Showing 3001 words to 6000 words out of 19558 words
shiga ita , taja mana kema wallahi ki dena yarda da ita Alkur'an tsumma ce..,
da sauri nanne ta tashi tace '' haba hafizu wannan ba mahaifiyar ka bace kake jifan ta da mugayen kalamai..,
iyamu kuka ta fashe dashi tare da kifa kan'ta a kafaɗar nanne tausayin ta ne ya kama nanne ta soma rarrashin ta
kwafa hafizu ya saki yace '' wallahi nanne ankar saboda kina cika min cikina ya saka duk abin da naga zai cutar dake da ya'yan ki nake nuna miki hanya amma ke bakya andasata (understand ) ba ruwa na jizos ba Allah mabane an'aike ne ankar ankar itama waccan zan tela mana tafi ta daga sabgar rocas yasin ko na sabule mata tafar cikin ta tas nayi mata ƙaramar tiyata..,
Hafizu ya zaka tafi mahaifiyar ka , tana cikin wani hali
Nanne ta faɗa cikin wani irin yanayi.
Chak ya tsaya ya juyo yace '' yasin nanne dan kece nifa na ma manta da wannan sunan ke kike tuno min dashi ne idan wani ne ya fadi wannan sunan da sai dai yaga haƙoran'sa suna yawo a ƙasa tas sai na cire mai su tofa dan kece nake raga miki..,
shege tsinannan ne karka raga mata dan ubanka wallahi hafizu ka kiyaye ni.
iyamu ta faɗa cikin ɓacin rai
hmmmm iyamu iyamu wallahi ki guji ranar da zanyi wa kowa na gidan nan zindir har kura ta cewa da kare maye gwara ni ba zambo cikin aminci nake yi ba kuma wallahi ido na idon wannan abin sai na hako shi duk ba ke kika samu a cikin bala'i ba.
rarrashin ta nanne take yi dakyar tai shiru sannan suka zauna nanne tace '' hakuri za kiyi da lamarin yaran nan kowa da yadda Ubangiji ya tsara mai rayuwa idan aka saka hakuri da juriya sai kiga Ubangiji ya kawo afuwa be kamata ki dinga tsine mai ba kina la'antar sa iyamu kama ta yayi ki dinga tausasar zuciyar ki tare da faɗa masa magana mai daɗi.
sai kiga ya shiryu ya bi kan turba kukan nan da kike mai ba ƙaramin bala'i bane a rayuwar sa dan Allah ki dena jifan sa da mugayen kalamai.
ajiyar zuciya ta sauke tace '' Allah yana gani ba saboda dashi nake kuka ba nanne kalli irin maganar da yake fadi wai bana zama dake tsakani da Allah...,
kara rushewa tayi da kuka taci gaba da cewa ai saiki zargi wani abin a zuciyar ki tunda zuciya bata da ƙashi idan ba kyautata miki ke da ya'yan ki ba me zanji a rayuwa ta iya so da kauna kin nuna min shi idan na musguna miki dai-dai da rana ɗaya sai Ubangiji ya kama ni haka dazu abin da jamila tai min banji dad'i ba wai na dauko farar alawa na bawa Areej ta karɓe ina kallon ta , ba komai nasan ba laifin ta bane irin maganganun da hafizu yake yi ne shi ya saka zargi ya shiga zuciyar ta ni kuwa ina zan saka kaina kowa yana yi min wani irin kallo me cike da ma'anoni kala kala duk kuma hafizu shine sanadi.
kama hannun ta nanne tayi tace '' karki damu wallahi ko ɗaya matsayin ki yana nan a zuciya ta Allah ya dada shirya mana yaran mu..,
kuka ta ƙara rushewa dashi tare da rungumar ta tana cewa Nagode nanne hakika ke faccala ce ta dabam Allah ya bar mu tare.
amin ya Allah tace , tana tashi ta duba targen ta zuba gari ta fara sannan ta mai da tukunya ta rufe lokacin iyamu ta tashi daga bakin kofar dakin ta zama tayi tana jiran dawowar Areej.
jin kukan ta asoro da sauri ta tashi ta leƙa tace '' ZAHID wai me yake damun ka da yarinyar nan yanzu daga aiken ta siyan Maggi sai ka dake ta me ta yi maka..?,
karaf Areej tace '' ganin sana yi a gidan wannan yar iskar matar me tara mata shi ne nace mai lah daman anan budurwa ka take sai ya dinga dukan baki na har muka ƙara so gidan nan abokin sa ma yaya Tahir sai da ya hana shi.,
kai nanne ta girgiza tace '' ZAHID ba sai na tsaya ina maka dogon bayani ba ita dai Areej kasan matsayin ta a gurina bazan zuba ido ba naga ɗaya daga cikin ku yana ƙoƙarin takura mata ba ko dan kaddarar da ta same ta be kamata ku tausaya mata ba kuji ƙanta ba amma kai halin ka yafi na kowa, kowa yana nuna mata so da kauna ban da kai Allah ya ganar dakai gaskiya...,
har ta gama maganar ta be ce komai ba sai da Areej tabar gurin yace '' nanne kiyi hakuri naga ranki ya ɓaci..,
bakomai Allah yayafe mana baki ɗaya , ta faɗa tana barin gurin bude dakin sa yayi yana shigowa tahir ya shigo shiga cikin gida yayi ya durkusa har ƙasa yace '' nanne ina wuni an wuni lafiya..,
cikin sakin fuska tace '' lafiya qalau alhamdulilah ya maman taku..,
tana lafiya qalau ya su Areej yar lukata..
murmushi nanne tayi tasan ya fadi haka ne dan ya saka Areej kuka ai kuwa ashe tana kusa ta leƙo tace '' na faɗa maka nanne zata kai ni gurin rage tsoka tace tsoka ce tai wa Kamatuna yawa..,
dariya yayi ya fita yana cewa da ta kuwa kyauta nanne tace '' ina gama girkin nan kafin su najwa su dawo zan miki kitso...,
idanuwanta tane ya ciko da kwallah tace '' nanne dan Allah kiyi hakuri mu bari sai gobe..,
haɗe rai tayi tace '' gobe yau she..,
tunani ta shiga yi da sauri ta za bura ta shiga cikin daki a guje jakar ta , ta dauko tace '' an bamu assignment Dan Allah ki bawa yaya yayi min ni idan na kai mai yana yi min yana rankwashi na yace min me kan kwakwa ina tsayawa wasa bana karatu kuma nanne duba fa ki gani ......
kalli rubutuna ina yin me kyau haka ma aunty din ajin mu tace..,
amsar littafin tayi sosai rubutun Areej ya bata dariya ita kan'ta idan za'a saka mata huka a wuya ta faɗi me ta rubuta ba lallai ta iya fadi ba Areej a kwai wasa da shiririta su, suke hanata fahimtar karatu tace '' Areej zo..,
ɗurkwusawa tayi tana kallon littafin nanne tace '' haka malamar ku ta rubuta treesing ne fa amma ga yadda kika sauya musu kamanni kalli tittafin naki yawa ankwato abakin ƙura Areej kefa yanzu kin fara girma kina ECC 3 wata shekarar primary zaki shiga..,
idanuwanta tane ya kawo ruwa daman bata da wuyar kuka tasan yau sarai yaya sai ya jibge ta zama tayi tace '' nanne gyara min in dauko pencil ki fiƙe da sharpener domin yayi kyau sosai yauwa harda cleaner..,
ke bayan magariba idan su joud suka dawo kuzo na ga littafin ku mu kuma yi karatu sannan wallahi gobe idan baki tafi islamiyya jikin ki zai faɗa miki kin gama cika wa mutane kunne sannan ku zauna haka siddan ba cuta kike ba.,
shiru tayi tana kallon sa haɗe rai yayi yace '' ina miki magana kin kafe ni da idanuwa zaki bar kallo na ko sai na shigo,
dauke kan'ta tayi ta kwantar dashi a cinyar nanne tace '' yaya kai hakuri..,
jin maganar nabeel a soro a guje ta tashi ta fita rungume shi tayi tana tsallen murnar dawowar sa , aya ya fito da ita a aljihunsa amsa tayi tana washe hakoranta duk cin zuma tace '' yaya nabeel nagode amma gobe idan ka fita aiki madara nake so..,
ɗagata yayi dakyar yace '' yar gidan nanne madara tafi karfina ban miki alkawari ba amma idan na samu hali zan siyo miki ita...,
murmushi tayi ta kunce ledar ta watsa kusan goma abakin ta , tace '' to nagode..,
Nabeel sauke min ya'karka fasa mata kai naga dakyar kake ɗaukan ta .
sauketa yayi yake cewa nanne barka da yamma kin dawo lafiya
Lafiya qalau alhamdulilah ya aikin naku da fatan dai komai lafiya
ajiyar zuciya ya sauke yace '' alhamdulilah sai godiyar Allah yaya barka da yamma..,
to Allah ya temaka
ZAHID yace '' barka dai mun wuni lafiya ya aikin naka..,
Alhamdulilah yana zama yace '' nanne wannan yar taki ce yawa bata san garin nan ba kullum dada fara shi take yi..,
tagumi tayi tace '' wallahi zan ɓatar muku akan yiwa yarinyar nan ba'a sai kun saka ta kamu da cutar gudawa ta zazzage ku barmin kaya ta ..,
dariya nabeel yayi yace '' an barmiki iya nanne yar gidan nanne ikon Allah..,
ya fadi haka yana doko ta komawa kusa da nanne tayi ta zuba mata aya a kan cinyar ta tace '' kema kici...,
murmushi nanne tayi ta dauka tana ci.
ZAHID yace '' kinde ji menace sauran kice kin manta..,
bata fuska tayi zuciyar ta ba dad'i tace '' to..,
komawa yayi fitar da da mintina kaɗan sai ga su joud da najwa gaishe da nanne sukai joud tace '' Areej bani ayar take inci naga ta jiƙa..,
ɗaya ta dauka ta bantara ta miƙa mata harara ta watsa mata tace '' rike kayar ki aini ba mayya bace ba..,
dariya najwa tayi tace '' maganin ki kamar baki san halin ta ba da shegiyar rowa idan kinga ta bada kayanta to nanne ce ko ya nabeel..,
munfi kyaurata mata ne shi ya saka ta bamu cewar nabeel
ba wacce ta , tanka shi suka shiga ciki cire kayan makaranta sukai suka fito, suka amshi girkin nanne
nanne tashi tayi ta dauko kum da kibiya Areej tana yan aya bata san ta tsaya akan ta ba sai ji tayi ta cire inner cap din ta kuka ta saka ,
zare mata ido nanne tayi ta zauna akan kujera tana taje mata tulin sumar ta , ta usul ba relaxer ko ɗaya ga ƙarfi kuka ta dinga yi har da majiya har aka gama kitson
ZAHID da yake cikin ɗaki shi da Tahir suna hira yaja tsaki yafi cikin kwando cikin tsokana Tahir yace '' nifa wallahi kana takurawa kanka me yarinyar nan tayi maka kuruciya ce wata rana ba za tayi ba...,
kwafa yayi yace '' idan suka barta ba tare da tsawatarwa ba wallahi haka zata ' shi abin takaici idan kaga hakoran ta to cine shi yasaka kwakwalwar ta , ta zama ta dusa bata iya fahimtar komai kaga saboda da ita na dauko wancan dankon a hanya dazu yau nasan hmmm balallai naga abin arziki a cikin littafin taba ga ƙin makaranta wallahi yarinyar nan ita take jawa kanta nayi mata duk wani abu da banyi niya ba , amma nanne ta dinga faɗa kenan ina jiye mata lokacin da za tai mata Aure ta kasa zaman auren ba shikkenan ba sai ta dawo baya ta gyara kuskuren da tayi...,
kwanciya Tahir yayi yace '' to aini ne mijin..kaga kuwa bazan hulakanta ta ba ...,
kai dakata wallahi ba zaka jawo min raini ba haka kurum ana zaune kalau ZAHID ya faɗa har cikin zuciyar sa
dariya Tahir yayi ganin yadda yayi maganar yace '' kai abokina ina harda su tada jijiyoyin wuya da ina cewa kai zaka fara kafamin gwamnati ...,
a'a gwamnatin tarayya zan fara kafa maka wallahi Tahir ka fita a idanuwana da wannan maganar taka me kama da kasha kwaya..,
tashi zaune yayi yace '' a'a giya nasha dan rainin hankali ni kuwa ina yar gidan dillaliya...?,
dan ya tura masa haushi ya fadi haka ai kuwa ya tura masa a fusace yace '' kaga malam lamarin naka yafara yawa zo ka fita ya za ayi ka dinga cewa mahaifiyar matar da zan aura mutunci ba zai yiwu ba kamata yayi a matsayin ka na amini na ka dinga daraja ta Kana marta bata amma kai kake fara kushe alakar mu..,
dole na kushe idanuwanka sun rufe kana shirin aikata babban kuskure a rayuwar ka haba abokina yawa wanda aka jefe ko akai wa sammu da fa kai kake kyamar rayuwar su amma yanzu ka saka kanka a ciki babbar damuwa'ta kar fa ta jaka wata hanya ba me bullewa ba...,
toshe kunnuwan'sa yayi yace '' wallahi da ace wani ne ya faɗa min wannan maganar da tuni na dade da shafe shi a cikin rayuwa ta waikai Tahir me ya saka baka so a zauna lafiya ne...,
*TSUMMA MAKUNSHIN CUTA*
Wolf in sheep's clothing
Ina meson logo ko invitation card
To ga dama ta samu
Werleedert graphics design
ta zo muku da graphic design na ban mamaki
Invatation card
VEDIO invatation
Logo
Banner
Poster
Menu
Acount sticker
Graduation stickers
Business sticker
Save the date
Business flayer
Birthday flayer
Engagement
Event program invatatin
Walimah invatation
Wedding invitation
Vedon invatation
Zaku neme ta a kan wannan number
+234 901 257 6569
Episode 2
Saboda ina son fahimtar dakai abin da ka manta.
tashi yayi ya fita jin ana ƙoƙarin kiran sallar magariba dai-dai lokacin malam ya dawo Tahir shima bin bayan sa yayi daukan kayan da malam ya kawo sukai suka shiga da shi cikin gida shi musu albarka yayi tare da amsa gaisuwar da suke mai.
daukan buta yayi da nanne ta ajiye mai ya dauro alwala suma su kayi, suka tafi masallaci a sukwane hafizu ya shigo yana cewa idan na yarda Allah ya tsine min albarka nanne nanne zo ki gani dan Allah yau wallahi wasu zasu bakunci Ingila me tukwane kuttumelesin kan baban ubancan lallai yau fa za ayi ta da dan kamfai idan na yarda nayi yawo tsirara sai da na shigo cikin gidan nan na ƙara tabbatar wa jiki na ya bani a cikin gidan nan aka cinye min kudin naman aska
da sauri nanne ta fito tana ƙoƙarin tada sallah tace '' lafiya hafizu me ya faru kake wannan kikirari...?,
zaro huka yayi ya soke a kugunsa tare da saka karan sigari da sauri nanne tace '' haba hafizu a cikin gidan namu za ka sha mana sigari kayi hakuri idan ka fita ka sha..,
cire ta yayi ya saka a kunnen sa tace '' dan girman Allah duba ki gani duba aska da kyau be rame ba..,
da sauri ta kalli karen da yake nuna mata wani irin baki ba kyen gani tace '' ni banda wata rama ba me ya faru..,
kina nanne na dade ina so ki an kare ko ba haka ba lamma..
abokin nasa ya cije baki yace ''hakane ka dade kana nuna mata way..,
yauwa lamma amma bata ganewa badai zance mata damsil basiratu ba tunda ko ba komai tafi waccan matar da wallahi idan bata sauya halin ta ba kaga dai ban yi wani karatun isilama nayi ba amma dai nasan ae yaneee to idan baya gyara halinta ba naru ce makomar ta kinga nanne ina umara na dinga turo kudi a siya wa aska yaci ya koshi abarshi da ciwon rashin ganina to wannan baiwar Allah sai ita take ci a cikin ta ko baki ga yadda ya rame ba daga zuwa umara na sati uku na dawo shine ya fita daga kamanninsa na tambayi wanda nake bawa kudin ya kawo mata yaci Alkur'an yana kawo mata amma zanyi maganin su dole a fito min da kudi na ko yau mutum yayi kwanan ingila me tukwane
Nanne tace "kayi hakuri hafizu nawa ne kudin naka na baka sai ka bar maganar bana son ƙara jin wani tashin hankali..,
kama karfen taga yayi yace '' ah wallahi ko karfanfana dattin aljihu bazan karɓa ba wacce dai ta cinye min kudina ta fito min dashi tun kafin nayi alkafura a kan ruwan cikin ta na caccaka mata wuƙa..,
toshe kunnuwan'ta tayi domin zancen nasa ba ƙaramin daga masa hankali yayi ba.
Kai da sauri suka juyo hamdala tayi ganin ZAHID domin dai-dai yake da shi tsoransa yake jima shiga daki tayi ta barsu fuskar sa ba annuri yace '' me nace maka kwanaki..?,
dauke kan'sa yayi daga kallon sa yace '' i get ..,
kwafa ZAHID yayi yace '' kai kuma karka ƙara shigo mana gida domin gidan nan ba sa'an wasan ka bane ..,
jan karansa yayi yana cewa albasa batai halin ruwa ba billahilazi ba uban da ya isa ya hanani shugowa da wanda na ga dama cikin gidan nan ni za'a tozarta a gaban abokina..
shiga daki yayi ya zauna yace '' nanne ki dena tsayawa ki saurari wannan yaron kine na sakar mai fuska kamar hakan da kike yi ya ƙara samin damar yin abin da ya ga dama cikin gidan nan ya shigo da wanda ya ga dama kuma kusan abokanan sa ba , mutanen arziki bane kinga su joud mata ne be kamata suna cuɗan ya da irin mutanen nan ba ko dan tarbiyar su..,
haka ne wallahi ZAHID abin da ya saka daman nake jan shi ajiki kaga irin su ba'a nuna musu tsana soyayya ake nuna musu ajawo su a jiki sai suyi hankali amma idan ana kyarar su ba za suji da dad'i ba haka iyayen sa kawai sai dai hakuri da addu'a Allah ya shiryar mana da zuri'a baki ɗaya..,
amin ya Allah yace najwa ta dauko mai tuwan sa zama yayi yana ci Areej sai matse kwalla take nanne ce ta taɓa jikin ta , taji zafi da sauri tace '' subbanallahi Areej me yake damin ki..? jikin ki zafi raɗau..,
kwantar da kan'ta tayi tace '' kaina ke ciwo da kunne na..,
joud tace '' nanne ba dole tai cuta ba yarinyar nan wasan ruwa fa take idan ta shiga bayi dan ruwan da muke ajiyewa wallahi tas sai ta karar dashi dan Allah ki siya mata fo ta dinga abin ta muna wanke mata..,
da sauri ta tashi ta kalli joud tace '' Allah ya kiyaye tab ni za kiyiwa tsarki wallahi ina neman tsari da wannan ƙaddarar nanne ka wata lukutar magana wai ni za tai wa tsarki sai kace yarinyar goye..,
dariya nanne tayi tace '' kyale ta ba wanda zai dinga yi miki tsarki..,
kwanciyar ta , ta gyara tace '' ai wannan abin ma salon su ganni ne yara su shigo suyi mini dariya nanne zafi nake ji..,
joud tace '' da nafi kowa murna wallahi.,
Hararar ta tayi tamkar idanuwanta za su fado ƙasa nanne tace '' tashi na cire miki rigar kya sha iska..,
satar kallon ZAHID tayi da yake cin abincin