Showing 3001 words to 6000 words out of 40846 words

Chapter 2 - NAUSHIN WUTA Book Complete by Ameera Adam .txt

05 Mar 2025

2772

ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce.
"Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa."
Har zai fita ta katse shi.




"Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa."




Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya ɗan yi jim ya ce.




"Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci."
Sai ya ɗan yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?"

"Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta yi wa firjin nan kuɗi, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da ake yi da shi."
Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana ɗauki, amma gaskiya ba na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu, idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a ɗaga a sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin ɗaci a ranta.




"To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki ko jari kya ja."
Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce.
"Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima."




Da yake hanyar banɗakin, da hanyar fita duka kusan hanya ɗaya ce. Da sauri Kabir ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta ɗauka tana faɗin.




"Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da wani layin na ji ya shiga."
Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa? Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin ɗauka? Gaskiya ban ji daɗi ba kada ki sake yi mini haka."
Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka.




"My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?"




Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa, yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana."




Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu."
Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..."
Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya.








07062062624
Ummou Aslam Bint Adam
[12/02, 21:42] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*




©®AMEERA ADAM




*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*




GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.




SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA BIYU




Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa yana faɗuwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar.
"Abban Na'ima wankan kenan?"
Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo ɗaya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi da gaskiya, a ɗan diririce ya ce.




"Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe ɗaurin aure ban gama mata ɗinki ba."
A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa.
"Abban Na'ima!"
Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta tsoro suke yi.




"Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?"
Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai kashe ba ya ce.
"Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya."
Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai abin da yake ɓoye mata.




"Hello!"




Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa.
"Uwar gida sarautar mata!"




Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi.




"Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaɗai."
Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya ɗauki karkarwa saboda ya yi tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba da magana.
"Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na kira yanzu na yi masa tuni."
A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri."




Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya ɗauka ya wuce banɗaki, ita kuma Fauziya ta wuce ɗaki duk sai ta ji ba ta ji daɗin abin da ta yi masa ba. Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta ji ba ta kyauta ba.




"Allah ka rage mini raɗaɗi da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane.




Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu kitchen a gidan.

Gidan da su Fauziya suke zaune, gidan haya ne mai ɗauke da ɗaukunan mata biyar. Kowacce daga mai yara biyu sai zuwa uku, kuma dukkansu ɗakunansu falle ɗai-ɗai ne sai banɗaki ƙwaya ɗaya da suke amfani da shi. Dalilin da ya sa su A'ilo suka kafa wa Fazuiya ƙahon zuƙa saboda, duk cikinsu mijinta ya fi nasu rufin asiri. Domin ta fi su yawan sauyin tukunya, don Kabir idan da 'yan kuɗi a hannunsa haka zai sayo musu nama ko kifi ko ba can mai yawa ba ta sarrafa. Kuma indai Fauziya ta yi sauyin girki duka sai ta zuba a 'yan robobi ta aika masu, saboda fita haƙƙin maƙotaka. Duk cikin gida Lawisa ce kawai ta su ta zo ɗaya, ba ta yi mata irin cin kashin da su A'ilo suke yi mata. Don haka Fauziya da Lawisa suka haɗa kai, su kuma su A'ilo suma su uku suka haɗe kansu. Da yake ita Lawisa ba ta da haƙuri, sai ya zama suna shakkarta don suna yi mata kan kara take yi musu na itace. Saɓanin Fauziya da ta kasance mace ce mai sanyi, tsananin haƙuri da kawaici. Duk abin da za su yi mata ko su yi wa yaranta, sai dai ta yi shiru idan kuma yara aka yi wa sai dai ta zaunar da su a ɗaki.
Babu damar yaranta su fita wasa tsakar gida, sai yaran su A'ilo su doke su da yake kusan duk sun girme su. Ita kuma Fauziya ƙiris suke jira ta yi wani kuskuren, ko ta taɓa kayan wani daga cikinsu sai su hau ta da faɗa. Don haka gidan suke zaune kara zube babu haɗin kai, hatta shara kowacce sai dai ta share iya ƙofar ɗakinta. Banɗaki ma kuwa sai dai kowacce idan mijinta zai yi wanka, ta ɗauki buta ta je ta wanke masa. Shara ce kawai idan ta cika suke haɗawa, idan ta cika wannan ce za ta biya idan wani karon ta sake cika sai wata ma ta bayar da kuɗi a kwashe.




Maman Sabir tun da ta fito tsakar gida take leƙen abin da Fauziya take dafawa, ana cikin haka Kabir ya fita ya sayo musu ƙwai guda huɗu. Nan take gidan ya cika da ƙamshin suyar ƙwai, baƙinciki da hassada suka ƙara cika zuciyoyin su. Bayan ta gama sai da ta gutsiri kaɗan-kaɗan ta saka a leda kowacce ta miƙa mata, sannan suka shige ɗaki ita da iyalanta suka karya. Da yake ranar Lahadi ce babu makarantar boko ya sa bayan sun gama ta yi wa yaranta wanka. Kabir ya ɗauki Fatima ya mayar da ita kemis, ya karɓo mata magunguna sannan ya wuce shagonsu na ɗinki.




Su Fatima ne suka fita tsakar gida wasa, abin ka da yaro duk kyarar da yaran su A'ilo suke yi musu da sun ga suna wasa haka za su je su shiga cikinsu. Zaman su a wurin babu wuya kenan sai Nabila ta fisge abin wasanta a hannun Na'ima ta ce, "Umma ta ce na daina wasa da ku, babanku ɗan shaye-shaye ne." Duk da ba su san me kalmar take nufi ba, amma tun da suka ji suna yawan faɗa musu cikin tsangwama sai suka ƙyamace ta, Na'ima ta ɓa ta fuska ta ce.
"Ba dai babanmu ba, sai dai babanku. Abi yana siyo mana alewa da biskit, ba ɗan shaye-shaye ba ne."




Duk cikinsu Sabir yayan Nabila ya girme su, don kusan shekararsa goma. Ya fi su wayo don haka ya ce, "Ke mu babanmu ba ya shaye-shaye, Ummanmu ta ce mu daina wasa da ku kada mu zama 'yan'iska. Wai babanku har shiga ɗakin matan aure yake yi."Yaron ya ƙarasa magana yana dariyar tsokana. Abin sai ya yi wa su Na'ima ciwo, don haka suka shiga mayar da martani abin har ya zame musu faɗa. Suna cikin kokawa su Nabila suka tararwa Na'ima da duka, da ta ji zafi ita kuma sai ta ciji Hafsa a hannu. Nan take iyayensu suka fito, dama kamar jira suke yi.




Cikin masifa Maman Sabir ta fisge Fatima tana ƙwalawa Fauziya kira, Fauziya da ke ɗaki ta yi saurin fitowa tana shirin yin magana Maman Sabir ta katse ta.




"Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, ko da wasa idan Fatima ta sake cizar mini 'ya'ya sai na ɗauki hannunta na tura musu a baki sun rama. Ƙarya aka yi uban na su ba mashayi ba ne? Na ga rannan da ya yi mankas ɗakin A'ilo ya faɗa."
Fauziya ta yi shiru ta rasa bakin magana, Lawisa ta ɗaga labule tana faɗin.
"Haba ku kuwa kamar ba ku san faɗan yara ba har za ku shiga? Wallahi indai yara ne kuna zaune za su ba ku kunya..."
A zafafe Abu ta katse ta. "Sai ki bari idan an ciji naki 'ya'yan sai ki faɗi haka, za ki fito ki yi wa mutane gwalangwaso. Don sun ce ubansu ɗan maye ne shi ne za ta cije su. Shekaran jiya waccan, ina ce butata ya ɗauka ya yi mini wurgi da ita ta fashe." Lawisa za ta sake magana Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta girgiza mata kai sannan ta ce.




"Don Allah ku yi haƙuri, In Shaa Allahu ba za su sake cizonsu ba."




Kusan lokaci ɗaya suka taɓe baki, Fauziya ta yi wa su Na'ima magana suka wuce ɗaki. Jiki a sanyaye ita ma ta wuce ɗaki, tana jin su A'ilo suna ci gaba da yadda mata magana da habaici haɗe da yin dariya.




"Mami wai mene ne shaye-shaye? Me ya sa kullum su Sabir suke ce mana Abi yana shaye-shaye?"




Tambayar Na'ima ta katse dogon tunanin da Fauziya ta faɗa. Ras! Ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta kamo hannunta fuska ɗauke da alamun tsoro ta ce.

"Kul Na'ima yara ba sa faɗan irin wannan maganar kin ji! Babu kyau kada na sake jin kun faɗi haka."




Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai, sai Hidaya ta ce. "Mami to ki faɗa wa su Hafsa su daina faɗa kada Allah Ya ƙona su a wuta."
Fazuiya ta yi murmushi ta ce, "Su ma mamansu za ta faɗa mu, sannan don Allah Hidaya ku daina zuwa cikinsu kuna wasa. Ba ga kayan wasanku nan ba, ku dinga zama a ɗaki kuna yi kun ji."
Lokaci ɗaya suka amsa mata, tana nan zaune ta ji sallamar Sadiya facalarta.
Daga wurin da take zaune ta amsa mata, Sadiya ta shiga tana faɗin.




"Uwar huɗu, wai har yanzu ba za ki kotse ba ne?"




Fauziya ta miƙa mata fulo ta ce, "Zauna uwar 'yan sa ido, ni kaina kullum jiranta nake yi."




Sai da suka gaisa Fauziya ta ce, "Ina zuwa haka da tsakar rana?"
Sadiya ta yi dogon tsaki tana kallon su Na'ima da ke wasa ta ce, "Ai tun da akwai radiyo mai jini dole na gyara zancan. Wallahi Fauziya komai ya yi mini zafi, kin san dai halin wancananka. Yau haka ya ƙare mini zagin cin mutumci, saboda kawai na ce ya biya ni kuɗaɗen da nake bin sa bashi. Ke dai shaida ce kin san ba yau ya fara zagin iyayena ba, ni ma yau na gaji na rama. Ke faɗa har sai da ya kaimu tsakara gida, shi ne fa o'o (Inna) ta shigarwa ɗanta suka yi mini zagin ƙare dangi. Abin da ya sake ɓata mini rai kwanana uku kenan ina zazzaɓi, kullum nace ya ban kuɗin magani sai ya ce mini yake ba shi da kuɗi. Amma ina duba wayarsa a chart ɗin da suke da budurwarsa, na ga ya tura mata dubu shida kuɗin ɗinki wai bikin yayarta ake yi."




Sadiya ta furzar da iska mai zafi, tana tuna ɗacin abin da mijinta ya yi mata ta cigaba.
"Kin san fa shi indai a kan 'yanmata ne duk arzikinsa a nan yake tafiya, ni kuwa ina gida ko oho wani lokacin na omon wanki ma gagarata yake yi."
Fauziya ta girgiza kai cikin damuwa ta ce, "Ke ma Sadiya tun tuni kin san halinsa, da kin sani ba ki biye masa ba kun yi ba daɗi a gaban yara ba. Ita kuwa dama kin san yaranta ba sa laifi, kwanaki fa a gabanta ya mare ki amma sai cewa ta yi ai ɓata masa rai kika yi."




Kamar Sadiya za ta yi kuka ta ce, "Idan ban biye masa ba Fauziya ya zan yi? Kina ga fa haka zai tsallake ya bar mu indai akwai tsaba babu ruwansa da kuɗin kayan mahaɗi, duk ni nake fafutukarsu. Ga shegen kule-kulen mata har da na hauka, don wallahi da kuɗin da yake kashe musu ba gara mu ya kashe mana ba."




"Eh to haka ne, lamarin ne sai haƙuri kawai. Ni dai ta nan fanin sai dai na ɗaga hannu na gode wa Allah, domin gaskiya babu macen da ta sha gaban Kb da har zai tsaya ɓa ta lokaci a kanta..."
Murmushin da Sadiya ta yi ya katse furucin Fauziya.




"Ban ga laifinki ba, da kika faɗi haka. Domin ruwan da ya dake ka shi ne ruwa. Amma ni dai a wannan gaɓar da zamantakewata da Ali, ta koma irin da zaman cin kunamar ƙadangare. Na rantse da Allah ko me aka ce mini ya yi ba zan musa ba, ki bar cin alwashin namiji saboda ko yaya basa rasa 'yanmatansu ke dai ki ga rijalu kawai."

Fauziya ta yi dariya ta ce, "A'a Sadiya, dole na bigi ƙirji wallahi ko a gaban mutanen duniya Kb ɗaya a cikin dubu, ya zamo mini tamkar zara a cikin taurari. Ni shaida ce wallahi-wallahi tun daga ranar da ya muka fara soyayya, har kawo yanzu babu macen da yake kulawa."
Sadiya ta miƙe tana gyara hijabinta ta ce, "To ni bari na zo na wuce, ko ba komai mun ɗan tattauna na rage zafin da nake ciki. Kada na daɗe uwar masu gida ta fahimci na fita, na ƙara wani laifin."
Har soro Fauziya ta raka ta, Sadiya ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Wai mutanen gidanku har yanzu zaman naku sai a hankali ne? Na ga da na yi sallama A'ilo ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login