Showing 18001 words to 21000 words out of 40610 words
Nifa babu wanda ya isa nace ya burge ni, domin kishin tsiya ne dani,shi yasa bana son soyayya da namiji me kule kulen yan mata, ni mijin da zan aura. Ba zan tab'a cewa ina son shi ba,sabida kar yayi amfani da wannan tunanin ya cutar dani.
Ina mamakin Yadda ku mata baku da wani jan aji, kawai namiji na zuwa, sai a fada mishi kamar wani yaƙi, toh taya ba zasu yaudare ku ba, ko zuwa yayi da gaske yana sonki, dole ki kame kanki balle kuma yazo da fuskar shirme, baku san wani abu daya ba, ranar da na fara zuwa dariya kuka min saboda hijab.
Har ana gaya muku cewa, munafukai ne ke saka hijab, toh baku san wani abu ba, hijab kariya ce ga ya mace, dan haka ne ba munafuka bace, kuma hijab dina kariya ce a gare ni, dan haka ku Cigaba da watsi da kimar ku, ana cin mutuncin ku a banza."
Mikewa nayi na bar gurin, yau har muka dawo, gidan ina ganin yadda Tasleem take ta rawan kai, Ashe mutumin zai zo cin abinci ne, ni kuma munyi Badar zai zo mu tattauna akan abinda na samu.
Muna cikin hira, a motar shi ina nuna mishi abinda yake faruwa, tare da cewa.
"Ina zargin bai san meke faruwa ba, domin kuwa har yanzun yana makale min. Kuma da yasan nice nake bibiyar abinda yake maybe da ya saka an kore ni!"
"Nima shi yasa na sake rai na, amma ya kamata ki nutsu dan Mr Mahir yana zuwa, abinda zaki yi yana dayawa, amma dole ki shiga jikin shi shima."
"Ni fa bazan iya mu'amala da wani namijin ba, kai ma sabida na yarda da kai ne, nake taimakonka. Amma bana jin zan iya wannan aikin, kowa so yake yayi amfani da ni, me yasa sai ni?"
Shiru yayi yana kallon bayan motar shi sakamakon hancin motar Mr Nazzir.
"Dama wannan gayen zai zo gidan nan ne yau?"
"Eh nima dawowa na daga aiki naga Mother In-law din shi tana ta shirya table bari naje na musu Iskanci." Ta faɗa a hankali.
Kafin ya mata magana har ta fita. Lokacin da Nazzir ya fito cikin motar itama ta iso inda yake, bata kalle shi ba, ta wuce abinta, tana zuwa cikin gidan,ba tare da tacewa kowa kome ba, ta nufi table din, ta dauki wani katon filet ta dibe abin da ranta keso, tana lashe yatsunta, sannan ta wuce ta daidai saukowar Tasleem.
Ganin yadda tsabar mugunta, ta bata ko ina, sannan tayi ficewarta, ta nufi motar Badar, shi kan Nazzir dariya ta bashi.
Tana tafiya tana murmushin mugunta, tana isa motar ta bude tare da mikawa Badar, tace.
"Kayan abincin da suka shirya wancan banza na dauko maka, maza ci rabonka ne."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ai ba zan iya cinye ba,"
"Toh ni kan nayi nan, zanje niman rigima."
Tunda na barshi ya girgiza kai, na shiga cikin gidan, na shiga zabga musu iskanci, na hana kowa sakat. Dan kaina na bar falon bawai dan sun roke ni ba. Ganin yadda Tasleem take zubda kwalla. Sai jikina yayi sanyi na kyale su.
Dan na fahimci amadadin. Yaji haushina sai ma jin dadin da yaƙe.
---
A hankali naga jikin Tasleem ya soma sanyi. Karshe dai ta sauko. Nima kuma muka dai daita, har iyayen ta suna jin dadin haka, ban tab'a jin na mata wani abu ba. Shirin da muke ya kuma samun kyakkyawan sakamako, dan har a kamfanin kowa yasan mun shirya. Dan haka Sir Nazzir ya dai na kokarin shiga tsakanin mu.
•••
Yana zaune a gefe, Haroon yana ta haɗa Mishi kayan shi, idanun shi na kan wayar shi. Tare da nunawa Haroon kayan da zai zuba mishi, kama daga suit zuwa jamfa har zuwa kaftanis din shi yana gamawa ya kira Number Ummi ya gaya mata, yau zai bar garin zai nufi Yola.
Fada tayi mishi tare da gaya mishi amma ai zasu tafi asibiti shine zai gudu.
"Ummi mafarki ne ba ciwo bane, Insha Allah zan dawo muje ba zan wuce sati Uku ba,"
Ya faɗa tare da dafe goshin sa, bayan fitar Haroon da kayan ya tashi sanye da farin jeans sai rigar black, ya daura wani top a saman shi, idanun shi manne da sunglass, ya fito a hankali yana murmushi, mota ya shiga yana kallon kayan aikin shi, kama daga wayar shi, Tap din shi zuwa laptop din shi, lumshe idanunshi yayi, yana kuma tuno mafarkin shi na jiya.
Fuskarta sanye da rufe, ta mika mishi hannu. Zai riko kenan, wani abu ya tawo da karfi kamar jirgin kasa ya shiga tsakanin su, sai muryan ta da yake ji tana dariya. Anan ya bude idanun shi...
🙏🏼
Zaku na samun Posting a ranaku biyu ne, Monday da Alhamis. Bayan nan zaku min Uzuri, gaskiya. Idan kuma bayi yi ba toh sai sabon shekara Insha Allah, sai na cigaba da baku kullum...
https://my.w.tt/oCPVBn764bb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 1️⃣1️⃣
MrsUsmaa400
For You Jikar kulu
BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM
#Interview
Idanun shi lumshe yayi cikin nutsuwa, yana jin wani irin yanayi yana shigar shi, ba zai ce na Meye ba. Ganin bai da hujjar sawa kanshi damuwa yasa shi bude shanyayyun idanun shi masu kama da wanda ya kwankwadi kayan maye.
A nutse ya dauki tap din shi ya shiga nazarin abinda zai kai shi Yola, tare da jin a ranshi koda ya isa yana bukatar yaji wani irin yanayi kamfanin su yake ciki. Kuma ya kome yake tafiya mishi.
•••
"Wai Noor me ya sa kike haka ne? Don Allah ki tashi muje kinji. Yau baki daya baki da kuzari!"
"Baby Queen! Jiki na ne babu dad'i, kawai kije ni ba zan sami zuwa ba kuma ki gayawa Badar."
Kura mata ido tayi sannan itama ta koma bakin gadon ta zauna tare da cire yar karamar fashion hijab ɗinta, ta zauna tana kallon Noorh din.
"Ok nima na fasa zuwa."
"Don Allah tashi kin san yau mr Mahir zai zo kuma koda ban je ba, babu matsala. Ke kuma Mr Nazzir zai damu akanki."
Cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Noorh, sannan tace mata.
"Noorh! Kin hakura mr Nazzir din ne?" Ta tambaye ta cikin tsoro.
Tashi zaune Noorh tayi tana kallon ta, sannan tace mata.
"Yanzun banda b'atar basira dama me zanyi da shi? Ai sai ke. Ni bana son irin shi.
Mijina Ready made ne, mijin da zan aura ya kere sa'a'o'in shi, first Class Handsome guy ne, irin me zafin nan, dai dai irina wanda bai damu da kyale kyale mutane ba."
"Toh idan kin gan shi kece zaki fara Crushing din shi ko shi zai yi crush dinkin.?"
Tashi zaune Noorh tayi tare da rungume kafaffuna, tana murmushi cikin wani irin ƙasaitacciyar murmushin da yaki barin fuskarta, lumshe idanun ta tayi tare da bude shi akan Tasleem. Sannan tace.
"Tasleem! A yayinda zamu hadu, zai zama na rana ce ta musamman. Ranar sai ya kasance mafi daraja a gare mu, domin zai zo mana a matsayin our first meeting, zai zama ranar da yafi Kowani rana Fantastic."
Ta faɗa cikin dariya.
Jikin Tasleem ne yayi sanyi sannan tace mata.
"Ke baki da ra'ayin soyayyar shan minti ne, kafin aure."
Sauka tayi daga gadon, sannan tace mata.
"Ai idan Kinga namiji ya tab'a ni, toh ki yarda akan kaddarar ce ya gifta tsakanin mu, bayan haka bana fatan wani ya tab'a jikina. Ke bana fatan wani ya tab'a hijab dina.
Ke nifa saurayi ganin asara nake nace mishi ina son shi, duk maneman da nake, bana cewa ina son su, haukar su suke kawai.
Sabida banyi imani da soyayyar duniya a, dan haka manta kawai taso muje."
Mikewa tayi cikin sauri, suka shirya. Koda suka iso falo babu kowa haka suka tab'a abinci sannan suka kuma fita daga gidan.
A hankali Tasleem take jan motar. Har suka shiga kwantar da zata kai su kamfanin kawai, suka daki motar kamfanin, cikin masifa Tasleem ta fito tana bawa driven motar hakuri, basu bude motar Ba, kuma bai sanya sun tafi ba. Abinda ya bani haushi, ina zuwa na make glass din motar, sauke glass din motar aka yi. Na zubawa driven motar ido.
"Toh ishashe zaka bamu hanya mu shige ko dai na kara dukar motar ku, ka zauna da uban gashin baki kana hura hanci kai gaka nan ishashe.
Tabbatacce. Toh bamu hanya ko kuma na fasa tayar motar. Wallahi ka godewa Allah ban iya mota ba, da ka shiga uku sai na budeka da kura. Dube shi kawai katon mutum da kai."
Can bayan motar ta jiyo wani murya yana cewa.
"Wali ya katsaya?"
"Ok sir naji kace na tsaya ne."
Siririn tsaki ta ja, sannan ta bar gurin su, ta nufi motar su tana cewa.
"Ke kiyi overtaking din yan banza, dan na lura akwai wani kazan gidan gona ne a cikin motar."
Dariya Tasleem tayi tare da jan motar a fisge, tana zuwa kuwa tayi wani irin shan kansu, garin kauce wa, sai da drivan ya buge kanshi motar kamar zata kifa dasu. Shima Mahir da yake bayan motar sai da ya kusan fasa hancin shi.
Da sauri ya dakatar da Wali.
"Sauka mu shiga asibitin kamfani."
"A'a sir zan iya tuka motar hancina ne kawai yake jini, amma zan iya fa." Duk da wali babban mutum ne bai hana Mahir rufe shi da fada ba, akan lallai ya sauka shi ya ja shi. Aikuwa haka ce ta faru, ya sauka Mahir ya ja motar, suka nufi cikin kamfanin ya wuce da Wali Clinic aka duba shi. Sanan shi kuma ya wuce cikin kamfanin a wani irin shiga na niman aiki taga jan magajan.
Domin anyi sanarwan za a debi sabin ma'aikata, da yazo parking spaces ya hango motar da tayi musu tsaya, takawa yayi ya saka wani karfe da ya gani a gurin ya daki tayar motar, sai da ta fashe. Sannan ya shige ran shi na kunna.
Yana son yaga yadda ake diban ma'aikata ne a kamfanin shi. Koda ya shiga, aka nuna mishi idan zai zauna, gashi ya b'adda kama sosai, har wani kasumba ya tara, dayawa basu san tsarin ba, dan haka sun dauka kawai za ayi masu tambayoyi ne, yana zaune wasu yan mata gudu biyu daya tacewa daya.
"Me yasa kika zo niman aikin?"
Dariya dayar tayi, sannan tace mata.
"Saboda bani da yadda zanyi, dole na amshi aikin kafin na samu wanda yafi wannan karki! Aikin gwamnati yana wuya a kasar nan, kuma ina da mahaifiya mara lafiya, ga kanena suna sun zasu lalace saboda rashin kulawa, Kinga nan kuma naji aikin su na da kyau, amma koda kabar aiki babu pension da garatuti, zanyi hakuri na rike wannan, idan yaso ko koyarwa sai na nima a makarantar gwamnati."
"Ayya! Kinga kuwa kusan nima haka ce, amma Ni mijina nane babu lafiya, sanan kuma matsalolin rayuwa, ya sani zuwa niman aikin..koda basu biyan pension zan rike shi haka, baka san inda rana zata fadi ba!"
Haka suka yi tattauna, tare da bawa juna shawara, can gefe wasu samaruka ne, suke tattauwar su, dayan yace.
"Kasan Allah da zaran na fara aiki zan fantsama gari fa"
"Ni kuwa idan na fara aikina, kafin naci kudin su, sai na bawa kamfanin gudunmawa ta sosai, domin zan tsaya ka in da na in, nayi musu aiki tukuru,
Nasan cewa gumina naci ba haram ba, nayi alfahari da abinda na tara, wannan shine abinda ya kawo ni, nayi aiki da kamfanin da zata yi alfahari dani."
A gefen Mahir wata mata ce, ganin yadda yake a dame, tare da rubuce rubuce, yasanta kallon shi.
"Malam! Ka nutsu sai b'ata takardan kake, kuma shi wannan yanayin na lallai bane ni na samu aiki amma kai sai ka samu, ka na al'amarin Ubangiji ba ayi mishi dole, ka nutsu Insha Allah zaka dace, ka bar damun kanka. Yanzun zasu fara diban mu."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Yanzun idan baki samu aikin ya zaki yi?"
Dariya tayi sannan tace mishi.
"Ya kuwa zanyi ban da Nagodewa Allah nasan yana sane dani."
"Tab wallahi bazan iya daukar wannan renin hankali ba, muzo tun safe ace ba a ɗauke mu ba, ai akwai renin hankali."
Inda wasu matasa. Yana kallon su. Shidai yana ta wasa da biron hannun shi, can yace musu.
"Time Up"
Fitowa Wasu mutane suka yi daga Office din CEO, tare rigar saman kayan suiter din shi, me zubin Overoll, ya ya mika musu takardun hannun shi, tare da cire katon madubin idanun shi.
Sannan ya cire gashin afro da ya saka, a hankali ya koma ya zauna ya cire takalmin kafarshi. Sannan ya amshi kayan hannun su ya saka a hankali yana gyara wuyar shi da zaman tie. Din shi,
A hankali Mr Nazzir da ya iso gurin, ya tawo da sauri ya rungume Mahir yana faɗin.
"Barka da zuwa Lion Man"
Tafawa suka yi tare da juyawa suka bar gurin, Babban sakataren Mr Nazzir yace musu.
"An gama interview. Kuma ya dauki wanda suka dace, sauran kuma yana baku hakuri."
A hankali aka fara kiran sunan su, mata na farkon nan an dauke su, haka matar da ta bashi shawara an dauke ta, daya matashin da yace zai yi aiki domin gina kamfanin ta samu cigaba an dauke shi, ya dauki mutanen da suka dace, sauran muka ya basu hakuri tare da cewa a basu wani abu da zai sanya ba zasu yi danasanin zuwan su ba.
A bakin wani kasaitaccen office, suka tsaya sannan Badar da Noorh suka iso, mika almakashi tayi bata damu da ta kalli me ake yi ba, hankalinta na kan wayar hannunta, ya yanka
Zaren Sauran staff Officer suna tare a gurin, bude mishi office din akayi yace.
"Wowwww! Tiger. Haka ka gyara min Office din"
"Abinda yafi haka ma, zanyi Lion Man!" Dariya aka saka shi kuma ta sake murmushi, daga nesa take son ganin waye ya mallaki wannan muryan wanda daga jin shi sai da ya karya mata zuciya. Kokarin duba shi take, amma bata ga fuskar shi ba.
Karshe haka ta hakura, amma tana iya hango kwantaccen gashin kanshi har keyar shi, ya juya baya ana tattauwar dashi.
..karshe rufe kofar akayi inda suka shiga tattaunawa a officen sun shi, su kuma suka dawo. Zama suka yi ita da Badar.
"Noorh! Lokacin yayi fa, sannan akwai wani abu da na gani yanzun lokacin da Mr Nazzir yake gabatar da wasu files ga Mr Mahir, kuma ban sani ba. Ko na meye ne domin domin jiya bayan fitar ki naga mr Jecob yazo gidan Mr Mahir.
Abinda na sani duk inda mr Jecob yake babu alkhairi a gurin, mutum ne da yasan kan shedancin."
"Toh ni meye nawa a cikin wannan al'amarin saura wata uku na gama abinda ya kawo ne don Allah karka sanya ni cikin damuwa."
A hankali ya maida kujeran shi yana fuskarta ta.
"Ban nemi ki tayani dan na salwantar da rayuwar ki ba, nayi haka ne domin kane na guda biyu, da suka rasa rayuwar su sabida gurbattacen lemon da aka fitar daga cikin kamfanin.
Kiyi nazari sosai, ba iya giya ake sarrafawa ba, sabida tsadar kayan sansu, a wannan shashin akwai inda ake sarrafa, gurbattacen lemon kwalba, a kara musu wasu sinadirai. Nasan kina da kima, kuma kina da kwarjinin da zai sanya kafin ayi zargin ki zai dauki lokaci, please ki bani hadin kai. Dole muyi aikin nan tare don Allah."
Shiru tayi tana kallon shi sannan tace mishi.
"Zanyi amma zan boye kaina, sabida ina tsoron matsala."
"Insha ALLAH babu matsala." Da haka suka yi ta tattaunawa har suka gama, sannan Tasleem ta shigo kanta na rawa. Ta nemi guri ta zauna, sannan ta fara yatsina fuska, tana cewa.
"Kinsan me?" Tayi magana cikin wani shegen yauki. Girgiza mata kai Noorh tayi sannan ta cigaba da cewa.
"Kinsan Dad ɗin Baby Naz shine me kamfanin nan, toh wai bro din Baby naz yazo, shine Baby yake gaya min, wai yazo cin Arziki ne"
Cikin sake gwiwa Badar yace mata.
"Toh Queen Tasleem! Hamoud Boualem Company na Mr Mahir ne, da kanen shi kar wani Shashanci ya kuma kwasar ki, ki gayawa wani wannan shirmen, ba Nazzir ba uban Nazzir cin arzikin Mahir yaƙe, na lura baki san inda kike ba, kina cikin kamfanin da d'aga murya idan kayi kora ne, balle kuma wani abu ya hada da CEO ki je ki tambaya shi idan zai dauki ma'aikata, Interview na musamman yake kuma a shekara, sau daya yake ɗaukar mutane kamar yadda yayi yau kuma kowani shekara da yadda yake ɗaukar su."
🤣 Baby Queen baki ya mutu 🙄
Jikar Hauw karki kuma damu na gobe babu typing 😠😡 domin basu Vote wallahi na gaji
https://t.me/joinchat/IQpnHR2pz0-DVPLh9lzhWQ
Shafin Telegram dina zaku iya samun shi Daga farko...
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 1️⃣2️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Ga
#Mr Arrogant
Wani irin kunya ce ya kama ta,ta kalle ni kamar zata yi kuka, tace min.
"Noorh! Kinji abinda yake gaya min"
Kallon shi nayi tare da cewa.
"Gaskiya wannan abin bai dace ba, kuma kar a kuma."
"Hmm!" Ya ce mana, tare da juya keya,
Nan muka shiga hidmar gaban mu.
••
"Lion Man! Dama akan gurbattacen lemon nan ne, ko zaka saka hannu."
Hannun shi rike da wata mug, ya juya musu baya, daya hannun shi kuma a cikin aljuhun wandon shi, yana kurb'an coffee a hankali kamar baya son sha.
Ajiyewa yayi a kan wani table,inda Coffee machine yake.
"Ba zan saka ba!"
"Amma kuma Lion!"
"Bana Crossing limit! Kuma kasan waye ni? Kuma kasan abinda nake yi da wanda bana yi, ba zan saka muku hannu ba, sai naji me zaku yi da gurbattacen lemon."
Cikin inda-inda Nazzir yace..
"Babu kome fa, domin zubda shi ake."
"Better! Kasan ina da Opinions akan abinda yaƙe gabana."
Shiru yayi tare da ɗaukar mug din shi ya cigaba da