Showing 18001 words to 19558 words out of 19558 words
, ta fita da gudun ta duk kuwa da tsoron dare da take yi, cikin rawar kai ta tura bayin tare da haske cikin bayan gidan da fitila.
da sauri ZAHID ya tashi areej yarda fitilar tayi, ta zun duma ihu tare da rufe idanuwanta.
a fusace ya kamo ta ya fito da ita ji yayi tamkar ya dauke ta da mari, ko ya samu sassauci a cikin zuciyarsa dan ma yana da yaƙinin ba , abin da ta gani, domin yana ƙoƙarin mai da wandon sa , ta shigo.
har yanzu da ya fito da ita bata bude idon ta ba cikin kakkausar murya yace '' areej me kika gani..?.''
ya fada haka ne domin yana son ƙara tabbatar da zargin sa.
a hankali ta buɗe idon ta , ta kalle sa tace '' au daman kai ne ba aljani na gani ba..?''
wani sanyi ne yaji ya shiga zuciyar sa, har izuwa babban ɗan yatsan sa hamdala yayi a ransa a fili kuwa sai yace '' a'a abin da yafi aljani kika gani..?''
da sauri tace '' yaya dan Allah karka tafi ka tsaya nayi fitsari amma fa ka rufe idon ka, domin ba kyau wani ya kalli wani ba kaya, yauwa yaya yaushe ka dawo sun sake ka kenan..?.''
dafa ƙansa yayi yace '' karki cika ni da surutu maza kiyi ina jiran ki..?.''
to dan Allah karka tafi.
areej ta fadi haka cikin shagwaɓa.
banza yayi mata , ya ɗora hannun sa akan bango.
iyamu fitowar ta kenan wani murmushi tayi najin dadi dama tazo da zata rusawa Maryamu farin cikin'ta dagewa tayi ta zun duma ihu tare da kuru ruwa da sauri areej ta , tashi tsaye ko mai da pant din ta ba tayi ba , ta rungume ZAHID tana cewa wayyo Allah yaya ZAHID.
Mutanen gidan ne suka fito ZAHID da yake kokarin raba jikin sa dana areej amma ta kankama sa iyamu kuka ta saka tana cewa Iya yau nake ganin tashin hankali ZAHID ya rasa wazai nema sai yar uwar sa, tare naga sun fito daga bayi.
nanne ji tayi duniyar na juya mata , haka ma malam, aunty Jamila da mijin ta a lokacin suka shigo suna tambayar lafiya.
ƙara maimaita abin da ta fadi tayi ZAHID saboda tsabar mamaki yama kasa musanta zargin ta da kallo kawai yake bin su areej da har yanzu nata jikin sa aunty jamila ce ta cire ta , daga rungume shi da tayi tana cewa a'a wallahi ko da ban gani da ido na ba ZAHID ba zai taɓa aika haka ba,
Iyamu ta share hawaye tace '' haba jamila da ZAHID da AREEJ duk ya'ya na ne gyara kayan ka ai ba zai zamo sauke mu raba ba, laifina ɗaya da nayi ihu abin ne ya razana ni ya girmi ƙwaƙwalwa ta amma kuyi hakuri.?.''
ta faɗa tana kara rushewa da kuka.
IYA tace '' ya'yi ɗin Allah ya sakaa kwance kika gansu turmi da tabarya kowa ya tafi ya kwanta bana son dogon zance,
jikin kowa a sanyaye ya tafi nanne kasa rintsawa tayi kallon areej tayi da taka ta mutsu mutsu nanne tace '' areej me kuka yi a cikin bayi..?.''
turo bakin ta , tayi tace '' bafa abin da mu kayi cemai nayi ya tsaya nayi fitsari tsoro nake ji kuma a waje ma nayi, na shiga bayi sai naga yaya sai nayi ihu shi ne ya fito dani yana yi min faɗa fitilar ki ma tana cikin ban daki.''
shiru tayi ta koma ta kwanta a hankali bacci ya dauki areej nanne kuwa tama kasa bacci, iya aminta ta yarda da iyamu dan haka, bata zargi komai ba , duk da wani shashi na zuciyar'ta yana ƙaryata hakan saboda ta yarda da ZAHID ta amince masa amma sanin halin dan yau sai, Allah dan haka bata musa ba ,
Wannan kenan..
kamar yadda bacci ya ƙauracewa nanne haka ya ƙauracewa ZAHID ban da juyi ba , abin da yake yi lura da halin da yake ciki Tahir ya tashi yace '' ZAHID lafiya me yake faruwa..?.''
gyara kwanciyar sa, yayi yace '' bakomai?.''
Tahir yace '' a'a, kar mu yi haka dakai abokin kuka ba'a boye masa mutuwa, wata ƙila faɗa min da kayi shi ne samin sauki a cikin zuciyar ka...''
ZAHID yayi shiru yana sauraron sa, sai da yakai ƙarshen maganar sa, yace '' Tahir wallahi areej ta saka ni a matsala wacce har ƙarshen ruwata bazan iya goge wannan taɓon ba daga jiki na...?.''
tashi yayi zaune yace '' kana yi min bayani a dunkule ka fito fili ka faɗa min me ya faru..?.''
rintsai ido yayi ya soma bashi labarin abin da ya faru yaci gaba da cewa babbar damuwa ta halin da iyayen mu zasu shiga Tahir sanin kan kane ni babbar mace ma ban bi ba balle wannan da bata da komai idan na neme ta amfanin me neman ta zai min.
cewar ZAHID.
Tahri yayi shiru yana tunani can kuma sai yace '' gaskiya wannan matar bata kyauta ba daman kuma can tana da mugun nufi akan ka, saboda me dan taga haka zata tara mutane..?' amma yice ko ka musa kai magana..?''
ZAHID yace '' wallahi Allah Tahir magana ma na kasa yin ta gani nake kamar a mafarki abin nan yake faruwa ba zahiri bane.''
Tahir yace '' kash dama bakai haka ba hakan ne zai ƙara karfafa mata gwuiwa su, kuma su ɗauka gaskiya ne abin..?''
Hmmm Tahir gaskiya bata bukatar ado ko rantsai rantsai yau duk wanda yayi maka sharri, to ka ɗauka taki ya zuba maka wallahi koman daran da ɗewa ubangiji zai saka maka
Cewar ZAHID.
Tahir yace '' kuma Hakane Ubangiji ya fito da gaskiya..?.,
amin ya Allah Zahid ya fadi haka yana mai da kai ya kwanta.
Washe gari.
fitowa suka yi domin tafiya sallar asuba a soro suka hadu da malam da Nabeel gaishe da shi suka yi kamar yadda yake amsa musu haka ya amsa musu fuskar sa bata nuna damuwar, komai.
tare suka tafi masallaci bayan an idar suka fito, da sauri Malam ya juyo jin kiran dan uwan nasa gaisawa sukai cikin faɗa Alhaji bilyamin yace
'' wato bukar ka nuna min iyaka ta ina cewa danka ɗana ne har ni zance yazo da dinga kai yarinya ta makaranta yace ba zai iya ba good yayi kyau to wallahi abin da nake baku kuke rainawa na dena kuje can ku ƙarata ai daman tsiyar talaka kenan an faɗa muku kudin nawa kwaso su nake da zan dinga diba ina baku..?.''
malam kasa magana yayi sai bin dan uwan nasa yake da ido zuciyar sa namai wani irin tafasa buɗe baki ZAHID yayi zai magana malam yace '' ka tafi ba ruwan ka..?.''
Alhaji bilyamin yace '' dan Allah bukar barshi da wallahi yau sai na nuna mai, shi ba kowa bane ba wato kai na mara kunya ko...?.''
hmmmm sai ya ja kwafa yana saɓa babbar riga da sauri ya shiga cikin gidan har yana neman tun tuɓe.
Malam da ZAHID bin bayan sa, suka yi su abdulraman suka tafi gida shiga cikin gidan sukai babu kowa a tsakar gidan.
ZAHID shiga dakin mahaifiyar sa, yayi bakin sa dauke da sallama.
Joud amsawa tayi tana gaishe dasu.
Zama Zahid yayi yana amsawa yace '' ina nanne..?''
tana daki ta bashi amsa tana ci gaba da yin guga.
shiga cikin dakin yayi ya durƙusa ƙasa yace '' nanne ina kwana..,
nanne ciki ciki ta amsa mai areej da sauri tace '' yaya ina kwana..?.''
wani irin soya zuciyar sa, ta shiga yi sakamakon amsa mai da mahaifiyar sa tayi ba yadda ta saba amsa mai ba.
kasa amsawa areej yayi ya cije lips din sa na ƙasa ya kasa ko da motsi ne.
Nanne tashi tayi tana kama hannun areej domin tayi mata wanka kar lokacin makaranta ya kure.
jikin sa a sanyaye ya tashi ya fito.
IYA da take cikin daki ta kwala mai kira, amsawa yayi tare da shiga cikin dakin yana cewa Iya ina kwana
IYA tace '' rasa kunya ba zan amsa gaisuwar ka ba yanzu har wuyan ka ya isa yanka da wannan yawon ɓaɓal ɗin da kake ba gwara ka tafi gidan kahun ka ba , kai ma ka samu na sakawa a bakin salati amma da yaje kai dan taura ne uban girman kai ba za ka yi ba...?.''
Zahid bece komai ba domin idan yace zai magana tofa, ba abu ne me kyau ba zai fito daga bakin sa dan haka shirun nasa yafi alkairi.
IYA tace '' tashi dan nema daman nasa ba zakai magana ba wannan miskilancin naka yana ban haushi kirawo min sani da bukar ka kirawo min sunusi..,
tashi yayi bece komai ba , ya fita, kai tsaye gidan aunty jamila ya shiga yana sallama
amsawa tayi tana fitowa daga kitchen tace '' Zahid kai ne da sassafe Allah ya saka lafiya ba wani abu kuma ta ƙara cewa ba..?.''
ZAHID yace '' a'a bakomai ina kwana..,
ajiyar zuciya ta sauke tana amsa gaisuwar sa.
ZAHID yace '' kahu sunusi yana nan..?.''
Aunty Jameela tace '' a'a baku haɗu dashi ba aikuwa ce min yayi ya yafi gaishe da iya nima yanzu zan zo gaishe da ita.,
zahid yace '' to bara na faɗa mata.,
ya faɗa yana juyawa be jira me zata ce ba , fita yayi ya shiga cikin gidan su yana saka
Ƙafafuwan sa a dokin kofar iya ya kusan sumewa saboda tashin hankalin da yaji.
Mu hadu a arewa book domin jin yadda zata kaya
08141785374
littafin nan dubu daya ne tafiyar telegram.
8141785374 amina alhsan Muhammad opay
Ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785374