Showing 6001 words to 9000 words out of 19558 words
sa hankali kwance tamkar baya gurin duk abin da suke yi ko tari be yi ba wayar sa na hannun sa yana daddanawa mai da kallon ta tayi gun nanne a hankali tace '' nanne ba kince ba kyau wani ya ga tsiraicin wani ba kuma Ubangiji yana babbaka mutum lokacin mutuwar sa be ba ya mutu kalli yaya yana gurin ni ba zan cire ba naje na mutu..,
Murmushi nanne tayi tace '' haka ne tafi daki ki cire ki saka me dan ƙaramin hannu ta shan iska..,
ihu ta saka za ta fara tirje tirje suka haɗa ido da ZAHID yace '' maza ku shirya lokacin karatu yayi...,
da sauri ta ɗago tace '' yaya ni zazzaɓi ne a jiki na bani da lafiya ko nanne..?,
ko sharafa kike yi sai kinyi karatun nan gobe ma idan zan fita ni zan dauke ki nakai ki ba nabeel ba.
wani yawu ta hadiya ta tafi daki kaya ta canza ta dauko jakarta ta fito lokacin har ya fara yiwa su najwa zama tayi ya gama yace '' zo..,
zuwa tayi kusa dashi gaban tana faduwa dauko littafin ta yayi ya fara buɗawa zaro ido yayi yace '' Areej me kika rubuta nan..,
muci muci ta fara da idanuwanta taja baya dan ƙo hannunta yayi yace "'zaki magana ko sai na kwaɗe ki ..?,"
Dan Allah yaya kai hakuri aunty namu ce mana tayi botiki botiyun kofi cofiyun kofa kofiyun haka ta karanta mana
what a you mad..?,
tuni idanuwanta suka cika tab da kwalla still bata dena taunar ayar ta ba ga wata kuma a hannun ta kallon nanne yayi yace '' kinga ko nanne wallahi yarinyar nan nagaji da halin ta wacce malama ce dan Allah zata faɗa mata wannan maganar da munafurci ne da ita ce kan gaba wajen bada labarin abin da ya faru..,
Shiru nanne tayi jin maganar iya ta dawo tace '' to bakin mugu wannan yarinyar dai bada ban Allah yayi ta kosasshiya ba wallahi mijina da tuni ka dade da ramar da'ita irin kune ku hana matan ku sakat ka bakar jaraba kullum cikin azumi..,
kunya ce ya kama shi ya saki hannun Areej agaban su joud iya ke faɗar haka kai sha'anin iya sai ita nanne tace '' iya sannu da zuwa..?,
zama tayi dakyar tana sakar salati tace '' wallahi maryamu bazan amsa gaisuwar ki ba tunda kema kin zama bakar muguwa me hana da ya danƙi hannun ta ki dauki muciya ki buga masa a hannu salon Ya karya min jika ta to yasin kana karya ta hmm ranar caji moshan za mu tafi..,
iya kiyi hakuri yanzu nake shirin yi mai magana.
nanne ta fada cikin sanyin nan nata
Uhmm kyaji dashi ciwon ajali a ɗayan tsa kowa na hango shi na hasko shi da fitila ta Hajara Hajara hajara uwar bakin hali..
da sauri iyamu ta shigo tace '' iya sannu da zuwa..,
wani kallo tayi mata tace '' bana bukatar gaisuwar ki naji ance wannan dan neman ya dawo tun a hanya lado sirikina ya faɗa min wanda yake aurar yar gidan kanwata mariya yake min jaje to akul akul karna ji karna gani billahuwar ramanu hajara ranar da dakin ya dauki kayana tofa dole sani ya sake ki agidan ku zaki kwana ina dalili haka kurum me ya nadani da shi ba dai uban sa na haifa ba to bana son zazzagar albarka abarni ma da ciwon hawajan jinin da yake damuna da hasfatatus (hepatitis ) da yake idi me camiris
(Chemist) yana namijin kokarin akan wannan ciwo nawa da tuni wani labarin ake ba wannan ba kwanaki maganin dubu biyar na siya har yanzu ina dashi ina watsa uku zuwa hudu na kwanta cikin salama shi ya saka za kuga dakyar nake tashi sallah asubayi..,
iya yaushe kika kamu da wannan ciwo likita ne ya gwada ki yace kina dashi juraij ya fadi haka yana kallon ta cikin mamaki tana da wannan ciwo amma lafiyar ta lau to yaushe ma ta kamu dashi..
cire mayafin'ta tayi tace '' mijina hmm daman cuta tana cina ranar nan na kunna gida radio suna wannan shirin da nake ji duk sati na kiwon lafiya ana hira da kwararran likita a Babban Asibiti wallahi kaf abin da ya faɗi ba wanda bana ji shi shine banyi ƙasa a gwuiwa ba na tambayi bukar kudi banma faɗa mai me zanyi da shi ba dan kar na daga mai hankali na tafi gurin idi me Chemist ya bani sauki goma ya haɗa min aunti battatik (anti biotics)..,
turƙashi iya hannu ta ɗora akan bakin ta tace '' shii bana son jin komai ku kuma da kuke dariya ku ci gaba dayi ku fito kuyi son ran ku masu kan luɗaya ni bani da duhun kai da naje aka bani magani gashi nan ina kan matakin farko haka yace min kuma naga amfanin haka domin bacci ina samun sa ishashshe.
shiru suka yi nanne ko matsi ta kasa dole ta saka ZAHID yaje ya jawa idi kunne ko ta kara zuwa ya bata magani karya bata zata zame musu yar kwaya.
kusan faduwa tayi da sauri ta ɗafa bango tace '' amma dai Hajara anyi mara kirki wallahi babban burin ki, ki kaini ƙasa to wallahi ubanki ma nafi karfin sa bake ba kurwar sani dai da kika gama shaye ta tas kika rufe sai yadda kikai dashi to wallahi nafi karfin ku duk abin da kuke yi a gidan ku na tsafi yana kunne na tas..,
a hankali tace '' iya kiyi hakuri ban san kin tashi ba..,
hajara ina kuwa zaki san natashi ta ina zaki sani bakin hali da munafurci ya rufe miki zuciya da ido.
shiru tayi ranta na suya ta rasa yadda za tayi da iya wata iriyar jarababbiyar mata ce ita ta iya masifa haka kurum sai ta zauna tana girgiza kafa a tsakar gida tana kallon mutane daddai ba wanda ta kyale a cikin sirikan ta gwara gwara nanne tana raga mata amma itama idan cin mutunci ya biyo ta kanta ranar tas za tai mata ke najwa dauko min mukulli ki bude min kofar nan..
tashi najwa tayi ta fito buɗe kofar tayi tace '' sannu Allah yayi albarka jameela jameela kina ina kina jina kin yi muƙus a daki ga dodo ta dawo nifa bana so na shigo cikin gidan nan ban ganku reras ba yawa yan matan amarya bana son fitina na lura yanzu abin da kika tsira ki dinga ware kanki kina kulle kanki a akurkin dakin ki me kama da shagon dan cirani wallahi ina mamaki ta yaya kike iya numfashi a dakin nan ranar da hamza bashi da Lafiya na shiga hmmm dawowa nayi da ciwon saman kai kwanya ta ciwo ta dinga yi yawa wata jaririya sabuwar haihuwa muɗigata sai harbawa take yi zafin dakin ki ya tada min da muɗigata ta haka na dinga addu'a ta koma ni jikina yana bani gidan nan anyi buso yasin zan kirawo malamai daga maradi abokin malam ne Allah ya jikan rai zai zo yayi addu'a duk dan kutumar uban da yayi min buso a cikin gidan mijina dan ya raba kan zuri'a ta tas zai koma mai kan sa dan haka magana nake muku da babbar murya duk wanda yasan yayi ya cire shi tas..,
aunty jameela shigowa tayi da yake kofar ta , tana waje ba'a cikin gidan take ba tace '' sannu da zuwa sallah nake yi lokacin da kika shigo ina idarwa naji kiran ki..,
Allah ko ta sallah..? to nayi nisa bana kuma dawowa kim sani yan uwanki suyi miki bayanin duk abin da nace Allah ya isa koda harafin magana kuka boye kunsani sarai ni bana munafurci bakuma nason annamimanci..
shiru su nanne suka yi har ta shiga daki ba wanda ya tofa tashi zama aunty jameela tayi tace '' yaya me ya faru..?,
Nanne tace '' gashi nan shi ta shigo tana zai daki Areej shikkenan ta fara faɗa..,
murmushi tayi tace '' Areej yar gata ..,
fadi da wai ki ƙara da ihu Areej yar gata ce dan ta rasa wani gibi na rayuwar ta bawai yana nufin mu ba zamu cike mata shi ba ,
Iya kiyi hakuri wallahi bada wata manufa na fada ba
banza tai mata tashi ga bayi sallama tayi musu ta fita iyamu ta koma ɓangaren ta.
da sauri nanne tace '' maza tashi kije ki kwanta karki min bacci anan..,
Nanna batai fa sallah ba cewar najwa.
Nanne tace '' najwa yaushe rabon ki da kika areej ta saka goshin ta a gabas..?,
Joud tace '' to ita dai mutuwa bata sallama wallahi rabona da ganin ta saka goshin ta a ƙasa tun wancan azumin shima saboda fita a sham da yake ta mai da abin kamar zuwa yawo ne shi yasaka take yi.
ZAHID yace '' bata sallah kamar ta..,
da sauri areej ta hau kan cinyar nanne tana zare idanuwanta.
dariya nanne tayi tace '' tashi kije ki kwanta..,
Malam ne ya shigo yace '' auta waya taɓa ki naga kina taɓa idon ki zaki tsiyar ki cikawa mutane kunne..?,
da hannu tai mai nune da su dariya yayi yace '' dan Allah ku sakarwa yarinyar nan mara tayi futsari wannan wa ce irin rayuwa ce haka..,
ZAHID tayi yayi yace'' malam sai da safe..,
To Allah yayi albarka yauwa zo..
dawowa yayi ya zauna su kuma su najwa suka shiga dakin su yace '' gani malma..,
dan jim yayi sannan yace '' Alhaji yace kaje ka dinga yi mai direba ga hakan ma alfarma yayi maka saboda wai Company sa yana da ma'aikata da yawa zaka dinga kai yaransa makaranta daza man ban zan da kake yi ka gama karatu ba aikin yi..,
Runtsai idanuwan'sa ZAHID yayi yayin da jijiyoyin kasa suka fito raɗa raɗa kanin mahaifinsa yana da damar da zai kaishi ko ina yayi aiki karatun ma dayaya ya ƙara sa ba inda beje ba neman aiki takardun'sa basu da wasu tangarda da first class ya fita amma ko ina yawa an musu baƙin shafi ba'a daukar sa da yayi wannan aiki gwara ya wuni beci ba ko da miliyan zai bashi akwai ranar da yaga yar tasa ta baɗa mai ƙasa ta wuce shi talauci hauka ne da ya zauna a inda za'a dinga hulakanta shi gwara ya bar gurin cikin son ya fahimtar da mahaifan nasa yace '' malma bawai zanƙi bin umarnin ka bane a'a ina so na tsira da mutunci na kaga nan gurin da nake zuwa ina dan samun abin da zan rufawa kaina asiri ba kyara ba hantara amma can sai abin da na gani kuma ba lallai zuciya ta , iya jurewa ba kaga na bata zumuntar da ke tsakanin mu bana so na zama nini silar rushewar wannan ahali koda zuwa nayi na faɗa muku za kuji ba dad'i ballantana bazan iya faɗa muku laifin dan uwanku ba ni kuma matsayin mahaifi yake a guri na, aiki lokaci ne wata rana sai labari bakowa aiki haifa da arziki ba kowa sai da ya sha gwagwarmayar rayuwa nasan abin da kake hange karfin ka ya kare ga najwa ga joud ga Areej wacce lokacin ba zaka iya yi mata komai ba saboda shekarun girma sun ƙara cim maka yanzu ma insha zamu zame muku katanga ni da dan uwana duk wani abu da ake yi ana samun halak zamu bi musa mo muku dan rayuwar mu ta inganta amma wannan aiki na Alhaji bazan iya ba zato yake yi haka zamu dawwama to insha'Allahu dan zaki zai girma alfarmar annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama wani ma sai ya more mu sai yaji daɗin mu karatun yaran nan insha'Allahu bazan gaza ba zan dauke shi har matsayin da zasu sami ilimin da suma zasu tallafi na kasan su...
Limshe idonsa yayi wani sanyi yana ratsa shi tabbas yasan ZAHID gwarzon namiji ne tsayayye duk abin da ya fadi yana ƙoƙarin cika shi ne Gwauron numfashi ya saki yace '' Allah ya dafa muku ya baku abin da kuke nema ta hanyar halak ya tsare rayuwar ku gaba da baya ya raba ku da fitinar zamani...,
ZAHID yace amin a zuciyarsa nanne ma albarka ta saka musu sannan ya tashi ya fita kai tsaye fita yayi a kofar gida yaci karo da Tahir tafiya cafe su kayi suna hira ganin me rake yayi ya tsaya, ya siya musu Tahir ya fara sha yace '' kuma raken akwai zaki wallahi kagan sa tamkar sugar..,
da alama dai santi kake yi mu samu guri mu zauna anan karka fadar min a hanya na rasa inda zan kai ka..
Tahir yace '' wallahi koma m zaka fadi sai dai ka fadi domin kai baka ji zaƙin raken nan ba..,
Tahir sweet da sauri suka juyo jin muryar juhud tana sanye da hijabi har kasa ga niqab a fuskar'ta murmushin jin dadi ZAHID yayi domin duk wayewar juhud tana burge shi idan zata fita tana rufe jikin tane, ta nuna cewa tasan abin da yake mata ciwo yace '' sweet ina zaki..,
kallon sa tayi me cike da ma'anoni kala kala sannan ta lumshe idonta lokaci ɗaya ta bude su tar akan kyakkyawar fuskar ZAHID yace '' unguwa zani nan soron dinki..,
ZAHID ABUBAKAR ABDALLAH GALADANCI yace '' ko mu tawo rakiya ne...,
maida idanuwanta ƙasa tayi tana wasa da yan yatsunta tace '' a'a Nagode barshi hakan zai zama da takura tunda ba kai kaɗai bane...,
murmushi yayi yana kallon Tahir da ya kasa cewa komai sai Yanzu yace '' juhud barka da dare..,
kan'ta yana ƙasa tace '' barka dai ya harkoki..,
Alhamdulilah yace yana zama a kan wani benchi.
To Allah ya dafa muku ya baku abin da kuke nema.
Amin ya Allah yace
sallama tayi musu, ta tafi dukan kafadar Tahir ZAHID yayi yace '' tashi uban son jiki yawa ba namiji ba..,
dariya yayi yace '' GALADANCI naga kai ka dade da zama soja shi ya saka na bar maka fagen daga..,
dariya yayi ya shafa sumar kan'sa yace '' wallahi ka tuno min da school ina kewar ta kai gabaki ɗaya ma karatun ina kewar sa da ba dan kanne na ba da sai na kara kuru na tafi karatu idan na tafi bansan wazai kula da su ba Nabeel bekai girman da zai dauki ragamar rayuwar su ba..,
Dafa shi yayi yace '' karka damu abokina Allah zai dafa mana insha'Allahu zamu cika burikan mu,
Tashi yayi suka fara tafiya suna hira har suka isa CAFÉ din su tarar da aiki sukai dan haka ko wanne ya zauna a mazaunin sa ZAHID buɗa laptop yayi yace '' Abdul Rahman ka samu kuwa website din nan ya buɗe ni wallahi har tsoron shiga nake yi ina shiga zai wullo ni waje..,
dariya dukkan su sukai wanda aka kira da Abdul Rahman yana zaune yana bushe gyaɗar sa yace '' ina fa kai yanzu da ace ya buɗe da network ai da yau sunana rich man..,
dafe goshi ZAHID yayi yace '' wallahi bansan ya zanyi da mutanen nan ba jibi yadda kowa yake jira kuma kamar sun saka headline din rufewa ko..?,
Wallahi sun saka karka damu yanzu haka jina nake kamar wani attajiri tun da ina cin dawisun talaka..
dariya dukkan su suka saka Asim yace '' shege shi ya saka tun dazu kake susar kunne da mukulli sai kaje kunnen ka ya burme..,
duka yakai mai yace '' dan Allah GALADANCI me ya ragewa takala yanzu ya Nigeria banda yayi susar kunne yaju dad'i idan da hali ka dan hada da yar gyaɗanli kana susar kunne kana tauna gyaɗa..,
kai kurum ZAHID ya girgiza domin in da basu sun saba wannan musum ga kuma mutane ana ganin su da kima karsu fara yar tanki tanka girman su ya zube fara danna laptop din'sa yayi yace '' ni dai wallahi ku cire ni a wannan batu ina da abin yi..,
Dole kace kana da abin yi zai kai wa me idon cin naira cewar Abdul Rahman.
Tahir yace '' la la Abdul Rahman kayi shuru wannan mutumin baya son gaskiya.,
tashi yayi ya leƙa wajen da mutane ke zaune ana ciki wani form na daukan aiki gwamnati ce ta fito dashi zata dibi malaman makaranta masu NCE yace "wanda ya ke kan layi yayi sauri ya zo ya haɗa komai website din ya buɗe..."
Wani ne ya taso ya shigo cikin sauri yake shigar mai da komai ya tura addu'a ya dinga yi Allah ya saka ya shiga kar su rufe portal din sanin kowa ne aiki yana karanci yayin da matasa suka rasa abin yi fitina ce ga al'umma bayan sune kashin bayan al'umma din wata ran sune iyaye me gaba ake so ta haifar ne yana wannan tunani yaga sun dawo mai da shi dafe kansa yayi yace "kawai abdulraman ka bawa sauran hakuri yaƙi yi..."
dariya yayi yace '' ashe bari ba shegiya bace da uban'ta ni yau nasan zamu yi tsalle mu duro da oga haka kurum ina zaman basir yace ko purewater ba zaka iya dauka ka siya ba sai abin da ya baka..,
da sauri Tahir yace '' duk wannan uwar gyadar da kuɗin sa ka siya..,
ɗaga mai gira yayi yana gyara zaman rigar sa da duk ta kode amma akwai guga saita glasses din'sa yayi ya zura yace '' galadanci ya kayi shiru ba zaka shigar min fadan nan bane..?,
Mutumin da ake cike mai portal yace '' ba dole yayi shiru ba ka dauko abin da yafi karfin sa..,
dariya yayi yace '' a'a galadanci baya taɓa gazawa damu mu nan da kake ganin mu tawaga ɗaya ce ko wanne a cikin mu da yan kwanaki ya girmi wani tare mukai kuruciya muka tashi shi ne babban mu duk wani faɗa shike tare mana tsakanin mukwai amana da son juna saboda haɗin kanmu kuma course ɗaya muka dauka muka zo muna aiki a waje ɗaya dan haka saniya bata taɓa gazawa da kawonta ko galadanci...,
kai bana son shirmen banza kayi abin da nace kafin ya dawo ka nemo mai kuɗin sa.
Tashi mutumin yayi yace '' to Allah ya bamu nasara da sa'a mu fita daga cikin wannan matsalar...,
amin ya Allah suka ce bayan abdulraman ya dawo ya zauna yace '' kuyi karo karo ku biya min kudin gyadalli...,
Tahir da takaici ya rufe shi ya ciro totuwar rake yace '' wallahi ko kobo bazan bayar ba raken nan ma ba zaka sha ba dan rainin hankali kamar shi yafi kowa son