baya iya buɗewa sbd wine ɗin da Taj ya bashi mai ƙarfi ce, bibbiyu haka yake ganin su Uncle Isma'il, Uncle B ya gyara zama ya dinga bin Abraham da kallo har ya ƙarasu ya zube akan qiwwoyinsa ya lumshe idanunsa. Uncle Isma'il ya ce "Khalil lafiya?" Abraham ya yi shiru, Abbu ya miƙe zai bar wajan Uncle Bello ya ce "Ka zauna plx" Ya koma ya zauna daman alrdy ya shaida musu everything daya faru. Dafa shoulder ɗin Abraham ya yi ya ce "Khalil me kake so?" Kansa a ƙasa a hankali ya ce "Mami" girgiza kai kawai Uncle Isma'il ya yi ya ce "Mamin take kake so yanzu kuma?" A hankali ya ce "Yes, ina so Mami" Ya ce "Khalil bana jin ko ka kasance Musulmi Majeederh zata amince ka aureta, ta raineka da hannunta ta kula da kai da ace tayi aure babu mamaki ta samu ɗa kamarka, addininmu da naku ba ɗaya bane, babu yadda za a yi ka auri Majeederh, yau da ace kai Musulmi ne ita Christa to da sauƙi, amma kana Christa tana Musulma kuma Malama? Ba zai taɓa yiyuwa ba, ka yi haƙuri Ibrahim" Abraham baya fahimta bai kuma san haƙuri ba ya ce "Uncle Mami, ina son zama da ita" Ganin kamar zai basu matsala ya sanya Uncle Bello cewa "Ohk, ka turo iyayenka sai a saka muku date na bikin" Da ƙyar suka lallaɓa shi ya shiga mota yabar gidan. Uncle Bello ya kalli Abbu ya ce "Wai lamarin Majeederh ke damunka ne Alhji Abdul'aziz?" Abbu ya ce "Me ya sa ba zai daman ba?" Uncle Bello ya ce "Gaskiya bai kamata ya dameka ba, sbd komai ya faru kai ka siya da hannunka, akwai ƙaddara amma tana zuwa da sanadi, tun Majeederh na da 20yrs a duniya ta nuna aure take so, amma kayi burus ka nuna kamar baka sani ba, kamar baka san meke damun ƴarka ba, Imran ya fito aurenta ta kure shi sbd kawai cikar burinka, bata san karatu amma haka ta daure ta maida kanta kamar namiji ta tafi wata ƙasar tsayin shekaru Takwas, ta dawo ka tilasta mata fara aiki, yanzu kuma ka samu abinda kake so shi ne zaka damu sbd ba tayi aure ba? Allah zaka ma wayo ko ka nuna masa dabara kenan? Muna rayuwa da ƙaddararmu wacce Ubangiji ya tsara mana, ƙaddarar jinkirin aure ta samu Majeederh sai ka tayata amsa kayi mata addu'a, kuma ka bar ƙaddara ta yi aikinta" Abbu kallon Uncle Bello kawai yake, Uncle B ya ɗora da faɗin "Yanzu da kake zargin Majeederh a matsayinki na mahaifinta mu kuma da jama'ar gari mu ce me? Da Majeederh zata lalace to da tun a Misira hakan zai faru, ka gode Allah ka masa mubaya'a akan yadda ya tsara lamuransa, komai ya sameta a rayuwa kai ne sila, sannan daza ka yi wannan lalataccen