Showing 27001 words to 30000 words out of 40846 words
ba shi da abokiyar hira sai wayarsa. Koda hira Maimuna ta zauna tana yi masa sai dai ya dinga ba ta amsa sama-sama, amma kaso casa'in cikin ɗari (90%) hankalinsa yana kan wayarsa. Da yake Maimuna tana da ɗan surutu ta dinga yi masa mita kenan, tana nuna ɓacin ranta. Hakan ne ya sa wani lokacin Nazir ba ya dawowa gida da wuri, sai ya gama uzurorinsa a waje. Ya kasance mutum mai takura, bin diddigi da rashin yarda. Don hatta maƙota ba ya barin Maimuna shiga, su ma kuma a ɓoye suke shigo mata bai sani ba. Duk inda Maimuna za ta je shi zai kai ta, kuma bai cika kai ta da rana ba har sai ya dawo daga kasuwa. Kuma idan ya kai ta duk taron da ake yi sai dai ya jira ta a ƙofar gida agama ya tafi da ita. Maimuna tun tana zama ta ci kuka bayan aurensu har abin ya zame mata jiki, kuma sannu a hankali Nazir ya aurensa ya sure mata har take jin Allah Ya kawo sanadin da za su rabu wala mutuwa ko sakin aure. Sakamakon halinsu da ya yi hannun riga da ita, tun da har babbar waya ya hana ta riƙewa a cewarsa duk wani abu da zai buɗe idonta ba zai lamunra ba. Tun da ai sai mace ta yi mu'amala da mutane ake ba ta munanan shawarwari, ko a zuge ta ta sauya halaye. Idan kuwa aka ɗora mace a doron da ya ɗora Maimuna, a ganinsa hakan ne zai daidaita mace ta zama kamila tun da idonta bai buɗe ba.
Tarihin Maimuna
Maimuna 'yar asalin garin Dutse ce da ke jigawa, mahaifi da mahaifiyarta duk 'yan can ne. Kuma su biyar ne a wurin iyayensu, yayanta Sadik shi ne babba sai ita take binsa ƙannenta mata uku suke biye da ita.
Maimuna ta yi karatunta na addini daidai gwargwado, ha boko kuma ta tsaya a secondary. Domin mahaifinsu mai sauƙin ra'ayi ne, idan yarinya ta samu miji zai aurar da ita ra'ayin mijinta ne ta cigaba ko ya hana ta. Idan ba ta samu miji ba kuma ta cigaba da karatu, kuma hakan ce ta faru da Maimuna.
Tun tasowar Maimuna 'yar gayu ce mai sosai, tana son ƙwalisa. Uwa-uba tana da wayewa, don ƙawayen da take hulɗa da su duk masu buɗaɗɗan ido ne. Maimuna tun tasowarta take da tsari, don ra'ayinta ne auren namiji mai kuɗi da iya soyayya. Kuɗin ma bai cika tasiri a ranta ba matuƙar namiji zai ba ta kulawa da soyayya koda mai rufin asiri ne za ta iya zama da shi. Dalilin haka ya sa ta gama tsara rayuwar da za ta gudanar a gidan aurenta, ita da mijinta.
Tarihin Nazir
Nazir haifaffan garin Kano ne, sai dai mahaifi da mahaifiyarsa asalinsu 'yan garin Katsina ne. Neman kuɗi ne ya kawo mahaifinsa garin Kano, a nan duk aka haife su shi da ƙannensa. Mahaifinsa yana da mata biyu da 'ya'ya takwas, ƙannensa da suke uwa ɗaya guda uku ne duka maza. Sai waɗanda suke uba ɗaya su shida kasancewar shi ne babba a wurin mahaifinsa. Nazir kasuwancin hulunan maza yake a kasuwar kwari, shagonsa babba ne kuma yana da rufin asiri bakin gwargwado.
Nazir ya haɗu da Maimuna ne a wurin dinner wani abokinsa da suka yi a garin jigawa, da yake tana daga cikin manyan ƙawayen amarya. Tun da Nazir ya ganta ya maƙale mata har aka tashi daga taron, amma kafin su a watse sai da suka yi musayar lamba sannan ya kai ta har ƙofar gidansu ya sauke ta.
Ko kaɗan Nazir bai kwanta a ran Maimuna ba, don tun daga yanayinsa bai yi mata kalar irin mijin da take burin zama da shi ba. Shi kansa Nazir ya fahimci haka, don ko kiran wayarta ya yi wani lokacin ba ta ɗauka. Da ya yi bincike a kanta, sai aka yi masa bayanin halinta tsaf da yanayin waɗaanda take mu'amala da su. Hakan ne ya sa Nazir ya lulluɓe kura da fatar akuya, sai da ya tabbatar da da ya siffantu da irin mijin da Maimuna take muradi sannan ya koma mata tsamo-tsamo. Tun Maimuna tana share shi har ya fara karkato da hankalinta kansa, don tuni ya saye zuciyarta ta hanyar ƙyale-ƙyale da kayan ƙawa. Ya shiga shayar da ita romon zallar soyayya tana sharɓa, har sai da ta dinga gina musu irin rayuwar da za su gudanar a gaba. Hakan ya sa Nazir ya bijirowa Maaimuna da maganar turo magabatansa, kafin ta amince da ta suka yi yarjejeniya a kan bayan sun yi aure za ta cigaba da karatu. Don tana da burin yin aiki a gaba, tashin farko Nazir ya amince mata. Hakan ya sa aka tsayar musu da lokacin aure, da lokacin ya ƙarato Nazir ya yu mata bajimta ta hanyar kama manyan kuma ƙayatattun wuraren taro na alfarma.
Matsalar farko da Maimuna ta fara fuskata a ɓangaren ƙawayenta ne, domin ko wata ba su yi ba da aka tashi bikin wata ƙawarsu ya ce ba za ta je ba. Lamarin da ya kai su ga yin faɗa, saboda Samira aminiyar Maimuna ce ta yi mata ƙoƙari a sha'anin bikinta. Wannan faɗan har sai da ya kai su gaban iyaye, a nan kuma kowa ya ba wa Maimuna rashin gaskiya da cewar mijinta yana da damar da zai hana ta zuwa bikin kowacce ƙawa, kuma mahaifinta ya jadadda mata idan har ta kashe aurenta ba tare da wani dalili ba sai dai ta nemi wani wurin ba gidansa ba.
Wannan ikon da Nazir ya samu ya sa kai tsaye ya yanke alaƙar Maimuna da ƙawayenta, tun suna yin kara suna zuwa wurinta har kowa ya janye jikinsa saboda ba zuwa wurinsu take yi ba. Hatta garinsu sai ta shafe lokaci mai tsayi.ba ta je ba, idan sun tashi tafiya kuma shi zai kai ta ya zauna a ƙofar gida idan yamma ta yi ya ɗauko ta su dawo gida. Sannu a hankali Nazir ya dinga bijirowa Maimuna da ɓoyayyun halayensa, tun daga wani faɗa da suka yi ya karɓe babbar wayarta ya ba ta ƙarama. Sannan makarantar da suka yi yarjejeniya ya ce ba za ta cigaba da karatu ba, da ta kai ƙararsa gida kuma sai iyayenta suka nuna mata tun da aure gaba yake da komai gara ta zauna ta yi ibadar zaman aure. Da zaman aurensu ya yi zama ne Maimuna ta fahimci kuɗin da yake mata facaka da su ba su kai haka ba, don a farko kallon mai kuɗi take yi masa sai daga baya ta gane duk munfurtarta y yi. Tun daga wannan lokacin Nazir ya sire wa Maimuna, tana dai zaune da shi ne saboda biyayyar mahaifinta. Da zaman haka ya ishe ta sai ta nuna wa Nazir tana buƙatar yin kasuwanci, amma fir ya ƙi ba ta dama.
Wata irin ƙaunar Fauziya ce ta lulluɓe Kabir, yana daga tsaye ya zauna a gefenta ya haɗe ta ita da jaririyar ya rungume su cike da so da ƙauna. Ƙwace kanta Fauziya ta shiga yi, ya riƙe ta tsam sai suka saki ajiyar zuciya kusan lokaci ɗaya.
"Don Allah ki bar ni na ji ɗuminku!"
Kabir ya furta cikin shauƙi, fa sauri Fauziya ta fisge zuciya tana ɗaci ta ce.
"Ni a wa da za ka ji ɗumina? Ka bari ka je wurin Hafsa ai tana da abubuwan da ba ni da su."
Kabur sam bai ji daɗi ba, ya marairaice murya ya ce.
"Duk fa wasu kalamai da kika ji ina na fatar baki ne, babu abin da ya taɓa haɗa ni da ita. Ni ko gidansu ma ban sani ba." Fauziya ba ta tanka masa ba, ta taɓe baki tana bin sa da harara.
Tun daga wannan ranar Kabir ya shiga nannan da Fauziya, ita kuma har lokacin ba ta ba shi fuska. Ya yi mata ɗinki kala uku masu kyau, sai jaririya da saya mata rigunan kanti kala uku. Su Na'ima kuma suja tashi da atamfa ɗaiɗai, ba ta yi wani taro ba. Tsirarun mutanen da ba a rasa ba, ta yi kyau sosai kamar ka sace. Kabir da ya shiga gidan ya ganta sai ya shiga rawar ƙafa, ganin kada mutane su fahimci ba sa shiri ya sa ta saki jiki 'yan uwa suka shiga ɗaukarsu hoto. A wannan lokacin Kabir bai samu damar yanka wa jaririya hakika ba, sai haƙuri da ya ba wa Fauziya da yake ta san yanayin samunsa ya sa ba ta damu ba.
Sannu a hankali Kabir yake ta shawo kan Fauziya har ta saki jiki da shi suka dawo kamar da, amma kafin nan sai da ta tasa shi a gabanta ya kira Hafsa ya ci mata mutumci don a ganinta duk budurwar da za ta tura wa namiji tsiraicinta ba matar aure ba ce. Saboda kafin ta sa ya kira shi sai da ta tambaye shi idan auren Hafsat zai yi ya ce a'a, don haka ta hura masa wutar sai sun rabu idab ba haka va ta bar masa gidan ya zauna da ita. Wannan shi nw dalilin rabuwar Kabir da Hafsa, saboda duk rashin zuciyar mace sai ta ji haushin irin wulaƙancin da ya yi mata. Don Kabir yadda ya dinga cin zarafinta nuna wa ya yi kamar dama can Hafsan ce ta maƙale masa, a yadda ta fahimta ma nuna wa yake ba su da dpguwar alaƙa ita da shi.
Ranar da Kabir ya je ƙofar gidansu ba ƙaramin cin mutumci ta yi masa ba, duk yadda ya kai ga son lallashinta ko kaɗan bai shige ta ba. Saboda a ganinta Kabir ba mijin aure ba ne tun da bai isa da matarsa ba, domin ya bayyana a fili ba zai iya adalci ba.
Ranar Juma'ar da suka wayi gari ita ta yi daidai da saura kwana biyu rak su tashi, don tun ranar Laraba Lawisa ta tashi suka kama haya a unguwar rimin kebe. Ranar Juma'ar kuma ita ma A'ilo ta tashi, sai su Maman Sabir da suka haɗa kayansu su ma washegari Asabar za su tashi.
"Abban Na'ima ban gane maka ba, har yanzu fa ba ka ce mini komai game tashinmu ba. Ka san halin mutumin nan ba sho da mutumci, mutanen gidan nan duk sun fara tashi. Saboda gudun tozarci fa na sayar da firjinmu domin mu samu mu ƙarasa abin da ba a rasa ba."
Fauziya ta yi maganar zuciya babu daɗi tana ƙoƙarim danne ɓacin ranta. Saboda tun da kwanakin tashinsu ya ƙarato, ta ga wata alama daga wurin Kabir. Kuma idan ta yi masa naganar ko dai ya bagarar, ko kuma ya fara faɗan ta cika gajen haƙuri. Haɗe rai Kabir ya yi ya miƙe yana shirin fita ya ce, "Eh haka ne, amma duk tsiya ai ba za mu rasa wurin zama ba." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai dama ba ina nufin za mu rasa wurin zama bane ina maganar ginin can ne. Ko a rana ɗaya za mu kwashe? Amma ko rana ɗaya za mu kwashe sai dai ko zuwa gobe, tun da jibi na tabbata sai ya zo da masu fitar da kaya."
"Wai me ya sa kin fiye mita da takura ne Fauziya? Mtsww Allah Ya sawaƙe da wannan halin naki, ai ki kammala haɗa kaya gobe za mu koma gidan Inna kafin na ƙarasa."
Kabir yana gama magana ya fice daga gidan.
A yi haƙuri da errors kwana biyu kuma ban zauna ba ne, shi ya sa ban yi typing ba.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624
[18/02, 18:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA GOMA
UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳
Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya
Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731
***
Kamar wacce ta ci karo da sabuwar hallita haka ta bi bayan Kabir da kallo, nan take ta cigaba da nanata kalaman da ya faɗa mata kamar mai yin hadda. Ba ta yi aune ba ta ji murfin idonta ya buɗe, hawaye ya shiga kwarara kamar idaniyar ruwa mai gudana. Duk yadda ta yi hoɓɓasar dakatar da shi sai abin ya gagara, maƙogaronta ya shiga ɗaci tana jin wani abu ya tokare mata ƙirji. Nan take ta ji ƙirjinta ya hau ciwo, don tun daga mummunan ganin da ta yi a wayar Kabir da ranta ya ɓaci sai da ta ji wani abu ya tokare mata ƙirji, sai bayan wani lokaci kuma ta ji ya lafa mata. Don bala'in da yake cikin zaman gidan Inna ba abu ne mai sauƙi ba, duba da irin abubuwan da take gani tana yi wa Sadiya. Da kuma wanda ita kanta Sadiyan take faɗa mata, wani tunani ne ya faɗo mata don haka ta yi saurin janyo wayarta ta latsa layin Kabir. Sai fa ta kusa katse wa ya ɗauka yana faɗin.
"Ina hanya."
Tana jin yana shirin kashewa ta ce, "Magana nake son mu yi Abban Na'ima." Kamar ba zai amsa mata ba, sai kuma a daƙile ya ce.
"Ina jin ki."
Gaban Fauziya ya shiga faɗuwa, tana fargabar irin fassarar da zai yi wa kalamanta. Jin shiru ya sa Kabir ya ce, "Kin san ba ki da abin faɗa kika kira ni?"
Maganar da ya yi ba ƙaramin bugun zuciya ta saka ta ba, ta yi ƙarfin halin faɗin.
"Abban Na'ima don Allah ka kama mini haya!"
"Saboda me?"
Ya wurga mata tambaya a gaggauce.
"Haka kawai, ina ganin kamar za mu fi sakewa. Na ga gidan Inna kamar babu ɗaki, ga kuma yara."
Guntun tsaki ya yi ya ce, "Duk ɗakunan gidan Innar ne za ki ce babu? Ko dai zama da mahaifiyar tawa ne ba kya so?"
Kamar Fauziya za ta yi kuka ta ce, "A'a na ga ɗakin da ya rage ba kowa shirgi suke ajiyewa."
Ajiyar zuciya Kabir ya sauke ya ce, "Na sa yara sun gyara ɗazu, idan Allah Ya kai mu da sassafe akwai mai motar da na yi wa magana zai zo ɗaukar kaya."
Murya tana rawa ta ce, "Ko na kira dillaliya ta sayi keken ɗinkin nan nawa? Idan ya so kafin jibi sai mu nemi ɗaki."
A hassale Kabir ya ce, "Wai me kike nufi Fauziya? Mahaifiyar tawa ce ba kya ƙaunar zama da ita? Ko kin manta ita ta ɗauki cikina wata tara ta haife? Saboda raini har ni kike cewa za ki kamawa haya, a kan ki zauna da mahaifiyata?"
Nan take ta rikice, don ta san dama ba lalle ya fahimci irin abin da take gudu ba. Tuni hawaye ya wanke fuskarta, tana shirin magana ta ji Kabir ya katse a fusace. Kuka Fauziya take yi wanda take jin ɗacinsa yana fitowa daga ƙasan maƙoshinta, tsakar gidansu ta ƙura wa ido tana hangen ɗakin Lawisa. Tana ji a ranta yadda zuciyarta take zafi, da ace Lawisa tana nan ita ce mutum ta farko da za ta fara faɗawa halin da take ciki ko ta ji sanyi. Duk da wannan ba ɗabi'arta ba ce, amma tana jin idan ba ta sanar da wani ba zuciyarta za ta iya bugawa. Tashi ta yi ta fara kai wa da kawowa domin neman mafita, amma gabaɗaya kanta ya cushe. Tunanin tafiya gidan mahaifinta ta yi, a nan ma ta ga sam ba mafita ba ce domin mahaifinta ba zai taɓa goya mata baya ba.
Da wannan tunanin Fauziya ta wuni har sai da zazzaɓi ya rufe ta, haka daren ranar ya zo mata cikin ƙunci. Da Kabir ya dawo ta ga yana fushi ba ta tanka masa ba, da ta miƙa masa abinci kuma ya ce ba ya ci. Ita ma da yake a cike take da haushinsa, ba ta sake bi ta kansa ba ta kwanta. A daren ranar kwana ta yi tana miyagun mafarkai a kan zamanta da Inna har gari ya waye.
Tun da farar safiya mai motar da Kabir ya yi wa magana suka yi sallama, ya fara fitar musu da kaya. Fauziya tana haɗa kaya tana hawaye, Na'ima da Fatima tun da suka ji mahaifiyarsu ta ce gidan Inna za su koma duka walwalarsu ta dusashe, amma da yake Hidaya ba ta san dawan garin ba haka ta dinga tsalle tana murna.
Sai da aka gama kwashe kayan tsaf sannan ta leƙa ta yi wa Maman Sabir sallama, da neman yafiyar juna.
Tun da suka doshi layin ƙirjinta yake bugawa, tana fargaba irin zaman da za su gudanar a cikin gidan. Tsayuwarsu a ƙofar gidan, ya yi daidai da tsala ihun da Salim yake yi. Jiki a sanyaye Fauziya ta tsoma ƙafarta cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Inna ta hango a zaune ta maƙure Salim a ƙasan ƙafafuwanta tana tsala masa dorina