Showing 21001 words to 24000 words out of 40846 words

Chapter 8 - NAUSHIN WUTA Book Complete by Ameera Adam .txt

05 Mar 2025

2764

lamarin nasa ƙara yin gaba yake yi. Don haka ta shiga alla-alla gari ya waye ta leƙa gidan Maimuna ko ta ba ta shawarwarin abin da za ta yi.




Washegari




Tun da Jafar ya yi sallar Asuba bai koma ba, gari yana yin haske ya shiga cikin kitchen ya ɗauke tukunyar cilinder gas ya fice da ita. Da yake Maman Nana ba ta tashi da wuri ba, saboda a daren bacci bai ɗauke ta da wuri ba ko kaɗan ba ta san wainar da ake toyawa ba. Sai da ta ji alamun buɗe gate ta tashi ta fito, a tsammaninta Jafar fita ya yi kasuwa.
Banɗaki ta shiga bayan ta fito ta shiga kitchen za ta shirya wa su Nana abin breakfast da na makatanta. Amma sai ta ga wayam babu clinder, ba ta kawo komai a kanta ba; sai ta yi tsammanin ko ƙaro musu gas zai yi saboda idan ya ga ya kusa ƙarewa yana ɗauka ya ƙaro mata.
Tana daga ƙofar kitchen ta hango shi yana kokawar shigowa da ƙaton buhun gawayi, sai da ya ƙarasa ya jingine shi sannan ya sake fita gate ya sauke mirgino buhu na biyu. Maman Nana tana tsaye ya gama dire buhunnan gawayin har guda biyar, sannan ya ɗauko kurfoti ya dire a gabanta. Fuska a haɗe ya ce, "Daga yau ga abin da za ki dinga girki da shi, gas ya sake tsada ba zan iya sayensa ba. Cilnder ma na sayar wa mai shagon da nake sako mana gas, sai a ci gaba da malejin rayuwa tun da komai tsada yake sake yi." Jafar yana gama faɗar haka ya shige ɗaki.




Kabir kwance ya yi a kan gado, yana jin haushin kansa a kan abin da ya aikata. Fushin Fauziya ya fi komai ɗaga masa hankali, don Fauziya mace ce mai haƙuri da sauƙin kai. Amma idan ta yi fushi ba ta iya zuciya ba, juye-juye ya fara yi yana hangen ta da take kwance idonta biyu tana hawaye. A hankali ya tashi zaune ya tsugunna a gefenta murya a sanyaye ya ce.




"Fauziya! Don Allah ki tashi mu yi magana, ba na son ki saka kanki a cikin wani hali saboda yanayin da kike ciki."




Ɗagowa ta yi ta dube shi, tana jin sautin muryar martanin batsar da yake mayarwa da Hafse a cikin kunnuwanta. Zuciyarta ta shiga zafi, wani abu ya tokare ƙirjinta. A hankali ta fara jin mararta tana tsira mata, ta cije bakinsa tana girgiza kai.




"Don Allah ki yafe mini..."




"Idan ka sake yi mini magana zan fice daga gidan nan na ba ka wuri."
Ta katse shi da wani irin sauti, kamar sabon munafiki haka Kabir ya ja jiki yana sunne kai ƙasa ya koma kan gadon ya zauna.
A cikin wannan daren daga shi har Fauziya bacci rabi da rabi suka yi, sai bayan Asuba ta samu bacci mai hauyi ya yi awon gaba da ita.
Tun da Kabir ya tashi bai koma ba, saboda ya san ya yi wa Fauziya laifi a hankali ya dinga aiki don kada ya tashe ta. Shi ya dafa wa yara abinci, ya shirya su suka tafi makaranta. Sannan ya shiga ɗakin ya share mata, kwanukan wanke-wanken kuma ya ajiye a bakin rariya zai wanke mata. Lawisa tana sanye da hijabi tana girki a bakin ƙofarta ta hango shi ya tsugunna zai yi wanke-wanke, miƙewa ta yi ta ƙarasa wurin ta ce, "Baban Na'ima ka bari zan wanke mata, ko jikin Maman Na'iman ne." Kabiru ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ta tashi ba ta jin daɗi ne, shi ne ta ɗan kwanta zan rage mata aikin."




"Subhanallah! Allah Ya raba lafiya, bari na ƙarasa girki sai na haɗa na wanke da nawa."
Godiya ya yi mata sannan ya koma ɗakin, tun da ya shiga yana son ya tambaye ta abin da za zai girka musu da rana yana shakkar tashinta da ɓacin ranta. Tukunyarta ya buɗe ya ga akwai sauran miya, sai kawai ya ɗora taliya ya dafa musu. Kafin Fauziya ta tashi tuni Kabir ya gama komai, hatta turaren wutar da take sakawa ya saka musu. Ya shiga ɗakin ya same ta a bakin gado a zaune ta tashi, fuskarta ta sauya sosai daga jiya zuwa yau duk ta rame.




"Ga ruwan wanka zan sirka miki sai ki yi wanka."




Kabir ya furta yana satar kallonta, ko kallonsa ba ta yi ba har ya sake maimaita mata.
"Don Allah ka matsa daga gabana Kabir." Da sauri ya fice daga ɗakin, ya shiga banɗaki ya yi wanka. A inda ya bar ta a nan ya same ta, bayan ya shirya ya tambaye ta abin da take buƙata a wannan karon ma banza ta yi da shi. Don haka ya zaro dubu ɗaya ya ajiye mata, bayan ya fita ta bi bayansa da kallon tsana.




Miƙewa ta yi ta ɗauki wata 'yar babbar leda ta ɗebo kaya a drowerta, sai da ta yi wanka ta ɗauki kular abincin su ta zuba, sannan ta saka wata doguwar rigar atamfa ko man kirki ba ta shafa ba. Bakin ƙofar Lawisa ta ƙarasa ta ce.




"Lawisa ga abincin yaran nan da kayan makarantarsu, idan sun dawo don Allah su wuce makaranta."




Lawisa ta karɓa tana faɗin, "Ai na leƙa kina bacci, wai ko abar ce ta zo." Fauziya ta girgiza mata kai ta ce, "Ga wannan mukullin kuma koda babansu zai dawo."




Da mamaki Lawisa ta bi Fauziya da kallo, don ba ta taɓa tafiya unguwa ta ajiye mukulli ta ce a ba wa Kabir ba, amma sai ta haɗiye abin a ranta don tun daren jiya ta fahimci akwai abin da yake damunta saɓanin maganar da ta faɗa mata.
Sallama Fauziya ta yi mata ta fice daga gidan, tana fatan wannan fitar da ta yi daga cikinbaƙin gida ya zame mata ita ce fita ta ƙarshe da za ta yi masa.








+2347062062624




[14/02, 17:27] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*




©®AMEERA ADAM




*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*




GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.




SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA TAKWAS




UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳




Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya




Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731




***




Kabir tun da ya fita daga gidan ba a nutsuwarsa yake ba, kwata-kwata ya rasa me yake yi masa daɗi. Zuciyarsa ce ta shiga wassafa masa laifin abin da ya aikata, har yake jin kamar ya rabu da su Hafsee ya rungumi matarsa ita kaɗai. Ɗaya tsagin na zuciyarsa kuma, ya shiga kwaɗaita masa haɗe da harsaso masa surorin jikin Surayya da Hafsat. Nan take ya ji sam ba zai iya rabuwa da su ba, koda a ce bai auri su duka ba. To tabbas dole zai auri ɗaya, domin zuciyarsa ta jima tana kaɗayin dandalar ni'imar da Allah ya yassare musu. Rashin walwala da sukunun da yake ciki, ya sa mutanen cikin shagon suka lura da shi. Har suke tambaayarsa ko ba shi da lafiya, saboda Kabir mutum ne mai faram-faram yana da sakin fuska sosai. Ganin ya gagara gudanar da aikin da yake yi, yamma liƙs ya yi wa Ogansu sallama ya ce zai koma gida saboda ba ya jin daɗin jikinsa. Lokacin da ya tunkaro gida, kamar ya kira Fauziya a waya ya tambaye ta ko akwai abin da take buƙata ya sayo mata. Sai kawaa ya haƙura, saboda ko sunanta ya tuna gabansa faɗuwa yake yi.




Lokacin da ya ƙarasa gida kusan shida saura, su Na'ima suna jin sallamarsa suka fito daga ɗakin Lawisa da sauri suka rungume shi. Mukulli ta ba wa Fatima ta ce ta kai masa. Kabir turus ya yi a bakin ƙofar ganinta rufe da kwaɗo, kamar yaran sun san tambayar da take cikin zuciyarsa Hidaya ta ce.




"Mami ta je unguwa!"




Gabansa ne ya faɗi, ƙafafuwansa har rawa suke yi saboda tashin hankali. Da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa hannunsa yana karkarwa ya buɗe ƙofar ɗakin suka shiga, yana shiga ɗakin ya fara kiran layin Fauziya sai dai tashin farko ya ji an ce masa a kashe take. Kamar zai yi hauka, haka ya fara zagaye ɗakin da sauri-sauri. Wani tunani ya faɗo masa cikin sauri ya sake riƙo hannun yaran, ya kai su ƙofar ɗakin Lawisa ya ce su shiga zai je ya dawo. Rufe ɗakin ya yi ya sake ba wa Lawisa mukullin sannan ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama.




"Ina Fauziya ta tafi? Ko dai ta tafi gidansu ne? Fauziya ba ta taɓa yin yaji ba, ko ƙarata ta kai gidansu? Yanzu haka za su dinga yi mini kallon mutumin banza? Kai Fauziya ba za ta yi mini haka ba, ina da tabbacin ba za ta bankaɗa labulen sirrina ba."




Haka Kabir ya dinga tafiya yana surutai kamar sabon taɓin hankali, domin kafin ya ƙarasa bakin titi gani ya yi hanyar ta ƙara yi masa nisa. A gurguje ya tari adaidaita sahu ya nufi uguwarsu Fauziya, yana zuwa ya samu mahaifinta a ƙofar gida yana sallar magriba. A hargitse ya zube a gabansa yana faɗin, "Baba barka da yamma."




"Baba ya yi masa kallon tsaf ganin ƙafafuwansa duk sun yi butu-butu, da mamaki ya ce. "Barka dai Kabiru, kai ne da doshin magriba haka? Ya Fauziya da yaran?"




Turus! Kabir ya yi ya ɗan sosa kansa, gabansa ya cigaba da faɗuwa saboda fargaba. Amma gudun kada Baba ya gano shi sai ya ce, "Duk lafiyarsu ƙalau, dama wucewa zan yi na ce bari na biyo mu gaisa."

Baba ya saki murmushi ya ce, "To Ma Shaa Allahu, ai jiya mun ga abin alheri. Allah dai ya raya zuri'a." Jiki a sanyaye Kabir ya amsa sannan ya cewa Baba zai wuce.
Haka Kabir ya cigaba da tafiya yana kiran layin Fauziya har lokacin a kashe, gidan ƙawarta Jamila ya je suka gaisa. Ita ma ta wurga masa tambayar Fauziya, don ta yi mamakin ganinsa a ƙofar gidanta. Saboda rabon shi da gidanta, tun tana amarya da suka zo mata shi da Fauziya kusan shekara biyar kenan.




"Kabir ko ƙawar tawa ce ta haihu?"




Jamila ta jefe masa tambaya tana gyara mayafinta.
"Amm dama na ɗauka ta ƙaraso nan ne, da yake ta fita ɗazu ta ce mini idan ba ta yi yamma ba za ta biyo ta nan. To mukullin yana hannunta, kuma akwai ɗinki wata Mai jego da aka zo karɓa daga nesa, ga ɗakin ta rufe shi. Na kuma kira wayarta a kashe." Ita ma Kabir ya zabga mata ƙarya, Jamila ta ce.




"Ai kuwa ba ta biyo ba, ina jin ko kun yi saɓani a hanya tun da magriba ta yi."
Amsa mata Kabir ya yi suka yi sallama.




Tunanin duniya ya shiga yi a kan inda zai je ya lalubo Fauziya, saboda tun da suke duk faɗan da za su yi ba ta taɓa yi masa irin haka ba. Wayarsa ce ya ji ta fara ƙara, da sauri ya ciro ta a tsammaninsa ita ce sai ya ci karo da lambar Surayya. Guntun tsaki ya saki ya ƙi ɗauka, amma sai ta cigaba da kira. A ƙufule Kabir ya ɗauka yana faɗin, "Wai Surayya me ya sa kin fiye naci ne? Idan kika ga ban ɗauka ba ai kin san ina uzuri."
Daga can ɓangaren Surayya ta kwantar da murya ta ce. "Haba sweet..."




"Babu wani sweet, Surayya ba na cikin nutsuwata yanzu haka duniyar ta yi mini zafi."




"Me yake damunka baby? Ko za ka zo na rage maka damuwa?"
Kamad Kabir ya buɗe baki ya faɗa mata abin da ya faru, sai kuma ya tuna idan ya yi haka kamar ya rusa soyayarsa ne, idan Surayya ta ji labarin hotunan tsiraicin da hafsa ta tura wa Fauziya ne ya sa ta fita daga gidan.




"Wannan ba damuwarki ba ce, family issuesne."




Daga haka ya katse wayar, sai ya sake lalubar layin Fauziya amma a kashe. Gida ya ƙarasa ya laɓe a soro, don kada mutanen gidan su fahimci akwai matsala tsakaninsa da ita.
Ganin har lokacin ba ta dawo ba ya sa Kabir ya nufi gidan Inna domin ya sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin da ya shiga gidan har an fara kiraye-kirayen sallar Isha'i.
Yana shiga ɗakin Inna ya nemi wuri ya zauna haɗe da haɗa kai da gwiwa. Inna da ta gama alwala ta shiga ɗakin ta ce.
"Kabiru nake gani da daren nan?"




Kabiru ya share ƙwallar idonsa ya ce, "Inna ni ne."




"To ashe Fauziyan ta isar maka da saƙona, amma ba ka samu zuwa ba sai yau. Yau kuma me ka kawo mini, saboda dama garin tuwona ya ƙare."
Inna tana yin gama magana ta ji Kabir yana shasshekar kuka, a ɗan kaikaice ta leƙa fuskarsa ta ce.




"Wai kuka kake yi Kabiru? A cikin yaranka wata ce ta mutu?"




Kabir ya girgiza mata kai, Inna ta sake cewa.
"To Fauziyan ce ta mutu?" A nan ma ya sake girgiza mata kai.
"To uban me ya sa ka kuka tun a farkon daren nan? Ni dai na san rabon da na ga kukanka tun ranar da mahaifinku ya mutu."




"Inna gida na koma na ga Fauziya ba ta nan, na je gidansu da niyyar tambayarsu sai mahaifinta ya tambaye ni ya take, kin ga kenan ba ta je can ba. Ga shi dama ba ta tambaye ni ba, ban san inda ta tafi ba."
Kabir ya ƙarasa maganar yana zubar da ƙwallah. Wani takaici ne ya maƙure ziciyar Inna, ta dube shi a wulaƙance tana sakin dogon tsaki ta ce. "Mttssswww amma dai Kabiru ka yi asara wallahi, yanzu a kan mace kake zubar da ƙwalla? Ashe abin da ake faɗa gaskiya ne, yarinyar nan ta gama wanke hannu a kanka."




Inna ta koma bakin gado ta zauna ta cigaba da cewa, "Yo wai ma Fauziyar yarinya ce? Da za ta fice har ka dinga neman saboda ta ka ganɗma lalacewa"




Cikin damuwa Kabir ya ce, "Wallahi Inna ni ne da laifi, ni na ɓa ta mata rai, duk macen da ta ga abin da na yi fiye da haka ma za ta iya aikatawa."
"To ai sai ka yi ta yi tun da wahala ta aure ka, yanzu kuma a ina ta bar yaran?"
Kabir ya ce, "Suna ɗakin matar gidanmu."




"Amma wannan yarinya an yi baƙar munafika, haka kawai ina zaune ƙalau ta ɗaga mini hankali. Sai ka fita ka kai cigiyarta gidan radiyo, tun da lalacewarka ta kai haka." Daga haka ta saka hijabinta ta tayar da sallah. Kabir da ya lura zamansa a wurin Inna ba mafita zai kawo masa ba, sai ya miƙe ya fice. Kasancewar Sadiya ta ji duk abin da yake faɗa, sai ta tsayar da Kabir tana tambayarsa. A nan ya zayyane mata duk abin da ya faru, duk da bai fito ya faɗa mata laifin da ya aikata ba. Shiru ta yi tana nazari, amma har cikin ranta take ji Kabir ne bai kyautawa Fauziya ba, domin ta san tana da haƙurin gaske. Saboda damuwa Kabir haka ya dinga takawa a ƙafa, yana tafe yana jimamin halin da take ciki da tsohon ciki a wannan lokacin. A haka har ya ƙarasa gida.




Tun lokacin da Fauziya ta tashi daga bacci ta ji mararta da bayanta suna ciwo, don haka ta yanke shawarar zuwa asibiti. A ranta tana fatan koda haihuwar ce ta zo mata, tana fatan ta kasance silar tafiyarta lahira. Duk haihuwa ukun da ta yi Kabir ne yake kai ta asibiti, daga baya kuma sai ya kira matar mahaifinta ya sanar da ita idan sun je. Amma da yake zuciyarta a cunkushe take da haushin Kabir, ya sa ta ɗauki duk wani kaya da za a buƙata a asibiti. Ta ƙi sanar da Lawisa ne, saboda ta san idan suka tafi ita da Lawisa asibiti babu a inda su Na'ima za su zauna ballantana su ci abinci.
Sai da ta fara biyawa ta gidan Dillaliya ta roƙe ta, da ta ba wani abin daga cikin cikon kuɗin firji, bayan ta karɓi kuɗin ta fice daga gidan.
Fauziya ba ta damu da kallon da mutane suke yi mata ba, tana tafe tana hawaye haka ta dinga tafiyar ƙafa domin ya taimaka mata wurin samun saurin naƙuda. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu adaidaita sahu ya kai ta asibiti, a lokacin da ta je asibiti ana duba ta aka ga tana 5cm. Wayarta ta ciro ta fara kiran ƙanwarta da suke uba ɗaya ba ta same ta ba, ta kira ta matar babanta ita ma a kashe. Na'ima ba ita ta haihu ba sai bayan sallar magriba, ta haifo jaririyar 'yarta mace kyakkayawa mai kama sak da Kabir.
Ido ta ƙurawa jaririyar tana kallo, saboda tsananin kamar da suke yi da mahaifinta. Wani irin takaici ya kamata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login