Showing 21001 words to 24000 words out of 40610 words

Chapter 8 - MAH~ NOOR (MY FIRST WIFE) BY MRS USMAN-1.txt

06 Mar 2025

3515

kurb'an coffee din shi, yana kallon yadda suka b'ata fuska.
"Tiger! Ya naga ranka ya b'aci? Ko akwai abinda na rushe muku ne?"

"A'a wallahi! Kawai dai gani nayi kamar aka samu saka hannunka akan kome, za a samu cikakkiyar nasarar da ake bukata." Ya faɗa a sanyayye.
" Toh kasa hannun mana, ai kane wakilin Kamfanin, ni ban zo zama bane har yanzun."

Ya fadi haka yana murmushi, tare da kallon su.
"Lion!"
"It's about business matter! Babu abinda ya dame ni nazo holiday ne kuma kuna fara damuna zan gudu inda na fito. Dan haka ni ba, kuyi duk abinda yayi muku."

Ya fadi haka, tare da nufar Hanyar waje, yana rike da mug. Ya nufi cikin kamfanin, tafiya yake tare da nazarin abinda Nazzir yazo mishi da shi.
Kan shi a kan cup din da yake hannun shi, bai san lokacin da ya sake hanyar shi ba. Sai dai da ya hango wata mace tana daukar abu, tare da leke. Da sauri ya isa gurin.

A tunaninta Nazzir ne, dan haka cikin wani irin sauri tazo zata bangaje shi ya fisgota, ji yayi kamar an jona mishi lantarki, da sauri ya saketa, tare da kallon fuskarta wanda yaƙe cikin niffab, sake ta yayi tare da kai hannum shi zai cire abin fiskarta, zuciyarshi tana wani irin bugawa.

Exactly itama abinda take ji kenan, kurawa juna ido suka yi lallai ala dole suke san tuna lokacin da ya shude. Hannun shi ya kai a karo na biyu, ta buge hannun shi tare da saka hannun ta dukkan biyu ta ture shi. Yana tsaye akan kafar shi, sai mug din hannun shi da ya zube a Whiter hijab din ta, cikin takaici ta kalle.
Dariya ta bashi yayi wani karamin murmushi sannan ya kuma takowa gaban ta, zai cire nikaff. Da bangaje shi sai da ya jingina da bango, da zura da gudu, ya kai hannun shi ya riko wuyar hannun, warwaron azurfa ta wanda na mahaifiyarta ne haka ya zare a hannunta. Ya fadi durkusawa tayi zata dauka ya taka hannunta tare da dauke kan shi.

"Kai wani irin mugu ne? Zaka kashe ni ne?" Ta faɗa muryan ta na rawa, san ko a jikin kamar ma irin bada shi take ba, sake take hannun yayi tare durkusawa gabanta, yana kallon yadda Eyelashe ɗinta suka jike alamar zata sake kuka. Murmushin mugunta yayi sannan ya d'aga kafar shi akan hannunta da suka yi jajjur. Ya mike abin shi.
Ya bar gurinta, juyawa yayi cikin jin haushi tace mishi.
"Mugun banza kawai! Kuma sai na saka Nazzir ya kore ka. Dube shi me kama da yara ƙanana."
. Cak ya tsaya tare da juyawa yana kallonta, kawai yayi tafiyar shi amma dole yaci kaniyar wannan me dodon fuskar nan.

Tashi tayi tana yarfe hannun,.da suka yi ja. "Mugu ban tab'a ganin shi ba. Ahala yana cikin sabida daukar da aka yi ne, banza dashi da fuskar shi kamar Imran Abbas." Tabi hanyar da harara, (🤔🤓 toh meye laifin hanyar kuma)

Dakyar ta mike tare da barin gurin, ita godiyar ta daya da bai damu da abinda ya kawo ta ba. Tana shiga office d'insu ta sami Tasleem tana kuka.
"Baby Queen! Waye ya tab'a min ke?"
Cikin shashekar kuka ta d'ago kanta tare da kallon Noorh, tace mata.
"Amma kema ai kuka kika yi?"
Murza idanunta tayi, sannan ta ce mata.
"Wannan ba matsalar ki bace domin abu ne ya faɗa min a idanu!"
"Ai ba zaki gaya min kome ba? Sannan ni kina son na gaya miki kome?" Inji Tasleem,
"Toh Kiyi hakuri! Wallahi abu ne ya faɗa min a idanu, waye ya saki kuka?"

"Ni da baby Naz!"
"Kayyasa! Da wuri haka, toh kiyi hakuri amma tabbas bai kyauta miki ba. Sai ki dauke mishi wuta kawai."
"Wai ai nasan idan ya huce zai kirani." Ta fadawa Noorh haka, takaice ne ya kama Noorh. Ta ja kujeranta tana kallon ta. Sabida banzan haukar son da takewa Nazzir, haka suka gama aikin su. Ana tashi suke fito zasu shiga motar su, sai me? Taya a fashe.
Rike baki Tasleem tayi kamar zata yi kuka.
"Yanzun wani mugu ne yayi mana wannan aikin?"

Ta faɗa tana kallon yadda aka fasa tayar, wani dan sanda ne ya fito daga motar da yake kusa ita, yace.
"CEO Mahir Hamoud Boualem! Shi ya fasa kuma ya kira mu, alama ki saboda yunkurin kisan kai."
Dafe bakinta tayi tare da kallon Noorh.
"Motar da kuka buge bayan shi, ta kamfani ne, kuma ya dauko me kamfanin ne, sai gashi kun buge shi bayan haka kuma kuka kuma buge mishi motar wanda yaja driven shi sai da ya fasa hancin shi, dan haka zamu wuce da ita Office din mu."

"Akan uban me waye MAHIR?" Inji Noorh, tana isowa gurin. Dai dai dan sanda yana tasa keyarta.

Nan dan sandan yayi mata bayani, ai kuwa tayi tsalle ta dire bata san da zancen ba sai ta ga CEO, ko kuma tayi musu hauka. Mutane dayawa dakatar da ita suka yi. Amma bata ji ba. Fitowar shi tare da Nazzir, tace.
"Ina yake Shi Mahir Hamoud Boualem din."
Nuna mata shi Dan sandan yayi lokacin yana gyaran botirin rigar shi, yana magana fuskar shi a sake.
"Kaiiii! MAHIR Hamoud Boualem CEO, kazo nan" ta faɗa da karfinta kamar wacce aka karawa karfin hali.

Bai kulata ba, yayi tafiyar shi. Amma dake yau din tana jin wani irin masifa ce da tsiwa, da sauri ta sha kanshi tare da rike k'ugun ta.

"Kai waye da zaka saka a kama mu? Eyye kasan darajar dan adam kuwa? Eyye ka wani dauko farin fuskarka, kasa an kama min yar uwata."

Kura mata ido yayi yadda take masifa kamar zata kwad'a mishi mari.
"Ke Noorh!"
D'aga hannu yayi tare da musu alama da yatsun biyu, dole Nazzir yayi shiru takaici na kuma kama shi,yarinyar ta lalata mishi kome,

Duk wannan shirmen da take bai sanya shi mata magana ba, sai ma ratsa gefenta da yayi tare da wucce ta, zuwa motar shi, aka bude mishi kallon inda dan sandan yake yayi sannan ya mishi alamu ya kyaleta. Ita kan bai kuma bin ta kanta ba. Ya shiga motar shi. Abu daya ya zauna a kan shi. Ƙwayar idanunta, da kuma yadda ta hana shi cire nikkab din ta.

Ciwon kai ne ya saukar mishi. Har ya isa Hamoud Boualem Estate.
Cike da karfin gwiwa yake gyara hannun rigarta, irin yau da bai sake an sake Baby Queen ba, da ta mishi shegen duka. Amma kuma taji haushi rashin tankawar shi, da shegen girman kai a gurin kaman dutsen abuja.
"Noorh! Dama shine CEO?"
"Oho ina na sani? Bafa shi bane, kuma idan da shine, wallahi korata zayi kawai sun fada ne, dan kar na kwatar miki hakkin ki."

Isowar Badar ya kalle su, tare da tambayar su, me ya faru da motar Noorh ta gaya mishi. Ita kuma Tasleem ta labarta mishi kanun labaran.

"Toh wallahi gobe kiyi zaman ki a gidan kawai domin zai kafta miki rashin kirki." Da wannan hirar suka isa gida, tun daga kamfanin bata kuma magana ba, har suka shigo anan taga motar Nazzir.
Badar yana ajiye su, ya fito daga motar shi, ya tawo gaban ta.
"Meye amfani yarinyar da kuka yi?" Kallon shi Tasleem tayi sama da kasa, taga babu ta inda ya kama Mr Mahir, tsaki taja tare da riko hannun Noorh, duk yadda yaso Noorh ta tsaya Tasleem taki karshe ta tsaya ta mishi tijara, tare da cewa.
"Toh anyi walkiya, kuma mun san kome, dan haka kar mu kuma ganin mutum a gidan nan"

Tsakani da Allah Tasleem ta juyawa Nazzir baya, shima dama baya yinta abu ne kuma ya samu, tunda suka shiga cikin gidan, ta kasa sukuni, irin wannan mijin take buri, sai yanzun ta tuna hirar su da Noorh yau da safe. Duk bayanin da Noorh tayi duk ita tafi dacewa da samun haka.

Cikin sauki zata nemi sauyin daga Mr Nazzir ta koma Office din CEO. Da wannan shirmen ta saka a ranta.

Koda dare yayi zama tayi tana ta bugun cikin Noorh, tana son jin halin da Noorh take ciki akan CEO.
"Noorh gayen nan ya hadu ko?"
"Wani gaye kenan?" Ta mai da mata tambayar ta,
"Mr Mahir!"
Tsuke fuska tayi, tare da cewa.
"Ina ruwa na, kin ajiye ni ne domin nayi ta kallon mazajen layi.
.ke nifa nafi karfin na kalli namiji da wata fuska ina ruwa da haduwar shi, mutum da fuska kamar fanke kike tambaya ya hadu toh bai hadu ba, kina da matsala, ina zaki kai shi bayan ga Nazzir?"
Ta ture laptop din cinyarta tana kallon Tasleem. Cikin nuna ko oho Tasleem tace.
"Hmm! Kawai gani yana yi yafi baby naz haɗuwa, kuma."

"Kinga dakata, ni ba yar kaza nace wacce tana samun abu zata ci ta manta da danginta, sannan idan kika juyawa Nazzir baya kin zama butula, wai ke maza nawa kike so?"
Sosa kanta ta fara, tare da Basar da zancen tace.
"Ke nifa ba don shi nake ba, kawai mamaki nayi naga yadda yafi Naze kyau ne. Amma ina ruwana."

Ta tashi daga gadon, ta koma nata, ta. Kwanta tare da kashe side lamp dinta, zuciyarta ta gama zagaye mata asali ba son Nazzir take ba, Mahir take so bata sani ba, gashi nan ta kaita ta baro, amma zata gyara kome kuma zata shige mishi yadda dole yayi da ita.

••
Washi gari.
Suna karyawa a nutse ta kalli iyayen ta, tace.
"Mommy hmm! Kunga CEO din mu kuwa?"
"Baby Queen! Muna jinki,"
Kallon Noorh tayi tana tsoron karta kwafsa mata, amma dake makaryaciya ce tace musu.
"Daddy! Hmm, haka ga ban dawo da motar mu ba, ai ta sami matsala ce, da ta CEO. Toh yace na bar shi zai saka a gyara min."
Ta kalli Noorh cikin fuskar tausayi kar ƙaryatatta. Cigaba tayi da cin chips ɗinta, dan ta lura da Tasleem da Iyayenta zamu ce ta tadda muje mu.

Mikewa Noorh tayi, dan bata mason jin karyan zata iya cewa karya ne, ta kuma lura yadda iyayen suka badda amanna akan labarin, zasu iya mata rashin mutunci dan haka ta hutar da ranta, ta dauki kayanta ta nufi hanyar waje.
"Gettare idan kin ga ma getta musu ina jiranki."
Sai da ta gama zagaye su da karya sannan ta bar gidan, suna ta mata addu'a, wai yanzun tunda suka fara aiki a kamfanin yarsu tafi Noorh farin jini.

Haka suka gama shirmen su, suma.
Dakyar suka sami abin hawa, suka nufi kamfanin, suna shiga suka sami ma'aikata kusan rabin kamfanin suna tsaye..ana kiran asalin wanda ya dauka da hannun shi, domin yana da record din su. Sauran kuma ɗaukar Nazzir ne, shi yabawa ya gama kiran su, sauran kuma yan Alfarmar ne, sai yan bautar ƙasa.

Bayan sun shiga ciki, Noorh da Tasleem hana su shiga, sai da Nazzir ya fito yayi mishi bayanin su din ai yan bautar ƙasa ne, yace Tasleem ta wuce, kanta na hayaki ta shige, zata tsaya mishi iyayi, ya mata wani irin kallo da yasa ta shige da sauri, Noorh kuwa. Takowa yayi har gabanta, ya kalli harabar Kamfanin, yace.
"Ku bata tsintsiya ta share mana harabar tayi kura."
"Wallahi ba zan share ba!"
Ta faɗa da karfi. Juyawa yayi cikin zafin rai ya daka mata tsawa.
"Sai kin share! Maza ku bani tsintsiya."mika mishi tsintsiyar akayi yazo har gabanta, ya mika mata.
"Malam ba zan share ba, da akan na share gwara na." Buge mata baki yayi sai da yayi jini. Yazo gabanta ya tsaya sosai yadda sai ta d'ago kai zata kalle shi.
"Sai kin share!"
"Shine zaka fasa min baki?"
"Ko zaki rama ne,"
"Allah ya isar."
Sake buge bakin yayi, yana jin takaicin ranshin kunyar da take mishi.
"Ban yafe ba!"
Finciko nikkab din ta yayi ta tafi kamar zata fadi, ya wular gefe.
"Sai kin share."
Kwalla ce ta zubo mata, ta mike tana kallon shi, shima ya koma kan wani kujeran da aka ware mishi, yana me jin haushinta, dan ta rike nikkab din yaƙi barin fuskarta.

Haka ta gyara zaman shi, sannan ya shiga sharan harabar, tanayi tana huci, tare da hararar shi, karfe sha daya ta gama, koda ta juya ta samu har ya bar gurin.
Taja mishi Allah ya isa yafi cikin kwando, dakyar take tafiya sabida bayanta, da ya rike mata. Hawaye na zuba mata. Koda ta isa Office din su, ta sami Tasleem da Badar, tana shiga Badar yace.
"Ranki shi dad'e, ki wuce Office din CEO."

Cikin takaici ta suri jakarta, tana nufar Office din taga sakatariyar karamar tana share kwalla, tace mata.
"Lafiya?"
"Sir Mahir ya kore ni!"
Bata rufe baki ba, Babban sakataren su ya fito shima ranshi a b'ace alamar an dakatar dashi ne. Koda ta shiga office din yana tsayar a gaban table din shi Nazzir yana bashi hakuri.
"Kayi hakuri Umaima bata da laifi, karka kore ta don Allah Lion, wallahi ba ita ta yad'a videon ku ba."

"Amma taya aka gani a Status ɗinta?" Ya fadi haka tare da kallon inda Noorh take a tsaye, yana jin kamar ya mata shegen duka, duk ita ta ja mishi wannan cin fuskar, a take yacewa Nazzir.
"Ka kawo min A4 tare da duk abinda aka tsara, kabawa wancan mara kunyar tayi copy din shi, idan kuma ta kuskura nan da karfe hudu bata gama ba, gobe zata fara daga farkon!"

Zaro idanu Nazzir yayi, tare da kallon Noorh! Ya kuma kalli Mahir wanda ya hade fuskar shi kamar wanda aka zaga, sai ka rantse ba shi ya fadi haka ba.
"Lion! Wannan da babu ruwanta, kuma da tayi laifi ka hukuntatta, ta share harabar Kamfanin, yanzun kuma tayi copy din abu a jikin A4 don Allah ka duba wani abu amma banda wannan."

"Dani da kai waye a sama?"
"Kai!" Ya faɗa a sanyayye,
"Dole tayi!"
"Ba zanyi ba!"
🤓🤣 Wasa farin girki
Hmmm. Inshallah na kusan ajiyewa na gudu....
https://my.w.tt/LFTaVMaeacb
MAH~NOOR
My First Wife♡
        Chapter 1️⃣3️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

🙄🤔 _Wai ya naga kuna harara ta ne Aunty Mami, Jikar kulu Ni meye nawa ne, Yar gatan mijinta, Mommy Sayeed! Zahrah Adda Ramla, Maman Abdul, Faization. jaderah, Halima, matan quarts grp, Ruwa biyu comments section, Maman Batul, Maman Nana, Sister Nusaiba. My Wattpad fans, kuna manne a button din heart dina, ina yin ku sosai, Wayyo 😲 My Telegram fans ga naku kuma 😜❤️ Allah yabar kauna! Idan baku takawa Noorh birki ba, zata rasa kafaffuna, domin Major ha shirya tsaf dan suburbudar duk me rena mishi hankali!_
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
#hateatfirstsight

Cire rigar saman yayi tare da nad'e hannun a kirji, tare da cire daya hannun ya kalli Nazzir, wannan y sake wani irin murmushi.

       Takowa yayi gabanta, sannan ya zuba hannun shi a cikin aljuhun wandon shi, tare da juyawa cikin isa da girman kai, yana kallon ta, tare da sake murmushin mugunta. Fakonta yake ya cire nikkab din, itama da ke ta ankara da nufin shi, kaf kaf take da nikkab ɗinta, tana kuma kallon motsin shi.

              Cikin wani irin zafin nama, ya kai wa nikkab din cakfa tare da riko hijab din ta, ya sab'a riko nikkab din, ture shi tayi zata fita, ya fisgota tare da wurgata tsakiyar Office din, ya zuba mata ido, tare da balle botirin hannun shi, ya kalli Nazzir tare da daka mishi tsawa.
"Dauko min A4 din!"
Ya kuma takowa gabanta, tare da  zuba mata ido, dukawa yayi tare da jan dogon hancin shi.
"Zaki kwafe!"
Cikin tsiwa da rashin tsoro tace mishi.
"Idan naki fa? Zaka saka a b'atar dani kamar  yadda kuke sawa ana yiwa mutane."

   Cikin fusata, ya kai hannun shi wuyar shi tare da jan iskar bakin ciki, tare da bude idanun shi, ya sauke akanta.
Hannun shi ya kai keyartar da, daidai shigowar Nazzir, ya ajiye A4, ya janyo ta ya wurgata gaban takardun sannnan ya koma table din shi ya dauko takardun ya zuba a fuskarta, sannan ya juya bayan shi tare da yin wani motsa hannun shi, yace.
"Zaka iya bamu guri!"
Ya faɗa haka, fita Nazzir yayi tare da cewa.
"Please Lion!"
"Ka karo wani A4 din!"
Haka ya kuma karawa fahimtar da yayi matukar ya roke shi, kamar yaja mata rashin mutunci ne ya sashi fita, tana zaune a gurin bata d'ago domin tayi magana ba,asalima ma itama wani karsashin rashin mutunci take ji, dan ta rantse a ranta ko gawarta za'a fitar ba zatayi rubutu ba. Ai ita ba baiwar shi bace.

              Juyawa yayi ya cigaba da aikin shi bai kuma d'ago kai ya dube ta ba, asalima Mantawa yayi da ita a cikin office din, wani silent Office din ya bada, baka jin kome sai karar Ac. Babu wani alamar motsin rai a cikin gurin.

        ---
"Me yasa Aeesha Omar take da taurin kai, gashi can mahaukacin can ya sakata aikin da ba zata iya ba.". Tsaki yaja,

   Haka yayi ta yawo a Office din shi, shi kuwa ya damu da ita ne, kamar zai zubda kwalla, domin yasan halin mutumin tunda bai kore ta ba, tabbas haka zai sanya ta.
        ... Awa daya ta wuce, biyu yazo ya kuma wuccewa, d'ago kai yayi daidai lokacin da agogon Office din ya buga, ganin yadda ta manta da abinda ya saka ta, tana zaune ta daura  daya akan daya, irin ga gidan Ubanta. Ranshi ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login