Showing 15001 words to 18000 words out of 40846 words
amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce.
"To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da wuri za ku wuce ne Fauziya?"
Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce. "Yanzu za mu wuce Inna, da ma zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki." Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin.
"Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na yi mata."
Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?"
Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya, wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa."
"Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?"
Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen kuma su yi rayuwa kamar kowa."
Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar hankali.
"Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri ɗaya dama yana kawo haka, ki cigaba da addu'a sai ki ga watarana sai labari."
"Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a gidan."
Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abin da ya fi ƙarfin addu'a."
Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta. A tsakar gida ta samu mahaifinta yana ta bambamin faɗa, a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu. Su Nai'ima kuwa dama tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu.
Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakin dandamalin rijiyar sannan ya ɗauka.
"Gimbiyar mata!"
Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce.
"An ya kana jin abin da nake ji na soyayyarka kuwa?" Kabir ya sake kwantar da murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faɗin haka."
Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp ɗinka na turo maka da hotuna."
Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya.
"Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana."
Hafsa da duk ta ji nauyinsa ya kama ta ta ce, "Baby gaskiya ka yi haƙuri, wallahi wannan ma da ƙyar na iya turo maka."
"Guda ɗai-ɗai fa kawai za ki yi mini, kuma kin san ai aurenki zan yi ko ba ki yarda ba?"
Shiru ya ji Hafsa ta yi, ya ɗora da cewa. "Akwai kuɗin da nake saka ran za su shigo mini nan da kwana uku. In Shaa Allah a satin nan za a kawo kuɗin aurenmu." Daɗi ya lulluɓe Hafsa, jikin yana rawa ta ce.
"Zan turo maka amma don Allah kana gani ka goge."
Cikin sauri Kabir ya ce, "Wallahi ina gani zan goge." Kashe wayar Hafsa ta yi ta shige ɗakinta ta yi masa bidiyo ta tura masa. Kabir yana ganin bidiyon a ruɗe ya shiga yi mata replay da kalaman batsa, tun tana jin nauyinsa har ta fara biye shi.
Yamma liƙis Fauziya ta koma gida ta ɗora musu girki, a wannan karon ma ana yin magriba ta kira Kabir ta sake tuna masa maganar da suka yi, game da alƙawarin da ya ɗaukar mata ba zai sake shan komai ba. Sannan ya ce ta tsala masa kwalliyar domin a cike yake da kewarta. Zuciyar Fauziya fes ta tsala wanka cikin wata doguwar riga marar nauyi, ta raba gashinta gida biyu kamar wata 'yar baby ba ƙaramin kyau ta yi ba. Suna nan zaune ita da yara kimanin ƙarfe tara suka ji sallamarsa. Kusan lokaci ɗaya ita da yaran suka rungume shi har ita suna faɗin.
"Abi oyoyo."
Rungume su ya yi gabaɗaya, sai Fauziya ta saci kallon yadda suke nishaɗi ita da yaran, saboda dawowarsa da wuri kuma a cikin nutsuwarsa, sai ta ji ƙwalla tana shirin zubo mata. Ɗaya bayan ɗaya ya tsugunna yana sumbatar yaran a goshi, sai ya ɗago ya dube ta suka haɗa ido. Rungumo ta ya yi a jikinsa yana kashe mata ido ɗaya, irin kallon da take bin sa da shi ya sa shi hura mata iska a fuska.
"Wannan kwalliyar zan biya tukwicinta an jima."
Ya furta mata a hankali, ta sakar masa murmushi ta ce.
"Na fa tsufa da yawa."
Kafaɗa ya maƙale mata cikin kwaikwayon muryarta ya ce, "Ni ban yarda ba." Duk da yaran ba su fahimci me suka tattaunawa ba, jin yadda mahaifinsu ya maƙale murya ya sa suka fara ɗariya.
Hula, agogo da wayarsa ya ajiye a gefen gado ya ɗauki bokiti ya zuba ruwa ya tafi yin wanka. Kabir ya manta shaf da abin da Hafsa ta turo masa bai goge ba, har ya iya ajiye wayarsa. Kuma ya bar hotunan ne saboda idan ya keɓe ya dinga kalla yana jindaɗi.
Fatima ce ta ɗauki wayar ta shi, da yake wani lokacin idan yana gida ya kan kunna musu game ko cartoon su kalla. Shige-shige suka fara yi masa har suka shiga cikin gallery ɗinsa, Na'ima ta zura kanta ta danna ɗaya daga cikin bidiyon da Hafsa ta tura masa. Fauziya da ke tsugunne tana jera masa kayan abinci ta ji muryar mace raɗau a kunnenta tana faɗin.
"Baby kana gani, wannan bidiyon..."
A gigice Fauziya ta fisge wayar daga hannunsu jikinta yana karkarwa, sakamakon ji irin bayanin batsar da buduwar take yi. Domin a bidiyon hafsa tana yi masa tana bayanin komai dalla-dalla.
"Lah Mami mene ne wannan?"
Na'ima da ta fi su wayo ta tambaya, sai da Fauziya ta saita nutsuwarta ta ce, "Bidiyon wata marar lafiya ne da take neman taimako, za a haɗa mata kuɗi a yi mata magani. Na sha faɗa muku idan mutum ya ajiye abu, sai an tambaye shi ake taɓawa ko?"
Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai, Fauziya da take jin wani abu yana taso mata a ƙirji ta yi ƙarfin halin faɗin.
"To daga yau, ko da wasa ka da na sake na ƙara ganin ku taɓa wa mutum wayarsa. Idan ba haka ba ranku zai ɓaci." Su Fatima suka amsa mata.
Ear pices ta ɗauko ta saka a kunne, ta shiga bidiyan ta kunna shi. Jikinta ya ɗauki karkarwa gabanta yana wani irin bugu da ƙarfi, lokaci ɗaya hawaye ya wanke fuskarta domin bidiyon ya matuƙar ƙazanta. Da sauri ta shiga whatsapp ɗinsa, ta ga yawanci masu saƙon duk maza ne, don haka take mamaki a inda Kabir ya samu wannan bidiyon. Har za ta fita ta ga an saka costomer Hafsa lace bubu, tana shiga ta ci karo da emojin heart ta turowa Kabir. Can sama ta haura ta fara cin karo da saƙonnin batsar da suka tattauna, a nan ta gano wannan bidiyon na Hafsa ne tun da ga muryar ta nan ta kunna voice ɗinta ta ji."
Jikinta yana rawa ta kifa wayar, sai ta jingina da bango tana jim wata irin tsanar Kabir ta mamaye ta.
Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[13/02, 21:15] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA SHIDA
UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳
Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya
Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731
***
Tun tana zubar da hawayen zuci don kada yaranta da ke zaune su fahimci halin da take ciki har ta gagara sarrafa zuciyarta saboda wani irin zafi da ɗacin da take yi mata. Hawaye taka sosai tana shassheka tamkar za ta shiɗe, saboda wani irin kakkarwa da jikinta yake yi ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri-sauri. Ganin halin da mahaifiyarsu take ciki ya sa suka ƙarasa wurinta suna tambayarsu, ba ta iya tanka musu ba sai ma wani irin kallo da ta dinga bin su da shi kamar ta ga sababbin hallita. A ranta ta ayyana ƙila yarinyar da suke musayar munanan kalamai da Kabir ko kaɗan iyayenta ba su san abin da take aikatawa ba. Sai kawai ta rungumo su jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, ganin haka ya sa su Fatima su ma suka rairai kukan su ma.
Duk da ya san ba hali ko ɗabi'ar Fauziya ba ne binciken wayarsa, haka kawai yana wanka da ya tuna ya bar wayar a kan gado ya ji gabansa ya faɗi. Nan take ya yi sauri ya kwakkwara ruwa ya fito, don ba ya so Fauziya ta fahimci irin alaƙar da ke tsakaninsa da su Hafsee. Kamar wanda aka kifa haka Kabir ya faɗa cikin ɗakin har yana tuntume, Fauziya ta ɗago tana kallonsa ta ƙura masa ido. Ganin yanayin da ya same ta ita da yaran da kuma mummunan kallon da take wurga masa, ya sa ƙirjinsa ya buga da wani irin ƙarfi. Da gudu yaran suka tafi wurinsa cikin haɗin baki suka ce, "Abi Mami ce take kuka."
Yanayin yadda ya ga hankalin yaran ya tashi ya sa ya kalli wurin da ya ajiye wayarsa, rashin ganinta a wurin ya sa shi tabbatar da tabbas mai afkuwa ta riga da ta afku. Ya san duk irin saɓanin da za sh samu da Fauziya ba ta iya zubar da hawayenta a gaban yaran, duk abin da za su yi ko wata tattaunawa ce sai ta bari sun tafi makaranta ko kuma idan sun yi bacci amma gudun kada ya bada kai bori ya hau sai ya yi kamar bai san dalilin ɓacin ranta ba ya ce.
"Ummu banat lafiya kike hawaye a gaban yara?"
Tamabayar da ya wurga mata ta ji ta yi tamkar ya zuba mata ruwan dalma, ta dube shi cike da mamakin wai ita Kabir zai raina wa hankali. Murmushin takaici ta saki sannan ta miƙa masa wayar ta ce, "Ungo wayarka, cikina ne yake ciwo." Ya san ta faɗi haka ne saboda gudun yaran su fahimci shi ya yi mata wani abin, Na'ima ta ɗauko kwalmar maganin tarinsu ta miƙa mata ta ce.
"Ammi riƙe ki sha magani ba na son na ga kika kuka!"
Ƙuri ta yi wa yarinyar tana kallo, murya a dashe ta ce.
"Wannan maganin yara ne Na'ima, cikin nawa ya sarara idan na tashi zan ɗauko maganina a cikin jaka."
"Amma za ki daina kuka?"
Na'ima ta sake wurga mata tambaya, gyaɗa mata kai Fauziya ta yi. Dai kuma ta ƙarasa gaban Kabir ta ce, "Abu ni dai ka kai Ammi asibiti, ba na son ta dinga kuka ni ma zan yi." Ta ƙarasa maganar tana janyo hannunsa. Tamkar wanda aka liƙewa ƙafa da super glue, haka ya ji ƙafarsa ta manne ta ƙasa wata irin shakkar Fauziya ta kama shi.
"Ko... ko... za mu... wuce asibiti..."
Ya furta bakinsa yana rawa, sai dai tun bai fire kalamansa ba Fauziya ta wurga masa mugun kallon fa ya sa shi haɗiye kalamansa.
"Ai jikin mamanku da sauƙi Na'ima, ba sai mun je asibiti ba. Yanzu dai bari na yi muku shinfiɗa kun ga gobe kuna da school."
Tana gee har lokacin idonta yana kan Kabir, da take yi masa kallo kamar tana som gano wani ɓoyayyan abu daga jikinsa. Shafa jikinta take yi don ta tabbatar ba mafarki take yi ba, ta saka hannu ta mintsini cinyarta jin zafin ya ratsa wurin ya sa ta tabbatar da zahiri ne. Tana kallo Kabir ya kashe wayar gabaɗaya, jikinsa gar rawa yake ya ɗebo kayan shimfiɗa ya yi wa yaran. Yana gama shimfiɗar ta ga ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin alamar fita ma zai yi daga gidan gabaɗaya.
Tun da ya fice Fauziya take saƙa da warwarar hukuncin da za ta yanke, ban da kai wa da kawowa babu agim da take yi. Hat yanzu zuciyarta rawa take yi a kan ko dai idanu da kunnuwanta ba su jiyo mata daidai ba. Babban abin da ya sake ɓata mata rai, yadda ta ga ya ɗauki wayar ya fice daga gidan wato duk ma abin da za ta yi ta je ta ƙarata. Ta jima tana ƙoƙarin dakatar da hawayen idonta, amma ta kowanne ɓangare ya gagara ba ta haɗin kai.
Shinshina jikinta ta fara yi tana son gano ta inda ta gaza, ta ɗaga rigarta tana kallon mamanta ko za ta ga hango aibun na jikinta. Domin Allah ya yi mata baiwa duk da haihuwarta uku ga ta huɗu za ta yi amma mamanta bai lalace, ballantana ta ce ko nata ne suka zube har yake hangen na wasu. Kuma idan ma lalacewa suka yi a tsawom shekaru bakwai da aurensu bai ci ace ya ɓoye mata ba. Har gara ya faɗa mata domin ta san matakin gyaran da za ta ɗauka. Ta matsa gaban madubi tana bin kanta da kallo, sai dai har ta gaji da tsaiwa ba ta gano makusar da za ta sa Kabir ya dinga musayar munanan kalamau da hotuna da 'yanmata.
Gajiya ta yi da tsaiwar ta zauna a gefen gado, sai ta shiga tausayin kanta da 'ya'ya matan da ta haifa.
"Wannan wacce irin rayuwa, aai yaushe zan sanu kwanciyar hankali? Sai yaushe zan samu nutsuwa kamar kowa? Sai yaushe..."
Wani sabon kukan ya sake ƙwace mata, a wannan ranar da take jin kamar zuciyarta za ta yi fiffike ta ɓullo daga ƙirjinta, ba ta shayi ko kunyar bayyana kukanta a sarari domin gurin ɗabi'u da halayen Kabir ba a ranar suka fara yi mata ba. Kamar kuwa Fauziya ta sani, su Ai'lo da ke ɗaki duk sun kasa kunne suna son gano dalilin kukan nata. Don sun san fa wuri ya dawo gida ba a buge ba, ballantana su ce takaicin rashin dawowarsa ne ya saka ta kuka.
Lawisa da ke ɗaki har sun kwanta ita da mijinta ta gagara haƙuri, ta fito zuwa ƙofar ɗakin Fauziya.
"Maman Na'ima! Maman Na'ima ke jaɗai ce zan iya shigowa?"
Fauziya da muryarta ta gana dacewa ta ce, "Shigo ni ɗaya ce."
Tana shiga ɗakin ta ɗan ƙasa fa murya ta ce, "Me yake faruwa MamAn Na'ima? Tun ɗazu nake jiyo kukanki lafita kuwa?"
Ta san Lawisa tana ƙaunarta tana ba ta kulawa, amma wannan wani gingimemen sirrin mijinta ne da ba za ta iya furta mata ba.
"Mahaifiyata na tuna Lawisa, mahaifiyata cw ta faɗo mini. Akwai abubuwa da dama da nake ganin iyaye mata suna yi wa 'ya'yansu Lawisa na rasa wannan gatan. Ban san wa zan raɓa na ji danshi da sanyin mahaifiyata."
Jikin Lawisa ya yi sanyi, da jin kalaman Fauziya. Domin ta taɓa ba ta tsakure kaɗan daga cikin labarinta, da irin baƙar wahalar da ta sha a hannun matan babanta. Sai ta yi tsammanin ko wani abin suka yi mata bayan ta je gidan, don haka ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Ba kuka za ki yi mata ba Mamam Na'ima, addu'a ya dace ki yi mata. Ki yi haƙuri watarana sai labaru."Fauziya ta gyaɗa kai sannan ta yi mata godiya Lawisa ta koma ɗakinta. Tana nan zaune kimanin sha biyu da rabi na dare Kabir ya shiga gidan, a ɗarare ya zauna ya san Fauziya sarai da zafin kishi. Duk sai ya ji haushin kansa da tun yana