Showing 30001 words to 33000 words out of 40610 words

Chapter 11 - MAH~ NOOR (MY FIRST WIFE) BY MRS USMAN-1.txt

06 Mar 2025

3513

Mahir ba mazinaci bane domin na zauna dashi a Militry College 2003, sannan mun kuma haduwa a team na a Kashmir 2007. Kuma dukkan mu course yake hadamu.

          Kawai nasarar shi nake son ta zama namu ni da Abokina, sauran da suke ƙoƙarin ganin bayan shi, sai su kara himma, Ni dai kamfanin shi nake son ya rufe."
           Murmushi Manager yayi sannan yace masa.
"Ba kai kadai kake son ganin shi ya fadi ba, amma ka sani duk abinda zaku yi, ku tabbatar kun gama shi cikin kwanakin nan. Idan ya wuce haka wani abu ya biyo baya toh wallahi zaku iya fadawa matsala."

        Sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi sallama.
---
Duba takardun tayi lokacin da take cikin napep, kamar daga sama taji an daki napep din su, haka tayi ta tangal tangal, kafin Allah ya taimaka suka tsaya, Motar Mahir ta gani amma bashi bane.
      Fitowa tayi tare da kallon mutanen da suka tsaya suka jajjanta musu.
"Wannan al'amarin ba su kyauta ba, Allah ya tsare ku."
    "Wato dan yaga bai samu damar min kome ba, shine ya turo a kashe ni?"
"Kin san shi ne?"
"Mahir Hamoud Boualem CEO!"

Shiru gurin ya dauka kafin kowa ya shiga darewa, sakamakon jin wanda ta kira, tare da sanin me zai aikata, tunda ya rigada ta bata mishi suna. Dan haka suka watse dakyar me napep din ya kaita gida, tana isa babu wanda ya ce mata me kika aikata me muka ji, asalima kamar ma tsoronta suke ji, cikin dare kuwa bayan ta idar da sallah dare, kawai ya shiga sake wasu bayanai tare da cewa yau ma Mahir ya kaiwa Noorh hari zai kashe ta, bayan abinda ya faru. Abubuwa da yawa ya kuma sakewa har da Voice din shi na karshe.

      --- washi gari abubuwan suka watsu a duniya, Nazzir shi kan shi sai da ya girgiza balle kuma Aysar Haladu, wanda suke tsammanin daga bakin Noorh na zahiri dan babu wnda ya san itace take wallafa shafin, sannan Badar ya bata kariya ta hanyar hacking din Acct ɗin, ba tare da sanin ta ba.

                Mahir kan zan iya cewa jinin shi ya haura sosai, domin kuwa baya iya magana sai kallo da ido.
    Da ta isa gurin aiki kuwa kowa sai da ya rufe tare da mamakin dama itace Noorh, Manager kasa zama yayi ya kasa tsaye, sabida bai taɓa dauka ta haɗu har haka ba, gashi dai riga da zani ne sai After dress da ta daura akai, tayi kyau sosai, domin tayi rolling kanta da dan karamin gyale, babu wanda bai yi farin cikin sake bayanin da Light yayi ba, musamman yunkurin kasheta da aka yi jiya da yamma. Haka da ya faru ya matukar girgiza duniya.

       Ranar ta tsara abubuwan da zata tuhumi shi tayi, dan ya gayyaci tashar ne. Su kuma suka tura mishi Noorh.

         A cikin kwanakin da aka shirya tattaunawa da yan jaridu, ta sami damar shiga Hamoud Boualem Estate, tana cikin napep tazo wuccewa shi kuma ya fito zai tafi gidan kakar shi, kallon juna suka yi ta sake mishi murmushi, dauke kan shi yayi tare da gyara zaman shi Wali na jan shi, wani irin bugu zuciyar shi yayi haka kawai ya rasa sukuni, dan har sunyi nisa, gani yake kamar yasan kwayar idanun da ta wuce, kamar ya santa. Amma ba zai ce ga ita ba. Ita kuwa ana sauke ta a kofar gidan Badar ta zaga ta bayan gidan ya shiga ta window, tayi ta yawo, bata sami abinda yazo nima ba, har ta gaji ta bar gidan dan tana tsora ce kar ya kuma sakawa a biyota, tana fita ta bayya, shi kuma yana shigowa ta gaban gidan.

        Ya shiga kallon ko ina, tare da bin yadda gidan ya kone, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kai kan shi zai fita yaga wani dan karamin frame bai kone ba, kawai ya ciro tare da fita dashi a gidan. Yana kallon gaban abin.

         Tsaki yayi tabbas, ya me irin idanunta sai dai ba ita bace, da yau itace ya kamata, abinda tace zai mata sai yayi ya barta a wulakance, wannan shine alkawarin da yayiwa kan shi, duk ranar da ta shiga hannun shi.

      •• cikin kwana biyu, ta gama shiryawa tsaf,ranar Talata ya kira taron manema labarai, lokacin da suka isa gurin, ana cikin tattaunawa, har Mataimakin Kwamishina yan sanda, ya tabbatar da cewa Mutuwar Badar kashe kan shi yayi sakamakon yana fama da ciwon hauka. Maganganun mara sa dad'i aka yi akan shi, wanda ya sanya aka dauko hoton kanen shi aka gwada domin ya zama shaida ga zargin da aka ga kamfanin.
"Mutuwar Badar ba Suicide bane Murder ne." Juyawa kamarorin Suka yi lokacin da Noorh ta mike tare da cewa.
"Idan mun fahimci Sakon da shafin Light take gabatarwa yana fada mana cewa, CEO yana sane da mutuwar yan jaridu guda takwas yan bautar ƙasa shida, sannan shaidar da ya fitar na muryan Badar yana cewa, Noorh ta fahimci abinda yake faruwa Mr Mahir... Anan aka ji karar harbi shine kashe kai?"
Shiru kowa yayi cikin tashin tsoro take kallon shi, yana kallon ta.
"Wacece ke?"
Inji Mataimakin Kwamishina,
"A'isha Omar Jimeta! Noorh!"
Wani masifaffe b'acin rai ne ya kuma cika mishi zuciya, tare da kura mata ido, wannan itace abar da take mishi Iskanci.

    Tunda aka tambaye ta, sunanta, Noorh ta shiga jefa mishi tambaya cikin, renin hankali tare da disga shi a gaban jama'a, wani irin yanayi yake ji na duhun bakin ciki, ya mike cikin zafin rai tace.
"Kunga abinda nake gaya muku ko, baya da alkibla sannan baya kaunar gaskiya! Mr Mahir, nifa akan aikina nake, dan haka zaka iya shafawa kanka ruwan sanyi, kasha ruwan sanyi."
Takowa tayi har gaban shi tana kallon shi cikin wani irin murmushin nasara, tace mishi.
"Nace maka zan dauki fansa? Kace idan na dauki fansa zaka baki kyauta na musamman, mr Mahir Hamoud Boualem, na gama ina jiran kyautar da zaka bani."

      Wani irin bugu zuciyar shi take, dan kamar zuciyarshi zata fado daga cikin shi, yana kallon ta murmushi yayi mata sannan yace mata.
"Zan baki kyauta! Zan kuma kara miki kyau, amma ina jiran ki gama wasanki da kike yine, domin Ni sunana Zaki ne, Ni zan farauto kuma na ci na barwa sauran, Ni sarki ne idan zan shimfid'a mulki dole ina bukatar irinki, tun anan zan gwadawa duniya ina shirye na fara aiki aikan iyayen gidanki."
Wani irin fisga yayi mata, tare da jiyar da ita, ta fada kirjin shi ta baya, ya Kuma kai hannun shi duka biyu ya rungume ta ya daura kanshi a kafad'arta yana kallon mutane. Wani murmushi yayi cikin kwarin gwiwa, sabida yadda yaga kowa ya razana, gashi sai kokarin kwace kanta take tana masifa tare da cewa yan uwanta yan jaridu.
"Kingani  ko? Kunga abinda ya tab'a min a gaban ku ma yayi min!"
"Mahnoor! Shine ya dace da sunanku!" Inji wani daga cikin tsirarun mutanen da suke gurin, bayan yan jarida, tureta yayi sannan yace.
"Ku fita ku fice min daga cikin kamfanina, kafin b'acin raina ya kwace ba baku mamaki, kuma tambayoyin da kika yi min, zaki kuma maimaitawa a kotu,.sannan wannan haukar da kike zaki gane baki da hankali, ba dai Aysar Haladu ba? Mutumin da yaci amanar kasar shi wani shege ne ba zai ci amanar shi ba, b'ace ki bar min nan kafin raina ya kuma b'aci na karasa kunyar dake a gaban mutane."

     Cikin zunzurutun rashin kunya ta shiga gaya mishi magana tare da tabbatar mishi, sai ta gallabi rayuwar shi, rikicin da takai ana rike su zasu daku, abun ya bawa kowa mamaki, yadda Noorh take kokarin sai ta zabga mishi rashin mutunci. Shima kuma ya rantse matukar ta iso gare shi sai ya nuna mata tsagwaron rashin mutunci, ganin abin ya kazamta yasa aka janye su aka tafi da ita.

     Wannan rikicin ya zama wani irin rikici, dan ta kai ta kawo ana fara hada sunan su, ana fashin baki kai, dayawan mutane suna alakanta abin da sunan hadin Ubangiji ne yake shirin faruwa kan su. Gidan jaridar ta kuwa sun kara mata kudi da uban matsayi, yayinda suka fara niman bude mata ido da kashe ta kudi na bala'in, abinda ya kwace ta a wannan lokacin shine mace ce mai ibada, bata wasa da sallah. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya tabbatar matukar karike sallah zai yi wuya ka tsinci kanka da aikata masha'a da wasu abubuwan da aka haramta su a musulinci.

   Daga Tasleem har iyayenta babu wanda yayiwa Noorh magana sai ma jin dadin da suke ta kwaso ruwan dafa kanta..

   A cikin sati guda, Mahir ya tasota a gaba, idan zata aiki sai ya tare hanyar, idan ta fito zata yi ta fita da kafa, yana cikin tafiya zai saka a tsare hanya babu gaira Babu dalili, haka zata rasa yadda zata yi ko ta kira Office, aka zo hanawa yake, idan kuma ta tsare abin hawa, Yasaka akwace ita kuma ya saka a hanata tsayuwa a bakin shagon kowa sai a tsakiyar titi, domin kashe hanya daya yake.
Gefe guda jama'ar gari sun kuma kamala musu sunan su a tare har kowa so yake yaga irin yadda suke Bala'i, a hankali sunan ya fara yawo cikin bakunar mutane, Mahir yana kuma shirya mata yadda  za a koreta a gurin aikin da take yi..  domin sanadin abinda ya faru an rufe Kamfanin shin, haka ya kuma harzuka shi. Yayi alwashin sai ya lalata mata kome na rayuwa..
Revengeful...
Babu Posting Asabar da Lahadi.. karku ce kuna jirana, please comments And Vote. Wallahi naji dadin Comments dinku na juya sai dai Vote ne sai a hankali. Baku son nayi labarin yayi kyau ne.
https://my.w.tt/gzD1s747pcb
MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 1️⃣7️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
#hypocrisy

  Bai fasa  alkawarin shi da da ya dauka ba , dan ta na 'n kawai zai rama abinda tayi Mishi.

       Yana zaune a Office din shi, yana sauraron  hirar da ake da ita, wanda yake cike da zallar yarantaka, uwa uba rashin hankalin da take sakewa ana wasa da rayuwarta, kalle shegen bakin rashin kunyar yayi yaga yadda take magana tana juya shi, dauke kai yayi zai kashe tv yaji ta bada amsar da ya sashi mik'ewa. Domin kuwa an tambaye ta.
"Shin haka zaki Cigaba da kallon Mr Mahir yana hana ki aikin ki zuwa aikinki?"

   Cikin shashantarwa tace.
"Ba zai hana Ni aiki na ba, amma kuma na san shima na zame Mishi kalubale ta kowacce fuska, domin dani Nasan dani yake kwana dani yake tashi zai tab'a dogon lokaci yana nazarin meye ya kawo haƙa! Amma kuma ba zai tab'a sanin amsar ba.

      Sabida yadda yake cutar da Alummommi masu yawan gaske, ya sani,. Sabida shi mutane da yawa sun mutu, tare da rasa matasa babu iyaka, dan haka na shirya domin na kai shi kasa, Insha Allah next shirina akan shi ba zai mishi kyau ba"

    Kura mata ido yayi cikin nutsuwa sannan yace.
"Duk abinda zan mata bai kai wanda tayi min ba, amma bari naga ta ina zata bullo min."

     Tabbas rayuwar ta shiga rayuwar shi, yadda baya tsammanin. Ta shige mishi hanci fiyye da tunanin shi, a duniya Noorh ce kawai ta iya tsayawa ta gaya mishi cutarta, kuma bai dauki mata ki ba. Mikewa yayi zai fita suka haɗu da Tasleem wacce take tsaye tana leken shi.

              Dauke kai yayi kamar bai ganta ba, har ya isa bakin kofar ya tsaya cak juyawa yayi tare da kallon ta. Takowa yayi gabanta, sanan yace mata.
"Ke yar uwarta ce ko?"
Jikinta na rawa tace.
"Eh sir!"
"Hmm! Zan baki cantract, me kike so?" Unexpected ta d'ago kanta da mugun sauri, tace mishi.
"Babu sir, iya haka ma Alfarma kayi min." Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ok! Ki san yadda zata ki da ita, kawai ki b'ata mata suna"
"Sir!" Ta faɗa a razane,
"Ba zaki iya bane?"
Ya tambaye ta cikin tsawa.
"But!"
Dakatar da ita yayi tare da cewa.
"Bar shi kawai!"
"Sir zanyi wallahi!"
"Karki soma, ki bar shi zan dauki mataki da hannuna."
Tafiya yayi cikin nutsuwa, abin shi zai dauki matakin da kan shi, dan haka yayi gaggawar dakatar da Tasleem, sannan yayi tafiyar shi.
       --- karfe biyar na yamma, ta fito zata koma gida, Aysar Haladu ta gani, yayi fakin din motar shi a gabanta, sauke glass din motar yayi tare da sunkuyar da kanshi yace mata.
"Jaruma!"
Murmushi tayi sannan ta kalle shi, tace.
"Barka dai, yallabai"
"Shigo Mu shiga daga ciki."
"A'a sir zan koma gida da wuri ne!"
    "Toh zo na ajiye ki."
Babu yadda ta iya amma da ba zata shiga ba, haka ta shiga motar cikin sanyin jiki, ta zauna ya shiga janta da hira, suna tafiya kallonta yayi yaga tana kallon agogon hannun ta.

"Karki damu zamu isa gidan akan lokaci but me zai hana mu dan tsaya na miki take away." Karamin murmushi tayi sannan tace Mishi.
"Nagode sir!"
"Ko kina tsoro na ne?"ya tambaye ta, tare da kashe mata ido,
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Da ina tsoron ka da ba zan shiga motarka ba, kawai ina Son na isa gidan akan lokaci ne." Ta bashi amsa, murmushi yayi tare da parking a wani gurin sayar da kayan ciye ciye, kallonta yayi sannan yace mata.
"Zo muje mu zab'i abinda kike so!"
"Sir nagode zaka iya kawo min kome nagode!"
"Taso muje," ya gaya mata, a hankali tafito kamar ance ta d'aga idanunta ya sauka a motar Mahir, gabanta ne ya fad'i. Dan duk sai taji babu dad'i, bata son magana yau din nan, a hankali take d'aga kafarta, cikin nutsuwa har suka shiga cikin gurin kayan abincin, suna zab'a kawai aka kira Aysar Haladu, ya ce mata tana zuwa.
           Ya fita, can sai aka gama zab'ar musu abinda zasu saya, ya tafi. Juyawa tayi ta ciki taga babu motar shi, gabanta ne ya fad'i, buɗe bag dinta tayi tare da ciro kudin zata biya kawai taji ana mata dariya a gurin, bata damu ba, ta dauka just funny suke, tana amsa ta juya, Mahir na zaune abin shi.

Wani dauke kai tayi tare da Cigaba da tafiyar ta, sai da tazo zata wuce, kawai ya saka mata, kafa.  Garin tsallake shi ta zube dake skirt ɗinta irin me pencil din nan ne bakin shi.

               Haka kayan suka watse baki daya, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Wow thanks Baby!" Sannan ta mike abinta, yana mamakin yarinyar nan, tana saka kai zata fita, wata yarinyar ta watsar da yorgot a kasar, gashi shoe ɗinta irin flat din nan ne, zuciyarta na dukar tara tara, kawai ta kai kafarta kai, ji kake zuuuuiiiiiii farrrr, tana zamewa skirt ɗinta yana yagewa ta baya, komawa tayi ta zauna, sakamakon buguwar da tayi a k'ugunta. Amma taurin kai ya hanata ta nuna fushin ta, asalima murmushi ne akan fuskarta, dariya suka saka mata,  abu daya ya hanata mik'ewa skirt ɗinta, gashi hijab ɗinta Dan Karami ne, ba kamar da, da take saka yadi uku da rabi har kwanjinta, yanzun kuwa yafi biyu ne, iya kacin shi k'ugunta yake rufawa, yagewar skirt ɗinta kuwa har samamta take jin shi, kuma ba karamin faduwa tayi ba.
"Yar jarida! Tashi mana, ko ba zaki iya daukar kanun labarai da yagaggen skirt bane?"

Cikin wani irin kuka ta d'ago kanta tana kallon yarinyar da take mata wannan maganar, hawaye ne suka shiga zuba mata sharrr.

"Sir Mahir Hamoud Boualem! Shi kenan naci kudina ku tayani murna, kace kana son ka ga faduwar ta, na fadar da ita har da sakata kuka, Sir Nagode sosai. Allah ya jikan Abbanka, Guys bye." Yarinyar ta mike tare da Kawayenta.  D'aga mata hannu yayi hannun shi dauke da jarida.

Ya cigaba da abinda yake a hankali, yana kallon ta da wutsiyar ido, yana son yaga zata iya mik'ewa ko ba zata iya ba, so yake yaga tana da kunya ko bata da kunya. Tana zaune a gurin Allah ya kawo karshen rikicin sai ga wata mata da yaranta, sun zo sayan snacks, tana shigowa taga Noorh tana kuka sosai, ga mutane na shiga da fita, a ka'idar Mahir idan zai sayi abu kowa fita yake amma yau dake ya hada mata mugun abu, yace kowa ya zauna kuma abar kowa ya shiga.

     Kallon Noorh matar tayi, dake babba ce.
"A'isha Omar Jimeta!" Subhanallahi, tashi mana!"
Cikin kuka tace mata.
"Ba zan iya ba, skirt dina ya yage."
           Kallon Mahir tayi sannan tace mishi.
"Na zata Major an haife shi domin ya kara kasar shi da mata da yara ne! Ashe shi kare kimar shi yaƙe, na zata bankad'o abinda yake faruwa zai saka Major ya farka daga barcin shi ashe shi lokacin yake niman me hanyar daukar fansa, amma ba zan maka shishigi ba, Aydah jeki cikin mota ki dauko min zanin nan!"

Da sauri yarinyar ta fita, cikin zafin rai ya fice daga gurin, yana ganin tayi mishi laifi amma kuma once ana bashi laifin ta, kawo zanin yarinyar tayi matar ta mikawa Noorh ta daura a hankali sannan tace mata.
"Nagode Ummi"
Murmushi tayi mata sannan tace mata.
"Idan zaki yi aiki, ki fara da bincike. Haka zai sanya ki fahimci abinda kike bukata."
Gyada mata kai tayi amma bawai tana jin zata kyale Mahir bane, duk da kuwa taji shawarar matar amma tabbas sai ta rama yau Insha Allah.
   Godiya tayi mata, sannan ta fita ko ta kan kayanta bata nufa ba, ta bar gurin, abin hawa ta koma ya kaita gida, sai dai ta manta bata amshi Number matar ba. Tana isa cikin dakin su, dan taga gidan babu kowa, dauko kayan ta tayi ya shiga isar da abubuwan da yayi mata, tana gamawa tare da wasu bayanai dangane da mutuwar Badar.

       Tana gamawa ta mike ta manta da abubuwan a gurin, ta shiga ban daki, Tasleem ba Shigowa taga, abubuwan da tayi, ba tare da shakku ba, ta tattara kome, ta tura wayar ta sannan ta juya ta ficcewarta, bata tsaya a ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login