Showing 60001 words to 63000 words out of 125146 words

Chapter 21 - MIJIN MALAMA BOOK 1 Complete writing by Nimcey Sarauta .txt

25 Nov 2024

4823

zai tabbatarwa da mai Kallonta a mugun gajiye take, kusan haka ɗin ne domin karatu ya yi mata yawa bata da lokacin komai da kowa sai karatu tsayin watanni biyar da zuwanta Egypt bata taɓa kiran number kowa a Nijeriya ba, haka kuma bata da ƙawa idan ba Ƙhulud Arzaan ba, hakan ya sa da yawan student suke mata kallon mai masifar girman kai suka yi tunanin ƴar gidan wani ce a duniyar ma bawai a Nijeriya ba, Ilimin da Majeederh take da shi ya ƙara mata kwarjini a idanun malaman jami'ar da sauran ɗalibai, ita kuma suka zaɓa matsayin shugaban ɗalibai duk da ta ce bata so amma aka tilasta mata amsa, da yawan Student na zuwa ta ƙara musu haske, wasu kawai don su ji maganarta wasu kuma ko Allah zai sanya suga fuskarta suga mene dalilin rufe fuskar. A cikin watanni biyar harshenta ya juye sak cikakken Balarabiya ba zaka taɓa cewa ta san hausa ko English ba idan tana larabci, to ta je garin larabawa uwa uba ɓangaren Arabic take karanta. Duk rashin son maganarta sai da ta saba da Ƙhulud Arzaan ba tare da sanin dalili ba, haka kawai take son yarinyar kamar Aaliyyah, Ƙhulud Arzaan ta taka rawa sosai wajan wayar da Majeederh ta jata har shopping ta kwasu mata abayas masu mahaukacin kyau tsada very expensive classic one and unique. Liƙab ɗin ma ta sauya mata irin na Larabawa da suke sawa, a cikin 5 Month ɗin nan Majeederh a rame take bata gaba bata baya jia iyau kamar kazar matsiyata ramar kuma ta samu asali akan abinda ke hanata bacci kullum yake sanyata azumi wanda babu fashi ya zame mata jiki kullum. "Majeederh... Majeederh" Kiran ya dakatar da ita daga tafiyar da take Ƙhulud Arzaan ta ƙarasu tana dariya ta ce "Shi ne kika taho ko?" Majeederh ta ɗan saki numfashi ta ce "Kin tsaya gulma" Ƙhulud Arzaan ta ce "Gulmar ta yi mini amfani kam" Ita dai Majeederh bata ce komai ba sbd an kusa kiran sallar Magriba bata so ta yi mata a hanya Ƙhulud Arzaan ta ce "Musabaƙar Alkur'ani za a yi, Ta duka ƙasashen duniya na Muslunci" Majeederh ta waro idanu ta ce "Ma sha Allah, za mu ga manyan malamai mu tada haddarmu mu ma" Ƙhulud Arzaan ta ce "Au haba? Kin san me gabaɗaya ko wacce ƙasa ta bada sunan wanda zai wakilce su, ƙasar ku Nigeria kawai ta rage" Majeederh ta yi shiru tana tunani wa Nigeriya zata zaɓa? Allah ya sa ko waye ya dawo musu da martabar ƙasar su. Kafin ta yi magana Ƙhulud Arzaan ta ce "Kuma Saudiya ta sallamawa Misira kamar yadda suka buƙata ayi Musabaƙar a nan ƙasar, kuma hadda Granny ta a mutanen da zasu zama masu tantance ƙasar da tayi nasara" Majeederh ta ce "Kullum ana bani labarin Granny Finally zan ga Granny" Ƙhulud tayi dariya sosai ta ce "Like serious, ba ruwanta idan kin ganta sam ba zaki ce ta haifi Sarki Sultan ba" Majeederh ta ware idanunta ta cikin liƙab ta ce "Kai, ke jinin sarauta ce?" Ƙhulud Arzaan ta yi shiru domin bata son cewa Majeederh ita surukar gidan ce babanta kuma ƙanin Sarki Sultan ne. Suna hira har suka ƙarasa gidansu Majeederh ta yi part ɗinta Ƙhulud Arzaan ta shige nata. Wanka Majeederh ta yi kana ta yi sallah sannan ta sha ruwa, tana mai yin watsi da maganar Ƙhulud Arzaan. A nutse ta jawo wayarta ta kunna cikin nutsuwa ta danna number Abbu, ringing ɗin farko ya ɗaga ta cikin wayar ta ji ya ce "Ko baki faɗa ba nasan Majeederh ce" Ta sauke numfashi ta ce "Asslaymu Alaika Ya Abbu" Ta faɗa a nutse.


"Ke ce Majeederh?" Ta faɗa a fili wanda ya jawo hankalin su Aaliyyah, sosai muryarta ta sauya ta zama ta Larabawa. "Ni ce Abbu" Abbu ya ce "Allahamdu lillahi shiru shiru har wata biyar?"


A nutse cikin tarin kamala ta ce.
"ليلة سعيدة ، أتمنى أن تكون بخير"
Ma'ana "Barka da dare, fatan kana lafiya" Abbu ya ce "Wallahi lafiya, kina lafiya ya karatu?" Cikin Larabci ta ce "Allhamdulillah" Ta tambayi kowa na gidan duk ya basu suka gaisa Aaliyyah hadda kuka wurjajjen. "Hawwa'u shiru ba kira ba saƙo?" Majeederh ta ce "Ka yi haƙuri Abbu" Ya ce "To na yi" Ta ce "Ma sha Allah" Jin shiru bata ce komai ba ya ce "Har yau dai gamo jiya iyau, ba wani abu" Sosai Majeederh ta ji babu daɗi ta ce "Zan tura maka kuɗi Abbu ta nita sai aje a cire" Abbu ya ce "Yawwa to nawa ne kuɗin? Daman an kusa bikin Ruma don ma anyi jinkiri ne" Majeederh ta ƙara yin shiru domin rashin son maganarta ya ƙaru fiye da baya ta ce "Ƙilan su yi 200k fam ne ban san nawa za su tashi a Nigeria ba" Abbu ya ce "Dubu ɗari biyu ya yi kaɗan Majeederh ina laifin Miliyan ɗaya" Majeederh ta zaro idanunta da suke farare tas ta ce "Miliyan? Abbu ina zan gan su wannan ma Albashin da gwamnatin Nijeriya ke bamu ne bana taɓa wa" Abbu ya ce "To babu damuwa amma duk wata idan aka baki kada ki taɓa ko ficika ko kwabo karki ɓatar" Mamakin mahaifin nata ya cika mata zuciya ya kira sunanta ya ce "Majeederh babu ke ba namiji, ko aurenki mutum zai yi ki ce ke ba zaki aure ba ki ce kina da miji kawai, Majeederh wallahi wallahi duk sanda na ji labari ko na ganki da wani namiji to Allah ya isa ban yafe ba, karatu kawai zaki a tsayin shekaru takwas ɗin nan........






Mijin Malama
0811923761628
Majeederh was listening to her father with great surprise, her heart was pounding, A ranta tana jin cewa ko mahaifin nata bai ce kada ta kula kowa ba, babu wani ɗa namijin da zai ce yana son ta balle ya yi ji sha'awar aurenta, This is her destiny, and she answered with both hands as a complete Muslim. "Majeederh" Abbu ya kira sunanta cikin kakkausar murya ta kasa amsawa sbd taraddadin rashin sanin abin da zai biyu baya ya ce "Ni ne ubanki, mahaifinki jinina ke yawo a duka jijiyoyin jikinki, ƙwayar haihuwata ita ce ta samar da ke, idan kina zaton a zuciyarki kiyi gaggawar cire zaton, wallahi tallahi nine mahaifinki Allah ya shaidawa, Manzonsa ya shaida, Mala'iku sun shaida haka.....,"
Majeederh ta katse Abbu jikinta na rawa ta ce "Na sani, na sani bani da wanda ya fika duka duniya Abbu don Allah ka yi haƙuri kada ka aibata ni" Abbu ya ce "Kin yarda da hakan?" Ta yi saurin ɗaga kai sbd ba zata iya magana ba, ƙirjinta ya yi mata nauyi. "Hawwa'u a matsayina na wanda ya haifenki wallahi wallahi idan kika kula wani namiji sau ɗaya tak da sunan soyayya Allah ya isa ban yafe miki ba, karatu kawai na yarje miki kiyi tsayin shekaru takwas ɗin nan" Maganar Abbunta ta sanya mata wata iriyar faɗuwar gaba mai tsanani da ƙyar ta ce "Na yi maka al'ƙawari Abbu, ka tayani da addu'a kuma ka yi mini alfarma ɗaya don Allah Abbu"
“.... Alfarmar me?” Abbu asked. Ta yi saurin cewa "Abbu ka duba halin da nake ciki idan da hanyar da zaka iya mayar dani jinsin namiji don girman Allah Abbu ka taimka ka mayar dani namiji,ni ma zan fi nutsuwa zan fi yin karatun yadda ya dace"
Abbu ya ce "A'a ba shakka, ni kikewa hannunka mai sanda? Ni kike son nunawa ban isa ba, duk abinda ɗa namiji zai kema zaki iya, daga yau yanzu ki daina kallon kanki matsayin mace ki fara ganin kanki tamkar ɗa namiji, wanda zuwa nan gaba yake fatan zama babba a ƙasar, ta hanyar zama Gwamna, shugaban ƙasa, ko shugaban wani katafaren kamfanin, amma idan kina jin ban isa ba go ahead Hawwa'u kina da full right na yi duk mai kikeso haihuwa ce a haife dai mun haifa" Cikin hanzari Majeederh ta girgiza kai ta ce "Wallahi ka isa, ni ikonka ce ba zan sake cewa komai ba ka yafe mini na bi Allah na bika Abbuna" Ya yi shiru jin haka ya sa Majeederh runtse Idanunta zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi. A takaice Abbu ya ce "Duk wata kina tura mini kuɗin Albashin nan, kada ki ciri ko kwabo idan kuɗi kike buƙata ki nemi taimako wajan wani" A sanyaye ta ce "In sha Allah"
Kashe wayar ta yi tare tsorawa kanta idanu ta cikin madubi, ta jima tana kallon kanta kafin a fili ta ce "What should I do?" She don't know What to expect and kept thinking about how her father would react to seeing her after so long, yanzu ma ya aka ƙare balle ta ja lokaci, ta dafe kanta dake juyawa azumi ta kai babu komai a cikinta sai ruwa. _“Majeederh, pray ki faɗawa Allah komai”_ Wata zuciyar ta bata amsa. She breathed out, trying to calm herself nerves.
Tana zaune har aka kira sallar Issha amma bata motsa ta yi nisa cikin tunani domin ko kiran ma Allah bai nufeta da ji ba, ta zama kamar zararriyya. Kafaɗarta da aka jijjiga da ƙarfin gaske ya sa ta sauke wani wahalallan numfashi tana mai buɗe idanu a firgice ganin Ƙhulud Arzaan ya sa ta haɗe fuska sosai tana ɗauke kai, Ƙhulud Arzaan ta ce "Ƙarfe 10 na dare ke kam kina zaune?" Majeederh ta kalli Ƙhulud Arzaan ba tare da ta ce komai ba "Ki zo ku gaisa da Kalb" Majeederh ta ce "Maimaita" Ƙhulud ta ce "Kalb ya ce na kira ki ku gaisa" Majeederh ta girgiza kai ta ce "Kafin wannan, kin ce wani abu?" Ƙhulud Arzaan ta dinga kallon Majeederh kana ta ce "Ƙarfe 10 kina zaune?" Zumbur Majeederh ta miƙe ta ce "Asstagafirullah Ya Allah" .... "Lafiya?"
"Ban yi sallar Issha ba" Ta faɗa a gigice kamar ta yi kisan kai. Ƙhulud ta nemi waje ta zauna tana mai cewa "Eh to da sauƙi, ai sallar Issha bata ɓaci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce; da ba don kada na matsantawa al'ummata ba, dana umarce su da yin sallar Issha bayan sun farka daga bacci, Talatainin dare" Ita dai Majeederh bata ce komai ba, Ƙhulud Arzaan sai bin Majeederh da kallo take zuciyarta fal tunani har ta iddar da sallah kana ta fara azkar. Ganin Majeederh bata da niyyar ta shi yasa Ƙhulud Arzaan miƙewa ta koma part ɗinta, ta samu mijinta Ajlaal zaune yana danna waya hannunsa riƙe da Apple sbd yana ƙaunar dangin kayan lambu, ta zube a saman cinyarsa idanunsa akan wayar ya ce.
"Meke damun rayuwar Yarima Ajlaal Sultan?" Ƙhulud ta kwaɓe fuska ta ce "Allah daga kai har Majeederh baku son ku gaisa" Ya yi kyakkyawan murmushi kawai yana girgiza ƙafarsa alamar rarrashi can ya ce "Ga ni fa... Call her" Ta tura baki ta ce "Gashi nan sai sallah take Allah don kar tazo ne" Ya saka hannu ya zame hular kanta yana cusa hannunsa cikin sumarta bai ce komai ba. "Ka zo muke part ɗin nata, ka ji Kalb my prince"
Ya waro dara daren idanunsa cikin murya irin ta masu mulki ya ce "Prince ɗin Saudiyya da zo wajan wata? Ni Ajlaal? " Ta yi shiru tana kallonsa ya ce "Uhm, shi ya sa kike ta zubar mini da ƙwayaye a hanya ƙasa ƙasa, kin kasa riƙe ko ƙwai ɗaya balle Sultaan ya saka ran samun grandson?" Ta daki ƙirjinsa dake buɗe cike da yalwataccen gashi kafin ta ce "Ajlaal wayo zaka mini, idan ka fara haka" Ya tsorawa lip's ɗinta idanu kana ya saki wayarsa a gadon ya ce
"Damn it...!"
"Me?" Ya miƙewa gabaɗaya tana wutsil wutsil haka ya cillata gadon yana kashe hasken ɗakin gabaɗaya muryarsa can ciki ya ce "Yarinya ina zama lafiya wajan aikina kika saka rigima ashe Allah ke sona da rahama"....... Cikin dare Majeederh ta kasa bacci sai juyi take saman gado tana riƙe cikinta a hankali take kiran sunan Allah, jin azabar ta yi yawa ya sa ta miƙe a haukace tana girgiza kanta tare da zubewa saman gwiwoyinta ta ce "Ya Allah ka ɗauke mini abin da na ke ji har gaban abada wlh ban so, Ubangiji ka karkatar da halitta jikina zuwa ta jinsin maza" Ta yi shiru duk da sanyin ac amma zufa take jikinta na ƙyarma da ɓari, ta zari hijabi tare da sakawa ta nufi wajan part ɗin. Lokacin data fito yana zaune saman kujera a daidai corridor wanda zai mayar da kai part ɗin Ƙhulud, daga shi sai wata Jersey fara tas faffaɗan ƙirjinsa a bayyane, ya ɗora ƙafarsa saman table hannunsa riƙe da system yana dannawa, lokaci zuwa lokaci yake yatsuna fuska yana ɗaukan green tea tare da sha a hankali, sumar kan nan nashi har wuya, Prince Ajlaal Sultaan gabaɗaya mahaifinsa ya ɗakko sak. Yana zaune ya ji motsi ya juya kansa ya hango mace durƙoshe ta cure waje guda tana yarfe hannu, taɓe baki ya yi tare da kwasar system nasa ya na jan tsaki..... Washegari dai wajan 11 ta shiga Al-Azhar University tun kafin ta nufi department ɗin su taci karo da babban malaminsu. Cike da tsantsar ladabi ta gaisheka ya ce "Majeederh Abdul'aziz Khan?" Ta jinjina kai ya ce "Follow me" Yana tafe tana binsa kamar bata son takawa har ya isa office ɗinsa, manyan mutanen data gani a office ɗin ya bata tsoro ta zauna gefe guda. Malamin ya yi gyaran murya ya ce "Majeederh ga jakadan ƙasarku Nijeriya dake zaune a nan Misira, bayan zaman tattaunawa da manyan ƙasar ku kama daga shugaban ƙasar, gwamnan sauren jihohi da naku, shugaban malamai na ƙasa dana jiharku daga ƙarshe sun bada sunanki matsayin wacce zata wakilci ƙasarku Nijeriya a gasar musabaƙar Alkur'ani ta duk duniya" Majeederh ya zaro idanu waje ta shiga girgiza kai a raunace ta ce "Ba zan iya ba, ba zan iya ba ni Ɗaliba ce"
Jakadan Nigeria ya ce "Zaki iya Majeederh, Malamin daya baki ilimi ya shaida hakan, mahaifinki ya shaida" Muryata na rawa ta ce "Duk duniya fa? Ba zan iya ba please a sauya wata" Ta faɗa a shagwaɓe Ajlaal Sultaan ya ɗago kansa dake naɗe da hirami ya ɗan kalleta kana ya taɓe baki yaci gaba da abin da yake. "Ki nutsu wannan dama ce da ba kowa Allah ke bashi ba, abin alfahari ne ko da baki nasara ba ace kina cikin jerin Ɗaliban da suka shiga, Nijeriya yanzu ke ya zubawa idanu, jikarki, unguwarku, Malaminki, mahaifinki ke ce hope ɗin su, sun yarda dake don haka ki basu mamaki" Majeederh ta yi shiru ta ce "Ina tsoran rashin nasara" Wani dake zaune ya ce "Good, than sai ki miƙe ki tashi tsaye ki saka yaƙini sai Ubangiji ya tabbatar, kuma sai nan da wata biyar za ayi kafin nan kin samu hurarwa" Ta ƙara yin shiru tabbas dama ce a gare ta ta bawa Abbu abin da yake buƙata.
"Zan yi" Suka sauke ajjiyar zuciya kana suka sanya mata albarka ta miƙe a hankali ta fice Ajlaal ya ɗan saci kallonta yana ɗauke ido.
Tun daga ranar Majeederh bata da lokacin kanta, manyan malamai suka sanyata a gaba, karatu safe, rana, dare. Daman tuni haddar Alkur'ani sittin ɗin suna zaune a kanta daram, Tajwid da mukarijin hurum ake tisa mata, da saita ƙira'a daman Ubangiji ya bata murya kamar haihuwar Larabawa. Ya zamana a tsaye bacci take sbd karatu, Ƙhulud Arzaan ganin Majeederh ya yi mata wahala idan tana bita da rigima Ajlaal baya ce mata kanzil. Majeederh ta goge harsu malaman mamaki kawai suke idan tana karatu, hakan ya ƙara sa musu hope mai girma akanta...


*5 Month later..... The day*
Ranar Musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa ya tashi ranar watan tafiyar alhazzai, watan zul-hajj. Tun ana sati ɗaya gabaɗaya Ɗaliban ko wacce ƙasa ta Muslunci suka sauka a ƙasar Misira, daga nan kuma manyan mutane, shugaban ƙasar ko wacce ƙasa, da gwamnoni, hatta Sarkin Saudiyya Sarki Sultaan ya halaccin Misira ana kwana ɗaya da shi da Mahaifiyarsa Zaytoon, hadda. Babban hall ɗin ya cika da jama'a fal, ƙabila da yare daban daban farar fata da ɓaka, jami'an tsaro kamar me. Saura minti ashirin a fara Ɗaliban duk suka shigo ko wanne da tambarin ƙasar shi a jikinsa, kowa aka nuna masa wajan zama kana zama computer zata nuna sunanka da kuma ƙasar da kake, gabaɗaya kuma ya kasance mata ke namiji ɗaya ne daga Qatar. Majeederh kanta a ƙasa sbd jiri da faɗuwar gaban dake riskarta na rashin sanin su waye a wajan. Zagaye biyar ne masu zafi, da kayi kuskure Computer zata tsayar da kai. Aka fara da ƙasar Saudiyya ta tayi karatu yadda ya kamata, a zagaye na huɗu dana biyar ta samu matsala. Abun kamar abin mamaki Majeederh ce ta zamo ta ƙarshe ma'ana Nigeria, Computer ta nuna mata farkon shafin suratul Yusuf, kana malamin ya ja.
Kanta a ƙasa ba tayi kuskuren ɗago kan ba, lokacin da tayi Basmala shiru wajan ya ɗauka ya zamana kamar ba a ji ƙira'ar kowa ba sai nata, sbd zaƙi da sautin muryarta daya zaga ko'ina na hall ɗin, a tare Sarki Sultaan da Zaytoon suka ɗago kan su, tare da kallon inda Majeederh take zaune fuska rufe, Zaytoon ya dubi computer gaban Majeed taga ansa. _“Majeederh Abdul'aziz Khan, from Nigeria”_ Karatu take mai ɗauke da zallar ƙa'idoji na Kur'ani. Tunda ta fara karatun idanunsa akanta ya kafeta da wani irin rikitaccen kallo yana mamakin yadda a ƙasar su Nigeria aka samu mai daɗin murya da ilimi kamar Majeederh. Tunda ta fara karatun babu gyara ko tuni, waƙafi, aya ko wasali har zuwa zagayen ƙarshe. Computer ta nuna mata Suratul Maryam tsakiyar surah. Cikin rashin sa a ta ɗago kanta da nufin sauke numfashi nan take komai nata ya kunce dalilin ganin dubban jama'ar da suke gabanta tare da kallonta suna kuma saurarenta. Ai gabaɗaya neman duk haddar Alkur'anin dake kanta tayi ta rasa kaf, a tare kuma Aliyu-haydar, Captain Alpha, Prince Ajlaal Sultaan da wani matashi dake kusa da Gwamnan jihar Kano suka ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!....






MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616


ALLAH ya nuna mana ranar Monday Monday Lafiya.... Have a nice weekend👑🍷29
Da sauri Aliyu ya juya tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login